Showing 249001 words to 252000 words out of 419207 words

Chapter 84 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1456

a hannun shi ina tsaye na jingina jikina da kujera.
Saida ya gama shigo da komai gidan ya tsaya yin waya daki na shige abina na barshi gurin ban fito ba sai safe na samu yaci abincin dana tuka na semo da mukaci da su anty farida wanda na raga zanci da dare na kasa ci.
Gyaran gurin na shiga yi har zuwa gidan na hada muna abin karyawa don satin ukun da yayi baya kasan naji dadi kasancewa ni kadai sosai.
Bayan na gama na shiga nayi wanka ina zauna na saka kaya ina dan kara gyara fuskana duk da ba wani yin kwaliya na damu dashi ba dama.
Ya shigo dakin ya samay ni ina rufe powder dana shafa a fuskana kallo daya zakai mai ka gane dan fadawan dayayi wanan lokaci.
Ga ba walwala a fuskanshi ko kadan tun shigowan shi na kula da hakan gare shi.
Ganin shi nayi saurin tashi tsaye ya nuna min indana tashi yana fadin komaki zauna magana nazo muyi dake ai.
Ban iya boye mamakina ba nakai zaune sai naga yakai zaune bakin gadona tare da hade hannayen ya tokare haban shi dashi yace.
Zarah may ye damuwan ki danazo na samu kina kuka ya tambayeni cikin kara tsureni da idanuwan shi.
Ban iya bashi amsa ba kaina kuma yana kasa na kasa dagowa in kalleshi ganin ba zan amsa shi ba ya sake fadin tambayan ki nake zarah ?
Na dago kai ina kallon shi nace ba komai yaya idona suna tara hawaye ko ina tauye maki hakkin kine zarah ki fada min ?
Jin hakan dayace yasa na dago idanu nadan kallo shi sai na kara dukar da kaina kasa.
Gani nayi yanauin fuskan shi ya sauya min sosai da alama yana son jin abindake damuna din lokacin.
Kiyi hakkuru zarah nasan ina danne maki hakkin ki nima hakan ba da son raina bane hakan ke faruwa a kanmu.
Wani mamakin ne ya kamani a karo nabiyu na sake dago kai ina kallon shi .
Hawaye suka soma zubo min naji yana fadin na tambaye ki maynene matalan ki zaki fara min kuka.
Jikin shi ya danyi sanyi ya dago a hankali ya mike tsaye tare da takowa zuwa inda nake naga ya miko hannayen shi yana kokarin mikar dani tsaye daga zaunen da nake.
Bayan ya mikar dani ya dago fuskana yana son mu fuskanci juna dashi da sauri nace yaya ni banda matsalan komai in ma ina dashi ai kasani.
Murmushi naji yayi ya dan rungumoni zuwa jikin shi kokarin kwace kaina nayi ina fadin amma kasan hakan bai dace ba a tsakani mu yaya.
Yace cikin mamaki kina a matsayin matata kike furta hakan gareni zarah ido na dago ina kallon shi jikina na rawa nace.
Na rokeka yaya ka barni inyi rayuwata a yadda nake kai mana adalci dani dakai tunda kasan a matsayin da auren mu yake .
Yace ban san komai ba ga auren mu sai kin fada min yanzu zan sani yana kallona cikin son jin bayani a bakina.
Amma kasan hjyn ku abinda ta furta akan mu ko ka manta ne yanzu ya girgiza kai ya sake ni tare da juya bayan shi yace.
Wanan kuma abinda ya shafeni ne nida zuciyata ba wani ba don nike auren ki ba hajiyata ba.
Amma ai tana iko a kanka ko don uwa ba wasa bace ya juyo ya fuskance ni yana fadin idan muna magana kada ki kara jefo zancen iyayyen mu ciki don ina so mutum mai daraja iyayye.
Naka ka sani don banga kana daraja nawa uwar ba don tsaban darajan da bata dashi a gare ku kowan ku kaf yan dakin ku maimuna kuke kiranta dashi babu darajawa.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:23 - ??5惙5惙5?: ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAH YAN UWA ALLAH YA BAMU WUNI MAI ALBARKA AMIN.

Littafina na kudine don darajan Allah da Annabinsa yar uwa kada ki karanta idan baki biya ba kibar shedaniya da nauyin ta wace ta fitar abokan halaka take nema daga cikin ku kada ki bari ta ribbance ki don karatu novel kiji tsoron Allah don akwai ranan tsayuwa gaban ubangiji.
Kai da yan uwan ka kuna muna daukan marasa daraja da gata a idon ku kun dauke mu tankar yan cin rani a gidan ku.
Duk kokarin da mahaifiyata take da kakan ku da mahaifin ku haka baisa tayi daraja a idon kowa a gidan ku .
A gaban kowa mahaifiyar ku tayi ikirarin bazan taba zama cikim ahalin ta ba muddin tana raye a duniyan nan.
Yanzu mai zaisa kake kokarin canza shawaran ka a kaina yaya kana son nuna min kana tausayin mu ne ko lalata min rayuwa kake son yi in sake jiki dakai ka jefani wani maraicin karo na biyu bayan na mahaifina dake cina a kullun a zuciyata.
Na dago ido na kalle shi tare da hade hannayena a guri daya alaman ina rokon shi hawaye na zobo min a idanuwa kamar an bude famfo.
Nace yaya ka barni inyi rayuwa a yadda yazo min ka bari ko da sau dayane ka kuyi muna adalci ta hanyan karatun da ka sakani don Allah.
Murmushin kunan zuciya da bacin rai naga ya sake a fuskan shi ya tsaya yana kallona har nakai ayah kafin ya furzo da iska daga bakin shi ya furta.
Naki tunanen ke nan zarah a zaton ki yan dakin mu basu son mahaifiyar ki a yanzu don tana kishi da tamu mahaifiyar komay ?
Kada ki manta mu mazane ba zamu saka kanmu a cikin zancen mata ba ba zamu fito fili mu nuna ga ra,ayin mu ba.
Amma mu maitai muna da zamu kita matar da itama tankar jinin mu take mun taso a tare mun ganta a cikin gidan mu tayi rayuwa damu akan dan wani dalili sai mukita ?
Idan kina tunanen hakan kinyi kuskure a rayuwan ki zarah ke yarinyace har yanzu shiyasa kike fadan wanan maganan haka.
Nidai nasan anbani auren ki na ruguma da hannu biyu a cikin mutunci tare da mutunta darajan aure na ga idon kowa.
Aure yaya aure fa kace auren da akayi shi a bisa kaddara da sabanin hankali auren da babu soyayya a cikin sa aiba aure bane.
Dan dariyan yake yayi a fuskan shi tare da fadin ai lokaci ne zai baiyanar da komai zarah.
Kada ki daukeni ban san abinda nakeyi ba, komai dake faruwa ina sane dashi ina kuma nawa tsarin akan shi don haka ki fito muci abinci yanzu ina dining ina jiran ki.
Yana fadin haka bai tsaya ba ya fice daga dakin bai ko karasa fita ba na sake wani kuka gami da ihu ina fadin wayyo ni Abbana ka tafi ka barni rayuwa tana min zafi.
Dan girgiza kanshi yayi daga inda yake zuciyar shi na mashi kuna da kala maina masu cin rai da wanan kokekoken banzan da na tsiri mashi a gida yana tayar mai da hankali.
Tsananin sanyin da ake a kasa ya hana kowa walwala a wanan lokacin don hakane ko tafiya yanzu ba ko wani lokaci akeyin sa ba a kasan jerabawa muke a wahalce domin hutu zamu koma kuma wanan zangon baida yawa kamar na baya.
Tun dana dawo gidan nasan yana ciki don ba inda yake fita yanzu tun lokacin da sanyin ya tsananta sosai motar shi ma dake waje ta rufe da kankara lif jikinta.
Don hakane tun dawowan shi yake min zaune gida kusan kwana biyar bai fita zuwa ko ina ba tunda ya dawo sai na dauka ko don matar shi bata garin ne.
Duk da daga gaisuwa ba abinda ke hadamu a gidan hakan bai hana shi fita da yamma zuwa wani resturan zai dawo da snack iri iri ya tursa ni a gaba sai naci ko da kuwa banson ci don ban isa in mashi gardama ba.
Soboda ya dasa mun tsoron shi a raina tun farko ina shakkun shi sosai a raina da girmama shi.
Yau kan garin ba dama saboda sanyi daya dami mutane ga har wani iska da kankara ke sauka yana batun rufe mutum da ran shi idan dai kana a sarari.
Kamar an koroni na banko kofan na fado gidan hankali tashe banyi zaton ma yana gidan ba a zatona yana can gidan shine.
Ganin shi nayi tsaye ya kunna wa tsakiyan falin wutan fire wood a dan wani guri da ban dauka da farko wurin amfani bane gurin sai ranan da naga ya fara kunna wuta irin wanan lokacin.
Yana tsaye ya ba kofan baya hannayen shi suna mike a gurin wutan kamar yana gasa su sai rigan suwaita irin na saka mai v neck brown a jikin shi da dogon wando fari kafan shi socks ne kawai a saye lokacin.
Do muna girmama gidan mu kamar na sauran musulmai don ba ko ina muke takawa ba a gidan da takalma sai dan kereriyan inda muke bi mu fita idan mun sauko daga sama.
Dan juyowa yayi kadan ya kalleni jin yadda na banko kofan falon lokacin kamar wani na bina a baya.
Easy yace ba tare da ya juyo ya kalleni ba na samu kaina da dan tsayewa ina kallon shi har lokacin bai juyo ba cikin kasaita yace min .
Yaya akayi baki saka rigan kwarai ba a sama kin kuma san irin sanyin da akeyi kallon kayan jikina nayi da sauri naga doguwar jallabiyace a jikina nayi rolling din kaina har mazaunana da gyalen rigan .
Duk da ina son in tsaya in sha dumi a wajen don sanyin dana kwaso ban samu yin hakan ba don har lokacin yana tsaye ba tare da ya juyo ba gurun wutan kamar mai gasa jikin shi.
Dakina fada da sauri na kuna heater dakin gado na fada ina maida numfashi Allah ya taimakeni ina fashin sallah a ranan don haka banda damuwa.
Sai dana dan huta hakana a kwance ba barci nakeyi ba can na bude idanuwa na wani leda babba na hango har guda biyu aje daga gefen gadona.
Tashi nayi da sauri ina kallon ledan cikin mamaki da sauri na karasa wurin ledan na shiga budewa da sauri.
Irin kayan da na gani a cikin ledan sun ban mamaki sosai har kala shida yadin mai kamar atamfa amma sai taushi dinkin su gwanin ban sha,awa sosai.
Da sauri na bude dayan hijjabai na fara fitarwa sai plat shoe daida kafana shima da yan jakkuna masu kyau sosai abin yayi matukan ban mamaki.
Wai yau yaya ne da sayo min tsaraba ko may don ban san abindama zanyi tunane a kansa ba.
Zaunawa nayi gaban kayan ina tunanen yadda zan mashi godiya wata zuciya tace min share shi kawai ai aikinsa ne hakan.
No ba dadi ai maka alheri kaki yabawa ba haka addini da iyayyen mu suka koya muna ba na fadi a fili.
Wanka nayi don on din da nake ciki nasaka wando da riga a jikina sai rigan sanyin dana dora saman rigan bai dai rufe min mazaunana ba ban damu da hakan ba tunda na saba zama a gida hakan cikin irin shigan.
Na sauko kasa na nufo falon wanan karon zaune yake ya bude laptop yana aiki a cikin sa a hankali na tako zuwa inda yake sai dana zauna dan nesa kadan dashi nace.
Ya naga kaya na gode Allah ya kara budi da sauri ya dago kai ya dan kalleni kamar wanda zaiyi magana sai kuma ya fasa yaci gaba da aikin shi cikin gyada min kai.
Mikewa nayi zan shiga kitchen sai lokacin yai magana tunda na sauko yace kada kiyi wahalan dafa abinci na sayo muna abinda zamuci.
Dan juyowa nayi ina mamaki sai na fasa shiga kitchen din lokacin falon na dawo na zauna na dauki remote na kunna tv tare da rage karan shi don kada in damay shi.
An dauki tsawon lokaci naji yace daddy ya bugo waya dazun suna gaida ke da sauri na dago kaina na kalleshi don jin ya ambaci sunan kawuna.
Ya jikinsa nace dashi yace da sauki a yadda naji muryan shi ya samu sauki sosai.
Shiru nayi ina tunane kafin na mike na shiga kitchen na hado tea mai zafi na dawo falo ina kallo ina shan abina hankali kwance.
Zamuyi hutu zango ina son zuwa gida in dubasu na fada a cikin rashin damuwa da abinda nace.
Ba yanzu ba ya bani amsa ba tare da ya dago kaiba sai yaushe yaya na fada a dan shagwabe don nasan tunda ya fada gaskiya ya fada har cikin ranshi.
Sai kin tara masu tsaraba mai yawa zan kaiki yanzu hannu sake zaki tafi masu ai kawun ki ba zaiji dadin ganin ki hannu sake babu komai ba.
May nake dashi da zan tara tsaraban da zai tsone masu ido yadda kake fadi haka ni abinda ke gareni zan kai masu bana karya.
Ai ba ina nufin ki masu karya ba don haka abinda ke gidan sarki akwai shi gidan bafade saidai kyawo da inganci ya banbanta su amma amfanin su dayane duka.
Kaina ya daure sosai don tunda ya fara harde maganan shi ban fahince shi sosai ba bansan inda zancen shi ya dosa ba.
Diban lokaci naga yayi sai ya mike da sauri yana fadin maza sallah don har lokaci yaso ya kure ba tare da ya tsaya duba ko na tashi ba ya wuce.
Niko nasan ban sallah na zauna abina kafin can in tashi zuwa kitchen na duba abinda ya sayo muna din.
Abincin kwali ne wanda zai iya daukan kwanaki bai baci muna ci idan munyi worming dinshi a ovon.
Tsada kega wanan tarkacen saidai babu dadi ko kadan kodon ba cimarmu bane bamu san dadin shi ba oho.
Da zafin shi don abinda yake ci har lokacun yana da sauran dumin shi sai idan yayi sanyi zaka iya dumamawa kaci.
Ina zaune na tasa kwali daya a gaba ina yagan kazar ciki hankali kwance ga dai hadi yaji na komai amma baiji maggi irin namu ba ??J0
Har na kusa gamawa sai gashi ya fito bai zauna ba ya dauki remote ya canza chenal din tv zuwana labarai.
Zama yayi naci gaba da cin abincina hankali kwance na gama na dauki tisue ina goge hannu kafi in mayar da hankalina kan tv ina kallon yadda suke nuna aibun da kankara keyi a kasan ko ina.
Ganin banda niyar bashi abinci yace ba za a bani abincin bani nakallo shi da sauri irin yadda ya tsareni da ido yasa na dukar dakaina da sauri na mike zuwa kitchen din.
Saidana dan tsaya na hada komai na dauko zuwa falon nakai mai saman dining na aje mai na juyo naga irin kallo da yake min a lokacin.
Sai naji wani iri a raina don ba irin kallon daya saba mi ya kawar da kanshi bane yake min.
A hankali na tako zuwa kujera na zauna sai lokacin naji ya sauke ajiyan zuciya yamike zuwa dining din.
Kallon jikina nayi ko yaga wani abin ne a jikina naga babu komai ina nan tsab a yadda na fito raina ya baci don ban san abinda yasa yake min wanan kallon ba haka.
Karshe ma mikewa nayi na barshi gurin a zaune falon na shige ciki ban ko kara juyowa ba dama sanyi akeyi.
Saida na kara dauraye jikina na kimtsa dana fito na saka rigan barcina tare da dan kara gudun karfin abin dumama dakin.
Nahaye gado na kudundumay a wuri daya har barci ya daukeni ina tunane a dakin ni daya.
Cikin dare ina barcina hankali kwance na tashi a gigice saboda bakon yanayin da nake ji yana sauka a jikina.
Na bude ido da sauri naga har lokacin fitilun dakin a kashe suke sai numfashin da nakeji a gefena cikin wani irin yanayi na daban da ban saba ji ba.
Innalillahi na furta firgice a fili ina shirin kwarma ihu naji an rikeni yana fadin easy baby easy nine fa zarah.
Irin rikon da yai mun yasa har lokacin jikina bai daina rawa ba sai tsuma nakeyi.
Da kyat na samu na kwaci kaina na koma gefe na mike a furgice saidai ban sauka a gadon ba sai mazurai nakeyi tsorona a fili.
Komawa yayi gefe naga ya kunna dim light din dakin ya dan dauki haske ta yadda zan iya ganin sa ko ya ganni da kyau.
Cikin rawan murya nace yaya may kakeyi a nan kuma ko kayi batan dakine kana barci ?
Nama rasa kalan tambayan da nake masa a lokacin na san dai karshe na hada hannayena guri daya alaman roko ina fadin.
Yaya may yasa zakai min hakan kana son ka lalata min rayuwa ne kamar yadda kukai guri yin hakan tun farko.
Yana kishin gide saman gadon yayi makari da hannun shi saman filo ya zuba min ido yana kallon yadda nake zuba a firgice.

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login