Showing 150001 words to 153000 words out of 419207 words

Chapter 51 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1478

da masu dan bujen nan.
Ban san da su a falon ba dawowa na ke nan daga unguwa nida su Aisha ina saye da les dinkin buje da riga yau anyi sa,a na saka mayafi a jikina .
Sai kitson da ke kaina daya dan fito don daurin dan kwalin danayi sai kamshin da jikina ke fitarwa don daga wurin bukin kawar Aisha muke don tare suka kare karatun su dasu salma akai mata aure.
Yana hangoni yaji gaban shi yayi mumunan faduwa saboda saboda shigata ra yau ya fitar min da surana na asali a fili.
A hankali ya lumshe ido daga inda yake zaune merry ko tana ganin mu ta shiga washe baki gare mu tana fara,a tace dama tana tunanen ta tambaye mu kada ta tafi bamu gana ba.
Kallon inda yake sukayi suna fadin yaya ina wuni kunzo lafiya ?
Ya amsa ba tare daya dago kai ba da lafiya nikan wurin Amma na nufa ina fadin Amma yau duk na gaji wallahi a cikin muryan da ban san inayi ba wanda mai saurare zan dauka shagwane.
Merry ta tace in zo kusa da ita tana son muyi sallama gobe zata koma kasar england maiyuyuwa ba zata dawo kasan nan maza ba idan ta haihu.
Jin haka na yasa Aisha ta ce ba zaki tsaya ki haihu a nan ba mu dauki baby tayi murmushi tace gaskiya ba zata iya zama nan kasa ta haihu ba .
Ban san ya akayi bakina ya furta amma uban babyn naki ai a nan aka haife shi kuma kema ai yar kasan nan ce.
Ba tasan may nake fadi ba sai kallona ina magana tayi tana fadin nayi fushi da kika zo gun grany kika nufa bayan kin gani a falon.
Dan rage murya nayi ina fadin ban kula ku bane a falon sai yanzu.
Idanuwan shi da suka sani saurin dukar dakaina ya dago ya watso min na jin nace ban farga sune a falin ba.
Nayi saurin dukar da kaina kasa tare da juya gurin Amma ina fadin Amma yunwa nake ji wallahi.
Ke yar nan yanzu kika dawo gidan buki zaki kira min yunwa a nan yanzun kuma?
Amma kin san Fatima kamar tsoron mutane take yi taki sake jiki taci komai da aka bamu a gurin .
Shine filancin ta nuna maku asalinta na kwarai ne ai macen kwarai bata zubar da mutuncin ta a duk inda take.
Amma mu zamu tafi sai kuma idan Allah ya kara sadamu da alheri don jirgin mu da safe zai bar kano zuwa lagos insha Allahu.
Yaya tafiya zakuyi ne da gaske Aisha ta tambaya bai bata amsa ba sai mikewan da yayi tsaye daga zaune.
Amma tace miskilin zai koma inda yafi wayau nan kunsan cizon shi akeyi komai tsiyan ka dai daga kauye kakani ka suke.
Ya dan murmusa yana fadin gara sai da kika tsaya akan kakanina da sai ince wani uban nawa kika gani ba kauye ?
Nikan dadi naji har cikin raina sosai jin zasu bar kasan gaba daya ina Allah yasa ma kun tafi ke nan namamajon kawai.
Jin kamshin shi kusa dani yasa na dago kaina shine kuwa ya matso kusa da Amma yana mika mata kudi tare da fadin ga wanan kiyi hakkuri sai idan na yo maki sako kuma.
Ya dan lakuci kumatun ta yana fadin Amma ki kula muna da kanki kin san muna ji dake sosai daga haka ya juya ya fara tafiya merry ma ta mike tana fadin zasu tafi tana kallon Amma din.
Hannu amma ta daga mata tana mata na bebaye alaman a sauka lafiya.
Wanan tafiyan nasu ni ji nayi kamar an min albushir da aljanna don ina ganin ya samu ya kurce masu ke nan ba zai dawo ba kuma nan maza.
Don ko hjy maryam sai daga baya take jin wai sun tafi basuyi sallama dasu ba dan gara ma mamu don shigan merry ta san zasu koma amma batai tsanmanin zai tafi bai sallame su ba ai.
Bata dauki wanan komai ba a gurin ta don ba bakon abu bane haka a wurin ta sai bayan sun tafi ne sai ga Aliyu da sako a boye ya kawo masu yana mai basu hakkurin rashin yin sallama dasu da bai sami daman yi ba.
Hjy maryam.tace ita kan ko ba sallaman baki ai ya gama mata komai ko Allah dai ya kaisu lafiya dashi da arniyar shi.
Sai dai mamu bata ji dadin hakan ba don taso suyi magana dashi a kan merry sai gashi kawai tafiyan shi taji daga sama babu sallama .


Ayi manege yau ban samu natsuwan typing ba yan uwa sai kun jini kuma zuwa gobe insha Allahu.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:09 - ??5惙5惙5?: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHEEM YA FATTAHU YA SALAM, , ,


Sun isa lafiya inda ya samu abokan arzikin shi suna kewan shi sunyi missing din shi sosai musanman a gurin aikin shi mutane da yawa sunyi missing din shi gurin.
Tunda suka kaishi gida suka dire ya shige sallah ya gabatar da ake binshi yana gamawa yadan ci abinci don shigan dare sukayi .
Ya kwanta bai fito daga dakin ba saida hayaniyan su merry da akazo yiwa adduan kore mata evils sprit din da ta kwaso a Nigeria ita da baby ta da maigidan.
Pastor mahaifinta ya dauko masu dungurun gun don yin addua gare su don ma a ciki dare suka sauka da abin yafi nan don da church za a kaita ai mata wanan adduan.
Saukowa yayi yana saye da wando three quarter a jikin shi sai riga fara daya saka a jikin shidon shan iska.
Tunda yake saukowa yake kallon merry da take tsugun ne ta rufe ido hannaye ta na sama alaman roko take yi kenan.
Pastor da mahaifin merry sukai mai alama da yazo gurin adduan shi ma ya kalle su da mamaki ya kara tsare gida a fuskan shi don haka yake masu idan zasu tursasa shi yin wani abu na addinin su .
Pastor din yace ya kamata kaima kazo a kore maka evils din da suka biyo ku a tafiyan ku yace cikin kada kai banda matsala ni yana tafiya yake fadin hakan ys nufi hanyan fita daga wajen gidan wurin wani dan shan iska na gidan ya tsaya yana karewa dogayen gine gine garin kallo daga inda yake ya sauke ajiyan zuciya a hankali.
Dafa dan karfen dake gaban shi yayi yana lumshe idon shi a hankali babu abinda ke zuciyar shi sai tunanen abubuwan da suka faru zuwan shi nigeria suke dawo mai a rai.
Ya sauke ajiyan zuciya yana kara lumshe ido tare da dan damke karfe da karfi yana hadiyan zuciya.
Daidai lokacin mahafin merry ya fito yana bin kusurwan gidan yana wasu sambatu irin nasu na kiristoci da sukeyi wai ana koran shedanu a gidan .
Bai kula shi ba don idan da sabo ya saba amma shi ko a jikin shi duk wana abubuwan da sukayi yakan nuna takar bai san dunayi ba.
Inda har yakan basu mamaki irin taurin kan shi akan riko da addinin shi don basu san zai iya riko haka da addinin shi ba sai zuwan nan da sukayi nigeria ne merry ta tabbatar da idan tushen rikon addinin shi duk yan gidan su tana ganin kamar malamai ne don irin shigar su da suke .
Ita babu abinda ke bata mamaki kamar yadda har da kananun yara suke saka zunbulelen hijab da nikaf a fuskan shi tunda wanan yar ta step mum din don tun a waya ta labarta wa iyayyen ta wanan akidan na yan gidan.
Muryan maman merry ne ta zo inda yake tana fadin my inlaw ya hanya ya mutanen ka can ya dan lumshe ido cikin rasgin son nagana yace suna lafiya ta sake fadin .
Munzo kana kwance tu safe don yiwa merry addua ta samu kariya daga evils ayes ta haihu lafiya ita da baby ta su samu kariya.
Yana da kyau ya bata amsa da fadan hakan yana juyawa don barin gurin matar tana kokarin ganin ta jawo shi a jiki kamar yadda suke da dan cikin su.
Wanda daga hakan zasu yi amfani da daman wurin samun jawo ra,ayin shi gare shi na addinin su sai dai kuma yaron tauri ne dashi da rashin sabo sam baida yarda da kowa ko sakin jiki wanan halin yana matukar damun su a rai.
Tsoron su shine kada watarana yaja ra,ayin yarsu tace zata juye ta koma tasa a kidar wanda wanan babban kalubali ne gare su don su din suna da wani mataki a cikin church din su na shugabanci.
Haka zai zama abin kunya sosai a wurin su shine dalilin su na kin yin fushi da halayan yaron garesu na rashin yarda da amincewa dasu da baiyi ko wani lokaci.

NIGERIA
Tafiyan ya umar da sati aiyukan yan uwan uwanshi ya fito yana daya daga cikin wanda sukai hanya aka samu aikin don mahaifin su yayi iya kokarin shi a samun aikin abu ya faskara .
Gashi bai son zancen komawan su waje yanzu koshi umar din akwai dalilan da yasa ya barshi ya koma din don ya koma ya karasa.
Habbib yafi kowa korafin wanan tsayar dasu da akayi din wanda ba haka yaso ba yaso ya koma kamar yanda yayan nasu ya koma can.
Kawune ya fadawa sauran mutanen gidan inda suka dinga layi zuwa yin murna wa hjy jummai yar mulkin tana amsawa da kyat don bata so haka ba ita a nata ganin ai sirin su ne hakan ba dole sai kowa yasan da maganan ba a saka masu baki.
Itako abinda bata so ke nan kowa ya kama fada ana nanata magana ta dauki hakan da yawan saka ido ga mutum.
Wata rana kuma sai gashi umar ya bugo waya yana sheda masu haihuwan merry din wace ta haifi diya mace wai har anyi sati uku a lokacin da ya bugo wayan yace ya radawa diya sunan mahaifiyar su Aminatu.
Gida sunyi mamaki kwarai da jin hakan kowa na tofa albarkacin bakin sa ga irin halin umar din wanda shi bai damu ya fadawa yan uwa wani abin shi ba idan ba yaso hakan ba sai dai daga baya suji.
Hjy su tayi fada sosai kan rashin fada mata da baiyi ba da wuri lokacin da aka haihu din yace mama ni dai a nawa bangaren nayi wa yarinya huduba da sauran abin da ya dace ayiwa yaro ida????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? n an haife shi.
Amma ta bangaren merry ita har yanzu basuyi nasu bukin sunan ba tukun tace yau ga hauka ?
Kace sati uku da haihuwa zakace basuyi bukin suna ba har yanzu yace eh mama ga nasu al,adan ai yarinya zata iya kaiwa har wajen shekara ba ai bukin suna ba sai idan an shirya akeyi.
Tsuki hjy taja tare da fadin wanan bakin kwashe kwashen naka babawa mukan bai karamu da komai ba sai dadin ta kaici ni a ina na taba jin wanan shirmay haka ?.
Yace haka sukeyi ga al,adan yahudawa da suke koyo yasa na barta da akidar su hakana idan sun tashi sai suyi sai hjy tace sai dai kuyi ku tafi church ke nan har kai ana faman raye raye ko a can ?
Shi dai yai dariya kawai ba tare da ya furta komai ba sai ta kara fadin to kaga kamar yadda nace ma idan ta haihu zamuyi namu hidima a nan ya zama dole yanzu ka aiko da wasu kudi ayi don wancen da ka bayar nayi amfani dasu bayan wucewar ku.
Yace ai da kawai ku bari tunda ba mai jegon ma nan itama batai komai ba aiko kamar jiran take ta fadi hakan ta haushi da sababi sai daya koma bata hakkuri da baki tare da alkawarin zai aiko mata da kudin kamar yadda ta bukata.
Sai take fadin saura naji wanan zancen bakin mahaifin ku don yanzu na kula ko wanka kayi baka bushewa sai ka fada mashi ya sani.
Dariya yayi yana fadin kai haba mama ni di kuma kike wa wanan shedan haka ya dai samu har uwan ta sauka daga fushin data dauka dashi da farko.
Daga shi sai Aliyu suka iya bi da ita a cikin yayan ta idan ka ganshi miskili zaka dauka ta ko ina baida dadin sha,ani.
Sai dai abin ba haka ba don fanin mahaifiyar shi yana kokarin kare mata hakkinta sosai yana gudun bacin ran mahaifan sa fiye da komai a duniya.
Ba laifi hjy ta dan shirya dan kwarya kwaryan walima a gidan wai matar danta ta haihu yan uwa da kawayen ta aka taru a gidan tun safe ana shagalin suna.
Bata gaiyaci kowa na fannin kawu ba har matanshi sai dai hakan bai hana hjy maryam shiga cikin tsabgan ba don ganin kwam.
Mamu kan ficewa tayi abinta unguwa bata tsaya ganin takaici ba gidan sai data daidaici lokacin dawowan mu school yayi ta dawo gidan saboda yara.
Ni kan ban san da zancen ba mun dai dawo na samu gidan dankare da manyar motoci tun daga wajen gidan dole haka muka raba muka shiga ganin part din mu a rufe yasa naja kanne ba muka nufi gurin Amma.
Tafe nake amma tunane ya addabeni a rai na may ke faruwa a part din hjy yau naga ana ta shagali haka ?
Da sallama muka shiga na zube saman kujera ina cire safan kafana dana kanne na Amma ta fito daga daki jin motsin mu.
Tana fadin har kun dawo ashe agogon falon ta na daga kai na duba nace Amma yanzu kusan hudu fa don munyi jiran mamu bata zo daukan mu dole motar haya muka biyo.
Tace nima bansan ina taje ba tun dazun nasan dai fitan ta bai rasa nasaba da wanan taro da taga anyi yau gidan nan.
Da sauri nace wai Amma taron may akeyi ne haka a gidan nan yau naga motoci har wajen gida ga mata zaune gungu gungu a wajen gidan.
Sai da ta tabe baki kafin tace wai yau suna ake muna a gidan haka tana fadi tana juyawa da kai da gani abin bai gamshe ta ba.
Da sauri nace suna Amma wa ya haihu kuma tace wai matar dan uwan ku kafiran nan mana matar saudaki.
Kallon mamaki nayi mata ina fadin tau a gidan nan ake bukin ko suna kasan nan ne ?
Tace ina fa daukarwa kaine kawai irin na jummai data iya abin kwarai batayi sai abin banza.
Kai Amma ba danta take tayawa murnan samun karuwa ba taja wani irun tsuki tare da fadin Allah kadai yasan irin riban data samu aurin wanan bukin.
An fada maki jummai tana abu don Allah ne ita barta nan inda kika ganta da halin ta sai kurum kawai.
Abinci na tashi na dibanwa kanne ba tare da basu ruwa sun zauna suna ci ne mamu ta dawo part din Amma ta nufo don ta diba idan mun dawo.
Bayan ta ganmu ne sun gaisa da Amma sai Amma take tambayan ta ina ta fito sai data kai zaune take fadin ina gidan kawu cewa mahaifin ta don haka take ce mai kamar yadda yayan Amma ke kiranshi.
Gwaggo yau gidan bai zaunuwa ne yasa na dan fita zuwa gaida shi dama na kwana biyu banje can din ba.
Sai dai idan kina da jiyar fita dama kan wanan shirmay da ake zaisa ki bar gida nan don kawai guje masu.
Nikan mikewa nayi na shige dakin Amma don akwai kayana a nan wanka nayi na dauki bakar riga na saka tare da dauko wani dan gyale daura a kaina na fito na samu har mamu ta tafi part din ta.
Wani flat takalmana dake nan kofan Amma na saka ina fadin Amma zanje inwa su fauziya wanka in dawo tace kada ki dade ki dawo nace tau Amma.
Kidane yau yake tashi a gidan ga mata nan gungu gungu zaune saman fararen kujeru da akayo hayan su sai dai duk cikin taro banga yan bangaren kawu ba.
Wasu yan mata ne naga sun zubo mi ido har na kawo kusa dasu naji daya na fadin ai wanan ce yarinyar dama ?
Ashe ma ba wata babba ce haka dama gaskiya dai wanan sai dai in an kwan biyu kan auren su ni dai yi nayi kamar banji su ba sai daya tace uwar ta fa ta cusawa daddy su ra,ayin ta amma wanan ina zai kaita shida yake dan gayu yadda ya waye din nan.
Allah ya sauwake ai hanyar jirgi saban data mota sai suka kwashe da dariya dayan ta kare da fadin a to kwarya tabi kwarya dan uwanta badai a cikin dangin mu ba don su mama sunce ba zai taba yuyuwa ba wanan zancen.
Dan murmushi na sake a fuskana nace a raina kuna da gaskiyan ku komai akai muna baku da laifi don dole yanzu na zama mujiya a idon jama,a ke nan .
Ban kula da wata mace dake zuwa ba sai ji nayi na buge da mutum na dawo

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login