Showing 231001 words to 234000 words out of 419207 words

Chapter 78 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1419

baki har ya sauka kasa ya taba mai tufafi da takallaman shi.
What noses is this zara ya fada cikin daga murya a fusace saidai yana arba da hanlin da nale ciki hankalin shi ya kara tashi sosai.
Don yunkurin fitar da wani aman nakeyi a baki saidai kasancewan cikin nawa babu komai yasa nake wahala komai yaki fitowa a lokacin.
Gashi ina son mikewa daga yadda nake inje toilet na kasa yunkurawa hakan jikina yana kara sakewa a lokaci daya.
Da taimakon shi na samu na mike tsaye da kyau ina fada da kyat zan iya zuwa da kaina yaya.
Yace ki bari na karasa dake koda kofane duk a rude yake magana lokacin ganin yadda jikina yake sakewa gaba daya.
BakinToilet din ya kaini ya tsayar dani tare dan jigina jikina ga bango ya shiga ya hada min ruwa masu zafi ya fito yace in shiga,
Saida yaga ina kokarin tube kayan jikina ya dauka a gabansa zan iya kwabe komai baisan ban karkare fita hayacina ba.
Naga yayi saurin fita tare da dan rufo kofan ya tsaya a tsakar dakin yana karewa gurin dana bata kallo.
Cikin daurewa ya sauka kasa zuciyar shi yana jin ba dadi ko kadan abin goge wuri yake nema da kyat yaga inda nake ajewa ya dauko kafin in fito ya gyara gurin har ya shimfida wani zanin gadon saman gadon.
Duk da halin da nake ciki bai hanani jin mamakin ganin ko ina na dakin a gyare ba lokaci daya.
Na samu baya dakin lokacin haka yasa nayi karfin halin saka tufafi a jikina a daidai lokacin daya shigo da room fresh a hannun shi yana feasawa a dakin ni kuma na tayar da sallah cikin karfin hali na gabar da sallolin dake kaina.
Wayan shi dake saman side drower din dakina yayi kara ya dauka a hasale merry ke fadin kaidawa ke magana Omar ka fita batuna.
Waima da wata yar iskan kake tarene in ji yace mind you tongue meery kanwata Fatima ce bata da lafiya nake bata kulawa.
Kashe wayan tayi ba tare data furta komai ba ashe a lokacin tana can ta haukacewa iyayyen ta da suke tare don bata shigo ba sai new year don sunfi ba bukin new year muhinmanci sosai.
Jin ta kashe wayan yaja tsuki tare da kallon inda nake yace idan kin idar ki tashi muje asibiti a dubaki.
Na shafa adduan da nake na dan juyo gare shi ina fadin murya ciki ciki naji sauki yaya ba sai munje asibiti ba.
Yace a hasale common ki tashi muje tun dare bai muna ba don Allah yana mikewa nima yunkuri mikewa nayi lokaci guda na kasa yace in kamaki ne idan ba zaki iyaba ?
Zan iya nace dashi cikin daurewa nake magana na samu na mike da kyat yana tsaye yana kallona har na daura karamin hijjab dina sama na kalle shi .
Naga ni din yake kallo shima don haka na nufi hanyar fita daga dakin ya mara min baya muka fice daga dakin.
Wurin saukama daga stairs din sai dayayi yana jirana har na sauka a hankali muka fito daga gidan yaja gidan ya rufe ganin ban sauri ya sukuce ni zuwa wurin mota ya saka ya juyo da sauri ya shiga yana ganin kamar wani abu zai samay ni ne a sanadin shi.
Mun isa asubitin kadan kadan yake juyowa ya kalle ni har muka kai asibitin nan ma bai bari nayi tafiya ba don dauka na yayi tun ina jin nauyin dauka da yake min har na gaji na daure da hakan.
Munga likita ya rubuta magani da kwantar dani don ina bukatan hutu da ruwa likitan yace.
Nan ya dinga kai da komowa a kaina saida yaga komai ya daidaita har na samu barci saboda maganin da akai mun allura dashi na samun hutu.
Bani na falka ba sai washe gari wuraren shadayan safe na bude idanu da kyat don sunyi min nauyi.
Shine a zaune dakin ya tsura min idanuwanshi masu ban tsoro da rikitani yana ganin na bude idanuwana yace kin falka zarah ?
Nace eh sannu ya na gode yace don't mind ina ke maki ciwo yanzu nace ba ko ina irin hausan mu na yaran yanzu.
Mikewa naga yayi ya tako zuwa inda nake sai kawai naga ya fara dan taba min jiki a hankali.
Nan daima sai daya kara tambayana idan ba inda ke min ciwo nace naji sauki.
Ya juya tare da fadin likita yace idan kin falka a kirasu haka kawai zaki kashe kanki gurin shegen zuciyar banza waike shagwababa.
Fuskana hade tare da dan kawar da kaina ina yunkutin mikewa zaune da kyau ya juyo yana fadin ki bari sai sun shigo sun duba ki sai ki tashi .
Yana fadin haka ya fita sai gasu tare da nurse da likita mace sun shigo suna magana saida ta gaidani tare da min ya jikin nace da sauki a cikin harshen turanci.
Ta tambayeni in akwai inda nake ji nace banjin komai yanzu ta danyi rubutu a takarda ta juya gareshi tana fadin .
Zasu bani sallama yanzu sai dai idan naji wani gurin na mun ciwo in dawo su kara teareting dina.
Tana bashi takardan suka fita tare yaje ya biya kudin komai ya dawo lokacin har na sauko daga daman gadon ina zaune ina jiran dawowan shi.
Ya shigo ya kalleni yana fadin zaki iya tafiya ko in taimaka maki nace zan iya da sauri don kada yace zai kamani.
Oya tashi muje yace yana dan ja gefe daya na mike da kyat don har lokacin ina dan jin rashin karfin jikina.
Ya rigani fita daga dakin ko ya lura da tsayawan danayi ina jiran ya fara fitane don ban yarda ya sani a gaba yana kare min kallo.
Har muka iso gida ba wanda yai magana a cikin mu ni kaina na hade da tagan motan cikin kasala har muka isa gidan ban dago kaina ba.
Daidai shigamu gidan wayan shi yayi kara ya dauko yana fadin how far merry banji may tace dashi ba sai dai shi da ya fadi an sallamay mu ai ya dan yi shiru kafin ya miko min wayan.
Ina dauka muryan merry ne tana fadin fatema yaya jikin naki rabon da inji muryan ta ko in gane ta tun zuwana gidan data dauko yi mun wullakanci nabar su na dawo gidana sai yau datake son ta tabbatar idan da gaske yake tare dani yake tace ya bani wayan.
Nace mata a cikin muryan marasa lafiya naji sauki anty tace min wish you quick recovering nace thank you na mika mai wayan.
Jin yana tambayan ta karfe nawa zasu iso yasa nasan merry zata bakunci London din ke nan daga America.
Jin sun shagala da waya da matar shi daga inda yake tsaye ta bani baya na mike har na haura da kyat zuwa sama dakina na shiga ban tsaya ba bathroom na shiga na hada ruwa masu zafi na gasa jikina dasu na fito tare da dauro alwala na fito.
Shiko yana gama wayan shi ya juyo gareni da zuman ya tambayeni abinda zanci sai yaga wayau bani gurin .
Sama yabi da kallo yana mamakin lokacin dana bar gurin baiji ba dakin ya shiga ya samu ina bathroom ina wanka sai ya fito.
Sallolin dake kaina na rama ina gamawa na shirya na hau gadon sai barci can cikin barci naji yana kiran sunana in tashi inci wani abu.
Idona bude da kyat don har lokacin maganin bai sakeni ba nace bancin komai .
Tsawa ya daka min yana fadin ki rashi nace kici wani abu kinji shagwaba da shiririta yayi maki yawa.
Baki na turo ina fadin ni banjin yunwane yaya zaki tashi ko sai na saba maki rai ya ce a hasale.
Jin hakan yasa na yunkura na sauko daga kwancen da nake na dago kai ina kallon shi yace a kawo maki nan ne ko zaki iya sauka kasan.
Nace zanci a nan na dan kalle shi a fakaice inji abinda zaice min sai naga ya juya kawai ya fita sai gashi dauke da kwalin pizza mai zafi ya jawo table ya aje min a gabana tare da aje min ruwan sha gefe daya.
Ganin na tasa kwalin gaba ina yamutse fuska ya matso ya bude min da kanshi ya gyara yace kici zai taimakawa dandanon bakin ki wanan.
Ganin na fara ci ya fice daga dakin hakan ya bani daman samu ci sosai dukda ba wani ci nayi da yawa ba nasha ruwa na koma na kwanta.
Wanan karon banyi barci ba saidai ina tunanen marin da yaya yai min sai gashi kuma ys koma yana jinyata da kanshi kamar bashi bane ya mareni din kan zargi.
Nasan banyi gaskiya bs don na fita bada uzinin shi ba lokacin amma ai hakan bai kai har ya mareni ba tunda na fada mai gaskiyan abinda ya fitar dani daga gidan.
Idan zaimun adalci abin baikai ga mari ba ai ga marin ya haifar min da kwanciya ciwo har asibiti duk da dai sanadin marin ya jawo muna dan kusanci a tsakanin mu don ban dauka yana da saukin kai irin haka ba.
Kamshin da naji ne yasani dago kai shine ya shigo dakin yayi wanka ya sauya kayan jikin shi zuwa yar karamar rigan t,shirt da bakin wando sai takalma bakake a kafan shi.
Kallona yake na dan dukar da kaina kasa ina wasa da yatsun hannu naji yace ni zan fita zan je in dauko su merry airport.
Wata kila ba zan dawo gidan nan ba sai zuwa gobe don haka ga maganin ki nan ya nuna min gefen gado.
Ai masu sannu da zuwa nace dashi bai amsani ba yace good night ya fita nabishi da kallo har ya bace min.
Ajiyan zuciya na sauke ina tabe baki nace ni yafi min nono fari kazo kawai ka wani tare min a gida ka hanani shakat .
Ashe bai tafi ba muryan shi naji daga kofa yana fadin ki sauko kasa ki zauna ko jikin zai kara warware maki kwanciyan nan yayi yawa haka.
Nan yayi mun tunda ko na fita falon ni kadai zan zauna a can yace baga tv nan ba ko ki tsaya a backkaloy kiyi kallo.
Baki na dan turo alaman ya takura min fa da wani lalarashi shi can da bansan dalilin yimun ba ya juya ya fice a hasale.
Na dade a zaune gurin kafin inji ina son fita falon har nakai kofa na tuna da wayata da rabona da ita tun ranan dana fita da safe mukai waya da Rita wata course mate dina tana min happy Christmas.
Dan dube dube na fara yi a dakin a hankali ina neman wayan da ido banganshi ba.
Nan dai na shiga bincike ban ganshi ba dan tunane na fara yi can na tuna yana cikin hand bag dina dana fita dashi ranan na duba da sauri yana ciki har battery's yayi sanyi yana batun mutuwa.
Dauka nayi tare da wayan caji zuwa falo na sauko ban zauna ba saida na kunna tv na hau saman dogon kujera na kwanta ina kallo .
Ba abinda akeyi sai bukin chrismati a ko wani Chanel nasu na kasan wasu film daya shafi bukin wasu kuma wai wa,azi sukeyi.
Tsuki nayi na jawo wayata na kunnanan na hauyin game abina ba tare da namaida hankalina gun tv ba kuma.

Sai dare jirgin su merry din ya sauka tunda suja fito take raba ido ta ganshi don a zaton ta ba zai zo tarbon su ba din kamar yadda ta bukata duk da akwai driver da zai iya kwasosu airport din a gidan..
Dan rugumay ta yayi kamar yadda al,adansu nacan yake kafin ya daga queen din shi sama yana subbatanta.
Hakan ya dan sasauta ran merry din a lokacin don tsananin son da takewa mijin nata duk bacin ranta dashi da zaran suyi arba komai take ji gamay dashi zai gushe mata a rai.
Bayan sun gama dan rugumay rungumay su ne suka nufi mota merry da yarta sai shagwaba suke zuba mai har suka isa gida.
Sun samu masu aikin su sun gama abinci har an jera mai kasa cin abincin yayi baisan may yasa yanzu baijin dadin abincin gidan nasa ba ko kadan.
Yana mamakin kanshi da yake iya bata lokacin shi gurin cin duk abinda na jagwalgwala a gidana ya zauna yaci hankali kwance.
Ga wani sabon akidan dake shigo mai zuciyar shi wanda shi kadai ya sanda hakan a ranshi yanzu sai yake jin kamar yana dan kyamatar merry din a ranshi wanda bai san dalilin hakan ba a ranshi.
Ya kanyi tunanen ko don irin akidojin da take tsiro mashi da sune wansa a da can baya ya hanata ta daina yanzu kuma takeyin su.
Ji yayi takai mai runguma ta baya tana dan kai mashi kiss sai ya juyo da ita zuwa gaban shi ya zaunar da ita saman cinyan shi.
Goran fresh milk data dauko tana dan sha a hankali ta nufi bakin shi dashi kai ya girgiza mata alaman baisha.
Tace saboda may yace just kawai yana dan bubuga bayanta a hankali yana lumshe idanun shi.
Tace na fahinci tun zuwan mu kamar kana da damuwa a tare dakai ya dan nisa yace haka dai kika gani banda damuwan komai a tare dani.
Dan kiss takai mai ya daure yana biye mata muryan yarsuce ya dakatar dasu tana fadin daddy na kasa barci.
Hannu ya mikawa yar alaman tazo gurin shi da sauri ta karaso zuwa inda suke zaune din.
Nan ya mayar da hankalin shi gareta yana mata tambayoyi tana bashi amsa cikin wayau ta irin na yara.
Ganin ya mayar da hankalin shi gurin yar shi merry taja tsuki tace yasan fa tazo da muradin shi a ranta kuma yana biyewa yarsu.
Ya kalli lokaci dare ya soma yanzu gashi sakko zasuyi zuwa church da safe dan kallonta yayi yace zaki dai tafi don ba inda queen dina zata tafi ita .
Why tace tana kallon shi da mamaki yace na fada maki tun farko ba zan barta tabi addinin ki ba kuma kin yarda da hakan may zaisa yanzu ki tsiro zuwa da ita church haka ?
Mikewa tayi saman jikin shi kafin tace wanan shine ba zaiyiyu ba kasani dolene in koya ma yata addinina ala bashin idan ta girma ta zabi addinin da take so a rayuwan ta.
Wanan kuma karya k???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ika sha merry a barta idan ta girma ta zaba din mudfin ba zaki barta ta koyi addinina ba.
Wasa wasa suka fara fada a tsakanin su har ya kaisu ga zagin junan su ranan dai fada sosai sukayi har yake fada mata ya gane ko yan uwan shi bata so yanzu.
Don wanan yarinyar da tazo kararu da gangan ta koreta daga gidan nan don kada yarsu ta koyi wani abu a gurin ta yana sane ya kyaleta ne kawai.
Itama ta mayar maida fadin ta gane manufan iyayyen shi na turo yar uwanshi gare su don a daukewa yarra hankali kan addininta ne.
Don haka ba zata yarda da kowa nasa ba yanzun a rayuwanta takare da fadin to hell da addinin shi.
Fadin haka ya mike ya yana kokarin daukan rigan sanyin shi ya saba ita a zaton ta daki zai shiga ta rigashi shiga ta rufo kofab da karfi.
Key di motar shi ya dauka ya bar gidan bata sani ba ya fice abinshi kai tsaye gidana ya nufo bansan da shigowan shi gidan ba nayi nisa da barci na rufe ko ina na gidan.
Ko ina duhu ya mamaye a gidan ya kunna wuta yana bin falon da kallo wayana yagani aje saman table sai juice din danasha na bar rabi a gurin.
Kashe wutan yayi bayan ya dauki wayan ya haura sama dashi a hannun shi ya nufi dakin shi sai kuma ya yi shawaran mika min wayan .
Ina kwance ina barci hankali kwance bansan wainar da ake toyabani har ya shigo ya tsaya yana kare mun kallo yadda na dunkule wurri daya da alaman sanyi ya takura min ga hannuna dana lankwashe zai iya min tsami a hakan.
A hankali ya tako zuwa wurin gadon ya dan duka ya aje wayan a gefena ya kai hannun shi da niyar gyara min hannu .
Cikin barci na dan gyara hannun da kaina ina fadin Amma akwai sanyi da yawa na kara dunkulewa a guri daya tare da takure kaina.
Samun kanshi yayi da tausaya mun tare da tunanen ashe har yanzu ina kewan yan gida haka harda mafalkin Amma nakeyi.
Dan jawo bargon yayi ya rufa min a jikina sai yaji na sauke ajiyan zuciya tare da rike bargon da hannun shi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login