Showing 309001 words to 312000 words out of 419207 words

Chapter 104 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1405

dabamu san yadda suka kwana ba tayi masifa sosai kafin ta fito zuwa part din mamu tana dukan kofan da karfi saida mamu ta taso daga inda take zaune tana lazimi ta bude kofan.
Ina yar nan take ta tambaya a hasale tana ciki mamu ta bata amsa ta wuce fuuu zuwa dakin sai mamu tace tana dakina a nan ta kwana.
Ina kwance bayan na sallame sallah na kara kwanciya ina jiran ayi asuba ta shigo da sultana tana fadin karbeta nace wanan daukan alhakin yayi yawa wallahi.
Amma dai Amma kinji abinda kawu yace kan yaran nan ki kaita wurin hjyshi kawai don Allah bana son kawu yaga na saba mai Amma.
Ba kawu ba kawulle nace tana min dakuwa ta kara fadi a hasale ba kawu ba nace maka wuya.
Dariya ne ya kubce min nace Amma kawun nawa kike zagan min tunda asuban farko haka an zageshi ko zaki rama mai ne nace wace ni hajjaju Ammalle na rama a fakaice.
Tare da mika hannu na karbi yarinyar a hannun ta da sauri sultana dake ta miko min hannu tazo wurina tana sauke ajiyan zuciya har lokacin bata bar kukan da takeyi ba din.
Kada naji ko in gani kin kaiwa wanan mara imanin yar nan a gidan nan dani take zance wallahi.
Ta fita tana fitina a tsakar gida ita kadai ba wanda ya lekota har taci ta sude ita kadai.
Baya nayi sallah nayi wa sultana wanka nima nayi banzo da wasu kaya ba dole na saka dogon rigar mamu a jikina lokacin.
Na koma muka kwanta zuciya ba dadi nasan yadda akai fama da sultana ko su Abdul haka zaiyi fama dasu a gidan duk da ga maria gashi suna ganinshi amma nasan sai sun taba rikici sosai a gidan.
Da tausayin mu a raina ina muna addu,a sosai don Allah kadai yasan halin da kowan mu ke ciki a ranan har mahaifan mu.
Har kawu dayai sanadin auren dashi nasan ranan baiyi barci da dadin raiba shima a nasa bangaren .
Kamar yadda kawu ke bin dakuna yauma haka ya shigo part din mamu da dan sandan shi dake karamai karfi yana dogarawa .
A falo ya samemu zaune muna karyawa muka shiga gaida shi da kwana ya samu wuri ya zauna yana fadin.
Fatima ina son ki saka hakkuri a ranki nasan mun cuta ma rayuwan ki mun bata maki lokacin kurciyan ki banyi hakan da niyar cutawa a gareki ba ko kadan.
A hankali na dago kai na dan kalli inda kawuna yake zaune yana magana nace a a ha kawu wallahi ni baka cuce ni ba don uba bai taba cutar da yarsa ai.
Yace na gode da wanan fahintar da kikai min Fatima hakan da nayi yanzu shine mafita gareku damu duk a barta ta aura mai wadda take so.
Abinda nake so dake ki kara kwantar da hankalin ki ki natsu kina dai da takardan ki ga hannu zan duba inga abinda ya dace ayi nan gaba kan aikin ki.
Na gode kawu nace a fili a ciki zuciyata kuwa sai wani irin harba min takeyi ina fadin yanzu shike nan an rabani da aurena ina ji ina gani ko may ?
Muryan mamu ya dawo dani ga dan tunanen dana fara tana fadin yanzu yaya yaran nan ba,asa makomarsu ba tunda, , , , ,
Hannu kawu ya daga mata ya hana ta karasa fadin abinda take son fadi a lokacin mikewa yayi yana fadin hajiya ta sameni kan zancen yar nan ita mace ce kuma karama zaku iya riketa a nan don kada a jawo mata wani matsala kuma.
Daga haka ya fita nasan part din mu shine karshen shigan shi a zagayen da yake yi don haka muna gamawa na mike na dauki sultana zuwa part din Amma don in gaida ita.
Hjy maryam ce na hadu da ita ta fito part din kawu muka gaisa da ita ta dan make murya tana fadi sai hakkuri fatima iyayye suna gaba da komai ba komai hjy nace mata tare da mata godiya na wuce abina inda zani tabini da kallon munafunci.
Na samu Amma a zaune falon su kamar yadda na zata ta tasa abin karyawan ta a gaba tana kallo .
Jin sallamana yasa ta dago kai tana kakaro murmushin dole a fuskanta tana fadin yanzu muka gama waya da mijin ki yace zasu yi tafiya shida yaran yau.
Gabana ne ya fadi sosai dan jin abinda Amma tace min yanzu ina kuma zasu tafi na tambaya a dan mamaki.
Bai fada min ba yadai kirani yana tambayana kwanan ku nace kuna lafiya yace min sai idan yazo zamu magana dashi.
Fitowan murja daga dakin su yasa na kalleta nace dama ina son in turaki ki dauko min kaya don ko yanzu na mamu na saka a jikina kina gani.
Ta kai zaune tana fadin wa ni ai in kin gani kasuwan maza gulma ya kaini yanzu ban ko son hanya ya hadamu da yaya don sai inyi zaton zaiga nice duk na jawo mai wanan abin.
Haba dai yaya zaiyi zaton hakan gare ki tunda yasan baki da laifi shi ba haka yake ba ai kawai dai baki gama fahintar shi bane.
Muna tsaka da hirane muke dan jiyo hayaniya a tsakar gidan sama sama shiru mukayi muna sauraren hayaniyar meye kuma akeyi.
Muryan hjy ce ke masifa da alama wani ya tabata a lokacin inda take shiga ba nan take fita ba.
Wai ashe yayane ya turo Aliyu ya kawo kayan abinci part din mamu shine hjy taji ta fito tana masifa hakana .
Saida fauziya ta shigo muke ji a bakin ta wai tana masifa da Aliyu bai kula ba sai kai kayan abincin tare da abin sha da suka jibgo mota dashi yake shiga dasu part din mamu abinshi.
Zata ko mutu da bakin cikin akan dan yau, idan tace bakin kishin matan diyan cikinta ta saka a ranta haka wanan abinda mai yai kama kiri kiri ta hana yaran nan zuwa garin nan saboda tashin hankali ana zaune a kasa daya amma ya dauke kafan shi da gidan nan.
Nace wanene Amma ta kalloni hasale tana fadin habibu ma da yarinyar nan Rakiya matar sa su ai sun fita iya iskanci indai fulanin dajine suna daidai da uwarta ai.
Jin hayaniyar yayi yawa yasa murja da Fauziya har mama hadiye fita da sauri sai Amma dake kokarin mikewa irin na tsofi ta rage a falon tana kiciniyar tashi tsaye.
Daga inda nake zaune naji muryan yaya kamar diran mikiya a kunnuwa na yana fadin don may ba zan kawoma matana kayan abinci ba tana matsayin matana har yanzu ?
Mama banso mukai haka dake ba a gidan nan na fada maki ba zan yarda ki rabani da matata ba don banga abinda ya shigo da fatima cikin tsabgan ku ba da kukeyi.
Ba zan yarda darajan aurena ya tabu ba a garin nan matana da yarana nike da hakkin ciyar dasu a kaina.
Don haka ba zan yarda wani ya ciyar min da mata ba alhalin ina dashi zamanta a nan wanan ra,ayin kune keda daddy wanan ni bai shafeni ba all what i know aurena yana bisa kanta.
Da hjy tana da kunya ranan data jishi a gidan nan don yadda yaran sukai mata a gaban kowa ta rasa abinda zata fada.
Sai Ammane ta amsa mai da fadin wanan kayi gaskiya tunda har yanzu a matsayin matarka take wurin ka.
Ya juya yana tambaya ina ina ne ?
Da sauri murja tace tana wurin Amma.
Ya nufo part din Amma din rai a bace a kwance ya same ni sultana tana saman ruwan cikina tana ramuwan barcin da batayi ba daren jiya.
Tsaye yayi yana kallon mu kafin yace ramuwar barci wanan keyi ko don Amma tace jiya bata barsu sunyi barci ba da dare .
Na amsa mashi da kai.
Ya dan kai zaune gefena yana fadin ke naga kamar zaman gidan yayi maki dadi sosai a ranki.
Nace to yaya zanyi wai yaya idan ban zauna ba so kake in binka in butulcewa iyayyen mu ko may ?
Dama su suka bakani na fada maka yanzu kuma sunce in dawo gida in zauna ai dole ne in dawo yace good may kuke bukata yanzu don yau zan bar garin nan ni.
Ina kuma zaka na tambaye shi saida ya dan furzo da iska a bakin shi yace lagos zan koma in na kwana biyu Abuja may zan zauna inyi garin nan kuma yanzu tunda sun kwace min ke ?
Nayi murmushi nace yaran fa da maria yace dasu zan tafi duka yau zamu bi jirgin karfe biyu zuwa Abuja motar ki yana nan kofan gida saidai ban son yawan yawo ki natsu wuri guda don Allah zarah kafin komai ya lafa.
Idan ka tafi auren naka fa sai bukin ya tashi zaka dawo ke nan wani kallo yayi min yace kina tsoron auren da ake fadin zanyi ne ?
A,a ha kan me zanji tsoro tunda ba a kaina zata zauna ba in tazo hanyar jirgi daban na mota daban kaima ka sani.
Mikewa yayi tsaye a lokacin Amma ta shigo dakin nace zancen tafiya na gida fa in duba su ?
Wani kallo ya jefa min yana fadin haba zarah muna ciki wanan halin kike wani zancen tafiya gida yanzu ?
To may nakeyi a nan din ai gara inje gidan mu asan ina da gida agolaci ba zama shegiya bace yafi yace good kina da gaskiya cikin bacin rai.
Wurin Amma ya juya yana fadin Amma zan tafi ba lalai bane in dawo ta nan kafin in tafi yana mika mata kudi tace wai ina zakane yace gani nan dai Amma.
Tunda yace hakan na gane baison kowa yasan inda ya dosa a lokacin naja bakina nayi shiru ya sake cewa ga amanan su nan na bari a hannun ki Amma don Allah a kula da su ban son yawo ta sani ita.
Babu ma inda zata insha Allahu harka dawo tace nace da sauri a,a Amma kada kice mai hakan idan fita ya kamani fa ?
Wani kallo yai min a daidai lokacin ya duka ya shafi kan sultana yana kiran sunan ta yarinyat dake cikin nauyi barci tayi firgigit ta bude ido kuka tasa tana mika mashi hannu ya dauke ta.
Dan dagata yayi sama ya sunbance ta sai kuma ya rungumay ta a jikin shi yana sauke ajiyan zuciya a hankali.
Abincin ta yana nan nasa an kawo mata don Allah zarah ki ba yarinyar nan kulawan daya dace sosai kallon shi nayi ina mamaki komai da yake kai kasan a cikin karfin hali yake yin shi.
Kudi ya ciro ya aje min gefena yace ki rike wanan idan na samu lokaci zan turo maki ki kara rikewa a gurin ki.
Yana fadin haka ya mike tare da kallon Amma yana fadin to Amma zanyi niya Aliyu zai kawo yaran nan suyi sallama da maman su kafin mu wuce.
Da sauri na furta masu ka barsu karsuzo su damay ni nan daga shi har Amma wani irin kallo sukai min lokaci yace don may kikace hakan nace haka kawai a cikin daure fuskana.
Barsu kawai sadauki Allah ya saukeku lafiya ka kula da kanku ka kuma kwatar da hankalin ka komai yayi tsanani maganin shi Allah ne.
Hakane Amma yace yana sauke ajiyan zuciya ya juya ya tafi ba tare daya kara min magana ba ko kallon inda muke.
Wani iri naji a raina saidai hakan shine saukina duk da nasan ban kyauta ba hanashi kawo min yaran danayi muyi sallama.
Bayan na idar da sallah ina zaune wurin da nayi sallah a falon Amma nake tunane duk inda suke yanzu suna shirin dawa su bar gari ke nan.
Biyu daidai na kalli agogon falon na sauke ajiyan zuciya a hankali na kai kwance a kasa ina lumshe idanuwana.
Muryan Amma ke fadin ni na taba ganin wanan bala,in haka kace kai baka kaunan kowa a rayuwan ka a dole sai ka mayar da kowa bawa a gurinka.
Ban dai yi magana ba ina jin ta tana maganganun ta na share abinda ya damu zuciyana a lokacin ya dameni.
Ban kira shiba shima ranan bai kirani ba sai washegari sai ga kiran shi a wayana na dauka lokacin muna zaune tare da mamu a falon ta.
Dauka nayi da sallama sai ya hauni da fada zahra may kike nufi da hakan da kikeyi ne wai ?
May kuma nayi yaya na tambaye shi kamar ban gane mai yake nufi ba ga maganar shi.
Yaci gaba da fadin kina ganin don sun daukeki daga gidana hakan na nufin sai ki shareni aiko ba don niba zaki kira kiji lafiyan yaran ki ko ?
Saida na dan saci satan kallon gefen mamu naga ta kura min ido don ta gama tambayana na kirasu naji saukan su nace na kira ban samay shi ba nayi mata karya da hakan don nasan zata iya min fada kan hakan.
Nace nakira bai shiga bane yaya sai naji ya kashe wayan shi na bata rai ina aje wayan a gefena cikin bacin ran kashe min waya da yayi.
Ya kamata ki tausayawa halin da bawan Allah nan yake ciki don dake dashi duk ba yin kan ku bane yana zaman zaman shi aka ja mashi magana.
Shi kanshi yaya yasan halin matar shi dalilin da tun farko naki wanan hadin naku ke nan amma sai ba a duba min ba.
Yanzu ga abinda ake soncin mawa kara lalacewa yayi bai yuyu ba don haka banga abinda zaisa kiga laifin bawan Allah nan ba duk yadda akeyi yayi muna halarci a rayuwa don ba haka mahaifiyar shi taso da shiba kowa ya sani shi dalilin yin wanan haukan haka da takeyi.
Su basu gane irin kiyayyan da hjy ke min da duk wani nawa cikin gidan nan don haka duk wani hanyar da zataga ta kuntata min shi take nema ta gasa min kwakwa a hannu na.
Ta manta Allah ne mai yin komai bawai ra,ayin ka ba yanzun da mun dage akan ba za,yi auren ki dashi ba ina rabon yaran nan zai kai mu.
Sai Allah ya dauke dayan mu ayi ba dashi ba shi yasa wani lokaci jayaya da hukuncin Allah baida kyau mutum ya rugumi kadara duk dayazo mashi maikyau ko mara kyau ya barwa Allah hukuncin sa nayin hakan.
Har yau sam ban taba badaman auren ki da umar ba don yadda duk ake halarci bawan Allah nan yayi muna shi a rayuwa .
Yadda yake aikowa uwarshi kudi duk wata haka nima yakan turo min da kudi ta account dina duk wata kuma yace kada in fadi don Allah.
Nasan halin umar tun muna kanana ba mutum bane mai son magana haka Allah yayi rayuwan shi shi tun farko.
Mamu ni bawai naga laifin shi bane kawai dai ina kaucewa bacin ran kawune don kada yaga yana kokarin min gata ni ina kokarin watsa mai kasa a idanu ga idon jama,a.
Zaisan kuyi waya dashi ne ko kuma koda ace rabuwa kukayi ai yanzu kun zama daya don ruwa ya dade da gaurayewa da jini ko.
Mamu zan kula insha Allah ni bawai ina ganin laifisa bane ni mai yayi min da zanga laifin shi may ye yaya bai mun ba na ingata rayuwa na da zan manta da hakan.
Zuwa yamma na fara jin ba dadi a jikina haka yasa nasha magani na kwanta ranan ban fito ba ga fitinan sultana da takeyi min ga ciwo sannan kuma zuciyana ba dadi lokacin.
Washe gari ne na tashi da zazzabi sosai don tun cikin dare nake dan jin jikina sama sama har yakai na fara amai sosai .
Ganin haka yasa mamu zuwa fadawa kawu banda lafiya yace subbahanallahi may ke damun ta ga mijin ta ina ganin kamar baya gari tun shekaran jiya rabona dana ganshi gidan nan.
Ko uwar shi naji tana tambaya wai munyi waya dashi bai shigo ba harshi har Aliyu tun ranan .
Mamu tace ina ganin kamar baya garin nan fa yaran fa suna ina su kawu ya tambaya cikin dagowa yana kallon ta.
Duk dai inda yake yana tare dasu ai tunda kaji baiyi magana ba bai kuma kawo su nan gidan ba.
Yanzu barin baki kudi kuje asibiti taga likita asan abinda yake damun ta yafi tace dama kabar kudin don tace akwai kudi a wurun ta yayi saurin fadin a, a karba dai ki kaita don nauyina ne yanzu kula da ita.

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login