Showing 396001 words to 399000 words out of 419207 words

Chapter 133 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1422

aure a gida a lokacin har ina ganin laifin shi kan hakan hjy ta fada a cikin takaicin abinda ke faruwa din
Kafira kafira wa yan nan mutane ai basu da dadi wallahi kansu kawai suka sani kan komai halin su yan akidan su don haka muka zauna dasu a kaduna.
Fita nayi daga dakin a daidai lokacin da merry ta rike yaya kan ya bata yarta don ashe tun cikin dare ya fada mata muddin tace sai ta tafi da yarinyar shiko zai dauke yarshi a wurin ta.
Ni dai hankalinane ya tashi kan fitinan danaga suna yi din gata, tana ta barazanan kai karan shi ga hukuma yana fadin sai ta dawo.
Kawu na kira nake sheda mai abinda ke faruwa a gidan yace zaiyi magana da yay din da ita merry.
Karan da naji tayi ya kara firgitani na fito da sauri ina ganin yadda yaya ya hankadeta yana fita daga gidan.
Nikan wanan abin ya isheni nayi dana sanin zuwa kasan na samu merry din a nan do hutun namu sam baiyi dadi ba ga laluran hjyn su ga fitinan matan yaya din ko yaushe sai na kwanmace ace ina can abina yafi mun wanan zuwan haka a gidan sarka.
Zuwa nayi wurin merry din ina bata hakkuru wani tsawa ta daka min tana dadin in barta duk abinda akai mata nima da sanina ai.
Mamakine ya kamani jin furcin merry din a gabana ban iya furta komai ba na juya na koma dakina na barta a wurin.
Tun wanan lokacin ban kara shiga tsabganta ba duk da ina jin yadda suke kwasa cikin kwana biyun nan.
Rikici sosai sukeyi don har kotu suke da merry din dukda tana gidan nasa zaune ga samira idan zamu hadu kiyayyanane karara a fuskan ta babu sassauci a gareta.
A karshe kotu tace zata ba yar tasu dama ta fadi inda take son zama a tsakanin su.
Wanan case din nasu ya kara kawo cecekuce ga mutane suke ganin illan auren matan da ba addinin su ba don gujewan irin wanan fitinan.
Karshe dai Queen ta zabi zama nan wurin mahaifin ta hakan yasa yan uwan merry shigowa har kasan nan kan case din nasu.
Sosai sukai rikici dashi kan ya basu yarsu ganin fitinan yaki karewane yasa suka dauki yar su suka tafi suka bar Queen tare da mahaifinta.
Ganun hjy ra samu sauki soai don har sun koma wurin likita ya dubata ya yaba da nasaran da aka samu sosai.
Ya kara diban masu lokacin da zasu dawo a kara dubata again maganin da zasu saya ya tsaya ya sawo a hanya suka nufo hanyan gida.
Saida ya shigo da mahaifiyar har dakin ta inda ya samu mun gyara dakin nida maria sai kamshi ke tashi a dakin.
Abinci maria ta shigo masu dashi bayan sun dan huta tana ajewa na shigo dakin dauke da abinsha ina gaidasu da dawowa.
Wanda yanzu idan na gaida hjyn tana karba min sai dai babu sakewa a tare damu dagani har ita ko wani lokacin don ba sabawa da hakan a tsakanin mu .
Nikan na gama na fito daga wurin su na koma dining muka zauna cin abinci da yarana har maria da yanzu na mayar da ita yar gida sosai tare damu don irin kokarin maria din da kula ga rikon amana.
Ban farga da shigowan Samira din falon ba don ranan bata saka takalmanta mai yawan sauti ba ta shigo.
Sai jin muryan ta mukayi a kanmu tana huci take fadin ke yar aiki da cewa maria .
Duk juyowa mukayi muna kallon ta ta nunani ta sake fadin nace kada ki kara shanya min kayan yaran ku a wurin dakina baki ji ba ko.
Wanan ne karo na farko da wani magana ya taba hadani da ita tun zuwa mu kasan da muka same ta a gidan.
Nace amma ke baki da wayau ko hankali ko yanzu akan shanyi kawai zaki shigo m???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?una nan da kashedin bar maki shanyin tufafi a kusa da part din ki.
Ko part din kine ta tambaya a gwatsale a cikin izgili a, a gidan ubankine nan din aikun sani.
Gaba dayan mu muka juya don jin muryan Nafisa data shigo gidan bada sanin kowan mu ba duba jikin mahaifiyarta da aka kai asibiti.
Ke kuma asuwa a cikin wanan maganan ko yanzu kuma kin fara kamun kafa da itane an gama zagin ta koda yake banyi mamakin yin hakan daga gareki ba don har manyarki ma haka suke nunawa bayan an gama bata ta da farko.
Duk wanda zai batani wata kila nayi masa ba daidai bane har ya fusata dani kada kuma ki manta Nafisa yar uwan hauhuwa nane na jini.
Ba abin mamaki bane don ta shiga magana na a yanzu kinsan ba, a raba anta da jini ai nake fadi a cikin zafin rai.
Ta juyo tana kallona kafin tace wai mamaki ke yanzu kina ganin kin samu wuri da har kike ganin kina iya taka kowa tau ki sani kijawa yar aikin nan naki kunne kada in karas ganin kayan yaran nan a gefen part dina don ba za,a tare min iskaba don isa da mallaka da ake takama dashi.
Isa da mallaka kan ai dole tayi shi a gidan nan tunda gida gidan mijinntane gidan diyan ta kuma nafisa ta fada.
Wani mahaukacin dariyan yan iska ta kwashe dashi tana fadin ke yanzu bakiji kunya fadin wa yan nan maganganun ba haka Nafisa ?
May ye baku fada ba akan wanan da farko daga ke har kowa naki sai yanzu ne kuma take mutum a wurin ki.
Ikon Allah ke yanzu wanan haukan ne ya turoki nan ina dai ni ban ma san da zamaki gidan nan ba don dake da babu duk dayane a gare ni don haka dani da yarana mu fita a idon ki.
Gida dai na uban su ne don haka ke kinyi kadan kice mun ga abinda za,ayi a gidan nan sai dai bari maigidan ya dawo muji idan ya raba gidan yaba kowa nasa kason ne ban sani ba.
Muryan hjyce ke dan tashi tana kiran Nafisa daga dakin da take a cikin damuwa a daidai wanan lokacin ne samira din taja wani tsuku mai karfi tana fadin aikin banza yiwa kare wanka duk a tafin hannuna kuke gaba dayan ku gidan nan.
Ta juya ta fita nan ta barmu da mamakin ta ina girgiza kai dalili daya zuwa biyu ya hana na bata amsa daidai da abinda tazo dashi.
Kudun hjy ta sake shiga wani hali kamar wancen na baya sai kuma yaran dake wurin tun shigowan ta sun kura mata ido a tsorace don basu saba ganin hakan ba isan ba a kasan nan ba yanzu.


Don Allah kuyi hakkuri wallahi kusan kwana biyar bamu da wuta layin mu a wahalce na samu har na karasa wanan din da fatan zaku fahince ni yanuwa nagode kuyi hakkuri don Allah.
17/11/2021, 07:22 - ??5惙5惙5?: Bayan Nafisa ta shige gurin hjyn su samira ta kada kai cikin izza da isa ta juya ta fita daga part din kowa na binta da kallon mamaki.
Ta na shiga part din ta ta wani sauke numfashi tare da sake dafa kirjin ta tana fadin ashe zan iya kuwa .
Waya ta dauko tana kiran mahaifiyar ta kira uku ta dauka bata jira sallaman ta ba ta fara fadin umma wallahi nayi duk yadda kikace in masu.
Koke fa da kin zauna kina wani kumshe a daki kamar wata matsoraciya dake nina fada maki kada ki ragawa kowa koshi maigidan da kuke zaman shi ya kawo maki wani gani gani ki face shi tas.
Da mamaki take tambayan mahaifiyar amma umma sai nake ganin shi ai ba daidai bane in masa rashin mutunci tunda kinga neman shiga muke a zuciyar shi.
Shiga ai mun rigada mun shiga samira kedai kawai ki zura ido kiga yadda za a kwasa dashi a karshen aikin kawai.
Ko yanzu me yake iya tabukawa a kanki sai dai ido kawai duk wani kulli kuma da aka aiwatar a kanshi zamu walwale komai da sannu.
Sun dan dauki lokaci suna tataunawa da yar nata kafin su gaji su kashe wayan don kansu .
A bangare na tana ficewa na girgiza kaina tare da kallon abincin dake gaba ina ci ina dan sakw murmushi a fuskana wanda ni kadai nasan ko na meye a lokacin.
Fauziya ce ta kawar da shirun tana fadin wanan matar kamar mara hankali komai nata ita fadane wallahi.
Ni tun ranan dana fara ganinta na gane tana da masifa don mun fita da yaya waje take bin mu da harara bata san na ganta ba a lokacin.
Eh dole ne tayi haka ai don babu abinda zata gwada a gun hjyna na kishi ga yaran nan da tsone ido jama,a duk wanda ya gansu sai yayi magana kan su dole hakan ya kara mata takaici a kansu.
Maria ke nan nace da ita nima kaina wanan abin yana min zafi don mutum wani baka san bakin shi ba sai zuwan mu nake dana sanin zuwa da yaran nan kasan nan a wanan lokacin.
Duk da nasan babu abinda zasu iya masu sai Allah don a tsaye nake kan diyana tun dana haife su don gudun irin hakan.
Na dade wurin zaune har lokacin na kasa tsayar da magana daya a raina wanda zanyi amfani dashi wurin nuna ma wanan samira din nima na iya kamar kowa.
Daki na shiga nayi alwala na gabatar da sallah a zahar da ake kiran sallah a ko ina dadina da kasata ke nan mu sanman arewa zaka ji abinda zai tunatar ma da addinin ka ta ko ina sai dai idan baka da niyar daukan darasi ga hakan.
Waya da nakeyi da anty Ramla ne ya dauke min hankali har lokacin shan maganin hjy yayi ban sani ba saida salma da ban san da shigowan ta gidan ba.
Muryan ta naji kamar daga sama tana fadin madam kece kwance haka a kasa da alama dai tun idar da sallah baki mike ba.
Ga hjy can tana zaman jiran maganin ta nace barin duba mata ke a nan na mike ina murmushi tare da fadin yaushe kika shigo gidan nan ne ?
Ban dade da shigowa ba don a hanya sallah ta riskeni ma mun gaisa na nufi bakin mirro dina na dan gyara muka fito tare da ita zuwa dakin hjyn don dubata.
Da sallama muka shigo dakin mun samesu a zaune dukan su har hjyn dake saman gadon dakin zaune gaida ita nayi tare da tambayan ta jikin ta.
Da sauki kawai ta bani amsa tare da fadin naga har lokaci yana shigewa baki zo kin ban maganin ba.
Sai na dauka wanan dan tsantsamin da kuka yi da samira ne yasakaki bacin rai har kikaki zuwa ki ban da mamaki na juyo a inda nake tsaye nace waye samira hjy don ni harga Allah ba wai na rike sunan ta bane hakana.
Nafisa ce a hasale take fadin kishiyar ki mana wanan yar iskan mai rainin wayau tana ganin kamar tafi kowa zata iya taka kowa duk lokacin da taso.
Salma ce ta tambaya da fadin anyi wani abinne kuma da ita a gidan nan bayan wancan sai mama Asabe ta amsa da fadin ai ita fitinan ta basai da wani dalili ba.
Kawai wai don me aka shanya kayan yara a kusa da bangaren ta shine fadan data shigo nan tanayi da yar uwa dazun.
Dake fatima take fadan hakan kodawa lalaima wanan ta samu wuri da yawa ni na rasa gane mai yaya ke jira har yanzu da ita bai sallame ta ba.
Salma ke nan da wani magana ina zai sallame ta tunda Alh yana son yaga iyakata da sune a yanzu.
Na fahinci komai Alh ne ya hana su daukan wani mataki akan abinda sukai min don kawai yaga iyakata dasu kawai.
Wa yan nan ai ba abin a barsu bane don wani dalili na kawu kisan kai fa suka tashi yi a nan badon Allah ya gyara abin ba .
Nan dai na shiga masu bayanin halin da hjy take ciki duk hankalin su ya tashi sosai nake fadin wanan likitan yaso ya cuta mata da wanan maganun da yake mata amfani dashi don bashi ya kamata ace tasha ba tun faruwan abin.
Mama Asabe ke fadin ai mun gode da zuwan ki don tun randa kuka sauka kasan nan muke samun barci da dare sabanin da can da muke kwana a zaune don zafin ciwon.
A ikon Allah wai yau Fatima ce tasan wanan aikin haka mama har kina fada lokacin data fara karatun nan kan baki yarda da hakan ba.
Ai karatun yana da amfani sosai musanman na diya mace yanzu wanan dawai niyar haka ai sai mace yar uwarka zata taimaka mata.
Ni dai har na gama na fita daga dakin dauke da dan salma da take goyo a lokacin ban kuma ji hjy tayi wani magana ba kuma.
Yaya bai dawo gida ba sai bayan sallah isha,i suka shigo gidan dashi da habbib dakin mahaifiyar su suka fara shiga suka duba jikin ta tare da dan zaunawa da yan uwan su suna dan hiran ciwon uwar tasu.
A lokacin Nafisa ta sako zancen abinda ta samu samira tanayi muna a gidan wanda banso hakan ba don matakin da nake son dauka a kanta lokacin.
Saboda na kula ba a part din ta ake girki ba gaba daya ake girkawa a part din mu akai mata tun bayan zuwan yaya garin ta hana mai aikinta yin girki taba masu aikin umurnin su girka su kai mata nata a can idan sunyi.
Duk da ran yaya ya baci dajin haka sai bai yarda ya nuna bacin ranshi a gurin ba ya hade abin a ranshi yana jin daci a zuciyar shi.
Tun da yamma na ba masu aiki umurnin kada su kara girka komai da samira a part dina da duk wani aiki da zata umurta suyi mata shi na hana ta ba shuganan su umurnin hakan.
Koda yaya ya shigo bai nuna min komai ba har yayi wanka ya fito suka zauna cin abinci dashi da habbib na fito ina gaida habbib din tare da tambayan shi iyalin shi .
Yace ai suna gari tare dasu ya shigo dazun dan washe baki nayi ina fadin ashe zamu hadu dasu wanan karon ma ke nan.
May ya hadaki da wanan yarinyar har ta shigo nan fada dake zahra yaya ya tambayeni cikin katse mu ga maganan da muke da yaya habbib a lokacin.
Wace yarinya ke nan na tambaye shi ina kallon fuskan shi da mamaki sai ya habbib ne yace samira yake nufi man.
Fuska na daure don jin hakan tare da kawar da kaina gefe ina fadin ina ruwana da tsabganta kawai dai tazo tana karanta min hauka a nan ne dazun.
Ya kara tambaya a kan me tazo fada nan din saboda an shanya kayan yara wurin bangareta da maria tayi wanki da safe.
Wanan akwai yar iska tana ganin har ta samu wurin yin hakan ga yayan mu kome habbib ya fada a hasale .
Abinci naga yaya ya fara zubawa kamar bai damu da zancen ba a lokacun hakane ya ban haushi na mike zuwa dakin yarana na barsu a gurin zaune.
Adduan kwanciya nayi masu kafin na juya zuwa dakina na fara kimtsawa don in kwanta sai dai tunawa da ban ba hjy magani ba yasa ni fita lokacin.
Yana zaune dakin wanan karon na samu su salma sun tafi ita da nafisa gida gaidasu nayi har lokacin babu walwala a tare dani.
Hjy magani za a sha nace da ita bayan na nufi wurin maganin kai tsaye ba tare da najira cewan ta ba na fara ballan maganin ina hada mata don tasha.
Har na gama bata maganin ban yi magana ba a dakin nayi masu saida safe na fito zuwa dakina kwanciya nayi don banda ra,ayin zuwa wurin shi ranan.
Can barci ya fara daukana naji shigowan shi dakin tare da kunna wutan dakin ya gauraye da haske lokaci guda.
Takowa yayi zuwa bakin gadon da nake kwance ga yarana sultana da Abbana sai Fauziya da muke kwana tare wani lokaci yauma a dakin ta kwanta.
Tashi muje daki ya fada a daidai lokacinda yazo ya tsaya a kaina ya fada yana mai tsareni da idanuwan shi.
Na dauka ai wacan mai fada a kan ka dani ce zata kwana dakai yau din na fada ciki ciki dan murmushin iya fuska kawai yayi yana fadin mene ?
Shiru nayi mai ban kara magana ba ina gyara kwanciyana ki tashi mu tafi idan zata kwana tare dani ai ba sai kin sani ba don da baki ganni nan ba yanzu yana fadin haka ya juya ya fice daga dakin.
Na

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login