Showing 165001 words to 168000 words out of 419207 words

Chapter 56 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1450

mai nakewa ihu haka don su basu masan manjo bata gidan ba a lokacin.
Wani ihun na kara karde hidan dashi da kubura saratu da mama saude suka nufo dakin da gudu don ganin abinda ke wakana da ni a cikin dakin.
Ni dayace a dakin an wani murdeni a lankwsa ni kamar ruboce jikina idanuwana sun wani firfito ga baki daya a lokaci guda.
Innalillahi mama saude ke fadi tare da tambayan ina tsohuwa ta fita ne ko mai ina babba ta shiga ko tana bandaki ne ?
Tana tambaya a kidime hankali tashe babu mai bata amsa don duk su kubura sun dare daga kofan dakin .
Ta juya zuwa bandakin manjo bata ciki haka yasa ta fita a gigice zuwa hanyan kofar gida hankali tashe sukaci karo da manjo da ta dawo dauke da leda maganin da aka hado mata chemist.
Ganin mama saude a kidime yasa manjo tambayan ta ko lafiya mama saude tace babba ba lafiya tafi ce a cikin wani yanayi a daki.
Wani itin rikicewa manjo tayi habkali a tashe suka shigo gidan tare kamar ba itace mai jan kafa ba na ciwo lokacin.
Ga su kubura da saratu cirko cirko da sauran yaran gidan nesa da kofa manjo din dun tsaya.
A ruwa, ke Aruwa lafiya ta fada dakin ganin yanayin da nake ciki yasata kara rikicewa tace ayi maza a kira mata baffana don Allah kada yar mutane ta mutu mata a daki ba a san sanadi ba.
Ganin kamar baffa zai dade baizo ba tace mama saude ta kira mata umma Atika da sauri a gidan su ta tafi don hankalin kowa ya tashi gidan .
Sai umma lami da bata gida itace bata san abinda akeyi ba gida tare da umma da Atika da wata bakuwa da sukayi suka shigo cikin tashin hankalin labarin da mama saude taje masu dashi din nawa.
Wanan karon ina wani abu ne kamar na kutare abar bankare ni din sai kuma abin kutare nake zaka rantse da Allah wata tsohuwar kuturawa ce ni.
Can kuma na juya ina wani marmar da idanuwa kamar wata yar bariki ina wani kwalliya da sauran su bakuwar tace wanan iskace gare ta haka dama ?
Iska kuma yaushe ta samay shi hakan ban sani ba don dai uwarta bata fada min ba gaskiya manjo ke fadi.
Matar tace kuban tsaba idan akwai mama saude tace babu tsaba agidan gaskiya sai umman Atika tace Atika tai maza ta debo gyaro a gidan su.
Bata jima ba sai gata ta dawo da gyaron matar ta fara surkule tana fadin kuke ganin mu bamu ganin ku kuyi hakkuri ku tausaya wa wanan boyar Allah ta huta hakana don Allah.
Abindata saka a baki ta tauna shita furza min a kai har sau uku ta juya tana fa????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? din kunyi ajiyan komai da ruwan ka ko hantiti gidan nan ?
Mama saude tace sai dai babba itace mai yawan sayen sa don kafanta manjo ba baki sai da hannu ta nuna inda yake imani ya kashe ta.
Dauko mu shaka mata da yardan Allah zasu sauka daga kanta insha Allah wanan iskan baya zuwa haka babu dalili dole akwai dai wata a kasa don manyan iska ne a kanta gaskiya.
Kaina ta daga ta shaka min hantitin a cikin hancina wani irin atishawa na sauke lokaci daya tana shaka min komai da ruka din a hanci na.
Sau uku ina sauke atishawa mai karfi kowa ya fara fadin alhamdullahi sun sauka wai sannu fatima ikon Allah wai dama yar nan tana da wa yan nan mutanen a kantane haka ko dai yanzu ta samay su ?
Umman Atika ce ke tambaya manjo da tayi mutuwan zaune bata iya bata amsa a da baki ba sai kai ta kada mata don imani ya kashe ta lokaci guda.
Suka fara jera min sannu ban amsa ba sai can kuma na fashe da wani irun kuka mai cin rai da ban tausayi .
Sunyi kira sunyi kira ban amsa ba sai matar tace wani ne yazo kuma nake gani basu gama takawa a kanta ba ke nan .
Matar tace idan da alheri kuka zo muna maraba daku don Allah kuyi magana musan abinda kuke so ?
Babu amsa har lokacin sai da ta kara fadin fatima kila sun sauka ne wani murya kamar na kato yace ba fatima bace mune .
Ba fatima bace kaine wa sai na ci gaba da kukan tana ta roko maishi yayi magana sai can akace ina ina wanan baiyuyuwa.
Muna kallo a cutawa jinjiran mu daga zuwa zumunci sai kuce zaku cuta mata yau akwai kaniya a gidan nan kaniya kaniya.
Subbahanallahi don Allah kuyi hakkuri ku fadi may kuke so ai maku ku tafi sukace bamu tafiya don tabamu akayi mun dade akan jinjiran mu bamu cuta bamu cutarwa amma ake son halaka muna jinjiran mu.
Ikon Allah manjo tace kun dade kuna tare da ita ya kada kai yana fadin duk inda take muna biye da godiyar mu mu ba masu fitina bane amma yau an taba mu an taba mu.
Haka kawai sai bakina ya dauke kuma dip ba magana ko kadan sai na fara abin kuramay salati umma Atika ta saka tana fadin kurma ke nan yazo kuma ?
A daidai lokacin ne bafa ya shigo a cikin tashin hankali ya samu abinda ke faruwa salati ya fara tambaya yaushe na samu wanan laluran haka ?
Yau dai muka ga wanan laluran gare ta manjo ta bashi amsa sai bayani nakewa matar nan tana bada amsa don da gani ita tasan halin iska can dama.
Ta juya tana masu bayani tana fadin abin da kurma ke fadin yau suna da fada a gidan nan don an daukowa jinjiran su mugun abu.
Matar tana fassara masu abinda kurman ke fadi tana fassara masu abinda yake fadi din hankali tashe.
Manjo tace ni hauwa,u wake bin yar marainiyar Allah nan da mugun nufi haka a rayuwan ta ?
May wanan yarinyar tamai wani har ta tsune masa ido sallaman umma lami data dawo zufa zufa gidan daga unguwa ganin yamma yayi ta dawo kafin ta laga na dare ta fita.
Kamar an tsikare ni na mike zubur na nufi waje ina tafiya kamar gurguwa sai wurin umma nako shake ta take diyan ta su hashim da su kubura suka hau bambarana har baffa sai dai sun kasa kwatar ta daga shakan da nayi mata din.
Gida ya rude da ihu da kuruwan neman agaji da kyat da boni ta samu kanta tana hakin ceton numfashin ta.
Har lokacin ba baki a gare ni sai kwatance a gareni kawai nake iya masu ina nuna ledan baka mai kauri data shigo gidan dashi a hannun ta.
Nan hayaniya ya tashi wasu na fadin tunda na dage ina nuna ledan dole akwai abinda ke cikin ledan ke nan ga umma duk shakan data sha taki sake ledan hannun nata.
Sai da kyat aka kwaci ledan tana wiki wiki da idanuwanta tare da fadin sheri zaki mun daga dswowana ban san hawa ban san sauka ba ki kulla min sheri ?
Sai da naga ana bude ledan na kuta sai gani kasa suuuu na fadi a cikin kasa kwalliyan da nayi duk ya baci wurin turmuzan dana sha.
Da sauri du umman Atika sukayo kaina hankali tashe yayin da baffa da manjo suka tsare ledan da ake budewa da kallon babu komai ciki sai wani abu da aka soke da allura da sauran tarkace itin na surukulle.
Fatima fatima umman su Atika ke kiran sunana na amsa a wahalce kin ganeni umma tace na gyada mata kai to wacece ni na sake kallon ta nace ummace tace sannu.
Na amsa mata suna fadin sun sauka sai sukaji na fashe da wani ihun kuma na tashin hankali nan kuma akayo kaina cikin tashin hankali.
Kamar bebiya nake fadin ba zamu yarda ba sai mun dauki famsa kan macutan godiyan mu kuyi hakkuri tunda kun baiyana komai don Allah ku sauka haka ku bar godiyan ku ta huta.
Ranan dai na sha wahala sosai kafin su sauka nayi barci sosai ban falkaba sai dare mutanen unguwa dama gari sun ji labarin komai daya faru gashi washe gari zan koma idan Allah ya kaimu.
Washe gari haka na tashi jikina ko ina yayi min tsami babu dadi ga kayana ko karasa shiryasu ban yi ba.
Ban iya tashi inyi komai sai manjo ne da Atika suke dan hada mun kayan ina kwance har suka karasa baffa bai fita ba don hankalin shi bai kwanta ba.
Ya shigo dakin ganin shi na yunkura zan tashi yace kwanta abinki gurin babba nazo muyi magana jin haka sai Atika tayi saurin ficewa a dakin.
Daga kofa ya samu wuri ya tsugunna ya sake duban inda nake yana fadin Fatima yaya jikin naki nace da sauki baffa yace zaki ko iya tafiya yau din kamar yadda sukace za a zo a daukeki ?
Zata iya idan ma ba zata iyaba sai mu tafi tare mu ratse mu dauki Adda mu kaita gida muyi masu bayani don ba zamu saketa haka a cikin wanan yanayin ta tafi ita kadai ba.
Ganin Atika ta fita dakin na mike da kyat nabi bayan ta a waje na samay ta zaune na zauna a gurin muna dan hira.
Baffa yace Nima hakan na gani babba tunda dama ga wanan zancen da bamu san ya ake ciki ba ranan jumma,a nima zan shigo kamar yadda nayi masu alkawari zamu zo din nidasu sha,ibu da sauran yan uwa.
Ina ga in zai yuyu da sai ku tafi koda lami ne ko kukai ku uku ke nan kunga a nata bangaren dai anga yan uwa aiko .
Da naso bayan tafiyan tunda yabar kudin motar zuwan ku din a dauki mota wasu mata suje ranan.
Yanzu ma wanan abin zai faru ga wanan al,amarin dayazowa yarinyar nan haka kuma zai yuyu mana wanan ba lalura bane babba taba su akayi shiyasa suka tashi da waya santa dashi.
Amma dai kuma sai naga idan kun bita da yawa kamar zaku bata masu shirin su don ba hakan aka tsara ba da farko.
Amma dai sai yadda kika gani babba tace maganan ka gaskiya ne kawai mu barta ta tafi din Allah zai kare a duk inda take ai manjo tace.
Karshe dai suka aje shawaran abinda zaifi zuwa rana ko sai ga driver yazo har lokacin bamuyi arba da umma lami ba .
Dana shirya zan tafi na shigo har part din su na sallamay su da kyat ta leko mukai sallama ta koma.
Na samu rakiyan yan uguwa da sauran mutane haka motar ya daga raina babu dadi na rabuwa da yan uwa da nayi ko kadan.
Bamu shiga kano ba sai gab da za a fara magariba ina takure a bayan mota ni kadai daga misau zuwa kano ina fada da zazzabi mai karfi a jikina.
Haka muka iso gida babu kowa waje har ya shiga min da kayana part din mu mamu na zaune a falo cikin damuwan rashin isowan mu taga na shigo.
Sai dai yanayi na bata babu lafiya don yadda na shigo falin ina gaida ita cikin makyarkyata na samu dogon kujera na haye na dunkule a wuri daya.
Ikon Allah ba lafiya ne kuma a hanya zazzabi ya kamaki ko tun can ne ban iya magana ba tace bari zo sai wayan ta yai kara tana dauka naji tana fadin sun iso yanzu sai dai gata tadowa ba lafiya kuma.
Nasan da kawu take wayan yana tambaya ko mun dawo a lokacin shine ta fada mai mun dawo din.
Sai bayan an sallamay sallah kawu ya shigo part din kai tsaye yana fadin fatima ba lafiya kuma kika biyo hanya hakana ai da sun barki har kiji sauki.
Mamu tace ina ganin dai a hanya ta kamu da masasaran kila don ba zasu barta ta taso haka ba ki shirya zan turo wani ku tafi asibiti.
Da sauri na dago kai nace kawu a bani magani kawai naji sauki murmushi yayi mamu tace kasanta da tsoron asibiti ruwan ki aike ke wahala a jikin ki ba wani ba.
Bamu dai je asibitin ba tasamun ruwa masu zafi nayi wanka asha tea mai zafi da magani sai na kwanta.
Koda su Amma suka shigo dubana duk nayi barci mai nauyi a lokacin ban san shigowan su dakin ba ma.
Washegari na tashi jikin nawa da dama ya rage min ciwon da nake ji ina son fadawa mamu abinda ya samay ni ina jin tsoron fadamata.
Don ban san halin da zata shiga ba idan taji yasa na kyale na bar maganan a cikina ban fadawa ko Amma da take abokiyar hirana ba.
Na dan daure naje part di Amma don na rage yawan tunanen da nakeyi din a raina muna falon duk dasu Aisha sai hira sukeyi ban saka baki na.
Ga hiran su Aisha tace lalai wata tana kewan gida dan murmushi nayi ban kullata ba sai murja tace wai baki san yadda muka matsu kidawo bane halan .
Yi nayi kamar ban jita ba saida ta dan zungure ni Amma tace kyaleta ai tana jinki tunda ta dawo take da wanan miskilancin haka ko kuma ciwon ne ya sakata haka oho ?
Kamar daga sama naga mutum yayi sallama falon Amma din ya shigo duk sai na tsargu don ban san da zuwan shi ba sai ganin sa nayi yanzu ya shigo.
Gaishe mukeyi kamar bai son amsawa ya dan tsaya hakan yasa muka mike don barin falin mu barshi da Amma.
Hanyar fita na nufa Amma tace tafiya zakiyi kuma bayan baki dade da shigowa ba nace a shagwabe Amma zanje in kwanta ne kaina naji ya fara min ciwo yanzu na juya na suce ba tare dana jira inji abinda zatace ba.
Kasan gida akwai dadi tun jiya data dawo mun rasa gane kanta a gidan nan har yanzu yi yayi kamar bai jita ba tace sadauki anya kuwa zaka iya rike wanan Amanan kuwa ?
Ya dago kai yace Amma kina magana ne tayi mai dakuwa da hannu tana fadin miskilin banza ai kunyi daidai da ita don yanzu tagamauna miskilanci wuri nan


Kuyi hakkuri wallahi duk kwanakin nan banajin dadin jikinane


ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:12 - ??5惙5惙5?: DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN KAI GODIYA DA YABO YA TABBATA GA ALLAH SARKIN BAIWA DA RAHAMAN SA UBANGIJI MUNA ROKON KA KA SADA MU DA RAHAMOMIN DAKE CIKIN WANAN GOMAN JUL, HAJJIN AMIN ???a


Kawu ne zaune a falon shi tare da yaran shi a daren jumma,a kallo daya zakaiwa kowansu kagane halin tashin hankalin da suke ciki lokacin.
Kowa yakasa magana baya sj fahinci dalili kiran da mahaifin nasu yayi masu sai zufa ke ketowa ko wani su a lokacin .
Umar ne yayi karfin halin yin magana a cikin su yace to daddy don wanan ai kowan mu yasan da zancen nan cikin mu.
Dama ka fada muna tun can a waya da sai a turowa mama da kudi ayi duk wani abinda ya kamata ayi .
Cikin farin ciki kawu ya kalli dan nasa yace Allah yayi maku albarka dama nasan ba zaku taba kinyatani a duniya ba .
Gaban habbib ya yafadi dake shirin fadln daddy nifa ban shirya ba sai yaji umar ya ari baki su yaba mahaifin su aamsa da fadin sun amince yana saka masu albarka da godiya tare da yaba masu.
Idan ranshi yayi dubu ya baci a lokacin hakan yasa ya kasa daurewa a ranshi ya dago fuskan shi daya gama nuna tashin hankali a ciki yana masu wani irin kallo.
Kawu yace yaya habbibu ko baka shirya hakan bane kai a wurin ka yace cikin sunkuyar da kai a,a daddy gani nayi dai baka sanar damu zancen da wuri ba sai yanzu muke ji.
Alh yace na isar maku ne yasa hakan sanan kuma daura aure a yanzu ba yana nufin tarewan su bane ranan sai nan da zuwa satin sama mai zuwa kaga zuwa lokacin aika gama wani shirin da duk zakayi.
Umar da takaici ya gama cikawa babu halin nunawa yace sai dai daddy ina ga ni ba zan kai wanan lokacin ba a kasan nan don ina da aikin da zamuyi a hong kong idan na koma.
Alh yace ai shike nan tunda an daura aure zaka iya tafiya da matar ka dama shine wajibin aure ai wanan ba wani matsala bane mai girma.
Takaici da badaman fadin haka ya rufe mai zuciya yace a fili shike nan daddy yadda kace haka za ayi.
Sai Alh yace saidai ina kara rokon wani alfarma a gurin ku don Allah don gujewa rigimar uwar ku kan hakan ina son ku rufe wanan maganan don Allah ba dan niba sai an

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login