Showing 399001 words to 402000 words out of 419207 words

Chapter 134 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1413

dade wurin kwance kamar ba zan tafi dakin ba can dai dole na mike na same shi a dakin bai kwanta ba koda na shigo yana zaune da wayan shi a hannun shi sai dai har ya gama wayan ban iya fahintar maganan da yakeyi ba a lokacin.
Wuri na samu na kwanta kafin inji hannun shi saman jikina ban hanashi komai ba saidai bai samu taimako daga bangarena ba har ya gama abinda yake dani.
Washe gari bayan munyi sallah muka kwanta bamu fito da wuri ba don na fahinci yau hutu yake ba inda zai tafi ke nan .
Don tun zuwanmu kasan ba zance naga ya yini tare damu ba ko yaushe yana zirga zirgan harkan business din shi zuwa wurare daban daban don zuwan nawa ya taimaka mashi sosai ta fanin hjyn shi da sauran abubuwa.
Can cikin barci nake jiyo muryan Samira a kofan dakin tana masifa wanda ni na manta da dokan dana ba masu aiki a kanta.
Ta turo mai aikin ta karban abinci su kace madam ta basu umurnin kada su kara saka mata abincin ko wani aiki shine dalilun wanan ashar din da take dura min da farar safiyan nan haka.
Yun kurawa nayi da niyar tashi in fita don in same ta in bata amsa sai naji yaya ya rikeni daga inda yake kwance yana fadin ina zakije kuma ?
Dan jiyowa nayi na kalleshi ina fadin wurin wanan mara hankalin kada ta firgita min yara da safen nan kuma don duk sun tsorata da fitinan ta tun zuwan mu garin nan.
Is Over ki kyaleta kawai tayi haushinta ta gaji ta tafi idan kin fita abin ba zai kare ba kuma yanzu yace.
Amma dai yaya kana jin irin kalamin da take fada min marasa dadi haka da safen nan yace nace ki barta ko bakiji bane wai.
Hakan yasa na koma na kwanta na lafe ban tashi ba sai shi da yaji hayaniyar yayi yawa ne ya fita daga dakin ina kallon shi.
Tana tsaye a tsakiyan falon sai masifa takeyi ido rufe jin kara bude kofan ne yasa ta juyowa tana fuskantar kofan.
Jallabiya ce fara a jikin shi sai takalman daya zura a kafafun shi ya fito fuska daure yake kare mata kallo a cikin tsana.
Itama kallon shi takeyi sai taji dan nauyin ci gaba da masifan da takeyi din tana fadin ashe kana cikima dama wurin ku nazo don matarka ta hana wai a ban abinci dayi min aiki shine nazo jin dalilin hakan.
Ke dakata idan ta bada dokan hakan laifi ne ko kin manta cewa nan din gidan tane ita da yayan ta tana da ikon yin komai da taso da kowa.
Don haka ki bace min daga nan tun baki hadu da bacin raina ba a yanzu mara hankali kawai zaki shigowa mutane da sassafen nan kina karanto muna hauka .
Ban gane abinda hakan ke nufi ba ke nan nidin may ye matsayina kake nufi a gidan nan yanzu.
Zaki iya shiga ki tambayi wace ta kawo ki gidan ai tana cikin gidan nan ko yanzu kuma don kinyi mata rashin mutuncin alakan hakan ya yanke a tsakanin kune kuma .
Kofan fita ya kara nuna mata yana fadin ki fita tun kan ranki yafi nan baci a gidan nan yanzu.
Ganin da tayi babu wasa ko kadan a fuskanshi yasa ta juya ta bar dakin da sauri dan saura kiris hawayen da take boyewa ya zubo mata a wurin.
Na shiga uku take fadi a ranta har hannun ta na rawa wurin daukan wayan ta ta kira mahaifiyar ta da sauri take kira tayi sa, a ta daga wayan.
Samira me kuma ya faru da safen nan yanzu kuma umma wallahi yau mutumin nan ya gama dani a gaban kowa a gidan nan.
Gaban kowa fa ya fada min maganganu masu zafi har yake fadin wai zaman mahaifiyar shi nake gata nan daki inje in tambaye ta.
Gida na matar shine da yaran ta don haka tana da iko akan komai dake gidan bani ba.
Ke nan umma may yake nufin da wanan maganan nasa yanzu yana nufin dama zaman wanan matar ke nan nakeyi a gidan ba nasa b, , ,
Samira ki natsu ki min bayanin komai yadda zan fahinta kina hada min magana cikin magana bana ganewa.
Umma abinda ya faru ke nan nake fada maki ni wanan abin gaskiya a yanzu ya fara isata gaskiya.
Ke gani nan zuwa yanzu tunda yana gidan sai da muka kashe duk abinda ke gare mu zaki wani ce wai kin fara sarewa da zancen haka.
Dakin ya shigo lokacin har na mike zaune ina sauraren abinda suke fadi daga falon jin shigowan shi yasa na mike tsaye ina kokarin saka hijjab dina a jiki.
Ina kuma zaki tafi yanzu yaran basu falka ba don babu kowa a waje a cikin su har maria ya fada.
Zan duba hjy ne kada taga yau ban lekota ba har lokacin nan lokacin shan magabin ta ya dan gwauta kadan na bashi amsa ina fita daga dakin.
Bina yayi da kallo har na bace mai da gani ya sauke ajiyan zuciya tare da girgiza kan shi don yana ganin wautana kan abinda baikai na fushi ba na dauki zafi dashi haka.
Kai ya kara girgizawa yana kokarin cire rigan jikin shi don shiga ban daki ya watsa ruwa a jikin shi ya fito zuwa duba jikin mahaifiyar su.
Ban shiga wurin hjyn ba saida nayi wanka na gyara jikina tsab na fito inda kusan lokaci daya muka shiga don banbdade a ciki ba shima ya shigo suna gaisawa tare da tambayan yadda take jin jikin nata yanzu.
Hjy bata kai ga bashi amsa ba muryan hjy sabuwa ya katsesu tana fadin ina mara kunyar yake yana ganin yanzu yafi karfin mutane don ya samu daurin gindi a wurin iyayyen shi yasa kake son taka kowa yadda kakeso.
Har kan wanan yarinyar kake kokarin wullakanta yar uwan ka ka fifita agaolan gidan ku da aka cinna maku da sunan mowan gidan ka komay ?
Hjy kin ban mamaki kina gidan nan har umar ya tsaya yana fadin wanan magana ga yar uwan shi baki kwabe shi ba tana fada ra sawo kai dakin sai taja ta tsaya don ganin mu da tayi a dakin don bata zaci hakan ba a lokacin.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
17/11/2021, 07:23 - ??5惙5惙5?: Shiru dakin yayi ana sauraron abinda hjy sabuwa da ta fado dakin babu ko sallama take fadin magana iya son ranta.
Babu wanda yai mata magana daga cikin wa yanda ta sama a dakin ita da kanta taji nauyi da kunyan kanta lokaci guda sai kuma ta fara dan kame kamen zancen.
Ina gida yanzu wanan yar ta kirani take sheda min wai umar ya ci mata mutunci tunda safen nan akan matar shi.
Shine ya mike tsam daga inda yake zaune ya nufi hanyar fita daga dakin ba tare da yama tsaya sun gaisa da ita ba.
Fita zakayi ne mama Asabe take tambayan shi bai juyo ba yake bata amsa da fadin ina da abin yi ne yanzu.
Amma kasan wurin ka nazo aiko don kaji abinda ya kawo ni gidan nan yanzu ai.
Juyowa yayi da mamaki a fuskanshi yake fadin wai dani kike magana hjy ?
Itama kallon mamaki take mai don babu alaman wasa ko girmamawa a gareta ko kadan a fuskan shi.
Eh matar kace takai karan ka gareni nazo jin dalilin faruwan hakan don zancen mata ba a san namiji da daukan bangare daya ba.
Har kana fadin wani zance dani kaina na kasa fahintar may hakan ke nufi a zuciyana.
Matata fa kika ce hjy ki dai ce yarki dake zama a gidan nan ko zaifi sauki matata kan ai ga daya nan a gaban ki yanzu kina ganin ta.
Ke zahra ko kece kika kai kara a wurin tane don ban fahinci zancen nata ba har yanzu gaskiya.
Eh lalai kana da gaskiyan ka don ba laifin ka bane idan kayi hakan a yanzu saboda alama ya nuna baka cikin hayacin ka gaskiya.
Zaki iya fadin hakan tunda yarki na son ta lalata min gida da fitina don kawai taga tana cin albarkacin wani a wurina.
Saidai ina son ki fada mata cewa zaman ta a gidan nan yana gab da karewa idan bata fita harkan iyalina ba.
Don ba zan lamunci a wullakanta min matana da yayana ba ko kadan a zauna lafiya ko yanzu taci albarkacin mahaifiyata ce da take zama gidan nan donta.
Koda yake ku din baku sanda hakan ba tunda ko ita sin bataci ragowa a wurin ku ba sai kokarin nakasa muna ita da kukeyi ba dan Allah ya gyara zancen ba.
Jummai kina jin abinda danki ke fada mi a gaban ki baki yi yunkurin hana shi fada min wanan maganganun da yake fada min ba.
Ashe taimako yana iya komawa tsiya kefa da kanki kika bukaci hada wanan alakan don a ceto maki danki daga hannun wanan matar tasa da kika tsana.
Sai haihuwan da take zubawa a gidan don ta mallake dukiyan shi ita da uwarta da wasu can daban da baki son hakan ya faru dashi.
Ashe kin san bakifi karfin daki bama tukun balle matar tashi da alama ya nuna duk ta gama dake da diyan nakima.
Ai ashe don ni kika dauko yarki kika kawo ta gidan nan ban sani ba don ni bansan ma da wata aba bacan dana nazo wai matar mijina don banga alaman hakan ba a gidan.
Ke fitsarara kada ki soma kawo min rashin kunyar ki da ake fadan kina dashi nan don gida kika sama na rashin mutunci.
Sabuwa dama kece daidai dani ba yarki ba don haka yanzu ki kauda yarki kizo ki share daki mu zauna dake sai mu kara ina ganin haka zai fi don kece daidai dani wurin daukan fansa ba lusarar yar nan da kika aje muna a gida ba kamar ba mace ba don ko gaba na mata bata dashi.
Kutumar uban nan har iskancin naki yakai ki kalli tsaba idona ki fada min haka kwarai kuwa tunda ke baki ji kunyar fada mi magana irin haka a gabana ba.
Aiko ta kara tasowa tana kokarin kaiwa gareni da sauri yaya yace hjy muddin hannun ki ya kai a jikin matana wallahi sai na daure ki a garin nan karyan masifa kikeyi ana kyaleki ne dama.
Muryan hjyn su yayane data fashe da wani irin kuka lokaci guda a dakin ya mayar da hankalun kowa a wurinta .
A daidai lokacin samira ta fado dakin tana fadin wallahi babu mai wullakanta min uwa ya zauna lafiya a cikin ku.
Don uwa bata fi uwa ba ehhe ki daina kukan munafunci ki tsaya a gyara zance zaki sakawa mutane kukan munafunci don zancen ya tsaya a, , , ,
Saukan mari da tajine a fuskanta har biyu lokaci guda ya hana ta karasa maganan da take son fada.
Yaya ne da take tsamanin ya bar dakin yaga shigan ta ya dawo a daidai lokacin da take wanan magana ga mahaifiyar su.
Hanyar fita ya nuna mata ita da uwar yace ku fice min daga gida yanzu nan ba sai an jima ba har hjy sabuwa zatai magana ya kara daka mata tsawa saida ta firgice don tsoro.
Mai hakkuri ance ranshi bai iya baci ba don yau kan ko mahaifiyar shi ta sheda hakan don bai ragawa hjy sabuwa ba ko kadan ranan tsaye yayi yana umartan yan aikin shi da su tabbatar basu kara shigo mai gida ba.
Sai kuma ga hjy sabuwa ta zube a kasa tana rokon shi ya rufa mata asiri ya dubi zumuncin su ya bar samira a dakin ta.
Zumunci zumunci fa kika ce hjy ko kin manta ke da bakin ki kika fada babu wani zumunci a tsakanin ku sai na zaman unguwa daya dasu mama.
Yanzu hat zaki kira min wani kalman zumunta a tsakanin mu dama talala na sake maku don inga iya gudun ku saboda albarkacin mahaifiyata da kukaci na bar yarki a gidana tana zama.
Yanzu ko kun kaini bango ta yadda ban kaunar kara ganin kowan ku a gidan nan .
Dama ance yar mace bata taba zama mace ta gari do gashi kin nuna min baki san darajan iyayyen wasu ba balle naki .
Kun duke ta kuna ganin kamar kun daki banza ba wani matakin da za, a iya dauka a kanku do kawai an maku dubaiyan da baku san ana maku ba sai gashi kuma har zaku maimaita hakan a gaba gun matana a yanzu.
Kin dauka idan idon mama ya rufe da abinda kuke dura mata nawa dana yan uwana zai rufene hjy.
Da har zaki dauko yar ki mai ciwo ki kawo min har gidana wai da sunan aure watau duk mu taru mu halaka bayan ta gama halakanta da taimakon ki.
Baki hjy ta bude tare da fadin sheri kuma zakai muna umar don kaga muna rokonka ko may ?
Habbib dake tsaye tare da iyalinshi dana Aliyu yace eh ai dole ki roke shi kan cuta azzaluman mata mun dade da sanin komai kyale ki mukayi muga iya gudun ki gidan nan ai.
Ko kin dauka idanuwan mu muma a rufe yake kamar yadda kuka rufewa mama gaskiyan abinda ke damun yarki taki aurowa a lagos din.
Shine do cuta zaki kwaso sheri ki haro dan uwan mu dashi har gida wai da sunan kin taimaki mahaifiyat mu da yarki.
Hjy dake wani kukan takaici da bakin ciki a zaune ta wani dafe kirji da karfi tana fadin na shiga uku dama yar nan bata da lafiya ashe sabuwa kika rufe min.
Abin nasu kamar hadin baki don sai jin muryan yan uwan haihuwan hjyn su yaya mukayi suna fadin dama ai saida muka fada maki bakiji ba hjy a lokacin .
Yanzu ba don Allah ya gyara ba da kin cuci zurian ki da kanki anty wanan maganan nake fada maki a kullun kuke gabin zafina a cikin mu.
Akan wani ra,ayi naki can na banza zaki cutar da rayuwan yaran nan ki halaka mashi zuria irin wanan ranan ake gudu dama ranan nadama ga bawa.
Godiya mu ga Allah a kullun da yake kawo muna dauki akan komai kafin wani abin ki yakai ga samun mu.
Yanzu gashi kin biyewa hjy sabuwa har auren ki na shekara da shekaru yakai ga samun tangarda wanan son zuciya dame yai kama haka don Allah ?
Gida duk ya kidime da yayan mutane shikan yaya yana gama magana da hjy sabuwa tun lokacin ya juya ya shiga part din shi ya rufo.
Haka nima naja kafa zuwa part din mu yarana na samu zaune a falon maria ta hadesu a guri daya suna kallo.
Zama nayi a cikin su a daidai lokacin da su Aisha da Rukkaiya suka karaso ina masu sannu da zuwa.
A cikin alaman mamaki suka karba min tare da fadin wanan abin mamakin dame yai kama hakane wai ?
Rukkaiya tace mu dai gamu muda ba,a so din dai mune na kwarai a yanzu ai don da bakin suke magana akan irin taimakon da kike mata a yanzu .
Koma dai meye ai naka sai naka ba don Allah ya gyara yaya yana da natsuwa ba da yanzu ya dade da kwasan wanan cutar ko tunda auren nasu ai yakai wata biyu ko uku yanzu tana gidan nan zaune.
Wana ma wani iri rashin zuciyane ace mutum ya nace kan abu idan ba yasan cutar da yake son yi ba a gurin.
Ni wanan zancen ma gaba daya duk ya kashe min jiki wallahi wai mutane mai yasa basu da imani ne yanzu Aisha ke fadi.
Sai yanzu nai magana tun zaman su wurin ina fadin rayuwa haka take zuwa da kalubali mai tarin yawa ga bawa sai idan Allah kareshi a cikin ikon shi sai ya kawo mashi komai da sauki .
Abinda hjy take nuna min da farko ne nake jin zafin hakan amma yanzu na daina rikon abin a raina ko kadan don dai jini ya riga da ya gauraye da ruwa.
Don ko yanzu na bar gidan nan sunana ba zai taba kankaruwa a cikin zurian dakin hjy ba dole sai ance nice uwar yaran nan jikokin ta.
Kwarai kuwa Rukaiya tace dole ne kan a fadi hakan dan ma hjy ta godewa Allah rabon yaran nan bai kasheta ba yara kusan nawa ta nuna bata kaunar auren iyayyen su da diyanta.
Allah ya riga daya tsago sai zurian dakin ta sun fito daga jikin mu ai dan ni kiri kiri hjy ta kira sunan uwana ta hada dana ubana ta zagesu tas

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login