Showing 111001 words to 114000 words out of 419207 words

Chapter 38 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1415

suna cin abincin rana nace Aisha zakije shagon linda wurin kitso ?
Tace yau kuma kin tuna da linda ne zaki wurun ta ?
Nace ban san may ya samu mamun mu ba yau na tashi na ganta a cikin bacin rai da nace tayi min koke ki min sai ta hauni da fada wai inje can ta kwashe min kai.
Amma dake zaune tana jin mu ta tabe baki tace mai ko ya samay ta banda halin nasu sukayi yau muna nan naji fada ya kaure a gidan.
Ashe munafukan nan ce maryam ta samu jummai da tsegumin taga sadauki zai shiga gurin maimuna.
Ita ko da bata da tunane sai ta taso da fada tunda bata girma hankali bai zo mata na tunanen may ya kaishi can ba.
Aisha tace kai maman su ikilima ita ko kunyan munafunci batayi may ye a cikin wanan halin don Allah ?
Nace ita mamu bata rabuwa mata da diya a zauna lafiya tunda tana da yaranta itama Ammace ta katse ni da fadin.
Don may zata rabu da dan dan uwanta akan wani dalili mara tushe can idan ta rabasu yanzu zata rabasu nan gaba ne da yake shirin zama surikin ta ?
Aisha tace suriki kuma Amma tace wayan gobe banda Allah abu suke basu tunanen gaba dan tsaban kishin tsiya.
Ni dai ban damu da zancen Amma ba don raina a bace yake ga halin da na ji ya batawa mamu rai har take son sauke haushi a kaina ga banza.

Hjy jummai ne a falonta tana zuwa tana dawowa ranta a bace kallo daya zakai mata ka fahinci halinda take ciki na bacin ran.
Su Aliyu dake zaune suna karyawa a lokacin don da dare sosao suka iso kano daga Abuja sunje can cika wasu takardu nasu ya dan kalli uwar yana fadin mama yau ko lafiya ?
Ta juyo gare shi fuska daure tace kira min yayan ku.
Yace to ya dauko wayan shi dake gefe ya shiga neman layin yayan nasu kira biyu ya dauka yana fadin Aliya ya akayi ne ?
Bros mamace ke son magana da kai yace lafiya wani abu ya farune kuma ?
Ta karbe wayan a hannin Aliyu a lokacin tace sai wani abu ya faru ke nan zan kiraka ko ?
Kiyi hakkuri mama ba haka nake nufi ba .
Ta dan gyara tsuke fuska tace duk inda kake kazo gida yanzu ko a ina kake ina son ganin ka yanzun nan.
Mama gashi yanzu ina, , , , ,
Ban tambayeka inda kake ba umurtan ka nayi da kazo yanzun nan ina jiran ka tana fadin haka ta katse layin tare da mikawa Aliyu wayan shi.
Aliyu daya gama karanta bacin rai a fuskan uwar tasu yace mama kila yana wani gunne kin san yanzu aiki yayiwa bros yawa.
Ta katse shi cikin daga mai hannu tana fadin Aliyu ka fita idona tun kan na saba maka rai a wurin nan.
Habbib dai yana zaune sai cin abincin shi yakeyi bai tsinka mata ba kamar bai gurin a lokacin.
Haka suka zauna zurun zurun zaman jiran zuwan dan uwan nasu don suji abinda ke damun mahaifiyar tasu haka tayi mashi kiran gagawa hakan.
Da sallama a bakin shi fuskan nan a daure da baka ganin fara,an shi ya shigo part din yana bin su da kallo a yadda ya samay su zaune din tare da fadin lafiya dai ko ?
Sai Aliyu ne ya nuna mashi mahaifiyar tasu da hannu yana fadin muma dai haka mukaji kiran bamu san dalili ba bros.
Hjy ta dago rai bace da idanun ta da sukayi ja jajir tayi mai kallon ni ka raina tace babawo ashe ban isa da kai ba a gidan nan ?
Ni zaka mayar mutumiyar banza a idon mutanen gidan nan kana kokarin ka nuna masu ni ba kowa bace a gare ka yanzu.
Haba mama mai yayi zafi haka har kike wanan irin magana yanzu tace daga yau nayi maka iyaka da duk wata mace a gidan nan.
Ba maimuna ba kawai kowa nake nufi da hakan idan kuma kace bazaka ji magana ta ba you will see my worse a kan ka mara tunane kawai.
Akan wata yarniyar matarka can kake son take magana ta don kawai ka dadada mata rai niko nawa ya baci suna shigewa suna maka kulle kullen sheri kai baka sani ba wake yarda da mace idan ba kuba sakarkaru.
Ka shiga hankalin ka dani a kan maimuna da wani tarkace nata if i see you near her again i will show you my true clour.
Haba mama bros namiji ne fa ba mace ba Aliyu ya ce wani wawan mari ta yarfa mai da bai zata ba a lokacin sai da kowa na falon ya dago yana kallon ta.
Aliyu ya dafe gun don marin ya shige shi sosai har cikin ranshi ya jishi idanun shi suka juye a lokaci daya sukai kwamcin jini ya mike tsaye tare da mata kallon ni kika mara ?
Daga haka ya fice a falon rai bace dakin su ya nufa ya fara harhada kayan shi a ckin fushi.
Yana fita ta juya gurin Umar dake kiran Aliyu din tace kai kuma ka kiyayyeni don ina kyale ku kuna abinda kuka ga dama kada ku dauka tsoron ku nake ji hakan.
Kai har ka isa ka turo dokan dana sa a kanka kake gani yanzu daga yau ina son ku sani ban magana yaro ya ketare min zance na a gidan nan.
Amma mama kan wanan maganan kika mari Aliyu haka a gaban kowa mu har da kannen sa ta daga hannu zata mare shi habbib yace kada ki soma mama is enough don Allah mama may ke damun ki yau marin bros wani fitina ne babba a gare mu.
Waye shi da ba za mare shi ba ko a gaban kowa da zaice zai fada min abinda ya dace dani mama wanan kuskure kike a rayuwan ki.
Kan maganan ku na kishi bai kamata ace kina sakamu a cikin shi ba ko salma da take mace ai bai dace su shiga zancen ku ba balle mu.
Irin haka ke sa muna nisa dake wallahi ni badon Aliyu daya matsa muna kan lalai sai mu dawo gida ba babu abinda zan dawo inyi a nan yanzu din nasan abinda zamu dawo mu tarar a gidan.
Haba mama yanzu ai mun wuce wanan hukuncin haka a gare ku idan kina muna haka ta yaya na bayan mu zasuga girman mu tunda a gaban su kike muna komai ni wanan zuwa gidan Allah ya gani banji dadin shi ba wallahi .
Dama nasan kai fitsarare ne sai ka zo ka rama mashi marin tunda kaji zafi abinda nai mai da bakazo ba kaga sakona ne.
Zai kara magana Umar dage gefe kanshi a sunkuye sai idanuwan shi da ke fitar da kwala ya daga mai hannu yace habbib mamace ka kyale ta tana da iko da daman yi muna duk hukuncin data ga ya dace damu idan mun kauce hanya.
Ya juya wurin ta yace Allah ya huci zuciyar ki mama shike nan ina iya tafiya ya fada murya a sanyaye.
Tace kadai ji abinda nace yace na gode ya juta ya marawa habbib baya daya riga da ya fita kafin shi yana kiran sunan habbib din.
Kafin ya kai Aliyu ne ke fitowa jaye da jakar kayan shi ranshi a bace ya nufi hanyar fita gidan da sauri suka nufi gurin shi .
Daidai da fitowan mu da Aisha zuwa gurin kitso ke nan muka tsaya muna kallon su don dagani ba lafiya ba dai kowa ranshi a bace.
Ban san lokacin da Aisha ta sulale ta kira Amma ba saboda kallon yadda suke faman rike dan uwan nasu da sukeyi yana fisgewa sai jin muryan Amma nayi tana salati tare da mama hadiye Amma na fadin yau may zan gani haka a gidan nan ?
Haka yasa na juya da sauri inda nake jin sautin muryan nata ina kallon ta tana sauri ta karasa gurin su.
Mama hadiye sai kokarin kiran kawu a waya takeyi a lokacin may haka kusan yaki may ya hada ka da yan uwanka da alama kokarin barin gidan kake gadanga kusan yaki.
Da kyat habbib ya buda baki yace bada mu yake fada ba tsohuwa da maman mu ne ya dau zafi.
May kuma ya hada shi da uwar taku tana kokatin kama hannun shi da umar ya rike suna kallon juna sai dai ya kasa magana a lokacin don zafin ran da yake ji.
Ina jummai din mai tayi mai haka naga kamar kwancin jini a idanuwan shi dukan ka tayi komay haka ?
Umar ne ya yi karfin halin bata amsa yace dan matsala aka samu amma shine ranshi ya baci yake shirin tafiya wai.
Ta kara rikeshi da kyau tana fadin ji nan gadanga ba, a fushi da iyayye fa daga yau ka daina hakan kayi fushi da uwar ka har kace zaka bar gida.
Ka nuna mata abinda tayi ma yai maka zafi ke nan ko may laifi ne idan iyayye suka tsawata wa diyan su baku gani ga mahaufin ku har gobe bai wuce fada a gurin mu ba ai.
Ina yake shirin zuwa muryan kawu ya na tambaya a hasale yana kallon Aliyu din a lokacin kam kowa na gidan yana waje har Ahmed da suka shigo da kawu din.
Kawu ya kalle shi yace maida kayan ka ciki kafin muyi magana ba musu ya juya da kayan zuwa part din su daga haka bai fito ba ya samu wuri ya zauna.
Kawu ya juya gurin umar yace umar faruq kaine babba kayi kokarin koyar da yan uwanka hakkuri .
Kana kallo yana irin wanan tabargazan haka a gaban kannen shi da kowa ba kunya wai gida zai bari.
Daddy kuyi hakkuri abinda muke lurar dashi ke nan kuka iso nan yanzu yayi kuskure ba zai sake ba insha Allahu.
Ku tafi bayan sallah magariba ina neman ku dukkan ku har iyayyen naku kawu yace yana wuce wa abin sa suka amsa da Allah ya kaimu daddy.
Daga hakan kowa ya watse cikin shi cike da gulma don ba wanda yasan mafarin maganan sai su yasu yasun su yan part din.
Umar kan fita yayi gidan yayin da habbib ya samu Aliyu a dakin shi yana kara bashi hakkuri kan kuskuren da yake son tafkawa.
Hjy jummai tana part din ta bata fito ba bakin ciki nadama damuwa da tashin hankali sun ishe ta a lokaci daya ta rasa inda zata dafa taji sanyi a ranta lokacin.
Don tana ganin yaran suna son sufi karfinta a lokacin don irin yadda take ganin take taken su a lokacin.
Amma kan dasu mamu da mamaki a ransu kowa ya shiga part din shi suna mamakin abinda yai zafi haka har ya jawo wanan matsalan.
Mun bar gidan tun kan su bar gurin muna hanya umar yazo ya wuce mu da motar shi lafiyayya mai daukan ido.
Aisha tace sukan masu kudi nan najin dadin su kiji wanan motar kamar a baka ka lashe don kyau na kalle ta nace ke motar yayan su salma ne fa baki ganta a kofan gidan mu ba aje da zamu fito.
Tace bata kula da motar ba ai yanzu shine a wanan hadadan motar nace sai dai babu matar sakawa a motar ba .
Kin kashe masa mata ne Aisha ta tambaye ni cikin kallona nace wanan arniyar zai nuna a matsayin matar shi idan ba don baida kunya ba.
Tace A ruwa kin san abinda ya daure min kai naso fa inji abinda ya hada yaya Aliyu da maman su har sukai fada haka wanan matar mai son diya kamar ta mutu balle tana ganin su sun zama taurari.
Nace wallahi niko haushin su Amma naji da suka hanashi wucewa don dai kawai ranta ya kara baci kamar yadda tasa Mamun mu bacin rai yau.
Ke muguwace Aruwa idan tsiyan ki ya tashi idan an barshi ya tafi wa yasan halin da zai shiga a can kilama ya wuce inda ya fito a daina jin labarin sa.
Nace to wa ya damu dasu dama mutanen da basu taimakawa iyayyen mu uwar su kawai suka sani ni kin san karin takaicina dasu tace a, a sai kin fada.
Nace yadda suke kiran mamu da sunan ta gatsau hakana kai tsaye ai ko banza taci hjy ko gwaggo a wurin su dai.
Tace ba mamaki fa hjy ce ta hana su kirata aiko su salma haka suke ce mata wani lokaci yanzu dai ne naji suna dan cewa maman fauziya din.
Wallahi duk ranan da suka kira sunan mamu a gabana sai naje gaban uwarsu ince ke jummai kaza sai ta kai min duka a kafada tace zaki iya shi shago ina son ki wurin jidali ai.
Haka mukai ta shakitanci a kansu har muka isa saloon din bamu dawo ba sai gab da magariba muka shigo gidan yana tsit kowa na dakin sa nasa ya damay shi a rai.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:04 - ??5惙5惙5?: ONCES MORE AGAIN ASSALAMU ALAIKUN YAN UWA MUSULMAI YAYA RUWA YA LOKACI ALLAH YASA MU FI KARFIN ZUKATAN MU AMIN, , , , ,


Na idar da sallah har isha,i na fito falon inda su mamu suke ta dago kai ta kalle ni tace koke fa gaki da gashi sai ki tsaya ana dunkula maki shi wani iri gashin ki na wullakancewa nan gaba idan ya zube ai kya nemay sa.
Nace mamu ni idan zai zube duka ma ina so in huta wanan wahalan kitson har shawan kai askake ne idan na gani.
Tace shike nan kin zama irin su meery yayan ku Faruq nace da sauri arniya fa ke nan mamu ?
Tace to ba haka kike so ai yana daga cikin bambamcin mu dasu don Allah ya halasta muna aje gashi mu gyara shi yana daga cikin bambamcin da maza sai kumshi a kafa gashi ke duk bakya son yi.
Nace mamu harda kushin tace kwarai musaman irin namu na asali yana bada sha,awa da lafiya da kariyan mace daga tarkon aljannu.
Koda a hannu ne ko yan tsun ki ya kasance kina saka lale dai nace tsiyan abin makaranta basa barin aiyi kumshi.
Tace ba jakkadun shedan bane su ta yaya zasu bari muyi abinda Annabin mu ya umurce mu muyi wayan ta ne yayi kara ta dauka sunan mijin su ta gani take fadin Alh ne ko lafiya yake kirana yanzu ?
Nace ina zama zan fara zuba shinkafa da salad din da suke ci mamu kin manta da yace bayan magariba yana neman ku falon shi ne ?
Ba ruwa na da rikicin yayan hjy sayadi wanan matar bata sona da alheri na gama karanta ta har wayan ya katse bata daga ba ina kallon ta can ya sake kira ta daga yace kin manta da ina neman ku ne a sashe na bayan sallah.
Tace naga maganan bata shafe ni ba Alh tunda tayi min iyaka da yayan ta don Allah ka fitar dani cikin wanan zancen ban iya jidali kullun kan dan kankanin abu a gaban diyan mu.
Yace haka kikace ya kashe wayan ko mai mamu ta gani ta tashi tana kunkumi ta fita daga dakin naci gaba da cin abincina muna kallo da kanne na kafin barci ya dauke su.
Daya bayan daya suke shigowa falon da sallaman su kowa nayi wa kansa wurin zama a gefe daya samu inda yaran suka ware kansu a gefe daya.
Kowa na maganan zuci a ransa banda hjy da ta tasha mur wa kowa har diyan nata abin alfaharin ta a duniya.
Har Amma yau a falon dan nata tazo don amsa kiran gagawan da yai masu a zauna da yaran shi ba wanda yasan manufan yin hakan.
Wai Alh zaman may muke a nan haka ina kowa ya halar ai a kan mutum guda zamu tsaya mu bata lokacin mu haka ?
Ido kawu ya zuba mata cikr da zafi da takaicin ta yace lalai jummai baki da ta ido mutum dayan ita bata da hakkin jin tsarin gidana ne kokuwa ?
Yadda kike da hakki da ke da diyan ki haka take da hakki da ita da diyanta a gidan nan don haka ki kama bakin ki sai ga mamu tayi sallama a falin cikin zubulelen hijab din ta wanda ya rufe mata ko ina sabanin sauran dake zaune kimkan a falon don dan gara jummai atamfane a jikin ta.
Bayan kowan su ya zaunane kawu ya bude masu da addua kamar kullun ya dan ja lokaci kafin yace yau ina kasuwa aka kirani hankali tashe a gidan nan.
Wanda banji dadin abin danazo na sama a

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login