Showing 234001 words to 237000 words out of 419207 words

Chapter 79 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1434

ina kara dunkule kaina a takure naci gaba da barcina hankali kwance.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:20 - ??5惙5惙5?: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM AL,HAMDULLILAHI RABBIL ALLAMIN, , , , , ,

Kamar a mafalki nake jin kamar numfashi a kusa dani yayin da na sake jina a jikin mutum kuma sannu a hankali na bude idanuna don tabbatar da yanayin da nake jin kaina a cikin wanan daren.
Gabana yayi mumunan faduwa saboda tabbatar da cewa bani kadai bane kwance a wurin lokacin.
Na zabura da karfi bakina na furta , innalillahi da karfi shima zabura yayi daga barcin daya fara daukan shi a dakin bayan ya gama tunane tunanen shine barci ya dan dauke shi.
Yana fadin relax zarah nine na dawo kina barci don in duba jikin ki na samu kin kwanta a takure, shine na zauna dake ajiyan zuciya na dan sake a hankali ina kokarin zare jikina daga nashi.
Saidai rikon da yai min ya hana in iya zarewa a lokacin gabana ya sake faduwa ina fadin may hakan ke nufi kuma a raina.
Ido ya zuba min yana kallon yadda nake kokarin kwatar kaina daga jikin shi lokacin.
Cikin natsuwa yace may kike yi haka kamar wata karamar yarinya dake da sauri nace zan kewayane dama a dan rude.
Kina iya tashi ai yace tunda naga alaman kinji sauki yanzu da rawan jiki na tashi saboda gaba daya na tsorata da hakan .
Ido ya zuba min na samu na mike da kyat zuwa ban daki na dan dauki lokaci kafin in fito a zato zai bar dakin kafin in fito daga bayin.
Na bude kofan kamar mai sanda sai ganin shi nayi yayi kwance rigigine ya dora kanshi saman hannayen shi yana kallon kofan kamar mai tunane.
Ba komai yake tunane ba a lokacin sai yadda yar karama dani ya tsinci kanshi da jin dadin dumin jikina don bai taba zaton zai ji wani abu daga gareni ba haka.
Na dan zabura da ganin sa dakin har lokacin ya lura da hakan danayi naji yace kizo ki kwanta abinki .
Kamar ban jishi ba naci gaba da tsayuwa a wurin kamar mai tunanen wani abu a raina ya sake fadin bakiji bane ina magana ?
Nan ma shiru nayi mai tare da ja da baya kamar zan koma bayin naji muryan shi yana fadin idan baki zokin kwanta ba zan iya zuwa in dauke ki tsab ida baki dawo kika kwanta ba.
A hankali na tako zuwa bakin gadon nakai zaune a takure ban iya juyawa na kalle shi ba don yana a yadda yake kwance har lokacin.
Ki saki jikin ki don ni a matsayin yayan ki nake gare ki ko ba haka na dan gyada mai kai a hankali.
Yace idan kin san hakane ina son ki fada min may ye matsalan ki ko da damuwan ki shiru nayi don ban gane inda tambayan tashi ta dosa ba lokacin.
Ina tambayan ki kina shiru may yake damun rayuwan ki ne zarah ki saki ranki ki fada min ko maynene ke damun ki a kasan nan ?
Na dan juyo kadan na kalleshi kafin ince ni banda damuwan komai tare dani sai dai na rashin kowa a tare dani.
Yanzu ni da nake bata lokacina ina kulaki ba kowa bane a kusa dake kike nufi ko may ?
Na dago ido tare da dan juyawa ina satan kallon shi a daidai lokacin da hawayen da nake dannenawa a idona suka silalo min a fuskana shar lokaci daya.
Nace da zan samu kaima din ka nisanceni da zai fi min sauki zanso kaimun adalci ka barni kamar yadda kace kana bukatan in nunawa kowa a kasan nan da ba wani alaka a tsakanina dakai sai na yan uwantaka.
Yace wanan kuma abinda kika san ba zai samu bane a gare mu don ke kin sani nima na sani akwai hakki mai girma da ke kawunan mu.
Na tare mai numfashi da fadin amma mu kaidai muka sanda wanan zancen ai a kasan nan kaf.
Yace wanan kuma abinda ya shafe mune don bai shafi kowa ba ko ince tsarinane nida zuciya kan a binda zai fisheni nan gaba.
Duk da nasan kina kokari wurin bin dokan dana saka maki don nayi maki umurni kin bi abinda na sakaki bada gardama ba.
Saidai a guri daya kina kokarin kin bin dokana ta hanyan yin mu,amula da wasu mutanen dabaki sani ba.
Har yakai kin janyo fushin zuciyana na mareki wanda hakan har ya janyo maki kwanciya ciwo na dan lokaci .
Dago kai nayi tare da dan juyowa gare shi na kalle shi hawayen idonane keta kwaranya a lokacin da kyat na iya bude baki nace .
Banayi hakan bane don in bakanta maka rai yaya zaman kadaicine ya isheni har na fita don in mike kafana a can muka hadu dasu Ramla da mijin da suka kawo ni gida ranan.
Amma kin san na hanaki yawan mu,amula da wa yanda ban san su ba tun farkon zuwan mu kasan nan dake .
Yaya kike zaton ina mijin ki hakan ba zai ban haushi ba inga wasu sun saukeki ba tare da sanin inda kuka fito dasu ba.
Na sake fadin to kayi hakkuri yaya bazan sake hakanba in Allah ya yarda yace ai zancen ya wuce a gurina tun lokacin.
Yanzu ki kwanta ki ci gaba da barcin ki ni sallah zanyi yanzu yana fadin hakan naga ya mike yabar gadon a zatona dakin shi zai nufa sai naga ya doshi hanyar bayi na.
Na ja a hankali nakai kwance na kwanta a takure tare da jan bargo na rufe kaina dashi ina jin ya fito gurin da nake sallah ya dosa ya tayar da sallah ina mamaki shi a raina.
Kusan kwana nayi a tsorace saboda ban fahinci sauyawan da na gani a tare dashi ba har lokacin.
Don a rayuwata ban taba zaton ganin sauyawa haka a gareshi ba tun ba a kai wani lokaci ba tun ina jin motsin shi yadda yake karatun sallah har yakai barci ya dauke ni ban sani ba.
Ban san lokacin da ya kara kwantawa ba saidai na wayi gari na sake ganin shi a kwance gefena ya takure a guri daya .
Saida na karewa yadda yake kwance kamar baison inji motsin kwanciyan shi a dakin ya kwanta lokacin a hankali na sauka daga kan gadon na nufi bandaki don dauro alwala.
Sai dai ina zuwa na samu fashin sallah yazo min lokacin na dan kimtsa na fito don in dauki pad sai na ganshi a falke ya dafe kanshi kamar yana mai ciwone.
Bina yayi da kallo a lokacin da yake shirin tashi zaune har na dauko pad din a boye ina kokarin komawa bandaki in gyara jikina.
Naga ya mike ya fice a dakin da sauri na saka komai har rigan da buje dana saka baki don kada a gane abinda nake na koma na kwanta ke nan ya sake shigowa dakin .
Ganina a kwance ya tsaya da mamaki yana kallona sai yace sallah fa ko ba zaki iya yi bane nayi na bashi amsa kai tsaye har zaiyi magana sai kuma naga ya nufi drower din gado ashe wayoyin shi ya manta a dakin ya dauka.
Yana fita na sake sauke ajiyan zuciya tare da tunanen ko yaya akayi merry ta barshi ya dawo nan ban sani ba.
Bansan ya akayi har barci ya dan daukeni ina rike da marana dake dan min ciwo kadan kadan lokacin don ina son gari ya kara haskawa in sauko in nemi abindana karya dashi in sha magani.
Ban falka ba sai da rana yayi sosai na tashi naga gari ya dade da wayewa lokacin da sauri na mike duk da jikina baida karfi har lokacin sosai na shiga bayi na kara gyara kaina na fito zuwa kasa.
Zaune na hango shi yana aiki a cikin laptop din shi yana duke jin karan bude kofana yasa ya dago kai ya dan kalleni ya mayar da kanshi ga abinda yakeyi.
Kin falka ke nan ga abinci can kici kisha maganin ki ya fadi ba tare daya dago kanshi ba a daidai lokacin da nake step din karshe zan sauko.
Zuwa nayi har kusa da inda yake nakai kasa ina fadin ina kwana yaya kaina a kasa do ban iya kallin shi gama ga irin yadda muka kwana gado daya tare dashi a daren jiyan duk da ba abinda yai min.
Amma sai na tsunci kaina yau da jin nauyin shi haka kawai kici abinci kisha maganin ki tun maran bai matsa maki da ciwo ba.
Gabana ya yanke ya fadi don jin abinda ya ambata min ina mamakin ya akayi ya sani a cikin raina.
Kin zauna kina tunanen banza a nan ki dubi lokaci rana yayi sosai baki sha maganin ba yace min.
Haka na mike da sanyin gwiwa jiki ba kwari na nufi table din haushi da takaici na sanin ina period daya wanda bansan yadda ya gane hakan ba.
Na zauna na bude warmer din abincin mamakin inda ya samo wanan abincin nake na dan zuba kadan na zauna ina tsakura don bakina da bai mun dadi danaci abincin sosai don dadin shi yai min a baki saida ban iya ci lokacin.
Ban san ya mike a inda yake ba sai gani shi nayi yana miko min magani gabana da sauri na dago kai na dan saci kallon shi.
Fuskan shi a daure daure yake lokacin kamar bashi bane mukai magana a cikin dare dashi karbi kisha yace min a daidai lokacin da wayan shi ya dauki rurin kira na karba da sauri yana tsaye bai dauki wayan dake a inda ya tashi yazo bani magani.
Ina sha ya juya zuwa gurin wayan da sauri ya dauka sai naga ya aje ya zauna yaci gaba da abinda yakeyi.
Zama na danyi zuwa wani lokaci kafin in mike ina dauke kayan abincin daga gurin zuwa kitchen.
Na dawo sai ban zauna ba kamar mai shawaran komawa daki naji yace ki samu wuri ki zauna nan kwanciya baya isan kine ke ?
May zanyi to yaya na fadi a dan shagwabe ya dago kai ya dan kalleni sai ya nuna min kujeran dake gefen shi in zauna.
A hankali na tako zuwa wurin kujeran na zauna shiru dani dashi ba mai magana a hankali na kai kwance ban san ya akayi ba na tsunci kaina ina karatun suratul maryam.
Yana jina baice min komai ba saida na dan kage naji ya gyara min dago kai nayi ina mai kallon mamaki na jin ashe shi din mahadacin kur,ani ne sosai.
Wayan ta kara daukan kara yaja tsuki yana ignoring din kiran kallon shi dayaga ina yi yasa ya mika hannu ya dauki wayan .
Daga inda nake kwance ba nisa sosai dashi yana dauka ina satan kallo shi naji muryan merry kamar cikin fada take magana dashi ya tsaya yana sauraren ta kafin yace.
That is my final decison merry live my daughter alone tayi addinin dana zaba mata a rayuwan mu.
Naga ya danyi shiru yana sauraren abinda take fada mai ya dade a hakan baiyi magana ba naji yace good mu zuba ni dake merry zakiyi regret din wanan shawaran karshe.
Ya kashe wayan ya dan juyo yana kallona nayi kamar ba saurare su nakeyi ba ina karatuna a hankali.
Yaushe zaku koma school ne ya tambayeni kanshi a duke sai lokacin dan juyo ina fadin nan da two weeks in Allah ya kaimu.
Banji yace komai ba haka yasa na rufe fuskana da hannayena ina tunane ji nayi shiru yace ko zakici wani abin nace na koshi.
Ba tare da na dago na kalle shi ba jin muryan shi nayi yaja tsuki yana fadin zaki wahala kuwa idan kince harda abinci bazaki kula da ci ba gidan nan.
Don ina auren ki bashi zaisa in maki magana kiki bin umurni ba don ba zaki mai dani dan yaro ba so kike sai ciwo ya kaiki kwance ki ba mutane wahala ko may da rashin cin abincin nan da bakiyi.
Shiru nayi ina sauraren shi ba tare da na yarda nayi magana ba don yadda naga yana magana a hasale nasan komai zai iya faruwa a lokacin.
Ni dai a raina Allah Allah nakeyi ya bar gidan zuwa wuri matar shi don ban son yace zai kara kwana a gidan nan sai dai banga alaman haka a gare shi ba.
Lokacin sallah nayi zai mike yaje yayi dukda ba fada min yake yi banice kawai ke lura da hakan tunda ba kiran sallah akeyi ba nan.
Da yamma kwatsam sai gashi ya fito a cikin shirin shi ina tsaye ina dan goge goge a falon ya kalleni yace.
Ki shirya zamu gidan can mu kwana biyu tare dasu don suna gari munyi magana da merry dazun tace ki zo nan ko zaki sake jikin ki.
Dago kai nayi da sauri na dan kalle shi a cikin mamaki kafi ince yaya nan ma yayi min banson zuwa gidan nan don nan yafi min can.
Shiru ya na dan lokaci yana kallona kamar yana nazarina kafi;yace cikin natsu da nan da can duka gidane kin sani.
Akwai abinda nake so zuwan naki can kiyi min do merry da yata ciki natsu yake min magana don i fahince shi a lokacin.
Hawaye na soma fitarwa daga idona ba tare dana kalleshi ba yana tsaye shiru yana kallona.
Niko nasan muddin naje can zan matukar takura ne kawai don a gaban merry ba wani abinda zai iya min.
Ya marairaice murya a karon farko ga zaman mu yana min magana a tausashe yace.
Kiyi hakkuri ki shirya mu tafi nasan zuwa can kina takura sai dan zan so kiyi min hakan don ni da yata.
Zamuji dadin kasancewan ki tare damu a daidai wanan lokacin yin haka garemu kamar ki mutuntamu ne ai.
Haka na daure ba don naso ba na shiga ba shirya duk wani abinda tafiyan nawa zai bukata a can na fito na samay shi tsaye yana jiran fitowana.
Bamu tsaya jiran komai ba ya rufe komai na gidan banda frezer dake aiki muka tafi.
Tafiya mai nisa mukayi saidai shi waya yake da abokin shi Nasir dana fahinci daga Nigeria ya kirashi suke magana kan filayen da aka sai mai naji yana fadin har an dora gina kamar yadda ya umarta.
Har muka kusan kaiwa wayan yakeyi sai can suka katse ina mamaki a raina kamar ba kudi suke batawa ba lokacin don da Nasir din ya kirashi yace ya kashe zai kirashi shi.
Mun isa gidan lokacin duhu yayi inda ys shiga get ya samu wuri yayi parking mun fito shike gaba ina binshi baya zuwa cikin gidan.
Merry na zaune a falo tana waya daga ita sai wani dan rigarta iya cinya sosai ya tsaya mata.
Tana ganin shi kafin in shigo gidan ta kalle shi tare da fadin where is she banace kazo nan da ita ba ?
Baiyi magana ba ya wuce ta zuwa wuri yarsgi dake kwance a kass tana wasa ya daga ta ta juyo gare shi tana dariya.
Niko saida na tsaya nayi adduan neman tsari da kariya ga duk wani sheri da wani abinki na shiga gidan da sallamana a bakina duk da nasan yana da wuya a amsa min a gidan.
Tana ganina na shigo ta katse maganan da take mai tace tana min wani irin kallon mamakin ganin sauyawa a tare dani sosai don na kara mata girma na cika sosai a idon ta.
Wanda ni kaina nasan na canza a lokacin don ban nemi komai na rasaba banda kewan ya uwana da gida da nake kwana dashi nake tashi dashi a raina kawai.
Bata san lokacin da tace mamaki wai kece kika koma haka fatema kodai gizo idona keyi min.
Dan murmushi na sake a fuskana ina gaida ita zan iya gane tana cikin wani yanayi na bacin rai ko tashin hankali a lokacin don yanayin ta daya nuna hakan.
Dan murmushin dole ta kako tana min tace kin girma kinyi kyau sosai har kin so kifi mijina fa.
Zama yayi a daidai lokacin shi ya nuna min kujera in zauna nakai zaune nan ma aikatan gidan ke fitowa daya bayan daya suna mai sannu da zuwa suna gaidani kuma da zuwa.
Sun dan juye harshe suna maganan da ba jinsu nake iya yiba a lokacin don akwai dan tazara daga inda nake zaune .
Kadan kada merry take satan kallona ina nuna ban san tanayi ba don baczan manta canza min da tayi ba a zuwana karshe gidan ba.
Don hakane nima ban yarda na sake jiki da ita ba don na mayar da hankalina ga wayata sai shine ya dago daga tabar gazan da sukeyi a gabana yace a kawo maki abinci ne zarah ?
Wanka nake son yi na bashi amsa yace zaki iya shiga dakin ki ai yana nan a gyare ba kowa a ciki

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login