Showing 312001 words to 315000 words out of 419207 words

Chapter 105 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1505

Ina kwance na rufe har kai sai naji muryan mamu tana fadin ki tashi murja ta rakaki asibiti ko maman ki hadiya.
Don ni ba zan kaiki ba kada kuma yazama wani abin magana a gidan nan yanzu suna ganin mun fita tare za a dauko wani zance a dora muna kuma.
Ina fadin ba sai naje ba zan iya treating din kaina ai tace a, a ku dai je asibiti zaifi a auna ki asan abinda ke damun ki muryan mama hadiye ne a falon mamu tana fadin ina take nai yar gidan gwaggo.
Mamu ta amsa mata tana fadin gamu nan dakina ai ta shigo tana fadin fatima ba lafiya haka kuma ?
Nayi karfin halin tashi zaune ina fadin mama jikin nawa ne banjin dadin shi yau.
Tashi muje asibiti tace min dole na mike ba wani complain na shirya muka fita da motan ta muka fita tare da murja hjy maryam ce ta ganmu take fadin uwa da yarta sai ina kuma haka da safe asibiti ta bata amsa nayi karfin halin gaida ita da kwana ta amsa min tana bina da kallon kurulla.
Munje anyi min dan gwaje gwaje result ya nuna ciki ne dani dan sati biyar ma,ana dai a nan gida na samu cikin ke nan zuwan mu.
Nike fadin abinda ya dace aban saura nace su bari zan rubuta in sayo idan na koma gida.
Maganine kawai ba aimin allura ba muka tsaya muka saye a hanya muka dawo gida a lokacin har hjy maryam taje part din hjy sarakuwana ta fesa mata fitan mu da mama hadiye.
Sukace karya muke ba asibiti zamu ba wurun biye biyen bokayen mu zamu tafi tunda yanzu bamu ga zama ba ai sai abinda ya turewa buzu nadi kan dan ta.
Allah sarki sha daya da wani abu muka dawo gida itace dai still taga dawowan mu na tsaya ina amai a waje daidai shigowa get din gida.
Wani sabon gulma ta kara gundawa a cikin ta lokacin bata samu zuwa ta fesawa sarakuwana ba don kawu ya kirata part din shi.
Saida nasha magani na kwanta koda Amma tazo har na samu barci yadan daukeni lokacin din haka bansan shigowan ta ba.
Ta dawo shiyanta cikin ikon Allah sai gashi ya kira Amma bayan sun gaisa tayi mai yaya hanya yake tambayan ta ko muna lafiya yakira bai samu wayana ba.
Tace yanzu daga wurin ta nake sun dawo asibiti bata da lafiya naje na samu barci ya dauketa ko .
Cikin wani irin murya yace da sauri subbahanallahi Amma may ke damuwan ta kuma har asibiti tace wallahi jiya uwar tace daren jiya basuyi barci da dadi ba.
Amma idan ta tashi akai mata wayan ki ko ta kunna nata wayan ya fada tare da yi mata sallama ya dan shiga tashin hankali don shi yana tunanen ko damuwane na saka a raina yaja min ciwo.
Don maganin dana sha na samu yin barci sosai a lokacin ban falka ba sai uku na rana na danji dadin jikin nawa lokacin saidai nauyin da yaimin ke damuna irin na wanda ya kwanta ciwo.
Lokaci daya na danyi fayau dani bayan na sallame sallah ne mamu ta shigo da kofin shayi yana tururi ta aje a gabana tana fadin ki daure ki sha wanan ko hanjin ki zai dan warware maki ki samu kici wani abu mai nauyi anjima.
Mamu ba kunu insha shi nake son sha yanzu kawai tace akwai da kamu sai a dama maki yanzu.
Barshi idan babu nace mata ina kokarin kaiwa kwance kasa a wurin da nayi sallah.
Tace sanyin kasan ba zai maki yawa ba idan kin kwanta a nan nace sanyi sanyin kuma nake so bata ban amsa ta juya ta fita daga dakin .
Ba a dauki wani dogon lokaciba sai ga kunun an dama min shina samu na dan kurba sama sama na aje cup din sai ga Amma ta shigo dakin tana fadin sannu yarnan .
Jikin ya kiya haka kuma ina dai ba danuwa kika saka a ranki haka ba Aruwa babu mai rabaki da mijin ki kinji muddin ina raye.
Shima ja,irin tun dana fada mai baki da lafiya ya hani zaman lafiya a gidan na ya bugo waya yafi a kirga yau yace ki kuna waya ko ki karbi wanan.
Kawun ki ya dawo nayi mai magana ya mayar dake dakin ki in ba so yake sadauki ya tare muna a gidan nan ba .
Maganan mamu ya katse Amma mama ta koma ina kuma ai gara dai kowa ya rike nasa kuma zaifi saukin wanan fitina na hjy.
Maimuna ki fita min a idona tun ranki bai baci ba jin abinda mamu tace yasa na gane nufin ta nace cikin karfin hali Amma bazan koma gidan yaya ba idan kuma kin matsa in koma gidan mu bauchi da zama.
Shike nan ku kasheni ku huta zaifi min saukin wanan bakin cikin da kuke sakani a gidan nan kan auren yaran nan.
Karan wayan tane ya hanani magana ta miko min wayan na dauka da sallama zahrah me yake damun kine haka Amma ta fada min har asibiti kuke yau.
Muna fara magana sai mamu ta mike ta bar dakin zuwa falo kusan tare suka fita ita da Amma a lokaci daya daga dakin.
Banjin dadin jikina na bashi amsa a sanyaye ya yace asibiti may sukace nace sun dai dubani sun ban magani.
Ko kinsa damuwa a ranki ne haka zahra da sauri nace damuwa akan may kuma yaya kawai dai ciwone sukace dani na bashi amsa.
Kina amai ne nace nayi daga dare zuwa safiya har lokacin da muka dawo gida sai lokacin na samu barci.
Kinci abinci nace na dai sha koko yanzun dana tashi komai naci baya zama a cikina sai kokon dana sha yanzu banyi amai ba.
Yace zahra na amsa anya ba ciki kika samu ba kuwa da sauri nace ni banda ciki dawa kukaje asibitin nace murja da mama hadiye.
Ok ina maman twices nace yanzu ta fita falo ita da Amma bata wayan zan yi magana da ita.
Da kyat na iya mikewa na kaiwa mamu waya ta karba na dawo dakin na kwanta lamo banji yadda sukayi da mamu ba.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:34 - ??5惙5惙5?: Washe gari ina barci kamshin turaren yaya Umar ne ya karade min hancina haka yasa na bude idona da sukai nauyi saboda zafin ciwo a hankali.
Har bedroom din mamu yake yana zaune saman side drower ya tsura min ido yana taba wayan shi.
Ganin na bude idanu na ina dan motsawa ya bar abinda yake da wayan shi ya dawo da kallon shi gareni.
Zarah ya jikin naki yace lokacin da yaga ina kallon shi a cikin mamaki na zuba mai idanuna.
Naji sauki na bashi amsa dashi ina kokarin tashi zaune tare da fadin ka dawone kuma yaya ?
Dole in dawo zahra don hankalina bai kwanta yadda Amma ke fada min kina jin jiki jiya ai naji sauki na bashi amsa a daidai lokacin dana kai zaune ina mamaki kuma a raina shine yau har kuryan dakin mamu haka zaune ?
May yasa kika boye min abinda ke damun ki badon na kira gwaggo hadiya ta fada min ba daba zaki fada min ba gaskiya ke nan ba ko may ?
Ai ba saina fada ba idan lokacin ka sani yayi yaya sani zakayi do ba,a boyon ciki ai.
Don may ba zaki fada min ba in sani nace kawai dai ban son ka raba hankalin ka gida biyu ne nabari sai idan Allah ya dawo dakai lafiya muyi magana.
Ajiyan zuciya naji ya sauke tare da dan karkatowa inda nake yana kokarin taba jikina yaji jikin da zafi har lokacin sosai.
Yace ba zan barki kasan nan ba zamu koma London dis week insha Allahu muyi rainon cikin nan a can hakan zafi mun kwanciyan hankali.
Da sauri na dago kai na kalle shi nace yaya ka matana da kawu ya mayar dani hannun mahaifiyata yanzu itace keda iko dani ko ka manta da kawu yace kowa ya rike danshi ne.
Robish wanan wani maganan banza kike kokarin fada min ne haka wai suyi iya yin su a kan mu sun daura muna aure a tsakanin mu yanzu kuma basu da hurumin rabamu don aure a hannu na yake ba,a hannun wani ba.
Idan na bika mun koma yaya a wani matsayi zan zauna dakai alhalin mahaifiyar ka ta fito gaban kowa na gidan nan tayi ikirarin bata sona bata kauna zaman ka dani.
Kawai ni ina ganin mu hakkura da wanan aure kabi zabin mahaifiyar ka don a zauna lafiya kaida za a aura ma sabuwar amarya ka angonce kwanan nan kake batun barin kasa.
Wani kallo yake min wanda na kasa fassarashi a lokacin na tsanana ne ko na tsanar kalman da nake furtawa a lokacin.
Sai daya daga yace fine kinyi gaskiya zahra koda yake banyi mamaki ba don yanzu kin fadi hakan dama auren bai damay ki ba tun farko nasan da hakan.
Saidai ina son ki sani yace daidai lokacin daya kara ran kwafowa saitin da nake yana fadin babu wani mahalukin daya isa ya rabani dake a garin nan duk wani abinda zaku kimtsa ku kimtsa shi dakyau ina jiran ku yana fadin haka ya juya ya fita daga dakin.
Saida ya dan jima da fita mamu ta shigo tana fadin sai ga mijin ki mun gani da safen nan kuma.
Nace rigima yake son jefani a ciki wai na shirya mu koma London yace haba dai ina haka zai yuyu shiko.
Nace ai na fada masa ya manta a hannun ki nake yanzu tunda kawu ya mayar maki dani kamar yadda ya karbe ni a hannuki ya bashi ni da farko.
Kyalesu dani duk wani abinda zakiga nayi a gidan nan naki goyon bayane kawai gareni idan ita son danta ya rufe mata ido har tana ganin kowa ba kowa bane sai yayan ta yanzu zan nuna mata kema yace kamar kowa.
Nace ni yanzu mamu damuwa wanan cikin dana samu kuma shine zullumina tun jiya da aka fada min ban so yaya yasan da zancen ba wallahi sai gashi mama hadiye ta fadamai komai.
Ai dole ya sani sayadi tunda nasane a boye mashi cikin shi ai haka baiyi ba dolene yasan da zancen cikin ai.
Mamu so nayi na fitar da cikin may ye amfanin inta haihuwa dashi ina tara diyan da ba,a so har ana kiran su da yuyu a gaban kowa tana kokarin sheganta min yara.
Kissa kike son yi sayadi ina wanan shawaran ya fito maki haka a bakin ki kuma kota sheganta su tunda mahaifin su yana son abinshi fiye da tsamani ai zance ya kare.
Shigowan murja wurina yasa mamu fita daga dakin murja ta zauna tana fadin ashe yaya ya dawo.
Nace yanzu na ganshi nima tace na ganshi ya fito dakin hjyn su sai a bace nasan tayi mai sababin ta data iya kan mayasa yake kulaki.
Nace ita tasani ni basu gabana yanzu abinda ya damay ni ya damay ni murja .
Tun da yaya ya fita ban kara ganin shi ba sai dai yana bugo waya ya tambayi ya jikina sau uku a rana tare da tambayana idan ina son wani abu ya turo min da kudi na saya.
Nakan bashi amsa da ban son komai don akwai komai kuma mamu tana tsaye a kaina .
Hakan bai hana inji alert din kudi ya shigo min ko a wayan mamu danace tana tsaye dani a gidan .
Da yazo ya fadawa iyayyeb shi zancen cikin dake jikina hjy tace ashe samun wurun nawa yayi yawa har ina gwarne a gidan har yaushe na haifi sultana da zan kara samun ciki.
Yace shike da diyan shi koda zan cika gidan da diyane hakan bai damay shi ba a wurin shi hjy tace taga a kaina yana son fara mata rashin kunya tana fada yana fada yace auren shi yake karewa mutunci ba wani abu ba shine fitan da yayi har murja ta ganshi ranshi a bace.
Ya samu kawu ya mai bayanin yana son zamu koma tunda zuwa nan yana yana da matsala gare mu.
Kawu yace umar nasan abinda nakeyi kasa min ido kaga guduna ka bari jimmai ta aurama auren da tace zatayi ma mugani tukun.
Ya dago kai yana fadin daddy may kake nufi da hakan bansan ko wace mama ke shirin aura min ba banda ra,ayin kara wata mace a gidana don ban rabu da merry ba mata biyu sun isheni a rayuwana.
Ko merry kurciyane ya cine na aure ta lokacin yanzu haka auren mu yana rawa akan rukicin yar mu da mukeyi da ita kan akidar ta da take son yarinyar ta bi.
Kawu yayi murmushi yace yanzu ka fara hango abinda nake hango maka har yasa na dauki yarinyar nan Fatima na baka don ka samu diyan da zakai alfahari dasu nan gaba.
A hallul kitabi ba abin yarda bane garemu Annabi yace kada mu yarda dasu domin su din mayaudara ne a garemu.
Saidai mahaufiyar ka ta kasa gano hakan gatane a gareka nayi maka ta dauki wani manufa na daban tasa a ranta yana wahal da rayuwan ta.
Yan uwanta kuma suna kara ingizata tana hauka babu mai bata shawaran kwarai a cikin su ta kasa gane ba son ta suke da gaskiya kyashi da hassadan ta sukeyi.
Daddy ni zan koma duk yadda ya kasance sai a kirani don ba zan dawo garin nan maza ba zan duba duk yadda shawara ya kaya zan kiraka in fada ma ka kara hakkuri dai kawu yace.
Ya mike ya fita ranshi ba dadi a lokacin tunda ya sa kai ya tafi yau kusan satin shi shidda ke nan ba wanda ya kara jin duriyan shi har yaran.
Bansan may ya hada hjy da mamu ba a falon kawu sai dai jin muryoyin su mukayi suna musayan baki har hjy ke fadin ke har kina da bakin magana wace tunda uwarta ta tafi ta barta cikin zanin goyo bata kara waiwayota ba har yau saboda mugun hali irin naku.
Shine zan yarda a hada min zuria da ku ku bata min zuria nan gaba saboda son kai ko may ki rike yarki ko yanzu burina ya cika a kanki maimuna don dana ya sako maki yarki ga yara ga ciki sai a nufi wani wanda kaddara ya fadawa kuma.
Ina zaune kasa falon Amma ina sauraren maganan su ina lumshe idanuwa na a hankali.
Tunanen da nakeyi ne a lokacin yasa na mike daga inda nake Amma tace ina kuma zaki nace ina zuwa yanzu zan dawo Amma.
Kada ki saka baki a cikin zancen su kyalesu suyi abinsu su gama na danyi murmushi tare da fadin ba wurin su zan tafi ba ni.
Part din mamu na nufa na dauko wayana dake caji na koma saman kujera ina duba nomba naga nomban da nake nema yana nan a wayana har lokacin.
Mamu ta shigo falon tana kuka banyi mata magana ba har saida tayi ya isheta nace mamu kiyi hakkuri din Allah.
Komai dake faruwa da bawa yana da karshe a wurin Allah barta tayi abinta yanzu watarana koda ance tayi ba zatayi hakan da take maki ba.
Sayadi ni fa ba shegiya bace da ubana aka haifeni amma hjy kullun dan magana ya tashi a gidan nan sai tai ta kokarin shegantani gaban kowa.
Don uwata ta tafi ta barni na bar kasan da yan uwanta kawai shi zaisa hakan ya zama min abin gori a wurin ta.
Kiyi hakkuri don Allah mamu ki natsu akwai maganan da nake son yi dake dama ban samu natsuwa bane da yardan Allah kwanan nan hjy???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? zatayi kunya a gidan nan insha Allahu.
Indai mahaifiyar ki tana raye ko yan uwanki sun kusa zuwa gare ki mamu cikin hukuncin Allah kuwa.
Da sauri ta dago kai ta kalleni take min kallon mamaki dan jin abinda na fada a lokacin.
Nace mamu akwai wata mata da muka hadu a London da ita matar ta damay ni wai ina kama da yan ahalin su sosai komai nawa irin nasu ne.
Da farko nace mata kamane kawai don ni dai nasan banda kowa a sudan lokacin.
Amma matsina da bi da matar tayi kan maganan har gidana tazo da photuna yan uwan nata tana nuna min saidai a lokacin duk ban dauki maganan nata da wani muhinmanci ba gaskiya.
Amma da yaya ya dawo ina fada masa yaba abin ma,ana sosai saidai lokaci ya kure don baifi kwana uku ba mu zo nan lokacin da matar tazo gidana shine yace mu bari sai mun koma mu neme ta muji komai.

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login