Showing 204001 words to 207000 words out of 419207 words

Chapter 69 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1443

shi da yarinyar tashi.
Wai ma may ya hana wanan yarinyar fitowa ne yau ya fadi yana mikewa don sanin babu mai alhakin kula dani in bashi ba ya kuma gane a takure nake zaune gidan dasu wanan zuwan.
Mikewa yayi tare da rike hannun yar shi suka nufi dakin da nake din yana rike da ita ya tura kofan dakin .
Babu kowa a ciki ga gadon a gyare don ban tafi ba saida na mayar da komai tsab kamar yadda na samay shi da farko.
Ya dauka ina ban daki ne haka yasa shi juyawa yana shirin komawa inda ya fito sai kuma yaja ya tsaya wuri daya da yai wani tunane .
Da sauri ya kara komawa dakin ya shiga ciki da kyau yana dan kalle kalle a dakin ya taka a hankali ya kwankwasa kofan dakin .
Shiru ya fara kira sunana nan ma yaji shiru ba amsa haka yasa ya tura bandakin da sauri wurin a bushe yake babu alaman anyi amfani dashi wanan lokacin.
Juyawa yayi ya kara fitowa yana dan dube dube cikin dakin ya daga filon yaji kamshin turaren da nake amfani dashi ya daki hancin shi sai kuma yaji gaban shi ya dan fadi.
Aje filon yayi da sauri ya juya ya fita don ita queen ta dade da fita tunda bata ganni ba a dakin da farko.
Fita yayi yana tambayan yan aikin gidan ko wani yaga fitana ko ina wani wuri na gidan kowa yace bai ganni ba sai Greco ce tace taga fitana da rana tun lokacin bata kara gani na ba kuma.
Hankalin shi yadan tashi gashi ba waya a hannuna balle ya kirani yaji ina ina a wanan lokacin don yamma yayi sosai a kasan.
Merry ce ta fito tasha kwaliya sosai tana waya suka hade dashi a falon cikin damuwa yace merry.
Where is dat girl ?
Wani kallo tayi mai tana katse wayan doba zaton ta ta dauka yarsu yake tambayan ta.
Tace faith tana cikin gidan nan mana na dauka tana nan gurin ka ne ai ta fara dan dube dube can tace may be tana gurin GRECO.
Yace not queen iam talking fatima nake nufi sister na ta dan tabe baki tace may be she is in her room ta fara tafiya.
Look merry ina tambayan ki ina yar mutane ta tafi kina tafiya bata dakin ta na duba ko ina a gidan nan bata gidan.
Tace is she a small girl ina zataje ai yanzu tasan gari yace ina ta sani banda gidan nan dan haka ina zata je kuma bayan nan.
Bata tsaya sauraren shi ba tajuya ta zuce dama fita zatayi takai kofa ta juyo tana fadin take care of our daughter shaaa.
Har takai kofa ta juyo kuma ko tayi mantuwane a lokacin tana sauri zuwa cikin gidan .
Yamma yayi sosai yasan ba karamin tafiya bane daga unguwan su zuwa central London inda nake.
Haka ya kwana yana juyi merry dake ta shagalin bukin su bata church bata gidan abokai da iyayyenta da suka zo mata easther a nan.
Bai maga hankalinta ba balle ta san yar akuyan shi ta bace a gari sai ranan yayi dana sanin barina da yayi babu waya a hannu na yafi sau dubu.
Sai faman juyi yake saman gado yana tunane yanzu in wani abu ya samu diyar mutane may zan fada a gida.
May zancewa daddy ya samay ta gaskiya yayi sakaci da duk wani al,amuran nauyi da hakkin yarinyar nan karama daya rataya a wuyan shi.
Ya juya a karo na barkatai yana tsuki merry ce ta mike zaune a cikin fada tana fadin may yake damun ka ka kasa barci tun dazun .
Yace will you keep quety merry ke har kin san damuwana yarinya tazo gidan nan ta bace ki nuna min rashin damuwan ki kan haka don ba yar uwarki bace ita komay ?
Tace amma dai kasan wanan yarinyar tunda tazo nayi kokari a kanta ko so yanzu na gane an turota nan ne tazo yin wani mition daga bangaren iyayyen ka don haka ba zan saka mata ido tana jefawq diya wasu akidu na daban ba.
I even ask faith how thet stat the coversition with her faith ta fada min komai daya faru a cikin hikima.
Though nasan ba wai yin kan ita fatema din bane amma duk da hakan zamuyi nisa da ita don kada ta raba min hankali yata.
Wani kallo yai mata tare da fadin good yanzun dai na gane cewa kece kika kori wanan yarinyar gidan nan ashe to ki sani idan wani abu ya faru da yar uwata a garin nan kece don bata san ko inaba a cikin garin na.
Tace ban kore ta da baki ba nadai kore ta da hali kamar yadda kaima iyayyen ka suka nuna min a can Nigeria.
Ok yace ya koma ya kwanta yana dana sanin yin watsi da yar uwan shi zabin iyayyen shi ga merry ta nuna mashi akwai matsala a gaba ke nan tun yanzu.
Kan yarsu yasan zasu kwasa da ita gashi yayi ta dauke hankalin ta kasancewan ta macen aure a yanzi har da ya ta daina wasu dabi,un da bai dace ba na akidun su na black American taki.
Yasan wanan ba shawaran ta bane daga abokanta wanan shawaran ya fito don da farko data barsu yana iya juya ta yadda yake so sai dai tana haihuwa dashi taga ai ta gama kamashi ga wautan ta.
Hakan yasa take mai duk wani abinda taga daman yi a yanzu don tasan ta gama dashi ko ta ko ina.
Sai dai merry ta manta da sanin halin dan Nigeria ganin irin halin data fara mai sannu a hankali yake tura komai da yake samu yanzu gida Nigeria da wasu kasashe ba tare da sanin yana hakan ba.
Yayi mata kifi na kallon maijan koma bata sani ba tana haukan cewa komai da yake nema da shi kan shi din yanzu mallakanta ne ita da yarta.
Ranan dai tunane kala kala yayi shi a gurin asuban fara tana barci ya bargidan ya kamo hanyan zuwa gidana kai tsaye cikin tashin hankali.
Merry bata san barin gidan nasa ba a lokacin tana kwance tana sharan barcin ta a lokacin hankali kwance ya barta don hankalin shi dayaki kwantawa yana ganin ban san gari kada wani abu yaje ya samay ni can.
Barci nake sosai don nima sai kusan asuba na samu barci ya dauke ni ina karatu daga nan na tashi nayi sallah na dade ina addua kafin in kwata.
Jin bell din gidan ana ta dannawa ba adadi yasani bude idanuwana da kyat na sauko dan shimin barci da wandon shi ne kawai a jikina don rudewa wakw min sallama da wanan safiyan haka.
Saboda ban taba dauka daga can zai iya zuwa nan ba a wanan lokacin haka yasa na fito a firgice zuwa kofan inga mai sallaman.
Ina budewa mukai ido biyu dashi sai lokacin na tuna da yanayin da nake ciki daga ni sai shimi a jikina da dogon wando kawai.
Haka yasa nayi saurin juyawa zan koma ciki a fusace naji yayi magana cikin daga murya yana fadin ke don may kika wuto nan baki fadawa mutane ba ?
Ban tsaya sauraron shi ba na juya don ni na farko ina son zuwa na rufe jikinane na biyu kuma yanzu duk wani tsoron shi ya fara fice min a rai yadda naga ya zama kamar bawan mace a nan don ban saba ganin hakan a gida ba wurin mazajen mu tun tasowa na.
Bin bayana yayi da kallon mamaki har na shige hijjab dina na dauko da sauri na saka nafito daga dakin baki daya.
Yana tsaye a tsakar falon bai zauna ba gani yaya nace mai ya dan juyo ya kalleni ya sake fadin ubanwa ya dawo dake nan nace.
Sai da na danyi jin kadan kafin nace uban wa yaya bakai ka kawoni gidan nan ba tun farko ?
Umar jin zancen nawa yayi da mamaki yace amma da yake dan duniyan namiji ne sai ya boye mamakin nasa yace nace waya dawo dake gidan nan jiya ?
Nace rai bace ni na dawo da kaina don ba zan zauna inda ake nuna min kyama ba alhalin su din ne abin kyama ai.
Ina fadin haka na juya na bar falon nan na barshi tsaye da mamakin irin kalaman dana fada mai kai tsaye yau ba tare dana ji shakkun shi ku tsoro ba yadda na saba.
Harshen shi ya sanya ya lashi leben shi na sama dayake jin ya bushe mai cike da takaicin kan shi.
Zaune yakai yana mamakin yadda na iya bashi amsa haka kai tsaye yau don kalaman sun firgitashi jin ina fada mai magana yau haka kai tsaye.
Idanuwan shi ya lumahe a hankali yana tunane wani irin hukunci zai daukan min wata zuciya tace mai hukuncin may zaka dauka kuwa tafika gaskiya.
Ban san yana falon ba har lokacin ganin gari ya haska yasa na fito zuwa neman abinda zan saka a cikina.
Ban ankara dashi ba zaune saida na kusa saukowa kan benen na tsinkaye shi zaune ya dafe kai yana kada kafa.
A firgice naso juyawa saidai nayi rashin sa,a shima jin takona ya dago jajayen idanuwan shi yana watso min kallo mai kama dana takaici.
Ina zaki koma ai gara ki sauko ki nuna min kin isa har ke kin isa ki kalli idona fatima ki zagi iyalina a gabana haka ?
Da sauri na dubeshi nace zagifa kace yaya ni ban zage su ba halin su kawai na fada ni may sukai min da zan zagesu ?
Ya gyara zama yana kallona kafin yace ke may kika fadawa Queen gamay da iyayyena wanda uwarta bata kaunan ta sani.
Nuna kaina nayi da mamaki nace ni din nan wanan yar har guda nawa take da zan fada mata wani magana da zai tayar mata da hankali.
Sai can na tuna nace ko zancen hiran iyayyen mu data tambaye ni na bata labarin kana da baba da mama har da gyany.
Yaya ko baka son yarinyar ta san da zancen iyayyen mu ne na fada mata a rashin sani na fada da mamaki ina kallon shi.
Yace sosai don lokacin fada mata baiyi ba a gare mu ban san may yasa na kaiki wanan gidan ba ma don kawai ina zaton kaiki can zai dan sakaki walwala na kwana biyu.
Ka cuceni yaya da kakaini wurin dabi,un kafirai nace babu tsoro a idanuna ko kadan lokacin.
A fusace ya mike tako biyu na ganshi a gabana yace ke wacece mara kunyar banza ina fada kina fada zaki rushe min plain dina.
Ganin yadda ya taso kamar zai makeni yasa na duka jin shiru bai kai min dukan dana zata ba yasa na dago kai.
Naga duk yanayin shi ya sauya a lokaci guda idanuwan shi duk sun kankance sai kuma naga ya juya kawai ya fita ma gidan ga baki daya.
Ajiyan zuciya na sauke jin bai tabi lafiyan jikina ba a yadda naga ya fusata din lokacin.
Karasa saukowa nayi zuwa kitchen din na dora abinda zanci ina ciki kuma naji shigowan shi sai abin ya ban mamaki sosai don a zatona ya tafi ke nan.
Ban fito ba sai dana karasa aikin da nakeyi na aje falon sama na hau tare da kulle daki don inyi wanka.
Na sako dogon riga na mai ruwan kwai da adon duwatsu a gaban rigan na fito don yunwa nake ji sosai.
Wanan karon a dan kwance yake yayi filo da hannayen shi kamar mai tunane banji komai ba a raina na nufi wurin abincin na.
Na zauna na fara cin abincin nayi kamar cibi uku naji muryan shi yana fadin ina nawa a bincin yake ?
Ban san zakaci ba na bashi amsa ya dubeni fuskan shi dauke da mamaki da kuma alaman magana nima ison na tsura mai don jin abinda zaice min din.
Da kyat ya iya bude baki shi cikin hadiyan bakin ciki yace kada ki zaton don ance an daura min aure dake raini ya shiga tsakanin mu dake haka.
Ina fada kina fada baki tsorana nace ba zan taba raina ka ba yaya ko dan zamanin da kukayi da mahaifiyata.
Na fadi ina kada idanuwana tare da rausaya kaina kan abincin da nake ci din har na soma ci naga rashin dacewan hakan kada na biye mashi ina dauki alhakin shi shida abincin shi.
Na mike na nufi kitchen abincin na hado mai nakai mai saman dining na aje da ruwa da komai na dauki nawa dana fara ci na koma saman kujera saidana zauna nace .
Ga abincin nan na shirya ma ban dauka zaici ba yadda ya share ni sai can naga ya mike ya tashi dauko wani leda yayi a gefen shi ya miko min ya wuce zuwa table din.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:17 - ??5惙5惙5?: ASSALAMU ALAIKUM YAN UWA MUSULMAI UBANGIJI YA BAMU WUNI DA DARE MAI AMFANI GARE MU AMIN YA ALLAH ???a

Ban bude ledan ba har ya zauna ya fara cin abincin sai dai nayi mamakin yadda ya ci abincin nawa sosai duk da ba wani hadi nayi maiba kamar yadda a girka abinci special a gidan shi don ina ganin merry nada mai girkin ta shima yana da nasa.
Yana gama cin abincin baice dani uffan ba ya mike ya fita a binshi sai bayan ya fitane na ja ledan na bude wayace???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? dallele a cikin kwalin da sim da komai ya saka min a ciki.
Idona lumshe tare da jin haushin kaina da ban duba wayan ba tun kan ya fita gidan gashi ban samu yi mashi godiya ba har ya fice don naji tada motar shi.
Na dade zaune a gurin kafin in mike na fara gyaran gidan sako da lungu don sanin cewa yan kwanaki suka rage min in koma school hutun mu ya kare.
Wanan dakin da nake ganin nasa ne na nufa na tura nayi mamakin ganin dakin a bude ban tsaya wani tunane ba na kutsa kai cikin dakin.
Tsayawa nayi ina bin dakin da kallo tare da mamaki a raina nace lalle ya umar jarumi ne a cikin mazaje.
Mai tsananin kwazo don abinshi ya ban tsoro yadda komai nasa a waye da tsada yake don wancan gidan nasu ba abinda zai nunawa gidana na jin dadi sai girma da jama,a dake cikin sa.
Yadda yaya yake matashi mai tasowa a lasan wasu ya mallaki wanan daulan haka kara matsawa nayi na shiga dakin da kyau.
Bin dakin naci gaba dayi da kallo can na hango yadda aka tsara wanan dakin da shimfido masu kyau ga gefe da yake ibada shima an kawatar da wurin gwanin ban sha,awa.
An aje kur,anai manya da kanana ga casbaha har da turare a gurin da mamaki nake kallon dakin wani irin tausayin shine ya tsargu a raina.
Watau mutum duk inda yake baya mantawa da ibadan sa dai ko wani irin akida yake bi kenan maganan kawu ne ya fado min a raina.
Da yace Fatima nauyi ne babba a kanki a cikin wanan auren kece muka ba wuka da naman jawo hankalin mijin ki ga addinin shi.
Na miji bai kammaluwa namiji sai da taimakon iyalin shi ki natsu ki gane ida yake da rauni a cikin addini dama wani hali da bai ahafi addini ba don in kin duba rayuwan mu na hausawa duk a addinece yake tafiya sai dai wasu gurare akan saka al,ada da yawa ya zarce sunna.
Idona lumshe tunowa da su kawu danayi yatin dana bude su kuma a hankali don sai yanzu na fara fahintan inda maganan kawu din ya dosa don a lokacin ban fahinci mai maganan yake nufi ba.
Ban dakin na nufa komai nan ma a natse yake na wanke mai shi tas duk da ba zama yake nan din ba sosai na fito na gyara ko ina a dakin sai dai nayi mamakin ganin takardun shi na komai dake gidan a cikin wardrobe din da gani masu muhinmancine sosai don yadda ya ajesu din a daure.
Ban fito dakin ba sai da nayi sallolina a gurin nan daya kawatu don ibada sai naji na samu natsu sosai da kusantuwa da Allah .
Addu,a nayi sosai tare da addua ga iyayyan mu dashi kanshi ya umar din na zauna nayi mai addua sosai ranan don ni a ganina merry tana gab data janyeshi zuwa nata a kidan ne yadda naga sunayi dashi a cikin yan uwanta din wurin picnic .
Bayan na gama na fito na samu ruwa na watsa ma jikina har lokacin bai shigo ba hakan yasa na rufe gidana da wuri.
Sam na manta akwai waya yanzu a hannu na karan wayan dake ringing

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login