Showing 210001 words to 213000 words out of 419207 words

Chapter 71 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1387

da ruwan kamar yadda yace.
Wayana dake cikin jakkar da zan fitane ya dauki ringing a lokacin ina fitowa naji na dauko wayan da sauri naga mai kirana din ?
Anty Farida ce ina dauka tana fadin kina ina ne sister baki fito ba har yanzu don mun saba duk safe sai mun gaisa kafin mu wuce department din mu sai kuma idan an tashi zamu hade.
Anty yau yayana ne yazo gidan kuma baida lafiya da sauri tace yana gidan ki ne ?
Nace eh yana nan gida jiya ya dawo daga gurin tafiya da ciwon tace kinga zauna gida kawai ki kula dashi.
Idan kin fito wa zai kula dashi kuma zan tafi department din naku inyi complain tace a karshe.
A sanyaye na amsa mata da nagode anty muka kashe wayan bayan sallama.
Na juya inda yake ina fadin yaya na hada ruwan kada ya huce shiru naji na koma kiranshi da yaya ga ruwan a bayi na hada.
Yayi firgigit ya dawo cikin hayacin sa tare da juyowa yana kallona yana fadin naji.
Fita nayi daga dakin zuwa dakina na aje jakkata dana dauka da niyar fita makaranta anty ta hanani.
Dan kwanciya nayi da niyar idan ya fito in shiga in gyara mai dakin shi ina game a waya har ya fito yayi breakfast ban sani ba.
Ya gama ya fita daga gidan zuwa sayo magani daga can ya wuce wurin wani abokin arkallan shi wata unguwa.
Bayan la,asar ina falona zaune cikin dan walwala don yanzu samun waya a hannuna yakan debe min kewan komai tare dani.
Wayana ne yayi kara na duba anty farida dai ne still take kiran layin don ita kadai keda layina a lokacin bayan ita banda wani layin waya bayan nata kuma.
Ina dauka take fadin sister gani a layin ku ki mun kwatancen gidan ki gabana ne ya fadi don sanin yaya yayi mun kashedin yin abokai barkatai tun farko.
Haka dai na daure nayi mata kwantancen gidan ba,a dauki wani lokaci ba sai naji bell din gidan yana ringing.
Dama ina falon na mike zuwa duba kowaye a wajen da anty farida mukai arba tana min murmushi ta shigo tare da bin gidan da kallo.
Muka samu wuri muka zauna har lokacin tana bin gidan da kallo ko mamaki hakan take a ranta oho.
Bayan mun gaisa ne take tambayana yaya mai jikin nace da sauki take fadin Allah ya sauwaka .
Take min bayanin ta daukan min excuse na one day a school an yarda nayi mata godiya muna cikin hiran school din ne ya dawo.
Gabanane ya fadi don tsoron matakin da zai daukar min idan ya ganni da bakuwa a gidan don dai a yanzu banson in masa laifin da zai jawo min matsala ga karatuna yanzu.
Sannu da zuwa nayi mai ina mai rakubewa gefen kofan tare da dukar da kaina kasa.
Yana ganin ta yaja yayi turus tare da kallonta da mamaki sai kuma ya fara tafiya itace ta fara gaidashi tana mashi ya jikin shi a cikin harshen hausa.
Lafiya ya amsa ba tare da ya tsaya falin ba ya wuce zuwa ciki kai tsaye ta bishi da dan kallo.
Bayan ya shige ta dan kalleni tana fadin shine yayan naki da baida lafiya na amsa mata da eh kawai.
Na dawo na zauna acikin dan tsarguwa da wasancewa ina fadin yaji sauki ai don tun dazun ya fita sai yanzu ya dawo.
Ke fatima yace daga saman inda yake tsaye hakan yasa na amsa da sauri ina mikewa a daidai lokacin kuma anty ke fadin nima zan tafi ke nan don ko gida ban karasa ba nabiyo inga jikin nasa.
Zan rakata tace da sauri a,a je gurin shi kawai ni zan tafi godiya nayi mata tare da dan rakata kofan fita falon taso ta dan bugi cikina taji shine yayan nawa kuwa kodai wani ne shi .
Naki sanar da ita komai don tsoron tonawa kanmu asiri da kuma warning dina dayayi tun farkon zuwana kasan.
Da sauri na juya zuwa guri shi ina isa na dan rakube ina fadin gani yaya.
Shiru yayi min yana tsaye a tsakiyan dakin ya dunkule hannayen shi a guri daya ina a rakube a guri daya na sake fadin gani yaya.
Ya juyo tare da tsareni da ido yace wanan wace matace na gani a gidan nan ita din wacece a ina kuma kika santa har tazo gidan nan.
Kaina na dukar kasa kafin ince anty faridace a makarantar mu take nan na santa a school din mu itama take karatu.
Yau ban shiga school ba shine take tambayana nace kaine baka da lafiya banzo ba shine tazo ta gaida kai.
Yaune farkon zuwanta gidan nan ya dago mi hannu yana fadin ya isa don Allah kin kama jero min magana kamar redio haka.
A raina nace kaida ka jefo min tambaya babu iyaka har na rasa wanda zan amsa ma ba laifi ba saini dana ba da amsa.
Muryan shi ya dawo dani yana fadin kenan kin fada mata alakan dake tsakanina dake ko ?
Dago kainayi na kalle shi nace eh na fada mata kafin in karasa ya dago kai da sauri yana kallona cikin zare mun ido nace na fada mata cewa kai yayanane kaine ma ka kawo ni karatu a kasan nan.
Yayi saurin kawar da kanshi daga kallo ya juya sai yace ban fada maki banson hurdan ki da kowa ba a kasan nan ?
Naga ita din ma yar kasan muce kuma a gari daya muka fito da ita kuma itace ta, , , , hannu ya daga min .
Yace bari kiji duk ranan da kika kuskura kika fadawa wani alakan dake tsakanin mu dake sai na batar dake a garin nan kowa ya huta
Na dago kaina kalleshi cike da mamaki da tsoron abinda ya fada sai ranan na tabbatar da baya kaunana har abada a rayuwan shi .
Hakan yasa nayi shiru ban karasa fadin abinda zan fadi a lokacin ba nayi shiru.
Ganin zai shiga bandaki yasa nayi saurin fita daga dakin zuwa kasa na kyale shi a dakin nashi na dawo na zauna ina mamakin wanan irin al,amarin nasa na boye matsayina a gurin shi.
Har washe gari bamu kara haduwa dashi ba har na gama abinda zanyi na wuce zuwa schoool daukan darasi.
Bamu samu haduwa da antyna ba sai da muka hade a school mosque wurin sallah azahar.
Daga can muka wuce zuwa wurin cin abinci sai dai na zauna ina kallon abincin ban taba ba yadda aka kawo min shi.
Anty farida tana hankalce dani saida tayi nisa da cin abincin ta kalleni tayi murmushi tare da fadin sister .
Hakan yasa na dago kai na dan kalleta abincin ta nuna min da idanun ta ma,ana inci abinci mana.
Hakan yasa na dan murmusa na dauki spoon din ina dan cakula abincin a hankali.
Amma dai yayan nan naki sai naga baku da kama na jini tare dashi wuri daya ko biyune kuke da kama shine hasken fata da tsayi kawai.
Nace ko anty ?
Ta sake fadin saidai sam sister bakuyi kamar wa da kanwarshi ba gaskiya.
Da sauri na kalle ta nace anty don may kikace tayi murmushi tare da fadi kanwata kunfi kama da miji da mata fa anya ba kina boye min gaskiyan wanan al,amarin bane kuwa ?
Dan murmushi nayi tare da fadin kai haba anty yayanane fa na fada maki tun farko ai.
Tace aina sani saidai kin san akwai aure a tsakanin wani wa da kanwa din wani lokaci kodai hakan ne kanwata ta tambayeni tana dariya.
Hannuna dake saman abin cin abincin ta dafa tare da fadin ina son ki sanu ciwon diya mace na ya macene yar uwanta.
Koda bamu zama kamar yan uwa na jini daya a nan ba matsayina na diya mace zaki iya fada min matsalan ki in magance maki shi.
A matsayina na wace ta girmay maki sosai ga haihuwa don haka idan har kin daukeni kamar yar uwanki na jini ina son ki fada min damuwan ki sister.
A hankali na dago kaina na kalleta da idanuwana da suka fara zubar da hawaye a lokacin nace anty yaya yayanane kuma mijinane.
Wani kallo tayi min tana murmushi kafintace ai na dade da fahintar hakan ban kara gaskanta zargina ba sai da naje gidan naga gidan ki da mijin ki.
Dan kankanin lokaci na fahinci cewa akwai matsala a zaman auren ku gaskiya alama ya nuna min akwai tauyewan rayuwa sosai a zaman ku don yawan tsorin mijin ki da kikeyi.
Nace hakane anty tiryan tiryan na fara bata labarin komai tun daga farko har zuwan mu gidan merry da tun lokacin yake dan kula dani da komai nawa.
Anty Farida ta cika da mamakin a zuciyar tbata labarin dana bata wanan wani irin mugun mutum ne ka dauko yarinya karama amana.
Kazo ka dinga muzguna mata duk da tana yar uwanshi kuma amana iyayyen su suka bashi don taimakon kanshi da kanshi nan gaba.
Wanan rashin imanin da mai yai kama ranan bata iya fada min komai ba sai hakkurin data bani muka mike zuwa gida daga nan.
A gida kuwa ya umar ya danji sauki ya mike da kyat baiji motsina ba ranan haka ya daure ya mike ya shiga bayi ya watsa ma jikin shi ruwa.
Saida ya fito daga bayin ya kalli lokaci yaga rana tayi sosai har kusan fast twelve na rana.
Ya fito rai bace da zuman yi min fada don sam ya manta da ina zuwa makaranta a lokacin .
Abincin shi ya fara arba dashi a dining din ya duba har kitchen din gidan na gyara komai neat kamar ba gidan karamar yarinya ba.
Tunane kala kala ya dingayi a ranshi sai can ya tuna da ranan akwai school abincin ya zauna yadan taba kadan ya fita.
Na shiga na watsa ruwa na dan huta na fito na dora girkin abincin dare duk da ban san ko yana gidan ba ko yatafine.
Kafin in gama ya dawo gidan lokacin duhu yadan fara ina rike da blender ina juye kayan miyan dana markada.
A bakin kofa yaja ya tsaya kamshin girkin na dukan hancin shi sai lokacin naji alaman mutum.a bayana na juyo na ganshi gabana ne ya fadi.
Nayi saurin yin dan kasa ina fadin sannu da zuwa yaya cikin rawan murya bai amsa ba sai fadin dayayi may kika tsaya yi har dare yayi maki ga girki , ?
Nace na dawo da wuri girkin daine ban dora da wuri ba don ban san ko ka koma gida ba.
Ya kara hade rai tare da fadin wanan bakin mai yawan surutun tsiya kan ya ja tsuki ya juya ya tafi naci gaba da aikina har na karasa komai na gyara gurin kamar banyi girki ba ciki.
Baya falon koda na fito na shiga daki wanka nayi nai sallah saida har isha,i na idar sannan na fito falon don cin abinci.
Turus nayi don ganin shi kwance saman dogon kujeran falon yana kallon labaran aljazzera jikin shi yana saye da kananan kaya lokacin.
Daga nesa kadan dashi na dan tsaya ina fadin na gama abincin.
Ya juyo ya dan kalleni baice komai ba ya mike zuwa dining din yans bude kulan abincin yaja kujera ya zauna ya fara kokarin zubawa.
Cikina ne ya fara min kugi a lokacin sai lokavin na tuna na kasa cin komai saboda kalaman shi na jiya gareni.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:17 - ??5惙5惙5?: ASSALAMU ALAIKUM YAN UWA MUSULMAI, , , , ,

Gida Nigeria kano ta dabo tunbin giwa gidan kawu sani yau tun da safe sun tashi da tashin hankali a gidan don ciwon kawu daya motsa mai tun yana dan yi a tsatsaye har ya kaishi kwance.
A cikin dare ranan dai basuyi barci ba don jikin kawu daya motsa mai da asuban fari mamu ta kira ya Ahmed a waya tana sheda mai halin da kawu yake ciki.
Yana idar da sallah a kofan gidan kawu gari ya dan haska mai don dan tazaran dake tsakanin gidan su dana kawu din.
Ya shigo kai tsaye gidan inda ya tun kari turakan kawu kai tsaye duk ahalin gidan har Amma suna cikin part din nashi lokacin.
Shigowan shi falon da sallama ya nufi inda Alh yake kwance matan shi dun kewaye shi gabaki daya da mahaufiyan har mama hadiye.
Ya dan dade tsaye yana kallon shikafin ya ciro wayan shi yana kiran layin Abubakar .
Ya amsa da gani kofan gidan na iso ba,a jima ba Sadiq din ya shigo falon shima ganin yanayin da surukin shi maigidan su yake ciki.
Ahmed bai tsaya jiran komai ba yace kamashi mukaishi mota ya fadawa sadiq kai tsaye yana kokarin dago Alh daga inda yake kwance.
Shima sadiq din yayi yun kurin dago dayan gefen da yake tsaye duk kawu bai san sunayi ba lokacin don jikin da yake ji din.
Mata da yara sai kuka sukeyi don halin da maigidan nasu ke ciki a lokacin hankali tashe da taimakon Allah suka samu suka saka tsohun a mota an rasa mai karfin halin shiga cikin su don a zaton su hjy ce ya dace ta shiga motan lokacin.
Saidai gane abinda suke nufi yasa mama hadiye fadawa motar a baya tare da Ahmed sadiq yaja motar tasu.
Asibiti suka nufa kai tsaye dashi cikin dan lokaci sun isa Ahmed ya fita ya kira akazo da gado daukan marasa lafiya aka dauki Alh .
Bayan wuce wansu ne Amma tace yau dai kun fara ganin manufar yaron nan da wanan hadin dayayi ga yaran nan .
Yau da yaran nan ba na jikin shi bane, ko suna rakan mu baza muyi bugun gaba dasu haka ba lokaci guda.
Kallon juna hjy da hjy maryam sukayi kafin su fara barin gutin daya bayan daya suna shiga daga ciki mamu tace gwaggo barin shiga in shirya in fito in bisu muga halin da suke ciki a can.
Ba abinda ya batawa hjy jummai rai kamar yadda Ahmed bai tsaya gaida su ba yana kokatin ceton ran surukin nasa a lokacin.
Wanda tun bayan badakalan da sukayi dashi lokacin buki bata kara ganin shi ba sai wanan ranan kuma.
Tana cika tana batsewa ga halin da take ciki na tashin hankali mijin su daya daga mata hankali kuma.
Kamar yadda ko wani gidan da ba hadin kai yake nan ma hakan ne ya faru don basu hada kafa wurin zuwa asibitin ba daya bayan daya suka isa gurin kusan lokaci guda.
Sun samu har an saka mai ruwa ana kara mashi har lokacin bai farfado daga yanayin da yake din ba har lokacin.
Suna zaune daga waje a cikin damuwa saidai babu mai ma dan uwan shi magana ko ta tsiya asalima ko gaisuwa hjy jummai ta yake duk wani alaka tsakanin ta da mamu a yanzu tun bayan faruwan auren yayan su.
Ahmed ne da sadiq suka nufo wurin dauke da lrdojin magani a hannun su wanda likita ya bukata su kawo.
Ganin su yasa sukaja suka tsaya sai lokacin suke gaida su ba tare da wani sakin fuska ba ko walwala a lokacin.
Suna gama gaidasu Ahmed yasa kai ya shige shima sadiq ya mara masa baya.
Bayan shigan sune hjy jummai dake ta hare hare taja wani dogon tsuki tana kau da kanta gare su.
Tare da dan maganganu ciki ciki wanda ita kadai tasan abinda take fadi a lokacin don ba wanda ke jin ta.
Daga nan kowa dai ta juya ba maiwa wani magana har lokacin kowa da abinda ke ranshi a lokacin.
Can hjy jummai ta mike ta nufi kofan dakin ta shiga sai lokacin hjy maryam ta iya kallon mamu da zuman munafunci sai mamu ta kauda kai gare ta don mamu ta gane nufin ta.
Ahmed ne ya leko yana fadin hjy ku shigo daga ciki ku ga halin da yake ciki numfashin yanzu ya sauko daidai.
A lokaci daya suka mike don shiga dakin inda suka samu hjy jummai tsaye a kanshi tana kallon yanayin da yake ciki din.
Tsayawa sukayi sun kura mai ido kafin mamu ta sauke ajiyan zuciya tace Allah ya sauwaka yasa ciwo kafarra ne.
Mazan da hjy maryam da mama hadiye suka amsa mata da Amin lokaci guda hjy dai tankar bata san dasu a dakin ba ta nuna.
London a nan hakurina kullun karuwa yake duk abinda yaya zai mun ina kokari shanyewa a raina ban fasa yi masa biyayyan da nake masa a kulun gashi yanzu duk kwana biyu yakan kasance a gidan tare dani duk da ba wani mu,amula a tsakanin mu hakan yasa na dan samu sakewa sosai yanzu.

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login