Showing 138001 words to 141000 words out of 419207 words

Chapter 47 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1436

ta yadda ba zan iya tsayar da shiba itama mamun kukanne ya kwace mata lokaci guda sai da mukayi mai isar mu ba mai ba wani hakkuri a cikin mu.
Itace ta fara tashi tabar falon na dade a wurin bata fito ba sai can gata tafito ta shiga kitchen bata wani jima a ciki ba tafito dauke da cup cike da tea a cikin sa yana tururi ta miko min tare da fadin ki karba ki sha.
Nasan rabon ki da abinci tun jiya da rana kafin kuje islamiya ko na dago kaina da idanuwana da suka kadai sukai jajir kamar gauta don kukan dana kwana inayi har fuskana ya dan kunbura.
Zama tayi gefena bayan na karba tana f????































!
"
#
$
%
&
'
(
)
*
+
,
-
.
/
0
1
2
3
4
5
6
7
8
9
:
;
<
=
>
?
@
A
B
C
D
E
F
G
H
I
J
K
L
M
N
O
P
Q
R
S
T
U
V
W
X
Y
Z
[
\
]
^
_
`
a
b
c
d
e
f
g
h
i
j
k
l
m
n
o
p
q
r
s
t
u
v
w
x
y
z
{
|
}
~

?
adi a cikin wani murya mai nuna rauni a zuciyar tace sayadi ba zaki daina kukan nan haka ba.
Sayadi ya kike son in yi nima fa al,amarin nan yafi karfin tunanena yanzu sai naga kamar dama haka Allah ya tsara abinsa a kanki.
Don dolene ni kaina nabi umarnin iyayyena don su manyane sun fimu hagen nesa nasan idan da babu alheri gwaggo ba zata taba yarda da wanan hadin ba sam.
Sayadi kiyi hakkuri badon bana son ki bane kikaga na kyale a, a sai don ban san abinda Allah ya shiryawa al,amarin ba .
Ba don wanan tunanen danayi a raina ba wallahi yadda kika nuna din nan baki so zan iya tsayin daka inga cewa an fasa wanan auren sai dai duk abinda zai faru ya faru.
To amma idan nayi hakan kamar nayiwa Allah shishigine ga al,amarin shi yanzu idan nace zan hana.
Sayadi baki san halin da nake ciki ba a yanzu don a halin nan badon nakai zuciyata nisa ba ko auren nan zan iya kashewa na huta idan hakan zai maki dadi a rayuwan ki.
Da sauri na dago kai ina kallon ta don mamakin furcin ta nace a razane mamu kada ki kashe auren ki sabodani kodon su fauziya mamu kina gidan nan ma yaya yaran nan suke fama a gidan nan.
Mamu ta daga kai ta kalleni naga idanuwanta sun canza alaman itama tasha kuka a daren jiyan sosai ke nan yanzu kuma ga furcin da tayi min koda nake yarinya ba zanso ace auren uwana ya mutu a sanadin aurena ba .
Haka yasa naji wani tausayin uwata ya kamani na karfafa hakuri da juriya akan komai gamay da auren nan har in ya tabbata a zuciyana.
Tea data miko min na fara kurba a hankali don hankalinta ya kwanta dani sai naji ta sauke wani irin ajiyan zuciya mai karfi tana mikewa ta shige daki.
Haka na daure nayi ta kurba tea din a hankali har ya saura kadan na mike nakai cup din kitchen ban fito ba don ganin yanayin kitchen din danayi alaman tun jiya rabon shi da samun gyara haka na daure na wanke kayan ciki na sharo na goge ko ina.
Falo na dawo na gyara na kakkabe kujerun na fara moping sai ga ta tafito don jin motsina da takeyi tace aiki kuma kika kama yi nace a kunyace eh mamu.
Na gama na shiga nayi wanka tun wurin shafa mai naji wani irin zazzabi mai karfi ya rufe ni a dadafe na karasa na zura digon riga kawai a jikina na haye gado na kwanta ranan dai a takaice ban shiga school ba.
Ban dade da kwantawa ba zazzabi mai karfi ya kara rufeni ni kadai a daki ina makyartan sanyi jikina ya gashe sosai saboda zafin jiki.
Shirun da mamu taji ta dauka ina part din Amma ne sai ta shiga kitchen ta dora girki har lokacin zuciyar ta ba dadi gareta.
Kayan yara da suka cire ta shiga daukowa sai hangoni tayi saman gado dunkule a cikin bargo ina kaduwa.
Mamaki ya cikata ta nufo inda nake tana yaye bargon irin yanayin da nake ciki ne ya bata tsoro da sauri takai hannunta saman jikina tana tabawa hakan ya sani bude iddanuwa na ina kallon ta cikin wahala.
Sai kuma na lumshe idon ina hawaye tare da kokarin fadin mamu banda lafiya ne a kidimay take fadin may ke damun ki ne sayadi nace nima ban sani ba.
Innalillahi tace tana kokarin fita daga dakin namu jima kadan sai ga su tare da Amma sun shigo Amma na fadin.
Dama abinda nakewa gudun ya faru ke nan, amma yan banzan yaran nan masu gadon uwarsu suka fadawa yarinyar nan maganan nan yanzu.
Takai hannun ta saman jikina da sauri tacire hannun tana fadin wanan sai asibiti kiramun sani yanzun nan akai yarinyar nan asibiti.
Ta juya gare ni tana fadin sannu uwata sannu kinji da jiki yaran nan basu kyauta muna ba gaskiya har uwar su naso koda zakiji zancen nan sai nan gaba.
Waya mamu ta dauko tana kiran layin kawu kira biyu ya daga kiran yana fadin maimuna yaya akayi tace yaya barka da kasuwa dama jikin yarinyar nan ne yayi zafi gwaggo tace a kiraka a sheda maka.
Yace subbahanallahi ga Ahmed nan zan turo ya kaita asibiti yanzun nan ni ina nan nazo unguwa ne daga haka ya kashe wayan.
An dan jima sai ga Ahmed ya iso gidan kofan mamu yaje yana sallama aka amsa mashi kamar kullun daga kofa ya tsaya suna gaisawa sai ga Amma ta fito daga dakin tana fadin ka iso ba dan albarka.
Fito muna da ita mu tafi takecewa mamu tana fada tare da Amma muka tafi asibitin Ahmed tun fitowana yake faman yi min sannu yadda nake tafiya ban ganin wuri yaji kamar ya kamani a cikin ransa sai dai ba halin yin hakan gare shi.
Privet Asibitin da suke zuwa gidan mukaje inda ya fara shiga ya samu hanyar ganin likita da sauri ya dawo ya taimakawa Amma ta kamani zuwa ciki.
Likita ya dubani yace zai ban gado in dan kwata tare da allurai a gani zuwa yamma yadda jikin zai sauka min.
A take Ahmed ya sawo maganin dayace basu dashi a lokacin sauran treatment za a saka a bill din Alh.
Bayan ya dawo ne Amma ta gaida shi da kokari ta fara korafin fadin ban taba ganin yan banza yara irin yaran nan ba ace kada wanda ya fadawa yarinyar nan zancen auren nan a yanzu amma don bakin tsegumi irin nasu sai da suka fada taji.
Da sauri Ahmed yace zancen wani aure tana gyara zama take fadin auren ta da yaron nan umar mana sanin bai fada ma bane.
Ai hadin gida yake son yi da yaran wurin su uku yabawa yaranan dasuka dawo da wasu dabi,un kasan turawa sai yanzu yake fadin har sauran ya bada su a tare rana daya zai wanke su duka.
Da Amma ta daga kai taga yanayin da Ahmed ke ciki a lokacin da bata karasa zancen ta ba gaba daya hankalin shi ya tashi da jin wanan zancen da tsohuwar ke rabtaba mashi.
Taja tsuki tana fadin ko ma ina umarun yake yanzu yasan halin da yarinyar nan take ciki oho ta dago kai tana kallon Ahmed din da bai san inda yake ba lokacin.
Ina kake ne tace tambayan ka nake layin wayan umaru idan kana dashi mu kira in sheda mai halin da ake ciki.
Ahmed da gaba daya hankali shi bai tare dashi yaji maganan ta kamar daga sama ta sake maimaita abinda tace din .
Ya sauke ajiyan zuciya yake fadin banda layin kowa a cikin su hajiya daga haka ya fara kokarin ficewa dakin zuciyar shi cukushe da bakin ciki yana fadin .
Shike nan nauyin bakina ya jamin hasaran abindana dade ina mararin sa a raina yanzu shike nan yarinyar nan ta subuce min ke nan mafalkina a kanta ba zai zamo gaskiya ba.
Wuri motar shi ya nufa ya shiga yai mata key ba tare da sanin ina ya dosa ba a lokacin hankalin shi gaba daya ya tashi da zancen tsohuwar da yasan bata karya.
Innalillahi ya ambata yana shafo kanshi tare da fadi a fili shike na an min sakiyar daba ruwa fatima ta subbace mani kenan .
Ashe yarinyar nan ba rabona bace sai kuma yace kai yana bugun sitiyarin motar da hannun shi mema ya hana in fito tun wuri in nuna ra,ayina gurin Alh nasa dana fadi da baiyi wanan shawaran ba gidan shi ya yanke shawaran zuwa a karshe.
Gaba daya lokaci guda ya fita hayacin sa ga zufa na karyo mai duk ilahirin jiki shi zama yayi a falon shi yana nanata innalillahi a fili kafin yaji dan natsuwa nazo mai a hankali.
Daga haka yakai kwance ya dafe kanshi dake sarawa da hannu shi daya yana sauke numfashi a hankali har barcin natsuwa yazo mai bai sani ba.
Mamu da taji shiru bamu dawo ba kuma ba wanda ya kirata tasan halin da ake ciki ta daga waya ta kira maigidan su hankali tashe tana tambayan shi halin da muke ciki.
Yace suna tare da Ahmed na shigo gona in zagaya ni tare da malam mudi amma barin kirasu inji halin da ake ciki.
Kiran Ahmed yai tayi wayan na rigin ba a dauka ba sai hankalin Alh ya kara tashi asibitin ya nufa daga gona shida malam mudi.
Yazo ya samu ina barci ga Amma a zaune ko abin sallah da abinci ba a kawo mata ba da mamaki yake tambayan Amma yaya akai haka inashi Ahmed din Amma tace tun dazun ya fita ina magana dashi naga ya juya ya fita daga dakin.
Kawu yace to lafiya don na kirasa wayan na shiga bai dauka ba ya sake gwada layin sa har ya katse ba a daga ba.
Yace to yaya haka don dai Ahmed bai taba yi min haka ba gaskiya gida ya nufa sai gasu sun dawo tare da mamu da mama hadiye.
Tare da abinci da duk wani abinda za a bukata a zaman asibiti har lokacin hankalin kawu bai kwanta ba na rashin daukan wayan Ahmed din.
Shiko Ahmed da kyat ya tashi yai sallah daga gurin da yake ya jawo wayan shi ganin misscalled ratata a wayan yayi saurin dubawa Alh ne da wasu yaran shagon su ke kiran shi kamar hadin baki sai ga Alh ya sake jefo mai kira da sauri ya daga yana sallama da kyat Alh yace lafiya kake kuwa Ahmed waya nata ringin baka daga ba haka kana ina ne yanzu.
Ahmed yace Alh banjin dadin jikinane ina gidana kwance da sauri Alh yace subbahanallahi gida kana may dabaka zo asibiti ba ?
Yace ciwon ba sosai bane Alh nasha magani ai na kwata ne yasa banga kiranka ba.
Allah ya sauwaka indai ciwon ya matsa ma kayi maza ka kawo kanka asibiti kaji ko yace naji Alh ya kashe wayan .
Su mamu dake jin yana subbahanallahi suke tambaya yace wai ashe baida lafiya ne yasa bai daga wayan ba.
Amma tace ikon Allah lafiya fa ya kawo mu asibitin nan ya danyi zirga zairga ya shigo har ina fada mai abinda ya jawowa yarnan ciwon ta nace dashi ya kira min layi umar din tun lokacin ashe baida lafiya shima dan mutum ba a bakin komai yake ba wallahi.
Ai ikon Allah yafi da nan ko mutuwa akace yayi aiba abin mamaki bane ga ubangiji yanzu suka ce hakane.
Amma ta juyo tana fadin a kira shi umarun yasan da zancen ciwon yar nan don kada muyi abu a cikin duhun kai tunda yanzu yana da hakkin sanin hakan .
Ba bata lokaci kawu ya sake ciro wayan shi ya kira umar din sai da wayan ya kusa tsukewa ya daga yana gaida mahaifin nasa tare da bashi hakkurin rashin zuwa kwana biyu.
Kawu yace ba matsala Allah ya tsare muna ku a duk inda kuke ya amsa da amin sai kawu yace dama na kirakane in sheda maka zancen ciwon yatinyar nan .
Da sauri Umar din yace wace yarinya ke nan daddy a cikin damuwa ya tambaya ?
Fatima yar gurin maimuna da zaka aura muna asibiti da ita tun dazun da safe aka kwantar da ita ba lafiya .
A cikin wani irin murya ya cewa kawu daddy Allah ya bata lafiya ina porthacourt yanzu zuwa safe zan dare zamu sauka insha Allahu.
Daga haka suka kashe wayan lokacin dakin yayi tsit kowa na sauraren abinda zai bada amsa a wayan.
Umar ko yana aje kiran daddy ya sauke ajiyan zuciya a hankali don hjyn su bata dade da kiranshi ba tana fada wai akan auren nan idan daddy su matsa sai anyi zasu iya samun matsala dashi.
Hakkuri ya ba mahaifiyar tasu yana fadin mama ki kwatar da hnkalin ki na fada maki nasan abinda nakeyi fa kwanan ma zamu koma America don haihuwan merry ya kusa insha Allahu mahaifan ta sun matsa mu dawo can.
Babawo yanzu da bakin ka kake fada min mahaifan matar ka sun matsa ma akan ku dawo can mai kake nufi da hakan a can kake nufi zata haihu ba nan ba ?
Ke nan mu nan bamu da wani darajan da matar ka zata haihu a gaban mu sai ka dauketa ka mayar can wata kasa.
Yaya kake son inyi da mutanen arzikina a nan auren ka ban samu yin wani shagali ba ga haihuwan kuma ka dauko wanan zancen ka aza to ban yarda da wanan shawaran ba.
Ya samu ya bata hakkuri tana bambami har katse layin abu goma da goma sun taru sun mashi yawa a kai ga mahaifin merry koda safe ya kirashi ya kara jaddada mashi akan ya kawo masa yarshi kada ya bari ta haihu a Nageria.
Ga kuma abinda mahaifiyar su ta fada yanzu ga kuma daddy da nasa matsalan ya kunnu kai hakan yasa ya dafe goshin shi bai karasa jin meeting din da sukeyi da abokan harkan shi na can.
Yana fitowa kai tsaye airport suka nufa don jirgin da zai taso zuwa Abuja na yamma zasu bi dama ya fito da shirin sa gaba daya.
Sai misalin bakwai saura ya iso kano gidan shi ya nufa kai tssye sallah ya tsaya waje yabi jam,i kamar yadda yake idan yana cikin unguwan.
Sai da aka fito ya shiga gida inda ya samu merry zaune ga kida na tashi tana dan ciye ciyen ta tana bin wakan wani iri yaji a ranshi ba dadi gaskiyan daddy da yake kyamatan merry a daidai lokacin daya dace bawa ya kusanta kanshi da ubangiji yakai kukan sa gare shi.
Ita a wanan lokacin ne take zaune tana bin rudin shedan yana kara zuga ta itako merry tana ganin shi taso yunkurawa ta tashi zuwa gare shi saidai nauyin da tayi ya hanata tashin.
Bai nufo inda take ba sai gurin speaker dake sake sautin ya kashe ya juyo zuwa gurin ta tare da dan dukawa ya rankwafo ya sunbace ta tare da fadin wanan kidan yayi yawa merry baki ganin is time for prayer's now.
I send my pray to god of heaven since morning wani addu,a kuma kake son inyi a wanan lokacin sai kuma idan zan kwanta idan na samu time sai inyi.
Kai ya girgiza yana fadin merry you have to fear god at dis situation you are yace weat Omar what d you mean with dis word ?
Don a zauna lafiya yace nothing ya fara balle maballen rigan sa yana kokarin shigewa dakin su da suke a kasa don saboda condition din merry hawa saman yana mata wuya yanzu.
Bin bayan shi tayi da kallon tare da fadin weat woo what dis man mean with me now ?
Shabi he want me to pray like him, d holl day no rest for humanbeing at all.
Yeeeeee sai ta ja tsuki tana ci gaba da gunguni a fili ita daya tare da kwalawa mai aikinta na kitchen kira.
Tazo da sauri da dan bujen ta tana fadin madam kina nemane tace eh ki kawowa maigidana abinci ya dawo.
Ta amsa da fafin yes ma ta juya zuwa kitchen din da sauri ta tana rawan jikin bin umurnin madam din gidan.
Ta dawo tana jera abincin sai gashi ya fito a cikin wasu kaya sai kamshin turare yakeyi yana gyara hannun rigan shi yace zan fita i will right back in thirty mins .
Tace how about your food is ready yana saman table kallon gurin yayi tare da aikawa mai aikin kallo yayi saurin kawar dakai gurin.
Ya fara tafiya take tambayan shi ina zaka haka ne kake sauri ?
Yace kai tsaye asibiti a dan firgice ta sake tambayan shi wirin wa yace yarinyar nan daughter din step mum take asibiti don shi baya karya kai tsaye yake maganan shi idan ya tashi.
Weat for me zan je in duba ta yarinyar da uwar ta suna da kirki gaskiya ba zan iya mantawa dasu a rayuwana ba.
Dole ya ja ya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login