Showing 3001 words to 6000 words out of 419207 words

Chapter 2 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1384

Kwata kwata hankaliba bai kwanta da zaman yarinyar a gidan bane amma ni ba naki bane da zaman nata a gurin su ai su din iyayyen tane na jini.
To kin san da hakan may zai tayar maki da hankali kuma yanzun kan wanan maganan sai dai idan kina boye muna wani abinda bamu sani bane a can.
Da sauri hjy maimu tace cikin girgiza kanta a, a yaya wallahi ko daya don kawai tarbiyan da yarinyar zata taso a cikin sane nake jawa nan gaba.
Dan murmushi ya sauke a fuskan shi irin ta manyan da suka gama sanin duniya tare da fadin yanzun dai na fahinci yar ki hajiya.
Ta fi bukatan rikon yarta ya dawo hannun ta ke nan hakan zaifi kwantar mata da hankali nake gani.
A sanyaye ta amsa da fadin hakan nake nufi sai dai kuma ina tunanen inda zata zauna isan na dauko tane don nasan ba zasu hani ita ba idan har na bukaci hakan din,
Wanan wani irin magana ne kikeyi ke a ina kike zaune yanzu koda baki gidan nan ai Fatima mai zama a gidana ne balle gaki a gidan baki daya.
Amma ta karbe da fadin yar nan tana da gaskiyar ta ubana hutu kawai yarinyar nan tazo ba a kwshe lafiya da matan ka ba ina ga tazo da zama baki daya a gidan yanzu ?
Haba hajiya yaya kuke wanan magana haka ne kamar ba gidana ba yata ce fa ta cikina Fatima ko ban hada alaka ta jini da uwarta ba ai na hada na aurataya da uwar ta yanzun ko ?
Kafi wani yai magana a dakin sallama hajiya Jumai uwar gidan Alh sani ne ta shigo dakin gaida Amma da kwana.
Wanda hakan doka ne daga maigidan da ya kafa wa kowa a gidan babba da yaro duk safe dole kowa yazo dakin mahaifiyar tashi ya gaida ita da kwana kamar yadda ya tsara masu a gidan.
Amsa mata sallaman sukayi lokaci guda inda ta karaso tana watsawa mijin nata da hjy maimu data samu suna wani maganan wanda bata san ko na may ye ba a dakin.
Ciki kishi daya motsa mata irin na mata ta gaida mahaifiyar tashi da kwana babu tambayan komai ta juya zata bar dakin sai Amma ce ke tambayanta kwanan yaran ta don ta gama fahintar halin da ta shiga lokacin.
A dakile ta amsa da suna lafiya har ta juya hjy maimu ta fara gaida ita da fadin yaya ina kwana kamar ba zata amsa ba ta dai amsa a cikin saurewa da lafiya kawai ta juya ta fita.
Kai Alh sani ya girgiza bayan fitan ta tare da mikewa do barin dakin yana fadin ni zan fita hajiya ina mu kare wanan maganan ke nan ko ?
Kallon hjy maimu Amma tayi tare da fadin ai ga tanan idan ta gamsu da maganan ka sai a saka lokacin da za a dauko yarinyar ko ?
Sai lokacin ta dan murmusa tun fara maganan yarinyar da sukayi tare da fadin a,a magana yana hannu uban yar dai gwago ni na isa in saka rana da kai inyi rashin kunya kuma ?
Ko ya manta a gaban mahaifiyar shi yake ya dan kalle ta cikin kulawa tare da fadi see you kamar ba ita bace ta burkicewa mutane yanzu kan yar tata.
Ranshin kunya ai kin riga da kin gama ko tunda kin nuna muna kin fimu son yar har hakan yana dariya ya fice daga dakin.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
16/11/2021, 17:31 - ??5惙5惙5?: ???SARKA FADI KI RIKICE???


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU


A KULLUN INA GODEWA UBANGIJI ALLAH SUBBAHANAHU WA TA, ALLAH DA YA BAN DAMAN FADAKAR DA DUKU TA HANYAN RUBUTUNA .
DANI DAKU, DUKA UBANGIJI ALLAH YA SHIRYA MU YASA MUFI KATFIN ZUKATAN MU.
LITTAFINA, NA KUDINE MAI SO ZATA IYA TURO DARI UKU TA ACCOUNT DINA 2254380105 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN DARI UKU KACAL DON KIRA ZAKI NEMAY NI A WANAN LAYIN KAMAR HAKA 08036959257
DON ALLAH KI DAURE KI BIYA KI FITA SHIGA HAKKIN WANI KI TUNA DA NAUYIN HAKKI WANI A GARE KI YAR UWA KULLA SABODA ALLAH.


2??_/Q

Tafiya take kamar zata tashi sama sai maganan zuciya take ita kadai wanda ba wani abu bane sai zafin kishin dake cinta a lokacin.
Ba komai take rayawa ba azuciyar ta sai yadda mu,amulan kishiyan ta da mijin ta kullun yake karawa karuwa a zukatan su yanzu ma ganin da tai masu a daki Amma.
Yasa zuciyar ta zargin su akan suna fakewa a dakin ne suna ha,intar su ta hanyar tsohuwar gidan wace take gani da sanin ta ake masu komai na cin fuska a gidan.
A,a giwan bukkan daji kedawa da safen nan kuma ke da ya kamata ace kin tashi da irin annashuwa din nan sai gaki kuma a haka.
Da gani dai wani ya tabaki da safen nan wanda bai san da ba,a taba giwan gida a zauna lafiya ba.
Hajiya maryam ce ke wana maganan mata tabiyu a gida;take magana cikin iri;zolaya da takewa uwar gidan nasu a kullun tana kara izata don ta tunzurata a gidan.
Duk da tasan zolayan ta take bai hana ta tsaya da ita ba cikin dan ja tsuki tana fadin barni da wanan zolayan naki na kullun.
Wanan yar rainin wayau ne mana da Alhaji sai su fake a dakin wanan tsohuwar suna zuba soyayya sun mayar damu wasu bi nan a gidan nan wanda basu san komai ba damu.
Dan dariya hjy maryam ta sake mai sauti tare da fadin hjy kina ban dariya ke sai yanzun kika gane hakan wai ?
Kamar ya sai yanzu na dauka abin nasu mai karewa ne sai gani nake abu sai gaba kawai yake a gare su.
Wallahi ya zama dole in takawa wanan makiran yarinuyar burki a gidan nan don ba zan iya lamuntan wanan cin fuskan da suke muna ba.
Wai ita shu,uma tu da safe zata dauki wanka ta shige wirin wanan tsohuwar da sunan gaida ita ta yadda tasan maigidan da ya shigo da ita zai fara tozali.
Wallahi hjy maganan ki wani zubin sai ya ba mutum dariya makircine fa irin namu na mata ke sa tana zuwa sashen tsohuwar don ta kara kafa gawunatin ta a gurin Alhaji da sauran yan uwanshi.
Amma ai hana wanan abu mai sauki ne a wurin mu nuna masu kawai zamuyi muma mun iya itama dake nata a fili ne zamu rasa ganeta .
Fitowan Ahj sani daga sashen Amma da alama sauri yake a lokacin sai dai ganin su yasa shi dan rage saurin da yake yi din.
A,a yaya na ganku haka kuma lafiya dai ko ya tambaya cikin nuna kulawan shi gare su baki dayan su.
Hjy jummai dake cika tana batsewa har lokacin ta aika mai da wani irin kallo na tuhuma da sauri hjy maryam ta tare da fadin .
Magana dai muke akan jikin hjy wai don jiya ta kwanta tana mitan kafan yana damun ta sosai cikin jin dadi da nuna kulawa ga abinda ta fada yace.
Ai ta samu sauki sosai da safen nan don yanzun ma zaune na samayta tana hutawa tare da yar ta au ashe yarta daya ne a gidan nan gara dai daka fada da bakin ka inji hjy jummai da sai lokacin ta saka masu baki a zancen su.
To hjy ko na fada ko ban fada ai ko diyan cikin hajiya musan maimuna yarta ce ko fadin hakan kuma yanzu laifi ne ?
Ya fadi yana mai tsure ta da idanuwan shi ta wani juya tare da jan tsuki tana kokarin barin wurin.
Kai mata dai baku ranuwa da zancen kishi yanzun kuma may ye a cikin wanan maganan na fushi.
Alh baka fahinci maman salma bane irin yadda kake nuna maimuna ita kadai ce ya gun hjy shine yake bakanta mata rai.
Yanzun dai ba wanan ba naga kamar fita zakayi ko da sauri yace eh fita nake son yi dom ana jirana a kasuwa yanzun haka kaya sun iso gare mu
Saida ta dan rausaya kafin tace da zancen tafiyana gurin maganin nan ne naso in tuna ma don gobe ne tafiyan nawa.
Da sauri ya juya tare da fadin aiko nima ina da abinda zanyi a bauchi kin ga ke nan sai mu shirya tafiyan tare don maimuna zata tafi don yarta dake can.
Wata maimuna kuma kaga Alh kada kama kawo wanan zancen don hanyar jirgi daban ta mota daban ina zan kwashi kishi zuwa tsabagata ta lafiya kuma ?
Don Allah kadama ka hada muna tafiyan mu don ba zani ba sai dai a fasa a fasa fa kika ce ke nan lafiyan taki bata damay ki ba.
Kaga Alh indai har da maimina zamuyi wanan tafiyan saidai a fasa haka kawai kallon mamaki Alh ya bita dashi yana mamakin irin wanan kishin nasu bai iya furta komai ba yasa kai ya fita don idan ya tsaya zata bata mai lokaci.
Shikuma ba zai so hakan ba don abindake gaban shi a lokacin kishin su a kullu kan maimuna ba mai karewa bane.
Ga wani kokarin hadin kai da sukewa junan su yanzu tsakanin ta da hjy jummai wanda yasa ba na Allah bane.
Inda ya barta tsaye da mamakin maganan shi tabi shi da kallon takaici a ranta kallon shiyan hjy tayi kamar ta fasa shiga don maimunan dake ciki sai kuma ta tuna da yin hakan wani laifi ne a gurin ta kuma.
Haka dai ta daure ta fada sasshen tsohuwan abinda ta guda shine ta sama do hjy ce zaune tana bare goron dags cikin ledan data dauko wanda ke cike da fararen goro manya kursa kursa dasu.
Sai hjy maimuna dake zaune a gefen ta tana dan motsa mata kunun da ake dama mata tun da safe ta karya dashi wanan al,adan tsohuwar ne a hakan.
Ga fuskunan su a washe alaman nuna farin ciki a gare su ke na take zuciyar ta ta raya mata wani zargi akan mijin nasu da ya fice daga sasshen yanzu.
Wanda shi ke halaka rayuwan mata da dama watau zargi zargin ma harda mahaifiyar miji za a hada a cuta mai idan ba rashin tunanen mu na mata ba.
Abinda zuciyar ta, ta nasa mata shine wasu kudi suka bukata a wurin alhajin don maimuna din ta kaiwa yarta shi kuma ya yarde masu zuciya ke nan uwar nashe nashe.
Kamar yadda hjy jummai ta gaida Amma ita wanan ta daure takai zaune a dakin cikin nuna kulawanta take tambayan lafiyan hjyn.
Maimu da tun shigowan ta dakin kanta yake duke ta dago tana gaida ita da kwana kamar bata ji ta ba haka ta share maimu din taci gaba da tambayan hjyn halin da take ciki ?
Tana dan bata fuska take fadin kafa da sauki sosai don yana samun kulawan daya dace don yar nan na tsaye a kaina dare da rana wuri ganin na samu lafiya.
Hjy ke nan aiki godewa Allah don shinr mai bada lafiya ba wani ba , lafin takai ayya hjyn ta karbe da fadin godiya kan kullun munawa Allah shi yar nan amma yabon gwani ya zama dole ai.
Yau da babu yar nan a kusa dani ai da ban san yadda zan karata ba mikewa hjy maryam tayi tana fadin.
Kai hjy maganan gizo dai bata wuce na koki ai ko ba ki fada ba munsan zaman ta a kusa dake yana da manufa sosai a girin ku ni zan tafi Allah ya sauwaka.
Har takai kofa ta ce a dai rage fakewa ga sabara a harbi barewa don a idon mujiya ake komai.
Allah ya sauwaka maimuna dake zaune ta fadi cikin rashin kulawa da maganan kishiryar tata don idan da sabo ai ta saba don basu haduwa basu sake mata irin wanan maganan ba na kishi wanda ranta yakan baci sai dai bata yarda ta nuna masu gazawan ta a kullun.
Bata dade a part din ba ta mike tana fadin gwago ni zan tafi don yaran nan nan san yanzu sun falka ban kusa dasu.
Hakane inji Amma yanzun ko zaki iya ganin su a nan don ba karamin aikin uwata bane hakan ta fado muna da korafin kin fito kin barsu kamar wata wace za a kama.
Yarinya haka bata da yarda da kowa a gidan nan sai kace bakuwa a gidan nan.
Gwago yanan gidan ne yasa ta tashi da hakan don in ba nan gurin ki ba babu mai kulasa ni shine matsalan dake damuna a gidan nan .
Ace kishi harda yara ake hadawa don rashin tunane an hana yara zumunta a tsakanin su saboda wani akidar banza can .
Daga haka ta bar dakin tsohuwan data barta a zaune ta bita da kallon tausayi don tasan gaskiya yar tata ta fada yanayin gidan yana nuna kowa dan shi ya sani.
Hakama yaran gidan kowa dan dakin su ya sani baisan wani ba duk wanan abin yasamo asaline daga gun hjy jummai dake zama da yaranta a daki tana tura masu mugun akida akan kowa na gidan makiyin su ne.
Dan garama yanzu da akwai dan shirin yaran nasu sukan dan kula juna a tsakani su wanda ya zama dole dama don alaka ta jinin dake akwai.
Sai dai diyan maimunanen basu yarda dasu ba a cikin su wanda hakan na bata ran uwar yaran shine abinda take tunane ga dauko yar tata tazo ta zauna a gidan tare dasu .
Yaran dama ta haifa a kidan an kisu balle yarda ba a gidan ta haife ta ba duk da maigidan yana iya kokarin shi wurin kawar da wanan akidar a gidan.
Yakan tara yaran nasa wani lokaci wuri daya yana nazarin halaiyar kowa a cikin su akan dan uwan shi.
Inda ya kula dacewa suna ware yan kannen nasu tare da nuna masu cewa yaran daban suke a cikin su wanda yakan yi amfani da wanan daman wurin nuna masu yaran nasa kanana ma yan uwar su ne na jini.
Ba laifi wasun su suna rage wanan akidar a cikin su suna dan kokarin kwatantawa akan yaran wanda wasu kuma hakan bai shiga zuciyar su ba don sun riga da sun samu huduban hakan daga gun iyayyen su tun farko.
A ko wani gida akan samu tsageran yara a ko wani daki hakan ne yake faruwa a gidan Alh sanin don yaran hjy jummai da koda yaushe ita akidan tane zama da yaranta tana nuna masu rashin yarda da kowa daga bangaren yan uwan su.
Abin ma bai tsaya a nan ba har yakai kowa suna mashi wanan kallon na maha,inci a gare na yarda basu da marmari a gun kowa da ya san su.
Sai mutane ke masu kallon masu ji da kansu ko marasa marmari a gun jamma,a din sai ba mai son wani mu,amula dasu sosai yana da wuya su yi saurin amincewa mutum wanan ke nan.
Rai bace hjy maryam ta karasa part din ta inda ta samu mai aiki na mata gyaran part din wayan ta dauka tayi waya da wata yar uwarta da zasuyi tafiya tare.
Inda take sheda mata yadda sukayi da maigidan nasu akan tafiyan da zasuyi a washe gari da wani irin mamaki aminiyar tata ke fadin .
A, a lallai wanan matar samun wurinta ya na son wuce wuri a gidan ku yanzun tafiyan neman maganin ki ma harda ita za,a tafi don son kure mutane ko may ?
Barni da Alh wanan karon za,a jimu sosai idan yace har da ita zamuyi wanan tafiyan don ba zan kyale su ba.
Sin dan dade suna tauna maganan inda yar uwar tata ba hakkuri take bata ba sai nausar da ita hanyar bata irin na matan da basu da fahinta.
A bangaren hjy maimuna ta samu yaran ta na barci har lokacin kasancewa ba school a lokacin yaran suna hutu makaranta a lokacin .
Bata barsu ba kokarin tayar da yaran tayi tana koya masu yin sallah a cikin lokaci duk da sun makara amma hakan take kokarin koya ma yaran sallah safe.
Suna gama sallah tayi masu wanka inda ta shirya su suka fito falo don karyawa duk da gaba daya ake abin karyawa a gida kowa yakai kayan shi dana yaran shi a zuba mai abincin sa a ciki.
Duk da tana kai nata kulan don karban rabonta amma hakan bashi ke sa suci wanan abincin ba don rashin yarda da masu aikin da batayi ba tun ranan da aka saka masu magani a cikin nasu abincin.
Allah ya taimakesu basu ci ba ta gani tun wanan ranan bata kara yarda da wanan abincin na taro da ake kawo mata daga cikin gida.
Har sai idan itace da girki ta shiga kitchen da kanta ta dafa kamar yadda takeyi a kullun idan tana da girki ita zata je kitchen ta girka abincin da kowa zaici

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login