Showing 216001 words to 219000 words out of 419207 words

Chapter 73 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1498

dakin zaune sun tsura mashi ido a cikin tashin hankali.
Jin an turo kofa yasa suka juyo lokaci daya suna kallon kofan don sin hana kowa shiga saboda rikicin dayaso tashi tsakanin hjy jummai da hjy maryam wurin jinyan.
Yasa suka hana kowa shiga a yadda sukaga dama da farko an rabawa kowa lokacin zuwa saidai hjy jummai tace basu isa ba zata zo a duk lokacin da taga damane ita.
Yasa suka kasa suka tsare don sanin halinta suna jinyar dan uwan nasu da kansu wanda hakan yasa duk wanda yazo saidai ya tsaya daga waje inda kowa yake sai idan suna bukatan wani abin zasu kira wacce keda duty a lokacin tazo ta taimaka masu da wani abin.
Ganin ya umar yasa su sauke a jiyan zuciya suna fadin umar ka taso ke nan ga Alh nan jikin yaki har wanan lokacin.
Direct wurin gadon da mahaifin nasa yake ya nufa kai tsaye ya dan tsaya a kansa ya tsura mai idanu .
Can ya juyo yana fadin likita yayi bayanin akan matsalan dake damun shi ?
Kawu balarabe yace eh to yayi bayanin don sunce akwai hawan jini da sugar sune mu sabbabi matsalan duka.
Ya umar yace zanso mu fita dashi waje don zaman shi a hakan ba ba dadi gaskiya tunda an gwada na nan ba aci nasara ba har yanzu.
Allah sarki mukan ai munga sauki yanzudon yau ma an samu cigaban samun lafiya sosai don yana bude idanun shi lokaci lokaci.
Ajiyan zuciya ya sauke don jin bayani su ya juya yana kurawa mahaifin nasa idanu mai nuna zallan tausayi a gare shi .
Ya kara takun shi zuwa wurin gadon ya tsurawa kawu idanu kamar yasan shine a gurin sai ya bude idanun shi a daidai lokacin ya kafe umar din da idanuwa kamar yana kokarin sheda ko waye a gaban shi lokaci.
Daddy sannu umar din yace mai sai ya lumshe idanuwan shi a hankali dan dukawa umar din yayi daidai saitin kan mahaifin nasa yana mashi adduan samun sauki daga Allah.
Yakai wani lokaci a hakan kafin ya dago daga dukawan da yayi din ya juya zai fita daga daki nmuryan kawu balarabe ne ya tsayar dashi.
Zaifi kyau ko zaka fita dashi a bari har ya kara samun lafiya zaifi tau baba Allah ya tada kafa dan shi yaba daddy lafiya suka amsa da amin.
Ya fito da sararen gwiwa don yadda yaga daddyn nasu a lokacin rai a hannun Allah.
Jin kara bude kofan yasa na wajen juyowa suna kallon mai fitowa daga dakin .
Umar ka fito mama hadiye tace dashi yace a wani yanayi na nuna rashin jin dadin shi ga ganin mahaifin nasa.
Ya dan samu wuri ya jingina bayan shi ga bango tare da harde kafan shi daya a cikin daya.
Ya lumshe idanuwan shi muryan mama hadiye ne ke fadin kaje gida wurin hajiya ka huta don da alama isowan ka ke nan daga airport ka nufo nan.
Bude idanuwan nasa yayi tare da sauke ajiyan zuciya yace Amman tana gidane mama tace eh dazun nan ta koma tazo taga jikin yaya din.
Yaya su Fatima dasu Amina sarka sarkin rikici duk suna lafiya ?
Ajiyan zuciya ya sauke kafin yace suna lafiya na barta saboda karatun ta da ya fara nisa yanzu,
Dago kai hjy jummai tayi ta watsa mashi wani kallon takaici ta kawar da fuska a gurin su.
Wasu daga wurin sunga abinda ya faru sai dai basuyi magana ba ya dan busar da iska yana fadin zan dan je naga likitan dake kulla da daddy din .
Suka amsa mai ya tafi ko juyowa baiyi inda suke zaune din zuciyan shi cike da damuwa ko kallon yanayin nasa yaje gurin likitan sun dan dade a office din kafin ya fito kai tsaye gidan mahaifin shi ya nufa wurin Amma.
Kamar a mafaki tagan shi falon nata sadauki kaine rafe ashe kana da labarin abinda ya faru da mahaifin naku ?
Ya kai zaune tana kokarin tashi da kyat yace ina kuma zaki Amma tace wai in kawo ma abun sanyi ka sha ko ta fada tana kallon fuskan shi.
Yace barshi kawai Amma ya mike ya nufi wurun fridgen din nata da kanshi ya bude ledan ruwa da sauran tarkace yagani yadai dauko ruwan ya dawo ya zauna a inda ya tashi da farko.
Tace tana kallon shi kai kadaine tafe wai banga mutumiyar tawa ba tashigo.
Ya kalle ta da idanuwan shi da sukai mai ja yace banzo da ita ba ni kadai nazo sai wani jikon zan shigo da ita wanan tafiyan bana hankali kwance bane.
A ikon Allah zan so ganin mutumiyar tawa inga yadda ta koma yanxu.
Ya dan tabe baki tare da fadin tana nan yadda kika santa sai karatun ta da yanzu yayi nisa sosai.
Mikewa yayi yace zanje in dran, huta na dan wani lokaxi tun yanzu baka ko huta ba ?
Yace eh nazo dai kawai in ganki ne yace yana kokarin fita daga falon nata kai tsaye sai dai cikin ran shi yana mamakin halin mahaifiyar su.
Don dai irin kallin da rake jifan shi dashi yasare masa gwiwa sosai do yasan tana cike dashi sai dai ba zaice ga laifin da yayi ba lokacin .
Sai ba bayan azahar ya falka wanka yayi yafito yayi sallah kai tsaye asibuti ya nufa.
Wanan karon iya hjy maryam ya sama a asibitin wurin mahaifin nasu itace keda zaman rana a wurin shi karfe shidda mamu zata karba ita kuma ta koma gida.

Tun dawowa na na kasa sukuta komai a rayuwana sai faman tunanen da nakeyi ni kadai zaune a falo ina yawan kallon kofa da wayana na dake gefena aje ina sa ran kiran yaya umar a lokacin.
Saidai har dare gashi bai kirani ba balle inji idan Nageria ya tafi a ban wani na gida muyi magana dasu.
Saidai bai kira ba har lokacin da nagaji na mike na kashe komai na shuga dakin kwanana na kwanta da kyat na samu barci ya zo mi lokaci.
Waahe gari ma haka na daure zuwa daukan karatu don fita zamuuyi yin pratical da malamin mu .
Ban yarda mun hadu da anty farida ranan don kada ta gane ina cikin damuwa tai min wani fassara na daban.
Gashi har lokacin ya umar baibugo min waya ba ni kuma banda layin kowa na gidan namu.
An shigaKwana uku shiru ba wayan ya umar ba dalilin kiran shi hakan ya kara tayar min da hankalina sosai.
Haka yasa na fara zargin ko dai wanu a babu ya faru da kawun ne hae ya saka ya umar ya tafi .
Gabana ne ya fadi sosai a lokacin take na shuga share kwallan da ya zubu min a idanuwana daka ganni kasan akwai damuwa a tare dani lokacin
A rana na biyar ne ina zaune nayi tagumi sai ga wayana yana ringin na dauka ina dubawa ya umar dinne ke kiran layina.
Da sauri na dauki wayan ina kokarin karawa a kunne na da sallama ya amsa min da kyat tare da fadin kina nan kin saka kanki cikin damuwa ko ?
Nace ya don Allah ka fada min idan wani abu ya faru da kawuna ne in sani yace ba na fada maki baida lafiya bane ?
Yaya kayi hakkuri ban son in rasa kawune yanzu ke kina masa fatan mutuwa ne ko may da kike fadin wanan magana ?
Kukan dana fara yasa ya kashe wayan gaba daya haushin kaina naji dana kasa controling din kaina a lokacin balle inji halin da kawu ke ciki lokacin.
Daga lokacin bai kara kirana a waya ba duk zaman garin ya isheni ban san ko ina ba daga gida sai school saboda sabon da mukayi tun a gida da rashin fita ko ina yasa ko a nan ma wanan halin ya bini hakana.
Na ramay na lalace ko wani gyara duk na daina karatuma kamar ya zama min dole nakeyin shi ban san ina son kawuna haka ba saida hakan ya kasance dani yanzu.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:19 - ??5惙5惙5?: SALAMU ALAIKUM YAN UWA MUSULMAI, , , , , ,


Wasa wasa saida ya share fiye da wata daya a gida duk da banda wani matsala a bangarena ko na abinci dana wurin karatuna ga baki daya.
Tun ina tunane har na gaji na fawwala al,amarin ga Allah ranan da kadaici ya isheni anty ta karbi wayana ta bude min whatsfapp naji dadin hakan sosai don ranan wuni nayi ina kallon yan makarantar mu da nake da layin wayan su.
Wani dp na saka inda mukayi da wasu coursemate dina nice a tsakiya sun rugumoni su biyun muna saye da labcoath a jiki mu cikin nishadi.
Tsananin hasken fatana na daya karu yanzu yasa mun saje da su dan banbancin dai kadan ne dasu a photon.
Son da nakewa photon yasa na saka shi don sune kawayen da nayi na kut da kut da muke karatu dasu.
Munyi photon a cikin farin ciki da so da kaunan juna a tsakanin mu don hakane na zabi wanan photon a matsayin dp din wayana.
Zaune nake saman dogon kujeran falon na mike kafafuwana ina kallon tv dake aiki sai corn dake hannu na ina ci a hankali ga waya da na mayar da hankali muna hira da anty farida cikin harshen hausa.

Nigeria Kano
Ya dawo asibiti gurin daddy da yanzu akafara ganin sauki gareshi sosai yasa hankalin iyali ya fara kwantawa .
Ya umar ne ya shigo falon shi a lokacin tun safe da ya fita zuwa asibitin yana can gurin daddy shida yan uwan shi sun kewaye mahaifin nasu a nan su salma da mazajen su suka samay su aka cika taro dasu har wani lokaci suna gurun Alh a zaune sai matan ne suka dan fita daga dakin zuwa inda uwayen su mata suke zaune.
Karfe hudu ya baro asibitin zuwa gida sai da ya zauna yaci abincin da mai aikin shi ya girka mai yaci don bai tsaya karyawa da safe ba ya fita .
Ya gama a wurin yai zaune tare da balance saman kujeran da yake zaune a kai ba gwanin shiga whatsf bane shi amma ranan sai yaga ya shiga don duba sakonne kamar yadda yakeyi idan sun taru.
Ya gama komai kamar ance ya duba sunana daya rubutawa kaddara sai yaganni a online da alama ina saman interneat a lokacin da sauri yace kai , tare da dan zabura da mamaki.
Da sauri ya tura sako ke may kike a nan ?
Waya bude maki wanan abin kike yi ?
Jin sako ya shigo min a jere lokaci guda yasa na aje corn din dake hannuna ina kallon waya da mamaki.
Baki na mere ni kadai a gida ina jan tsoki tare da fadin dan rainin wayau kawai so kake in mutu a garin mutane saboda bakin halin ka.
Ban bashi amsa ba sai ma sauka danayi ga baki daya na mike tare da kashe komai na falon na hau sama na kwanta.
Ina tsaka da addu,an shiga barci waya ya dauki rurin kira a lokacin dubawa nayi ya umar ne yake kirana .
Kallon wayan nakeyi ba tare da na dauka ba har ya gaji ya katse ban daga ba sai can naji sako ya shigo min again share shi nayi sai can na duba sakon naga ya rubuta ke ki dauki waya nace.
Kaci min mutunci daga can ko ka raina min hankali tunda har yanzu na goye kake kallona a idon ka kin dauka nayi na share shi barci yayi gaba dani a gurin.
Shiko yana can yana cika yana batsewa har akai magariba yana jin kamar yai tsutsu ya ganshi a London ya makeni.
Kallin dp din dayayi zooming a wayan shi yayi mun fito shar damu a photon da kayan gwaji a jikin mu inda nau,in jikin mu ya nuna mabanbantan kasa muka fito gaba dayan mu.
Kiran sallah yasa shi mikewa ya nufi ciki alwala ya dauro ya fita daga gidan a gaugauce kada ya rasa jam,in sallah magariba na lokacin.
Yana fitowa ya nufi family house din su kai tsaye wurin hjyn su ya nufa duk da hattaran shi da uwar keyi tun zuwan shi kasan .
Sai yake nuna baima sam tanayi ba don zai shigo ya zauna dukda nuna mai kin kulawan da take sai yayi zaune yana bata lokaci da waya a hannun shi.
Sai idan su Aliyu sun shigo ne suke dan zama suyi hira wani lokaci kuma su kwasa su fice zuwa asibiti.
Har yau hjy saboda bakin ciki ta kasa bude baki tayi mai magana ko ta tambayi iyalin shi ga baki daya batayi ba.
Yau ya shigo babu kowa a falon sai tv dake aiki yayi sallama ya shiga kai tsaye ya samu wuri ya zauna shi kadai a falon.
Nafisa ne ta fito jin sallaman shi tana amsa mashi sallaman nasa tare da fadin ya umar ashe ka shigo.
Yace ummm a dakile tace yaya in kawo maka abin karyawa ne duk da tasan ba zaici ba halin sa ne wanan tun lokacin da ya tare a gidan shi bai damu dayaci abinci a gidan ba.
Ta samu wuri ta zauna tana fadin ni yaya wai yaya A ruwa ban samu tambayan ka ita ba tunda kazo ?
Dan dago kai yayi yakale ta yace tana lafiya karatu ya hana inzo da ita daka koma da ita inda ka dauko ta.
Muryan hjy mahaifiyar su ne, dake fitowa take magana tare da hararan shi dan murmushi ya sake yana fadin barka da fitowa mama.
Ya dan zamo daga inda yake zaune yana gaida ita da kwana bata amsa mai ba sai cewan da tayi kana zaton na janye maganata akan auren wanan makiran yarinyar da kakeyi.
Idan sun mallake ka sun mallake ubanka ni basu mallakeni ba ni ba kuma ba zasu iya mallakeni ba yadda suke so.
Har yanzu ina kan bakana sai ka saki wanan yarinyar don ba zan hada iri da irin matsiyata ba a zuri,a ta.
Ayi hakkuri hjy lokaci na zuwa da hakan zai faru ina wanan abin ne saboda ke da daddy mu.
Sabodani ta fada da dan mamaki tana kallin shi tare da kada kai tace ka dauka zaka iya yaudarata ne babawo ?
May ka mayar dani ne wai kana nufin zaka zauna da yarinyar da baka so har tsawon shekara daya da rabi da ita kana kallon ta ?
Wani irin dagowa yayi yana kallon mahaifiyar tasu da mamakin kalamin ta gare shi tace kai waliyi ne ko shehi da zaka zurawa mace haka idanu kana kallon ta ?
Kiyi hakkuri mama ba hakan nake nufi ba wanan yarinyar karatu take yanzu haka a can sune dalilin da kikaga ban dauki wani mataki akanta ba har zuwa wanan lokacin.
Aliyu ne yayi sallama ya shigo kallon yanayin zaman su ya fara sai kuma ya juya wurin mahaifiyar su yana gaida ita da kwana kafin ya juya wurin dan uwan yana fadin bros ashe kana nan gidan ka na fito yanzu daga can nake nayo nan.
Yace na shigo ingaida su da kwana don in na tafi asibiti ba zan fito da wuri ba yana nan yana karanta min hauka don ya daukeni mara hankali.
May kuma akayi mama yana kallon dan uwan nasa ta tabe baki tana kawar da kai daga kallon shi.
Umar da dama yake neman hanyar gudu daga wurinta yayi saurin mikewa tsaye yace barin leko Amma mu gaisa in zo mu wuce.
Zaka dawo ka samay ni ai hjy tace tana hararan shi shidai ya fice ya barsu da Aliyu a falon zaune.
Ya samu Amma tare da mamu a part din mamu tana ganin shi nauyi da kunya ya kamata lokaci guda ta shiga dan kamay kamay taga surikin ta wai.
Gaida su yayi a daidai lokacin da mamu ke mikewa tace gwaggo zan tafi sai dai idan na dawo ke nan kuma.
A,a kardai ince yanzu kuma kunyar Sadauki kike ji kuma maimuna ta fada tana kallin mamu din da dan murmushi a fuskanta.
Mamu tace kai haba gwaggo kunyanshi kuma tana kokarin fita daga falon yace naso tunda nazo in baki layin wayan ta sai dai bamu samu kebewa da ke b.
Jin hakan yasa mamu ta dan tsaya daga tafiyan da takeyi din tace badai tana lafiya ba ?
Lafiya take yace yana kokarin ciro wayan shi a cikin aljinhun shi yana duba lamban na.
Mamu da za,a bude zuciyar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login