Showing 72001 words to 75000 words out of 419207 words

Chapter 25 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1400

kuma ?
Ni dai ko da ta dawo na dubi lokaci naga sha daya da rabi na dare na shige na barta a falo zaune.
Washe gari ne tunda safe zanfita na fito tunkan in karasa naji mutum yana waya daga kofan shigowa gidan haka yasa ban bude get din gidan ba na dan saurara inji ko waye.
Daidai lokacin kunne na jiyo yana fadin merry giwa kika sha da cikina a jikin ki kina haukane ko may ban fada maki shan giyan nan zai rabamu.
Gabana ya fadi ina sauri inga ko waye a cikin su yake wanan maganan bansan lokacin dana taba kofan ya bada kara kiiiiiii,
Ya juyo yana duban kofan yaga mai fitowa wanan lokacin da sasafe haka ina kuma mai shi zai tafi ?
Karaf muka hada ido dashi daga cikin nikaf din da fuskana ke rufe ido ya dan dauke gareni tare da ci gaba da wayan shi Umar faruq ne dai wanda yammacin jiya naji yana wayan shedanci da mace.
Yau kuma da safiya na kara jiyo kalamin da ya girgiza min zuciyana daga bakin shi wai cikin shi a wata mace bayan Amma tana fadin baiyi auren fari ba to a ina ya samo mace mai ciki kuma.
Na sakar mai harara bayan na kware dan nikaf din fuskana don ma ya shedani da kyau kuma na jishi.
Da ace a cikin su zanji wani yayi irin wanan magana a kanshi zan iya karyata mai shi a lokacin don shine yafi kowa shiru shiru da dan kirki zaka gaishe shi ya amsa kuma gashi ibada bai wuce shi.
Ke da wata murya a kausashe ya kirani kamar kada in tsaya sai kuma na juya ina dan magana da baiji nace ba sunana ke ba malam.
Ashe yaji abinda na fada yace idan ba sunan ki ke ba waye sunan ki ko da yake sunan ki da sanin shi da rashin sanin shi a gare ni duk daya ne.
Ina zaki fita da wanan safen haka kin wani bat da kama kamar wata ninja dake dan baki na murguda nace ba dai yawan banza zan tafi ba kaga abinda ke hannuna ai .
Juyawa yayi ba tare da yayi magana ba bayan ya sauke idon shi akan litattafan dana rika a lokacin.
Na dauke kai nima na fara tafiya yace kin iya labe kina sauraren mutun ko kamar kada in jiyo sai kuma na tsinci kaina da juyowa ina fadin.
Laben mai zanyi ko inji may inji aikin da kake aikatawa kana fuska biyu a gidan ku ?
Kallon mamaki yake min karamar yarinya da irin wanan maganan a gare shi har yaushe raini ya shiga a tsakanin mu haka ?
Fuska biyu har na wuce yana maimaita magana ta a ran shi koda ya dago kai nayi nisa da tafiya ko haka yasa ya kyaleni bai sake magana ba.
Nikan har nakai makaranta ban daina zagin shi a raina ba ina tsine masu gashi Ahmed ya hana ni fita yau ma ganin ya dade baizo ba yasa na fito sai naga na iso school din a cikin lokaci.,
Muna tashi na dawo gida da sauri don zuwa tafsiri da mukeyi da mamu har lokacin ina mamakin rashin zuwan Ahmed ranan.
Sai dai koda na shigo ban samu mamu ba ta fita na tsaya ina mamakin mai mamu ta samu ne ina take zuwa haka don ban santa da yawo ba yawan zuwa unguwa don ba wasu kawayene gare ta ba sosai.
Wanka nayi bayan na na fito na shirya na hada ma kanne na abinda zasu karya dashi sanan na kara kwanciya ina jiran dawowan mamu anan barci mai nauyi ya dauke ni na barsu suna kallon katun a falo.
Bani na falka ba sai daya na rana koshi fitsari ne ya damay ni a lokacin yasa na tashi bayan na fito daga falo ne na samu mamu ta dawo lokacin .
Tana zaune a falo da yara tana waya sai dai tana ganina tace bari ai zan dawo yanzu dama wanka nazo inyi a gida.
Ta dago bayan ta kashe wayan tana kallona nace mamu fita zaki kara yine kuma ?
Tace eh yanzu ma nake fadin in tayar dake ai don tun da na shigo kike barci a gidan nan kinga sai karfe hudu zaki dora girki idan ban dawo ba ta fada min abinda zanyi,
Bata dade ba ta fita na cewa yan uwana mu leka Amma mu gaishe ta muka dunguma zuwa sashen Amma din a zaune muka samay ta tana gyagyadi ita kadai.
Dan sanda nayi zuwa gaban ta nace agudu ta mike zubur tana waige waige tace ja,ira ubanki sani kika tsorota.
Na turo baki nace ke Amma daga dan magana sai ki kama zagin mutum dakuwa ta kara min tace gidan ku ki fita idona yar nan .
Ni zaki ba tsoro a dakina nace ke halin ki ke nan da anzo wurin ki sai kin batawa mutum rai tace yanzuma waya kiraki ko kinga sakona gare ki ?
Ina jiya nan kikai fushi dani aina dauka zuciyar naki zakiyi a yanzu ma nace da yake kin iya hadi ba inyi fushi ki hadani da mamu ko kiji dadi.
Baki da kirki wani lokaci A ruwa yanzu ki rasa wanda zakiwa sheri sai sadauki yaro natsatse mai hankali da sanin ya kamata .
A wurin ki ba nikan ai a tafin hannu na yake Amma don nasan abinda baki sani ba wanan mai fuska biyun zaki wani ce wai natsatse dashi.
Wani kallon haushi ta aika min nace ai in an kawo maki goyon dan shege kuma na kafira zaki bayani .
A take annurin fuskanta ya kara gushewa gaba daya tace a cikin wani murya da ban taba jinshi gare ta ba.
A ruwa sherin naki har yakai ki kalli tsaban idona ki fada mi wanan maganan lallai da akace da wasa da yaro gara kwana da yunwa na yarda yau.
Ganin ran tsohuwar ya baci sai jikina yayi sanyi nace Amma don Allah kiyi hakkuri naga tobashina ne ban zaci ranki zaikai ga baci haka ba.
Sai naji ta sauke ajiyan zuciya tana tana girgiza kai tace badon kece kikai min wanan wasan ba da yau anjimu a gidan nan.
Shiru nayi kafin in kara fadin yi hakkuri Amma don Allah tace ai ya wuce amma kayiwa dan uwanka fatan alheri shine kyau.
May ye laifin yaron nan da yai tsaye sai da yaga an dauko kakarki an kawo ta garin ya tsaya tsayin daka sai dan uwanshi ya dubata.
Da sauri na dago kai nace Amma ban fahince ki ba wai wa kike magana akai tace barshi kawai idan baki sani ba sai lokacin ta tuna da basu son in sani don kada in daga hankalina a yadda take.
Ganin tayi shiru yasa na kasa kwantar da hankalina kafin in magana sai tayi kokarin mikewa tana fadin lokacin sallah yayi kinzo kin tsatsare ni da wanan surutun banzan naki ni kinga tafiyata zuwa alwala.
Ta barni ina binta da kallon mamaki da sauri wani tunane yazo min nace a raina kodai shi yasa nake ganin mamu bata zama tana busy tun jiya.
Zubur na mike ina kokarin tattara yan kanne dake wasa a falon suka karbe key din suka sheka da gudu.
Ina tafe jiki ba karfi hankalina ya tafi ga tunane banyi aune ba mukai karo da mutum da sauri na dafe goshina da naji zafi ina dago kai don ganin waye.
Habbib ne sun fito zasu mosque da dan uwan shi yace a hasale ke wata irin balagazan yarinya ce mara tarbiya ke mahaukaciyar inace ?
Ka barta yace daga baya shin inji yayan nasu kila iskacin nata zai kawo gare mune da nine ball zanyi da yar iska a wurin nan.
Tsuki yaja yana fadin may yasa baku da tunane wanan yarinyar haka take da rawan kai ku kyale ta kada mu rasa sallah.
Daya bayan daya suka wuce ni suna magana akai a hankali nake bin su da kallo har suka fice gidan.
Naja kafana da kyar ban dade da shiga ba sai ga kiran sallah anayi haka yasa na shige bayi na dauro alwala.

Amma na zaune a inda ta idar da sallah a falon ta tana jan tasbaha ya shigo falon yayi sa, a babu kowa a falon ita kadai ce zaune.
Ta dago kai fuskanta cike da farin cikin ganin shi a lokacin ya tako ya zauna gab da ita yana tankwashe kafa tayi sauri ta shafa adduan da take ta dube shi tace.
Dan nan ina kake shiga kwanan nan baka zama ga azumi ga zafin rana kana cikin sa ya dan canza yanayin fuskan shi zuwa na damuwa yace.
Wallahi Amma wasu aiyuka masu muhinmanci nake yi suka dauke min hankali sai dai yanzu na gama kammala su sai dai damuwa ta daya ce.
Tace Saudaki maye damuwan ka kuma bayan gamu a raye muna gaban ka har wani abu zai damay ka.
Yayi wata sanyayar ajiyan zuciya tare da tsure ta da idon shi yace Amma ai barin ki da Allah yayi har wanan lokacin ina ganin kamar don nine gaskiya.
Gabadaya hankalinta ta mayar gare shi tana mai kallon a cikin rashin fahintar inda maganan shi ya dosa sai da ya gama tace kai ko may ke damun ka dakake tunane haka ?
Yayi shiru sai wani gumi ke feso mai a goshi ya kasa magana Amma ko sai tsura mai ido tayi a cikin gigita hankalin ta ya tashi ganin dan lelen nata a cikin tashin hankali.
Can tace sadauki kayi magana karka daga min hankali nima kan abinda ban sani ba tukun ka tayar min da hankali sosai.
Wani ajiyan zuciya ya kara saukewa yace Amma nasan ke kadai ce mutum na farko da zata fara fahintana a gidan nan.
Amma nasan duk irin abinda na dauko ba zaki taba guje min ba idan ma kowa yaki abin nasan kina tare dani domin fahintar ki.
Kayi maganan ka kai tsaye Umaru don in fahinci inda ka dosa ka tsaya kana min kwanaye kwanaye.
Yace cikin dukar da kanshi kasa Amma ina da aure har da rabo sai dai matar tawa a yanzu bata haihu ba shiyasa, , , ,
Sadauki, Umaru kace kana da aure harda rabo yace kwarai Amma sai tayi wani irin ajiyan zuciya mai karfi ta dukar da kai kasa tana tunane.
Can ta dago tana fadin sadauki haka kai muna ina daukan ka mai hankali ashe abin ba haka yake ba ?
Umar ya sunkuyar da kanshi ya kasa dago kai ya kalle sai ya ji wani nauyi da kunyar kakar tashi a karo na farko a rayuwan shi.
Cikin dakewa yace wallahi Amma kin san mai rai bai wuce kaddaran shi a zane yake nifa damuwa ta daya ne yanzu yadda su baba su amice mata a gidan nan.
Don ita din ba musulma bace ina dai kokarin ganun na musultar da ita ta zama musulma din nan gaba.
Jikin Amma ne ya fara bari tana tafa hannu alaman mamakin jikan nata da take gani mai hankali a cikin su tace ni Amamata na shiga uku yau ni jinina ya daukowa kafira a gidana.
Allah mayyasa ka barni inga wanan bakin ranan a gareni baka daukeni daidai lokacin da ka dauki mijina Attahiru ba a duniya.
Nan hankalin umar ya kara tashi kololuwa yake ji kamar ya hadiye ranshi a lokacin don zafin kalamin tsohuwar shi bai ga laifin a cikin auren da yayi ba da ake wanan tayar da jijiyoyin wuyar haka ?
Haka Amma ta barshi a zaune ba magana kamar bata san dashi a wurin ba lokacin sai faman salalami takeyi.
Can yaji muryan ta a cikin wani yanayi tana fadin idan ka gama zaman naka zaka iya tafiya tunda ka isar ma kanka ai.
Dan murmushi ya sakar a fuskanshi na karfin hali tare da fadin haba Amma a gurin ki nake kyautata zaton samun sauki a kan komai dana aikata ba tare da sanin ku ba don ke din ba jahila bace kinsan kaddaran rayuwan bawa.
Sai kuma yanzu na fahinci kuskuren tunanen hakan a yadda kika sanni kika san tarbiyar da kuka bani bai kamata ki mani fahintar da bashi ba Amma.
Umar ta ambaci sunan shi yace yau ta baci mai sau biyu ke nan Amma tana ambatar sunan shi da bata kira don yana sunan surikin ta.
Tace bawai ban fahince ka bane na yarda da nasan kaddara sai dai abinda baka gane ba shine niba auren ka na jahilta ba auren kafira arniya na jahilta a zuria ta.
Idon shi ya runtse lokaci guda yana jin zafin zagin da Amma ke surfawa matar shi merry har cikin ranshi.
Amma tace shike nan abinda mahaifin ku ke nunar da Jummai ya tabbata a kanka umar mahaifin ku a kullun fargaban shi ke nan da tsoron kada haka ya faru da dayan ku tun lokacin da ta sa fitinan sai kuje kasan waje karatu ita duk diyan kawayen ta suna waje .
Amma, Amma kin san ba laifi bane hakan ga addini ina sane da abinda nayi ita kanta yarinyar mace ce ta samu irin wanan kalubalin a gurin iyayyenta amma ta nace sai ni .
Ta bar komai nata da kowa nata tazo ta aure ni Amma don may nina miji ba zan iya hakkuri in rungumi kaddara ba tunda Allah bai hanani ba.
Wani irin nisawa Amma tayi tare da fadin Uhhmmm zamani yau Allah ya kawo ni kallon zamanin Annabi shaho da rayuwa a cikin zuria ta.
To ai sai ka je ka fadawa iyayyen naka abinda ka aikato masu can da bakinka ka fada masu tsaraban da kazo masu dashi.
Haba Amma ban taba tsamanin haka daga bangaren ki ba a duk iyaa tunane na dauka wallahi ke mai fahintar rayuwata ce ai.
Ki yarda dani Amma ba zan taba barin addini na ba don wata ko don wani abu ince na fita ga musilunci na sai ma abinda ya karu min a zuciyata.
Ai naga alama dan zamani tunda har kake iya kallon idona kana wanan maganan haka kan kafira data lasa ma zumar ta kaji dadi.
Dan murmshi ya sake tare da mika hannun shi ga nata ya dafa yake fadin Amma a gafarce ni nasan nayi kuskure amma a yafe mun.
Nan tayi saurin son jaye hannun ta yana fafin don Allah Amma ki gafarce ni kuskure na riga da na tafkashi idan kikayi fushi dani yau ban san inda zan jefa rayuwa ta ba a garin nan.
Saukowan ki shine kwanciyar hankalina Amma ki yafe min Umar din ki ya tafka kuskure mai girma a wurin ki amma don Allah kada kice kema zakiyi fushi dani a gidan nan ya kare yana hada hannayen shi guri daya.
Wani iri Amma taji a ranta yadda ta hango tashin hankali a tare da yaron lokaci guda sai tausayin shi ya kamata sosai sai dai a fili tace dashi.
Sai ka sanarwa iyayyen naka ai don ni wanan zancen yafi karfin fada a bakina gidan nan kasan komai kayi sai suce nice mai goya ma baya.
Ya kara fadin don yaga saukowa gareta ko yanzu kece dai mai sanar masu da halin da ake ciki don jiya Daddy ya fara min maganan aure.
Ai dole yai maka don hankalin mu ba akwance yake ba kunkai munzalin aje iyali ace baka motsa ba balle kannen ka su motsa.
Ashe mu bamu sani ba kai da iyalin ka a hannu mune ka mayar wasu bi nan can kana kallon mu wawaye.
Da sauri yace nina isa haba Amma kuna iyayyena zan ayyana haka gare ku lalacewan nawa bai kai can ba ai ya kare magana a cikin ladabi da kulawa a gareta.
Haka ya kara sa jikin Amma sanyi jikan nata ya bata tausayin kaddaran data samay shi gaskiya ya fada don kaddara na kan kowa amma dole ta nuna mai bacin ransu a fili don gaba.
Zaka iya tafiya ta bashi amsa sai yai shiru ta sake fadin bakaji bane ya dago a sanyayaye yace Amma fushi kike dani ke nan ?
Tace Umar ka barni in huta saboda Allah kasan a rike muke muna cikin lokaci ya fahinci mai take nufi ya mike a sanyaye ya bar falon nata zuciyar shi ba dadi a lokacin.
Bin shi tayi da kallo a ranta take fadin ban so haka gare kaba dan nan kaddara ta riga fata kai daya dace ace ka samu mace natsatsiya kamila mai rikon addini a cikin dangi kai ka aikata haka a kan ka.
Tirr da wani wayewan idan yai yawa bai haifar da alheri ta yaya yaro karami kamar sadauki zai yankewa kanahi hukunci a rayuwan shi.
Shiko umar yana fita ya sauke ajiyan zuciya tare da fadi a ranshi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login