Showing 126001 words to 129000 words out of 419207 words

Chapter 43 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1499

gulma ke nan sai kun shiga an baku giya yau zaku gane baku da wayau ai.
Aisha ta wurga mi harara tace dkn Allah A ruwa raba mu da wanan zancen banzan naki nace a, a ba aruwa ba a wuta ko amma zan kashe masu wanan sunan banzan ne a bakin su.
Zaune yake yana kallon duk abinda mukeyi tsab ganin bamu da niyar nocking mun tsaya muna budan ido yasa shi ya taso ya bude kofan fuskan shi a daure tamau.
Yana fadin kai wai su waye hakane kunzo kun cika mutane da surutun tsiya tun dazun.
Mu mm mune yaya Aisha ta fada tana dan inda inda tare da fadin ina wuni yaya ?
Bai amsa ba sai juyawan da yayi ya bar muna kofan a bude ga wani sanyi daga ciki yana bugun fuskan mu daga waje.
Ni kan dariyan keta ne ya kamani lokacin ban san har nakai wurin da sai an taka step ba sai jina nayi zan fadi kasa murja ta rikoni ta baya.
Ku zauna tana ciki yace ba tare da ya juyo inda muke ba ya shige ciki yana shiga mukabi falon da kallon gulma ido gulma hanci gulma ko ina mun baza shi sai kallon kallo mukewa junan mu.
Shiru muna zaune kamar ba wanda ya kula da zuwan mu har na fara hasala a raina sai jin muryan merry mukayi tana fadin.
Wawoo yau prity ce a gidan namu sun fito rike da hannun junan su yana saye da three quarter da farar riga a jikin shi ita kuma wani dan riga iya cinya armless ne saye a jikin ta sai cikin jikin ta dayai tsini ya dago rigan.
Tana zuwa ta sake hannun shi ta rugume ni ta sake ta rugume su Aisha kamar yadda tayi min din ta juya wurin shi tana fadin yau kaga su sisters a gidan mu sun kawo muna ziyara.
Ya danyi dariyan yake yana juyawa zai bar gurin tace idan ya shiga ya turo mata mai aiki daya ta bamu abin sha.
Satan kallon Aisha na danyi kadan ina mata alaman kada mu sha komai a gidan ban don ni na gama tsorata da su gaba daya sai sake sake nake a raina.
Ina kuma mamakinwai matace ke aiken miji haka a gaban mu ko kunya baiji to ina zaji kunya nace fitowan ma nan da falon saida ya rakota.
Shigowa yar aikin mai guntun buje itama ya katse min tunane na ta shigo tana gaida mu cikindan rusunni.
Kallon kwalban nayi ban gane kwalban lemun ba shiba fanta ba ba kuma cock ba da wani leda an rufe saman shi da gani dai kaga abin maye.
Tace mu sha mana sai muka kama kallon juna suna tuna zance na kafin mu shigo gashi ko ya zama gaskiya.
Hira sosai muke kwasa da ita tana bamu labarin kasar su har dai muka dan sake jiki da ita tace ita fa tana son rawa don haka kowan mu sai yayi mata rawa tagani.
Kida ta saka duk ya gauraye gidan sai nake mamakin yadda mijin bai damu ba ya kyale take wanan tabaran haka da alama dai yau taji dadin zuwan namu din sai take jin mu kamar wasu kawayen ta can.
Su kuma Aisha uwayen rawan kai sai suke ganin zatace basu waye ba yasa suke biye mata suna ta hauka.
Suna rawan sai gashi ya fito saye da wasu tufafin ya sauya kayan sun mashi kyau sosai sun fitar mai da kurciyar shi fili ta mika mai hannu wai yazo suyi rawan ko mai ya rada mata sai tayi dari ta sunbance shi yana dan dariya ya juya ya fita sukaci gaba da rawan su nan.
Ganin ya fita gida nima na mike nace haka ake rawan sai tace sai fa na cire hijjab a jikina za a ga rawana.
Naki nan suka kamani da kokawa sai da suka cire min hijjab din wai in taka hakana ina cire hijjab din nan kuma suka shagala da dada kyau danayi wai ina boye kaina.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:07 - ??5惙5惙5?: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM HASBUNALLAHU WANI,IMAL WAKEEL, , , ,


Yana tsaye daga kofan falon da waya a hannun shi yanayi ya tsura muna ido da mamaki yake kallon rawan da mukeyi din duk mun shagala mun buge da rawa bamun ya dawo ciki ba a lokacin.
Merry sai tafa muna take da hannayen ta duka biyu a hankali ya tako zuwa wurin remote din ya dauka ya kashe kidan.
Gaba daya muka mike muna mamakin abinda ya tsayar da kidan kuma juyowan nan da zamuyi mukai arba dashi ya daure fuska tamau kamar bai taba dariya ba a rayuwan shi.
Merry ta tako zuwa gare shi tana fadin why dear zaka kashe muna redio muna enjoyed din kan mu zuwan yaran nan gidan nan yasani yau na shiga nishadin da tun zuwa mm a kasan nan ban taba shigar shi ba tana magana tana kokarin kwanci saman kafadan shi.
Dan ture merry yayi ya yana fadin why merry why kin san hakan mu ba al,adan mu bane zaki saka yaran nan rawa kija muna hatering gun iyayyena.
Rawan kawai na nishadi da suke tayani yi diya bafa gun fati naje dasu ba da kake wanan maganan haka ya kara daga mata hannun yatare da fadin please, .
Daga haka ya shige ciki ya barmu zaune tsuru tsuru muna boye fuska ni dai kasa wani mosti nayi tunda na samu na saka hijjab dina a jikina na dunkule bayan Aisha.
Ina ganin merry ta bishi nace ku tashi mu fice don Allah kun jawa mutane abin kunya Aisha duk jece kika jawo min haka wallahi na fada a dan hasale.
Merry ta fito da dan murmushi a fuskanta tana fadin mu saki jikin mu nan fa gidan dan uwan mu ne taga mun tsorace dashi ta kai zaune tana fadin shi haka yake baison abin jin dadi a rayuwan shi sai idan shi yaso.
Can sai gashi ya fito bai ko kalli inda muke ba har yakai kofa ya dan juyo yana fadin ku fito in sauke ku gida idan kun tashi.
D way yadda yai maganan umurni yake bamu kowan mu ta mike da sauri muna shirin tafiya merry mamaki ya kamata ta take fadin don may zaka kore min abokan nishadina kuma kai ba zama zakayi a gidan ba.
Bai kulata ba sai ficewa yayi daga gidan mukan har mun daga kowa na kokatin daukan jakkan shi nidai hannun fauziya na riko muka fito tana biye damu da tikeken cikin ta a baya tana fada dashi.
Yana cikin motar dake rufe lif a lokacin muka karaso wurin motar muka tsaya ya sauke glass din motar yana fadin kanwata zagayo ki shigo nan gaba wurina da cewan fauziya don ita yake kallo yana magana.
Ban san lokacin da bakina yace zamu iya karasawa gida ai ba nisa don islamiyan mu ma yana gaba da nan.
Shoutup ban tambaye ki ra,ayin ku ba yace da sauri na rufe bakina muka fada bayan motar da tsoro da mamakin shi ashe yana iyawa matar shi haka yadda nake ganin su a soye kullun.
Maimakon ya mike damu hanyar gida sai ya dauki hanyar da zai fitar damu daga unguwar gaba daya.
Kallon kallo muka fara yi kasa kasa na radawa Aisha da ido ina kuma zai tafi damu haka ?
Sai muryan shi mukaji yana fadin sayar daku zanyi kin san ni dan yankan kaine ai ko baki sani ba yace ba tare daya juyo ya kalle mu ba.
Sai ya ja tsuki yaci gaba da tukin motar shi shiru na wani dan lokaci yace idan ni ba kafiri bane aike da kika buge da rawa yanzu kin dauki hanyar zama kafiran sallon kuje gida ku fada kunyi rawa a gidana ace zata koya maku kafirci.
Duk wanda naji wanan maganan a bakin shi sai na bata maku rai dukan ku baku san halina ba ko ?
Kina wani boyewa a cikin wanan abin kullun ashe shedaniya ce ke ko bai fada ba nasan dani yake fada nidake cikin hijab din ya kama ina rawan shakiyanci.
Ya furzo da iska daga bakin shi ta yadda muke iya jin sa bai kara magana ba sai daya tsaya a bakin wani katafaren shago da akaiwa manyan haruffa rubutu.
Ina dan kallo wurin naji yacewa fauziya barin maku tsaraba kuje dashi gida ko yana kallonta tare da fadin wa yan nan yan shagalan sun kwaso ki sun barki zaune.
Ya fita ya zagayo ya budewa yarinyar nata bangaren ya rike mata hannun suka fara tafiya a nan ya barmu zaune tsuru tsuru a cikin motar.
Murja ta fara magana tace ashe gaskiyar fatima da ki kace bahagon mutum ne sosai gashi ko ya nuna muna yau din.
Ni wallahi da nasan yana nan da banyi rawa ba har ya zargemu wai muna karya da uztazanci a fili.
Shiru nayi ban iya furta komai ba sai lokacin da naji Aisha ta fadi hakan na dago kai daga kallon wajen da nakeyi nace bafa daku yake ba dani agolan gidan su yake kukan ai kannen sa ne bai maku fada .
Ba yazo ya samay ku da farko kuna rawan ba baiyi fadan ba sai Aisha tace ke kila fa don yaga yadda mumun ku da hjy su suke yasa yayi gudun fitina.
Muna nan ciki zaune sai ga wani yazo da uniform din wurin yana fadin wai ance ku fito ku shiga daga ciki yana fadi ya juya abin shi.
Bin mutumin nayi da kallo sai kuma na juyo nace ku shiga ni ba inda zanje Allah.
Kallona sukayi kawai kafin suce mukan zamu shiga mu dibi rabon mu suna fita zuciyana ta bani in bisu muga gudun shi.
Da sauri na samay su har sun tura kofan sun shiga nima nabisu yana rike da hannun fauziya yace kowa ta dauki duk abinda take so.
Tsayawa mukayi muna shawara a tsakanin mu kunga mu dauki biscuit da sweet kawai koda bibiyu ne kada yaga haukan mu ko muyi kauyanci nace enyyeh kawai.
Ban tsaya ko inaba danaga sun nufi sashen kayan zaki nikan na nufi sashen wasu kaya dana hango.
Dogayen riguna mai tsaron wurin yana ganina ya taso yana fadin hjy a tayaki dubawa ne nace eh kawai nan ya shiga zakalo dogayen riguna masu tsadan gaske har guda biyar.
Nace sun isa na nufi gurin turamay nace ya zaba min ya dauko masu tsada gaske ni dai ban hana ba guda hudu na zaba nace ya saka a basket din ya bini da kallon mamaki na fuske sosai.
Sai na koma wurin turare da man shafi ina dubawa nan ma mai tsaro yace bari na zaba maki daidai da jikin ki ya zabar min turare masu tsadan gaske da kamshi na juya kowa sai kallona yake yana mamaki.
Daga haka na nufi gurin mai lissafi nan na samay su harshi suna jirana Aisha da murja suna ganina ido waje sun bude baki suna kallona da mamaki na iso inda suke tsaye.
Kallon kayan Aisha tayi tace A ruwa nace A wuta dan Allah niki kyale ni kin ji tace cewa fa yayi abinda muke so nace ai shine na dauko wanda nake so din tunda raina yana so.
Yana jin mu baiko kalli inda muke ba sai mai lissafin yace oya hajiya ina naki na tura mai basket din na ja baya sai da acounter din ya dago kai ya kalle ni ya girgiza kai yana dariya.
Ni dai na fuske ya buga tare da dago kai ya kalleshi yace 2,2500 a cikin rashin damuwa da komai ya mika mai dan kati naga sun cire ana saka kayan a leda.
Nace kai an saye duka ne ya dago kai yace har an biya ai hajiya sai kuma tsoro ya kamani dan ni ba haka na shirya a raina ba.
Naso yace don may na dauko wanan kayan kamar mara hankali ince bakai kace in dauki abinda nake so ba sai kuma aka samu akasin hakan ni yanzu may zance a gida idan mun koma.
Amma wallahi A ruwa ke yar iskace wai yaya akayi kikai wanan tunanen haka , ?
Nace ganin iyaka najeyi na fada a ciki akaga nawa ni mai zance akan kayan nan gida yanzu ya juyo a fusace yana fadin ba zaku shiga mota ba kun tsaya kuna gulma a nan.
Da sauri muka shige motar yadda mukazi haka muka koma ya sauke mu a kofan gida bai shiga ba yaja motar shi ya wuce.
Cirko cirko mukayiba kofan gidan ance ko lahira mai kaya shike wahala yanzu a nan sai aka barni da tarin ledoji a gaba ganin sun fara shiga sai dariya suke min yasa nabi baya su da sauri da tarin ledojina a hannu.
Muka shiga part din Amma sai dariyan keta suke min na zauna ina kumbura baki .
Amma da ta fito wanka tana saka riga a jikin ta ta kalle mu tace lafiya kuke wanan dariya haka ?
Nuna mata ni sukayi tare da kayan dana tara a gabana tace wanan kayan na may ye kuma ?
Aisha tace bari ke dai Amma ta fada maki da bakin ta yau tarko ne yakama mai shi a wurin nan.
A ruwa bata labari da bakin ki taji na kalle ta da harara bace A wuta dai wallahi Aisha ku daina kirana da A ruwa din nan na juya gurin Amma nace.
Amma ai duk keda manjo ne kuke kirana da wanan sunan har suka samu.
Baki son sunan ne yar nan ai wanda aka haifa ana ruwa akecewa A ruwa ko damana shi kuma namji ace mai Ana ruwa.
Ni har suna nawa za a saka min a barni da fatima na zai fi mun dadi wallahi amma wai wani a ruwa can babu dadin ji haka ?
Na karasa ina bata rai ledan na taka da kafana na tuna dashi a gurin itama Amma ledan ta kalla tana fadin wanan kayan fa na maynene a ciki ?
Sai suka kama dariya babu kakautawa har hakan yasa mama hadiye data dawo daga gurin aiki ta fito daga dakin ta tana fadin gaku kamar mahaukata mana ?
Nace a marairaice mama wani sukewa dariya don kawai wanan mijin kafirar da mukaje gidan ta ya kaimu shago yace kowa ya dauki abinda yake so nikan na kwaso wa yan na rigunan na daukowa Amma da manjo da mamu da Addah zannuwa shine suke min dariya.
Murja tace mama ba hakana bane taso yace ta mayar tai mai halinta sai gashi ya biya kudin babu tambaya.
Maimakon inga mama tayi fadi wani magana sai itama ta kwashe da dariya a gurin na kalli kayan cikin marairaice murya nace mama yaya zanyi da wanan kayan haka yanzu shiyasa ma nayo nan gurin Amma in samu mafita da kayan.
Mama ta dan tsagaita dariya tace aisai ki saka abinki wanda kika daukowa su hajiya kuma ki basu abinsu.
Da sauri Aisha tace wallahi sai dai mu raba Amma tace ta hanaku daukowa ne shifa ya bada bakin duk abinda mutum ke so ya dauka ku ina abinda kuka dauko a shagon ?
Sai lokacin suka dan shiga natsuwa suna fadin wallahi Amma a ruwan nan shegen wayau ne da ita mu san bamuyi tunanen haka.
Da mun sani ai muma jidan kayan zamuyi kamar haka mu biscuit kawai da sweet muka dauko daya daya .
Allah ko ya shirye ku da bakin kwadai yau kunga illar kwadai gare ku, sakarkarun banza kawai .
Jin haka murja ta kara fadin to mu munsan da hakane in bada mukaga ya biya wanda ta dauka ba mama hadiye tace ai kune abin dariya ba ita ba.
Yar albarka shiyasa nake sonki kamar yadda kike sona watau ko a ina kike ina ranki ke nan yar nan da har kika kasa mantawa dani.
Nan tayi ta samin albarka tana yabawa sai hankalina ya dan kwanta don nasan ko ba komai zata tare min fadan da nake tsoro na mamu.
Cewan da Amma tayi cikin maganan ta ashe Sani nada gaskiya wanan hadin da alama zatai kyau kyakayawan jumma,a tun daga alhamis ake ganewa.
Na shagwabe fuska ina fadin Amma yanzu ke zakiwa mamu magana ko tace maganan may zanyi abin yiwa kai idan yayi maki dawainiya ai kansa yaiwa ba wani ba.
Jin shiru da mamu tayi ashe ban sani ba fauziya har ta fice zuwa part din mu mamu suna tambaya akace da ita ina nan shine ta biyu ni don bata gane zancen da fauziya ke mata ba na gulman an saya muna kaya masu yawa wai nace ban so.
Hankali tashe mamu tayi sallama a falon tana fadin yanzu fauziya take

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login