Showing 162001 words to 165000 words out of 419207 words

Chapter 55 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1423

lami ne da yaranta zasu cinye su kadai.
Ruwa na debo a bakin famfo na surka na shiga wanka na dade a zaune ina shiri duk da ba kwaliya nake yi ba amma ranan na bata lokaci ina kwalliya.
Wani yello less na saka a jikina mai dan flawer da zare bulle a jikin shi sai duwatsun dake shana shi idan ka gitta.
Takalama da jakka blue na dauka sai dan oud dana shafe jikina ya dauki kamshi don mamu ta saba min da shafa turare mai mai na arab a jikina ko tufafina banda hammata da chest dina kawai ban shafawa don gujewa cancer.
Manjo na tambaya ko tana son wani abu sai cewa tayi bana son komai yar nan dan dama wanan lemon kwalban mai sanyi.
Murmushi nayi ina fadin wann bakin dai naki manjo na gane kwadai yake so a cikin sa fita nayi zuwa waje inda shago yake na sayo mata multina da fanta guda hudu na kawo mata .
Yayin da idanuwan su kubara dake kwaliya a kofan shiga wurin su yayo caaa a kaina har saida na tsargu da kalln da suke min din.
Ban dade da manjo nayi mata sallama bayan na aje mata komai a kusa da zata bukata a wuni hatta ruwan sha na sayo mata mai sanyi nayi mata dibara sakawa a wani tsohon kulan dake dakin tana fadin kin ga maganin ajiyan tsofi gwaggon duk zuwa sai ta min korafin in yarda shi naki.
Ina fitowa duk suna waje nasan gulmana wa yanda ke waje suka kai harda umma sai da nagani a wurin na taka kamar tarwada zuwa wurin su tun kan inyi magana mama saude tace yau kan yar gidan babba ina za a haka da wannan kwaliyar ?
Muushi nayi ina fadin zamu nan gidan samirace yar ajin mu da tai aure na juya ina fadin umma zamu ziyar ne yau zan tafi.
Ba zaki dade ba ke nan ko ta tambaye ni cikin kallon fuskana kada plan din ta ya baci nasan nace zuwa sha daya insha Allahu zamu dawo.
Tace to a dawo lafiya ina bada baya taja tsuki tana fadin sai na kasaraki ai yanda ko kare bai sunsun naki don bakin jini mu za,a kawowa barkado a gida ?
Ke a dole uwarki ta fifitaki akan yayan mu wallahi karya ne baku isa ba daga ke har uwartaki da kike kuri da ita.
Haba umma ni ban son irin haka wallahi fatima fa yar uwan mu ne umma idan kin kasarata ai mun kara yawa ke nan muku a gida ?
Kubura wallahi ki fita min a idona tun ban saba maki ba wawiya daba tasan inda ke mata ciwo ba kinfi bukatan ta dinga kwaso tsumakara tana kawo maku kwance kuna jin dadi sakawa ba ku hakan zaima ku dadi ko hakazaifi maku dadi ?
Nidai don Allah da kin barta har sau nawa fati kr zuwa garin nan da zamu ganta harara ta watsa wa yar nata sai ta kasa karasa maganan don kallon da uwar tai mata.

Hjy jummai tayi mamakin ganin yayan nata data gani kamar daga sama washe gari ne suna zaune Umar ya shigo falon kamar an jefo masu shi sai mamakin ta ya karu sosai.
Abinci aka gabatar mai bayan yan gaishe gaishe tana fadin ku lafiya wanan tafiyan haka babu sanarwa zuwa ai maku tanadi.
Daddy bai fada maki komai bane mama Aliyu ke tambayanta hakan cikin tsure ta da idanuwan shi.
Alh kuma ni bai ce min komai ba ta fada slowly a cikin muryan mamaki da tunane a ranta.
Ko ma dai mainene ai zai fada muna tunda ya kiramu kuma gamu munzo inji habbib ya fada a miskile shiko umar baiko ta kansu don ko abin karyawan da aka aje mai bai taba ba.
Kodai wani abinne ya taso yake neman mu hakan cikin zolaya Aliyu yace zancen auren ku ba kila wani kallo habbib ya watsa mai tare da fadin kainan daban ne idan ma auren ne ?
Wani aure kuma hjy tace tana mere bakin ta tace aure kai ai yabi ruwa kowa yaje gaba ya neme nasa badai diyana da wanan gamin gambizan ba.
Mama ni fa har yau ban ko san yarinyar da daddy ya lika min ba don koda yace inje mu gana wani zuwa danayi banje ba har na wuce.
Ai gara ma yar wurin bros wancan zuwa naga ta girma sosai tayi clean gaba daya lokaci guda kodan ban ganta da katon hijjab din nan bane oho ?
Umar ya dago kai daga abinda yake a cikjn waya ya watsa mai wani kallo ya kama dariyan mumuke .
Yace Allah bros da abin mai yuyuwa ne akwai iri mai kyau fa gurin don ko ina zaka shiga da ita nan gaba.
Kai karabani da zancen haushi a gabana habbib ke wanan irin magana ko da itace autar mata ba zata taba shigowa ahali na ba mudfin ina raye.
Kyau dan maciji ko kunama may ake da irin da ko asalin su basu gama sani ba maimuna fa har yau bata san uwar ta ba a duniya.
Kai wai mama da gaske ne wanan zancen ni tun tasowana nake jin ana wanan maganan fa ashe gaskiya ne ?
Yo ina tasan ta dama irin yan cin ranin nan ne ai ubanta ya gani ya aura da iyayyen ta zasu koma kasar suna sudan suka matsa saida ya sakae masu ya suka tafi da abinsu har yau basu kara waiwayan ta ba.
Shegiya dama ta tafi da wanan annoban amma hajiya ta hana a wanan lokacin dole ta tafi tabar yar a nan ashe annoba zata zomowa mutane nan gaba.
Umar ya dago kai ya kalleta don jin zagin da ta aikawa mamu din tace na zagi kanwar uwar ka ko miskilin banza.
Maimunan nan kamar tayi ma wani asiri a kanta tun kuna yara nake rabaka da ita kuna leke da juna.
Dan murmyshi yayi yace kai mama zagin dai ne ba dadi maimuna kuma tare muka taso a gidan nan muna yara shine shakuwana da ita ba wani abu ba.
Koma dai may na hana wana hurdan a tsakanin kai baka ko kishina da alama mai kina kake shigewa jiki.
Shidai bai daga kai ya kalleta ba sai dakilan wayan hannun sa yakeyi can dai ya mike ta kalle shi tana fadin ina kuma zaka yanzu.
Zan leka Amma ne a wurin ta nasan yanzu tasan nazo don akwai yarinyar data ganni gidan nan nasan zata fada mata nazo.
Ko dai yar tsanarkace ta ganta hjy ta kalle shi tana tsuki tace wanan yar banzan yarinyar bana wai ta tafi garin su ganin gida nima jiya maryam ke fada min tafiyan su.
Shidai yasa kai ya fita ya barsu a gurin yana ficewa tace wata kila wani abin ne ya bata mashi rai da zuwan shi haka ?
Yana tunane iyalin shi daya barone ba shiri kila don kiran gagawan da akai mai ba shiri yazo.
Arniyar matar nan zan waiwayeta don har yanzu bata kwanta min a raiba na tsani ganin ta a rayuwana.
Babu wanda ke son ta a gidan nan idan ka dibe shi daya kwasota gidan nan kaf in maka na mahaukaci kyamarta suke.
Ba wani abin kyama halin merry dai na rashin son yayi hurda da yan uwanshi shine matsala ranan fa munje gidan ta hana muna ruwa common ruwan sha fa mama.
Ta gyara zama tana fadin ita din da kanta lale arniyar nan ta samu guri da yawa zafin ran babawo na banza ne.
Shiyasa nake kara kyamatan wanan bakin hadin da Alh ke son yi maku don maimuna na iya kwace min da da kilibibin nan nata.
Shiru sukayi suna sauraren ta ba tare da sun furata komai ba ga kalaman ta da takeyi akan maimuna din.
Sallama yayi kofan falon tace lale marhabin da mutanen turai sadauki kaine yau ka leko mu kasan nan ai ka kyauta duk da dai kadade baka zo din ba ko yar nan da aka haifama bamu santa ba.
Zaku santa Amma idan sunzo don zuwan merry kasan nan ba yanzu ba don yarta sai kila idan ta girma zamu shigo dasu wani lokacin yana zama yake wana magana wa Amma din da take tambayan shi.
Sadauki irin dadewan nan haka ba a leko gida ba baida dadi wallahi an san aiki yana yawa amma mutum ya share gida har wani lokaci.
Ai hakkuri Amma nima hakan bada son raina nake dadewa ba don aikina ne da yaimin yawa ko wani lokaci.
Ina mai dakin naka take da yarta ina suna lafiya ya kuma jama,an wurin naku suke ?
Dan bata rai yayi yana fadin suna lafiya Amma baki san dalilin kiran mu da daddy yayi ba haka a cikin gagawa ?
Shiya kiraku kasa nan ashe tayi mai tambayan malam bahaushe mai ban haushi.
Mayar da kanshi yayi saman kujeran da yake zaune a kai ba tare daya iya bata amsa ba ga nata tambayan.
Itace tace wata kila dai akan wani maganan siri ne ya aika kuzo haka sai dai ni bai sanar dani komai ba gaskiya.
Shidai baiyi magana ba sai faman tunane yakeyi a ranshi ko dai maganan mama gaskiya ne idan haka ne mai zaisa daddy ya lakantani da zancen dukiyan shi bayan yasan ina da nikin baninkin din su a hannu na koma dai may nene zamu ji ai yace.

Ta shiga ta fito daki hankalin ta a tashe tana jan tsuki tana magana ita kadai kamar mahaukaciya mama saude ne da abin ya dama tace wai yaya lafiya yau kuwa ?
Tace uhumm bari saude abubuwa ne suke son yi min yawa a kaina yau ta fadi tare da shigewa dakin mama saude ta bita da kada kai tana fadi a ranta mugun nufi yabi mai shi.
Daga gidan su samira mun shiga wurin gida biyar muka dawo gidan su Atika muka yada dandali bayan karfe hudu.
Hankalina yana gida wurin manjo saidai kamar an kashe min jiki da zuwa gidan bayan muyi sallah na kwanta a gurin ina dakilan wayan Atika shiya dauke min hankali na manta da komai dake gabana a lokacin.
Bayan sallah magariba dana isha, kuma na dasa wani kallo ina kallon ci gaban shi hakan ya jani har goma da rabi ban shiga gida ba.
Saida umma ta leko dakin tana fadin nikan yau a gidan nan zaki kwanane dare fa ya somayi sosai take fada min na zabura da sauri ina kallon lokaci a wayan na mike ina fadin yau nasan zan sha fada wurin manjo kan don nace ba zan dade ba da zan fita.
Har cikin gidan mu Atika ta rakoni muka shiga dakin manjo da muka samu har ta kwanta a lokacin sai dai batayi barci ba.
Tana ji mu ta daga tana fadin yaran nan ina kuka shiga haka tun safe kuka fita nace wallahi manjo ina nan gida su Atika muna kallo ne ya dauke mi hankali.
Jin hayaniyar mu ne ya sanarwa umma mun dawo sai gata kofan tana fadin yau ina kuka shige haka yarnan tun safe ?
Umma muna gidan su Atika kallo mukeyi ya dauke muna hankali umma ayi hakkuri don Allah tace hankalinane ya tashi rashin dawowan ku gida har wanan lokacin.
Daga haka ta juya ta fita Atikama tace zata wuce sai manjo ke fadin ni yau bansan wani imani yazowa lami ba don tunda rana take neman ki gidan nan fa.
Kallon juna mukayi da Atika muka bar dakin har muka kai waje ba wanda yai magana sai da muka bar gidan kadan Atika tace yanzu yaya za a yi fatima.
Wanan matar fa da gaske take da nufin ta a kanki nace yaya kuwa Atika addua dai nake ko yaushe Allah ya tsare ni a duk inda na samu kaina.
Mun dan jima muna hira na koma ciki na samu wai miyar kaza umma tayi ta debo min bana nan taba manjo ta aje min.
Ina shigowa manjo tace wanan zuwa kan kinci da fari ga miya nan ummar ku ta kawo maki wai dazun tayi shi tace kinga ni dake gidan ko kashi bata ban ba.
Nace miya kuma tace eh wai kaza aka yanka mata yau shine ta zubo maki ki daure kici kafin ki kwanta.
Na bata rai duk dagabana dake faduwa da Naman nace na koshi bancin abinci da dare kuma ai na fada maki nama bai damay ni ba yanzu.
Kokarin mikewa naga tanayi tare da fadin bari indan taba kada tace ba a ci tayi maki abin arziki tana kokarin jawo kwanon silver dake gabanta.
Da sauri nace manjo kada kici naman na do Allah na fada ciki daure fuskana gare ta.
Wani kallo tayi mun na tuhuma nace manjo barta da halinta kawai tana dauka ban san komai bane da take shiri mun.
Wani abu ke nan kike nufi nace ba dai zakici naman nan ba wallahi naja kwano zuwa baki kofan mu na aje.
Sai kallon mamaki manjo ke mun na share ta ina shitin kwanciya abina ba tare dana kulata ba har na gyara wuri na haye kusa da ita tana zaune tana kallona da mamaki a fuskanta.
Bata iya ce mun komai ba don ba fuska a guna da zatayi min tambaya a lokacin sai da na tabbatar da manjo tayi barci baffa ma har ya shigo naji rufewa part din su na fito a cikin sanda na kai nama waje na zubar dashi can nesa na dawo gidan na kwanta.
Washe gari tunda asuba saiga umma dan dakin kwanon namu ta leko tana fadin babba an tashi lafiya ya dare ?
Lafiya kalau muka tashi manjo ta bata amsa da hakan tace fatima fa yar gidan babba an tashi lafiya ya gajiyan unguwan dai.
Umma ina kwana nace bayan na shafa addu,a a fuskana da jikina na waigo ina gaida ita idon ta na yawo tana neman kwanon naman ta.
Nace umma jiya na dawo na samu miya na gode shi naci na kwanta da guntun bread din daya rage bari in fito in wanke kwanon in kawo maki.
Tace ba sai kin wanke ba indan kinci ai shike nan bukatar maje hajji sallah dama ta duka ta dauki kwanon ta fita.
Kallo mamaki manjo ke mun har lokacin kafin tace A ruwa kaddai ince wanan lami din neman rayuwan ki take yi.
Kusan haka nake hasashe na bata amsa koma may ye ai ya kare a kanta shiru tayi kamar tana nazari na dan wani lokaci .
Wunin ranan sai ban fita ba ko girkin da nake muna sayowa na kira Atika akai muna umma ko taje ta dawo wata kila bokan nata ya fada mata wani abu zai samay ni ne ranan takewa wanan zawaron daga part din su zuwa namu tana dubawa.
Sauran kwanakin daya rage mun kuma sai naga umma ta canza min fuska ba kamar lokacin da take tarkona ba.
Shirin komawa na fara yi tunda akace min kwana hudu zanyi a nan don a yanzu na gaji do akwai tsoro da fargaban tarkon umma a kaina yanzu.
Na bar gidan kawuna ina murna zanzo gidan mu inda yan uwana jini zasu kaunace ni sai gashi nazo naga gidan kawun nawa ma ya fiye min nan kwanciyan hankali a yanzu.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:12 - ??5惙5惙5?: BISSIMILAHI RAMANIN RAHEEM HAS BUNALLAHU WA,NIMAL WAKEEL, , , , , ,

Da kyat na yarda zuwa wurin kumshin da kitson da Atika tace zata kaini don kada na koma hakana gida ban so ba sai dai ba yadda zanyi don ummata da ta saka baki tana fadin kinzo haka ba kumshi kice kuma haka zaki koma.
An min kitso da kumshi wanda hakan ya kara haskani sosai na fito wata shar dani ranan, na koma gwanin ban sha,awa dani.
Ni kaina nasan da nayi kyau matuka a gidan su Atika umma tasa aka wanke mun kaya na almarin su ya gogemun su koda muka dawo mun samu an kawo kayan wurin manjo.
Sai da na dan dade gidan su Atika muna hiran ban kwana nadawo gidn lafiya na shigo gidan Amma ina shiga kaina ya dan fara min ciwon da bansan dalilin sa ba.
Sai dai na dauka duk gajiyan kitsone don banson abinda zai taba min lafiyan kaina ko kadan shiyasa idan muna hutu nayi ba kwana da kitso ke nan sai mun koma school kuma.
Ganin ciwon kan nason ya kaini kwance ne manjo ta fita ta sayo min magani nasha kafin ta dawo ne a dakin ina kwance kawai akaji na yanka wani uban ihu ni kadai.
A cikin razana duk wanda ke gidan baffa a lokacin saida ya fito waje don karan ihun dana yaka din.
Suna tsaye cirko cirko suna son gano

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login