Showing 132001 words to 135000 words out of 419207 words

Chapter 45 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1426

iya balle naka humm kawai yace ba tare da yai mata magana ba.
Sai can yace zuba min fruit din nan in sha kafin a fara labaran kasa ya fadi ba tare daya kalleta ba yake magana.
Ta mike da kyat tinkis tinkis zuwa wurin data aje ta fara zuba mai ta kawo mai gaban shi ta aje tana zama ne tace wai ni wasu irin bakine haka suka zo muna gidan nan.
Da sauri ya dago kai yana fadin baki a ina suke don shi ya manta shaf da su manjo na gidan lokacin .
Tace wa yan nan bakin mana da suke dakin maimuna kasan fa muna da yara kankanu a gidan nan irin tsofin nan data kwaso ba abin yarda bane a yanzu da duniya ta lalace din nan.
Sai da ya kurba fruit din yace ai kin gama maganan ki da kika ce duniya ta lalace ko ba baki sai a samu mugai a cikin gidan nan ba a bin mamaki bane.
Tace Alh ke nan ai na gida an saba da halin su wlh gaskiya nake fadi a magana ta kasan tun farko ni ba son wasu suzo su zauna muna haka a gida nake so ba don tsaron lafiyan mu.
Yanzun may kike nufi da wanan maganan naki bakin nan fa ba wasu baki bane can na waje kakan yarinyar nan ne fatima tazo checkup da yarta su kike kira da baki ?
Tace baki ne kan tunda ba zuriam kowan mu bane banga dalilin da dan wanan halakan zaisa suzo su zauna muna a gida haka ba.
Don ni ban yarda da zubin mutanen nan ba kamar wasu muna fukai dasu kullun a daki kumshe.
Kai jummai kin san abinda kike fada idan ma hankalin ki bai kawo ba ki tuna mutanen nan nan gaba halaka zamu hada su mai karfi a tsakanin mu ba gida na ba har gidan dan ki watarana zasu iya ziyarta.
Wani kallo tayi mashi kafin tace gidan dana fa kace Alh wani dan nawa kake tunanen zasu ziyarta a cikin yaran nan , ?
Yanzu dai na fahinci abinda ya kawo ki dakin nan kinzo ne kawai ki tayar min da hankali na dawo da gajiyan kasuwa a jikina haka ?
Wanan kuma sai in kaso fadin hakan ni dai akan wa yan nan mutanen yanzu nayi ma magana ba fitina nazo nema da kai ba.
Yace bakina ne tunda bakin matatace don haka ki barsu nan inda kika gansu tunda ba a kanki suke zaune ba.
Mutanen da ko waje ban tsanmani suna fitowa zaki zo da wanan maganan ke yanzu ba abin farin ciki bane a gare ki yau bakin sun sauka a gidan nan zamu samu ladan da Aah ya kwadaita muna ga wanda ya ciyar da bakon sa.
Hjy data gama hasala da zancen shi don ba haka taso ya dauki maganan ba tace dama nasan abinda zaka fada ke nan akan may maimuna zata gaiyato muna su a gida haka ?
Wai maiye matsalan ki da mutanen nan kilan ma tun da matan suka zo baki sauke hakkin ki kun gaisa dasu ba to don may zaki zo ki sakani a gaba da zancen su yanzu.
Gidan nan gidanane fa gidan mata hudu kuma saboda ke sai in tauyewa sauran iyalina hakkin su ko haka kikayi a baya kan yan uwan maryam dake zuwa gidan nan kai da kai sai da kika samu fitinan da kika dora mutanen nan suka dauke kafan su da gidan nan.
Ta kalle shi tana fadin sheri zakai mun kuma yanzu akan maryam yace meye abin sheri a ciki tunda anyi hakan nasani.
Daga haka ya mika hannu ya dauki remote din shi ya kara ya barta nan tana cicika do ba haka taso ya dauki maganan nata ba.

Sauri nake na fito daga part din mu zan shiga wurin Amma dake kirana hjy jummai ce tsaye da wasu hamshakan mata a waje.
Tunda na gansu nasha jinin jikina dasu hakan kuma bai hanani saurin da nakeyi din ba nazo daidai inda suke naji hjy tana fadin kungama ga yarinyar nan da Alh ke son lalakawa yaron nan.
Gaba dayan su suka jiyo suna kallo na a raina nace kiyi ki gama ni ba ruwana da lamarin ki iyaka dai ki nunani kice nice agolan gidan ku ga kowa don na dauka shi take fada masu din.
Dayar matar dake da haske a cikin su tace tuburkallah ai Alh baiyi hadin banza ba a nan kina ganin ta nan idan ta samu wuri bajewa zatayi sosai yanzu akwai sauran kurciya a tare da ita.
Dayan mai tsayi kamar hjy tace eh da alama kan zai more auren sa sai dai matsalan abin ne ai yar kishiyar tace fa aka fada maki shine babban matsalan ai.
Ni ai ban hango wanan hadin ba don zancen banza naji kunayi a nan kamar baku tayani bakin cikin wanan abin ma ?
Har nakai Part din ina mamakin maganan su don duk abinda suke fada a kunne na yake ina jin su.
Ina shiga nace Amma ji min wanan matan tace wacece kuma na kai zaune ina fadin hjyn su salma mana yanzu na wuce ta da kawayen ta a waje suna gulman wata har da fadin wai ita ba zata yarda dan ta ya auri yar kishiyar ta ba sai fa da ta ganni take wanan maganan Amma ?
Ko an fada mata diyan ta suna burgemu ne oho indama ba yaran nata arna suke auro mata ba a matsayin sarakai.
Ni kan indan na tashi don taji haushi uztazu zan dauko gidan nan yazo yai ta maku wa,azi taji haushi.
Amma tace kaiya yar nan ai kaddara ta riga fata koda yake mijin naki ba laifi a wani wajen yana da gwargodon ilimin shi sosai.
Ji Amma don Allah ke kin san wanda zan aura din ne da kike wanan magana keda kuun kina a falo zaune murmushi tayi tana kallo na tare da fadin idan na sakaki a lale zaki bayani.
Fauziya ce ke fadin wai inzo mamu na kirana dama guduwa nayi kawai in tsokali Amma zamu tafi islamiya ne lokacin.
Hakan yasa na mike da sauri ina fadin bari in mun dawo sai inzo ki fada min mijin da kike min hasashen.

Bayan fitar mu islamiya mamu na tuka tuwon dona dora kafin in fita hjy maryam ta yi sallama a falon part din mamu din.
Daga ciki mamu ta karba tana fitowa falon don ta sheda muryan nata ko ta fito tace a, a hjy kece ashe da dan murmushi a fuskanta.
Wlh nice nace bari idan leko in gaida baki ashe baki kikayi haka gurin hjy nake ji da take fada akai.
Mamu taja ta tsaya tana fadin ikon Allah fada akan may kuma ko wani abu ya faru ne tace kawai dai kin san halinta ita kanta kawai ta sani ai.
Ta fada maki zancen bukin da sukeyi ne sai mamu tace hjy ke nan ina zanji tana da buki Allah dai yasawa auren albarka.
Ta tabe baki ba tare da fadin amin ba take fadin ai ko yaya ne dai zaka sanarwa wayanda kuke tare dan uwan ka na buki ko addua aikayi masu.
Idan da sabo aini na saba da halinku a gidan nan tun ban iyaba har na iya yanzu Allah dai ya huci zuciyar ku ya bamu hakkurin zama da juna tunda zama ya hada.
Dan dariyan yake tayi tana fadin kai maimuna akwaki da wani zance aiko ni ba zaki fada min haka ba a kanki.
Ida ban damu dake ba ai ba zan shigo yanzu in kula da bakin ki ba dama dai ai itace mai nuna bata son mu,amulan kowa a hade.
Allah ya kyauta mamu ta kara fada tana kwantawa sama ha;u kujeran da take tsaye kusa dashi.
Tace zama tare ne ya kawo hakan sai hakkuri da junan mu sai hjy maryam itama ta dafa kijeran kamar yadda mamu diin tayi tana fadin aiko kan maganan hadin auren nan bakiji abinda take fadi ba.
Mamu tace komai zata fada nafita baki ciki da wanan hadin don ni diyata na sani kamar yadda tasan danta.
Itama ta kyamace mu balle mu da za a tauyewa yarinya yancin ta na budurci a hada da mutum kamar umar ni ainafita jin zafi da kyamatan hadin wake son hada zuri, a da ita idan ba dole ba.
Anty bari kiji nifa badon gwaggo da Alh da suka roke ni in yarda da hadin nan ba babu abinda zai sa in yarda da wanan bakin hadin.
Mumu tasan zancen ta a kunnen hajiya yake yasa take bada sako a kai mata don tasan da dawowan ta sakon ta zai isa gare ta ta tsaya ta fadi magana iya son ranta kafin hjy maryam din ta fita.
Muna islamiya fauziya tazo min da kuka dan wurin hjy maryam ya duketa don suna fada da kanin su karamin.
Ina zuwa ban tsaya tambaya na rama mata dukan naja hannun ta muka tafi har mu fara hanya ikilima ta samay tana fada wai don may zan doki kanin su.
Nace na doke shi ki tambaye shi shi may yayiwa fauziya na rama mata shike nan don wani yafi wani karfi sai ya duke shi daga dan magana kawai.
Kamar zatai magana sai kuma tayi shiru na juya na fara tafiya naji muryan ta tana fadin wai ita A ruwa din nan don kawai taji ance zata auri yaya umar ne takewa mutane wanan rawan kan dama ba cusa mashi ke akayi ya aura dole ba balle kiwa mutane sallo.
Na juyo da sauri ina fadin wani ya umar din tace ai duk kin sani bari kiji idan ma cusa mashi ke akayi ba ya aura bai so shida hjyn su.
Balle ki dinga yiwa mutane rawan kai a gida kina kutin ke zaki auri mai kudi har asirin da akayi don hakan ya faru muna da labarin komai.
Ikilima shirin naku na gado har ya kawo gare ni dama kulle kullen da kukeyi ke nan daku da uwar ku don kawai ku bata muna suna.
Yau Allah ya matsi bakin ki ki fada da kanki kowa yaji sai dai ki sani ni har yanzun ma ban gama sanin sunayen diyan hjy ba a kaina balle in san ko waye umar a cikin su.
Nace kukan kunyi hasaran rayuwa uwa gulma diya gulma sai ko ta kai min duka nan fada ya kaure a tsakanin mu Allah yaban sa an ta na kaita kasa na haye na murji bakin ta sosai ban daga ba sai da naga hancin ta da bakin ta yana fitar da jini su Aisha dasu salma suka banbareni a kanta.
Har muka kawo gida ana cacan bakin maganan ida nake ji kamar dukan danayi mata bai isa hakana ba.
Dan tsayawan da mukayi a hanya fada yasa muka bata lokacin mu sosai a hanyar dawowan mu gida.
Muna shiga gida wani sabon fadan ya kaure don ban kai ga shiga gida ba su ikilima suka rigamu shiga gidan har sun fadawa uwar su tana ganin jini ranta ya baci ta fito da jidali.
Sunana uku da ake kirana dashi ta kirani dasu a jere tana fadin an aiko kine ki masu wanan dukan haka don jin haushi da takaicin su da kike ji ko may ?
Saratu kanwan ikilima tace wai fa don kawai tace kanta yana rawa don taga za a aura mata yaya umar ta daketa.
Hjy maryam tace dama ba asirin da rokon shi akayi akan ya aure ki ba din ba har uwar ki na wani cika bakin banza ga mutane.
Munsan komai wa zaku dagawa hanci nan idan ba asiri bane mai zai kai Alh yin wanan hadin haka tunda kowa yasan ba ajin ki bane shi.
Uhumm dama abinda kakeyi shi kake dauka kowa shiya keyi ai hjy maryam ke kika san zuwa wurin boka da malam ni ban gaji wanan ba a rayuwana.
Auren Umar da ya tsone maku ido ki wanko yarki ko wata naki ki bashi ki gani in ya taba ran maimuna ko wani nawa.
Fada ne na yara amma ke babban kanki kin fito kina wanan baran bakin a gaban yara haka.
Allah waddan wanan halin naki maryam ke da diyan ki yanzu don baki da kunya ke, ke fadan haka a bainan jamma,a waye baisan har gatin nan kike bari zuwa bin bokayen ki ba.
Mama hadiye ke magana a fusace tana kallon hjy maryam din wanan maganan da aka barshi iya mu manya gidan nan muka san da zancen nan ashe har kin feasawa yaran ki shi.
Fada sosai da musayar harshe ne tsakanin mama hadiye da hjy maryam da har yakai su Alh dawo gida suka samu suna wanan rikicin tsakani su da fadan ya koma tsakanin ta da mama din.
Wai may ke faruwa ne haka tun bakin get nake jin muryoyin ku haka cirko cirko akayi a gurin gaba daya saida ya kara tambaya mama ta juyo tana fadin.
Zancen yaran na fa sun dawo islamiya ashe sunyi fada a can tau shine sai abindai ya zama musu rikici har yakai ita ikilima tayiwa Fatima gori wai sunbi boka da malam ita da uwar ta don a aura mata umar.
Wani kallo ya watsawa su hjy maryam har yaranta kafin yace ita ikilima a ina taji wanan zancen ?
Shiru ikilima tayi ya daka mata tsawa sai data kada tana rawan baki tace dama daddy na sani zaki fada min yau ko hukuncina ya hau kanki.
Kuka ta fara ya sake fadin wallahi ko ki fada ko yau gidan yayi maki tsami da sauri yaron da ya jawo maganan muke fada akan shi yace.
Daddy ranan da kukai maganan ne maman mu tace taje ta labe taji mai kuke ma taro har da baba na dawanau.
Innalillahi ya fara ambatawa a bakin shi yanawa hjy maryam kallon tsana a fili kafin yace maryam abin naki har yakai can don kawai zan gana da yan uwana har ki tura min yara suyi muna labe ke a dole sai kinji kinga komai a rayuwan ki ?
Tir da wanan rayuwan da kika koyawa yara nan ya juya gurin ikilima da idon shi yana cewa ke kuma nasan maganin ku kafin ku karasa gurbacewa a gurin uwar ku ai.
Kai ranan dai sarka tayi halinta a gidan kawu don gidan ya rikice a baki daya don sarka gidan ta fadi kasa kowa ranshi babu dadi a ranan.
Don hjy maryam ta fadi har maganan da sukayi da mamu ranan cikin fadanta haka yasa hjy jummai hawa sosai.
Sai fada take da mamu wanda mamu na tsaye tun amsan farko da ta bayar Amma ta kada mata kai tayi shiru taja bakin ta gum tana sauraron ta.
Ganin hakan tana cin mutunci a gaban kowa duk abinda yazo bakinta na aibanci gareni ko mamu fadi take ba jin nauyin kowa a wurin.
Kawu da har ya shiga part din shi ya fito yana fadin kowa ya koma gurin shi a barta taita haukan ta aure dai ne ba fashi har salma da ikilima in Allah ya yarda rana daya zan wanke su gaba dayan su gidan nan.
Dama shi mutum in yayi ilimin iya shege idan ya rika sai ya koma yiwa kansa ai gaskiyar maimuna da tace albarkacin mu danki ya samu a gurin ta ta yarda da auren don haka na gode tunda har naci albarka gurin ta nida mahaifiya don mun fada taji.
Sai ga hjy na kuka da hawayen ta abinda yasa jikin duk wanda ke gurin sanyi ke nan itama hjy maryam din kuka ta aza wai har ikilima nawa take da zaice zai aurar da ita.
A cikin part din mu tunda kawu yai furucin sa na tabbatar da gaskiyar maganan ashe ba kake ikilima tayi min ba haka zancen yake na yanka wani uba ihu a gurin mamu ta bugeni a baki na shige dakin da sauri ina mai ci gaba da kuka ni kadai.
Mamu na shigowa falon ina takure a kasa gefen kujera nace mamu wai da gaske kawu keyi zai mun aure da ya umar don su Aisha a hanyar dawowan mu sun fada min ko waye ya umar din cikin yaran hjy.
Mamu ki fadawa kawu ban son shi don Allah a mayar dani gidan baffa na misau da ai min wanan aure.
Wani irin tsawa ta daka min saida na firgita na manne da kujeran dake kusa dani tace ke har kinsan wani so can yanzu.
Halan shima an fada maki yana son nakine ba biyayya yakewa mahaifin shi ba dake zaki kasayin abinda yayi ko butulci zakiwa kawun naki ne yanzu bayan ya gama inganta maki rayuwan ki na baya har kike fadi yanzu da bakin ki wai a mayar dake misau gidan baffan ki.
Kaina dake dunkule

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login