Showing 255001 words to 258000 words out of 419207 words

Chapter 86 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1488

ke nan kin fara sallah zuwa yanzu yayi magana kamar yana rada kada wani yaji mai yake fadi a lokacin.
Shiru nayi ban motsa daga yadda nake ba ban kuma yi magana ba ya kara kwanto da kanshi yana matseni a jikin shi ya kara fadin.
Bakiji abindana tambaye ki bane zarah bana son ina magana ana kyaleni hakan zai hadani dake matukar ina magana baki ban amsa.
Tambayan ki nayi kinyi wankan hailan ki nace a dan tsorace sai nan gaba har yanzu yana nan bai dauke ba.
Dan murmushi naji ya sake kafin ya kara manna jikin shi sosai da nawa kamar zai ballani yace tun bakizo duniya ba nasan wanan babin yarinya .
Don haka koya dauke ko bai dauke ba a yau din nan zan karbi hakkina gareki gabanane ya fadi na tsorata da jin kalaman shi da kuma abinda hannayen shi ke mun a jikina.
Cikin wani irin murya da tsorata dan hawaye yazo min a lokacin nace don Allah yaya ka barni kabani salama a rayuwata na rokeka.
No no no zarah kiyi hakkuri yau ki ban hakkina hakkurina ya kare a kanki zuwa wanan lokaci ki tausaya ki daure in karbi hakkina a gutin ki hakana ?
Ina kokarin kwatar kaina daga irin rikon da yai min a lokacin naji yayi murmushi naji ba zan so in tilastaki in maki dole ba .
Tunda na rigada na gane baki da niyar bani a cikin sauki kamar yadda nake son bi dake a cikin lumana baki da tauayine zarah a ranki ?
Ya tambayeni a lokacin da yake dan dago kanshi daga kafada na da yake kwance kin san ban tare da merry a kasan nan balle ta kawar min da abinda nakeji a yanzu.
Kaina na kawar gefe gefe nace idan wane neni banda matsala daku zaka iya binta kasan da take ai ba don ni kake zaune a nan ba dama.
Anyway komai zaki iya fada a yanzu do ina neman hakkina a gutin ki yanzu saidai ki sani ba zai yuyu in zuba maki ido hakaba muna zaune a gida daya in takurawa kaina tunda sadakina ya bani hakkin yi hakan a tare dake.
Da farko naso mu fahinci juna dani dake ki gane hakan da kanki amma sai naga ke wanan baya gaban ki ko kadan .
Don haka zan karbi abina nawane bana wani ba aduk lokacin danaso kuma naga dama a wurin ki in yaso daga baya sai ki dauki wanan akidar da kikasa a zuciyar ki ki yafawa kanki kuma don kina ganin in anyi hakan abubuwa zasu biyo baya a zaton ki .
Ganin maganan shi da gaske yakeyi ba gudu baja da baya gaskiyar zuciyar shi yake fadi a lokacin don ya koma min kamar wani zarare dashi nake gani ba kunya ko shayi ko kadan a idon shi namiji ke nan.
Ganin da nayi shifa da gaske yake bada wasa bs yasa na sake kokarin yunkurin kwatar kaina daga rikon da yai min a lokacin.
Saboda na firgita ainun da abinda yake fadi a lokacin don ba wasa ko kadan a fuskan shi lokacin.
Don Allah yaya kayi hakkuri ka barni kada ka rabani da daraja ka wullakantamin rayuwa kazo ka kini daga baya in zama abin dariya a gurin mutane nasan bani kake so ba rashin matar ka yasaka zuwa gareni yanzun din.
Ban an kara ba naji ya matseni sosai a jikin shi yana aika mi sakkoni a dukka sasan jikina kuka na fara masa ina magiya ina hadashi da Allah.
Amma shi ko a jiki shi lokacin yayi nisa baijin kira saida ya gaji don kansa ya janye daga jikina yana maida numfashi idanuwan shina runtse.
Ina jin ya sake ni na fito daga kitchen din da sauri na har ina tuntube da kafet din kofan kitchen din na rugada gudu zuwa dakina.
Ina fita ya jingina bayan shi da carvenet din kitchen din yana jin wani irin shauki a tare dashi don bai taba zaton jin gamsuwa a jikin wanan yarinyar yadda yaji ba.
Yarinyar daya raina yake mata kallon karamar alhaki sai gashi tun farko taba jikin ta ya shiga wani yanayi daya kasa control din kanshi akanta tun lokacin.
Taushi da kamshi jikinta zuwa dukiya kirjin ta ya sa ya raja,a daya kasa kama kanshi akanta yanzu yanzu ya gaskanta maganan Yusuf yola da yake fadin kai kake daukata yarinya.
Ita mace bata da kankanta ai yadda ka rainata saita baka mamaki idan kaje gareta sai ka raina kanka.
A da yasa a ransa zai daure dukda babu soyayyanta a gare shi zai daure ya sauke nauyin daya rataya akanta shiyasa ya fara tilastawa zuciyar shi zama da ita koda ita din bata da ra,ayin hakan dashi.
Da kyat ya iya daga kafa yabar kitchen din cikin dayi jiki ya nufi dakin shi gadon shi ya hau ya kwanta rub da ciki ya rintse idanuwan shi babu abinda yake gani sai suran fatima zarah aruwa sayadin mamu a lokacin.
A dakina ina shiga na rufo da zumar murza key a kofan sai dai babu shi babu alamashi gutin haka yasa na rufo kofan da karfi na nufi gado na fada zuciyana cike da tsoro da fargaban yaya da wanan sabon yanayin da yazo min dashi yanzu.
Sam ban kawo rashin ganin key dina a lokacin yana da nasaba da yaya ba don ba mutum bane daya kula da shiga min daki babu dalili tun zuwa na gidan key din yana makale a jikin kofan.
Na dade kwance a dakin can na tuna da girkin dana dora a gas da sauri na yunkura cikin sanda na nufi kitchen ban ganshi a falon ba na shiga kitchen din na samu ya rage min karfin gas din.
Sauri nayi na kammala na gyara gurin don kada ya dawo ya riskeni ciki ranan a dakina naci abinci nayi sallah ina gamawa hutu muke na danyi karatu na shiga nayi wanka don akidanane yin hakan ban iya kwanciya banyi wanka ba tun a gida na saba da wanan wankan daren.
Na fito har lokacin jikina bai sake ba a gidan tunda nasan yana gidan lokacin don ba inda zai tafi din yanayin sanyin da kasan ke ciki mutane in ha dole ba basu faye zirga zirga zuwa ko ina ba.
Bayan na kammala shirina na kwanta har barci ya fara zo min sai lokacin na tuna da ban rufe kofa ba don gujewa yaya ranan don a da haka nake barin kofan koda baya gidan ma.
Tashi nayi na fara tunanen ina key din kofan ya shiga duk iya neman da nayi mai ban iya ganin sa ba a dakin.
Haka na koma na kwanta jiki a sabule naja bargo na rufe jikina dashi har kai sannu a hankali barci ya fara daukata.
Banji shigowan shi dakin ba don barci ya fara daukana a lokacin ya shigo dakin ya tsaya yana kallon yanayin dana kwanta din a tsorace nake da alama.
Fitalan dakin ya kunna haske ya gauraye dakin ga baki daya zubur na bude idona daga barcin daya fara fisgata na bude idona na sauke a kanshi.
Yana tsaye ya harde hannayen shi ya zubamin idanu akaina ba wasa ko wani sayina fuskan shi yace ki tashi kiyi alwala sallah zamuyi.
Banga fuskan yin musu ba a lokacin na tashi kamar yadda ya umurceni ina tafiya kamar zan fadi don tsoro a lokacin.
Sai dana dan bata lokaci zuciyana cike da tsoron abinda zai faru a kaina wanda ban sani ban taba zaton haka zaizo min ba.
Har na fito na samay shi a tsaye a tsakar dakin nawa ya kurawa wuri daya ido kamar mai tunanen wani abu a ranshi jin karan budan kofana bai tsaya ba naga ya nufi saman sallayata.
Jiki ba kwari na fara neman abin sallahna na saka lokacin naji ya tayar da sallah ko.
Raka biyu mukayi saidai don dogon surar da yaja muna a lokacin yasa muka dan dauki lokaci muna sallah.
Mun idar ya tsaya addua a baiyyane godiya ga Allah da neman zaman lafiya da zuri, a masu albarka ya shafa nima na shafa.
Naji ya ambaci sunana a hankali haka yasa na dago kaina na dan kalleshi kafin yace zarah ki kwantar da hankalin ki ba ha,intarki zanyi ko wani abu ba idan nayi hakan na zalunci kaina na zalunceki riban mai zan samu a yin hakan.
Ki tashi mu kwanta ba komai zan maki ba kwanciya kawai nake son muyi tare har zuwa ranan da zaki bukaci ban hakkina da kanki.
Kuka na soma yi sosai a lokacin ya dago tare da dafa min kafadana ya kara matsowa gaf dani har ina juyo numfashin shi a lokacin.
Kidimaiwa nayi lokaci guda don gaba daya ya juye min daga yaya ya koma min wani abin tsoro yanzu s rayuwana.
Ban san lokacin dana kai kaina a kadan shiba ina kuka ya dade zaune yana sauraren kukan nawa bai hanani ba.
Harsai da yaji na sau#uta kukan ya mike ya dauke ni sai saman gado tare da kashe fitilan dakin yana sauke numfshi a hankali.


ZAINAB IDRIS MAKAWA

NOVEL DIN KUDINE DON ALLAH KI KIYAYI SHIGA HAKKIN WANI YAR UWA
16/11/2021, 23:24 - ??5惙5惙5?: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM IYYAKA NA ABBUDDU WA IYYAKA NAS,TA,IN, , , ,


Tun lokacin daya fahinci barci ya dauki ni yayi ajiyan zuciya tare da kallon yadda nake sauke numfashina a wahalce har lokacin a tsorace nake da abinda ya faru tsakani dashi din a wanan daren.
Jin ajiyan zuciyana a cikin barci yasa ya dan rungumay ni zuwa jikinshi yana sauke ajiyan zuciya a hankali tare da fadi a cikin ranshi.
Zarah kin shayar dani mamaki a rayuwata dama hausawa sunce samun abin kwarai wahala gare shi.
Wahalan da yasha da zuciyar shi da tashin hankalin mutane da dama daga ahalin shi ma duk akan cikan wanan burine na mahaufin shi.
Lalai hausawa sunce abinda babba ya hango yaro yaro ko yahau tsauni ba zai taba hango shi ba tabbas daddy yayi gaskiya wurin dawo da rayuwan shi ta asali.
Tabbas ance kowa yabar gida gida ta barshi duk daba wai ya taba wani abin asha ba a rayuwan shi saita hanyar sunna.
Zai iya cewa matan hausawa daban suke ashe ko ta jinsin su yau sai yake ganin kamar farkon shiga jikin wata mace ya fara a rayuwan shi don irin ganima da ni,ima da natsuwan daya diba a jikin yarinyar daya raina da farko.
A fili ya furta Allah ka yafe min daddy na tuba nayi kuskure ka yafe min daddy naso in yaudari kaina in yaudare ka.
Ashe ba zabin banza kai muna ba daddy ka fimu sanin abinda bamu sani ba a rayuwan mu yau da nabi ra,ayin mama na bijirewa daddy da na yaudari kaina ashe.
Da kyat ya samu ya dan runtsa idon shi barci ya dan daukeshi kadan da asuba alarm din wayan shi ya tayar dashi don sallah.
Firgigi ya falka yana kallona har lokacin barci nake ina sauke ajiyan zuciya saboda kukan dana sha.
Ya mike yana tunane a ranshi kodai zalaman shi yasa yajinwa yar mutane ciwo bai sani ba in ma zalaman ne yasan yayi mata haka kanta daren jiya zai iya cewa matsuwan shice ta ja mai yin hakan don a matse yake a yan watannin nan yana bukace da bukatan shi.
Har yakai bandakin ya shiga don yin wanka yaga wurin a tsabtace kamar inda ba,a amfani dashi ko yaushe komai na gidan yana nan tsab dashi don tsabta zarah badai tsabta ba .
Duk tsaba da kulawan shi saida ya yabawa tsabta irin na zarah a rayuwan shi yarinyace zarah karama amma tarbiya data samu a gida yasa ya fara kwadaituwa da halaiyan ta.
Don irin yadda ta iya boye sirin su tsawon shekara biyu da rabi ba wanda yasan alakan auratayan dake tsakanin don dokan daya saka mata kawai.
Tasan idan yana gidanta ta ciyar dashi yadda ya kamata sai dan gyaran da yai mata kadan wanan kuma yasan karancin shekarunta ne ya hana ta gane hakan.
Har ya fito daga wankan bayan ya hada ruwa masu zafi a ciki har lokacin ina kwance ina batcin wahala.
Sallah ya tayar a kada ya makara yana idarwa ya nufo gadon ya ya dan kira sunana a hankali haka yasa na dan motsa ganin da yayi ban da niyar tashi yasa shi sukutana a cikin barcin na danyi kara ina fadin a wahalce don Allah yaya kayi hakkuri na dauka wani abin zai kara yi min kuma.
Saida ya tabbatar da na zaunu da kyau a cikin ruwan dumin ya bar ban dakin zuciyar shi cike da tausayina a lokacin don kawai baida zabi ne har hakan ya faru tsakanin mu.
Don saboda da shakuwan da mukayi a dan zaman tare sai yake jina wani bangare na zuciyar shi yanzu.
Sauka yayi zuwa kitchen ya hada min tea mai zafi da kauri tare da dauko magani a dakin shi ya nufo dakina har lokacin ina zaune na kasa anyanawa kaina komai a bandakin sai kukan da nake wanda ba sauti ciki.
Muryan shi naji yana fadin ba zaki fito hakana ba lokacin sallah yana shigewa ko sai nazo nayi maki da kaina.
Jin hakan nasan yanzu ba karamin aiki bane gare shi don zai iya yin hakan tunda ya furta hakan a fili.
Da sauri na dan cudanya jikina yadda addini ya koyar damuyi ji nayi ba zan iya kara sanya zanin dana kwanta dashi ba na dan leko kai daga ban dakin sai na ganshi a tsaye ya ban baya kafita in dauki zanina don Allah na iya fadi a lokacin.
Da sauri ya juyo don jin abindana fada yana fadin a ina zanin yake in miko maki nidai ka fita don Allah in dauka da kaina nace cikin dan muryan da bai fita.
Baiyi magana ba sai naji ya juya ya fita da sauri na fito na dauki zani na daura na saka hijjab din sallahta na tayar ina idar a lokacin kuma abinda ya faru tsakanin mu ya dawo min a raina tiryan tiryan wasu hawayene suka ziyarci idanuna bal,bal,bal lokaci guda.
Kuka sosai na zauna nayi ni kadai a dakin mai faruwa ya riga daya faru a daren jiyan saura in tsura ido inga sakamakon da zai biyo bayan abinda ya faru din tsakanina da yaya yanzu.
Tun da har mahaifiyata ta kasa ban zabin kaina na matakin dana dauka da nake ganin zai fitar damu daga manufan su maganan ta kullun nakira ko takira shine inbi umurnin mijina in mashi biyyaya ma,ana dai in mika kaina a gareshi a fakaice .
Nasan yanzu sunana karamar bazawace a gurin shi kai ba wurin shi bama a gutin kowa dana sani don ba yadda za ayi indai ba hjyn su ce ta janye maganan ta akan mu ba ya zauna dani har madi.
Tau yau dai na mika saura mamu da kawu dasu amma su saurari hukuncin abinda zai biyo bayan umurnin su yanzu gareni.
Haka na zauna ban iya tashi a gurin ba balle duk motsi sai na runtse idanuna don ciwo da nake ji a karkashina har a cikin raina nake jin shi lokacin.
Ina zaune ina ta sake sake a raina in kulla wanan in warware ni kadai a dakin na kudundune kaina da gwiwa na.
Muryan shi danaji yasani razana da sauri na dago kaina fuska shabe shabe da hawaye ido ya kurawa yanayina ido a hankali ya kai tdugunne a idana nake zaune.
Dan rungumoni zuwa jikin shi yana fadin oh sorry zarah don't cry again don wanan abin ya faru tsakanin mu kike zubar da hawaye haka ?
Makin ki godewa Allah da ya tsareki ya baki ikon sadaukawa dan uwan ki da wanan abin mafi daraja ga mace.
Don't cry again kukan nan naki yana taba min zuciya matuka ba sai kinyi kuka zan gane abinda nai maki bada sin ranki ba and kuma wanan kukan yana nuna min irin kiyayyan da kike mun a filine zarah.
Ban iya magana ba ban kuma dago kai na kalleshi ba jin nayi shiru ba amsa ya mike tsaye a hankali ya dagoni daga inda nake zaune a takure.
Bakin gadona ya kaini ya zaunar dani a hankali ya mika hannu ya dauko flask din shayin daya hado min ina kallo ya tsiyaya a cup ya miko mi yana fadin karbi kisha sai kisha magani don jikin ya rage maki tsami.
Da kyat na iya bude baki nace dashi na koshi cikin muryan kuka kin koshi damay yaci yana kallona .
Maza karbi nan ki shanye in baki magani ko kuma ranki yanzu ya baci a dakin nan jin yadda yake magana fuska a daure yasa na mika hannu da sauri na karbi kofin shayin na fara kurba kadan kadan saboda banjin dadin shi ko kadan a bakina.
Yana tsaye ya dora hannayen shi saman kunkurun shi ya rike da hannu biyu haka yasa corth din jikin shi fara dan dagawa daga baya ta yadda zaki iya hango zanzaron shi da farar

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login