Showing 30001 words to 33000 words out of 419207 words

Chapter 11 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1386

may yake da mace har haka oho ?
Sai kuma ta juya gurin hjy maryam tana fadin ita kuma wanan munafukar yau rawan kai da jin kai zai tashi a gidan nan ke nan wai ita miji ya kula ta yau.
Dakin hjy maimuna ma cewa tayi akaiwa yaran hjy Jummai abin karyawa kafin uwar ta fito don su karya don shiyasa bata damuwa da yanayin yaran don tasan hjy maimuna na kula mata dasu.
Amma kishi da munafucin baisa taga halarcin hakan a gare ta kullun cikin tsangwaman ta suke don kada dai ta wala ita da miji a gidan.
Sai da ya gama shirin shi tsab ya fito zuwa part din Amma wace sanyin bai hana ta zama da yaranta a lokacin suna hira ba da hadiye da maimuna a part din suna debewa mahaifiyar su kewa.
Sai yaran su dake nasu harkan duk a cikin falo inda jefi jefi suke kula yaran wurin tsawata masu ga kijin da sukeyi a falon.
Sallaman shi da gyaran muryan shi ne ya sanar dasu zuwan shi a wanan lokacin don haka kowa ya shiga gyarawa banda hjy maimuna dake zaune a yadda take takure saman kujera ta kudundune a cikin hijabi sky colour don sanyin da take ji a jikin ta.
Amsa mai sallaman sukayi tare da gaida shi da kwana yana amsa masu ya zube kasa don gaida mahaifiyar shi shima.
Bayan sun gaisa ne sameer da salim suka haye jikin mahaifin nasu suna gaida shi yake tambayan su lafiyan su sai kuma ya juya gurin mahaifiyar tasa dake fadin yau antashi da yanayi a garin dama nasan ba zaka fita maza ba yau.
Yace wallahi hajiya hakana ne ina tsoron sanyin nan kada ya taba lafiyata in kwanta shiyasa na dan sahirta mashi kadan ya rage.
Hakan yafi ai riga kafi yafi magani yanzu ba gaka zaka fita ba sai ya juya inda hajiya maimuna take zaune ta mayar da hankalinta ga wayan ta tun shigowan nashi bayan sun gaisa ya fara gaida mahaifiyar shi ta mayar da hankalin ta ga wayan ta.
Ke ki shirya gobe zan shiga bauchi sai mu karasa katagum din zancen yarinyar nan yake ce wa hjy maimuna din da kanta yake duke.
Jin zancen katagum yasa ta dago kai tana kallon shi tare da fadin ai ina ganin iya misau zamu tsaya don can suke yanzu karfin maganar kuma hannun yaya sale yake dama.
Madallah inji Amma zancen dawowan Aruwa gidan nan ya taso ke nan ashe ina da babban bakuwa tafe ke nan ?
Hadiye ta amsa da fadin a, a Fatima zata dawo gidan nan da zamane ashe banko sani ba sai yanzu.
Amma tace kin san halin uwarta da zurfin ciki ai bata son wanan zancen a fili sai dai tabar abu ga zuciyar ta yayi ta cin ta a rai.
Murmushi Alh sani yayi tare da kallon su yana fadin shi zai fita ke nan sanin ita zata karbi girki kuma bai sallamay ta ba yasa ta mike tabi bayan shi do sirantawa suka fita a tare.
Sun dan taba tafiya yaja ya tsaya yana kallon ta kai ta sada kasa yace yaya naga jinkin ki yayi sanyi ne kuma ko an fasa dauko yarinyar ne tace.
To Amma yaya, sai kuma tayi shiru kallon ta yake har lokacin ya rasa gane may take son fada mashi kuma akan tafiyan sai yace amma kuma may ?
Gani nayi dai ya kamata in san da tafiyan da wurin don indan tanadar masu dan tsaraba da zan tafi dashi na tafi masu hannu rabbana hakana ?
Dan murmushi ya sake tare da fadin wanan ba matsala bane don na gama shirin komai a bangare na.
Nagode ta furta tare da dan tsayawa batare da tayi magana ba kuma hannu ya tura cikkn aljihun shi ya ciro kudin da baisan ko nawa bane ya mika mata tare da fadin sauran kyayi amfani dashi ga tafiyan idan da abinda zaki kara a wajen ki .
Godiya ta sake mai lokacin har ya fara tafiya tayi mai Allah ya tsare a dawo lafiya ya amsa da Amin ya fice daga part din sai dai ashe yar gurin hjy na shigowa komai akan idon ta akayi.
Wani kallo mai fassara yarinyar tayi masu ba tare da ta tsaya gaida maimunan ba tana kokarin shiga wurin amma dan gara ta hangota tana rusunnin gayu tana gaida mahaifin nata.

Yau saboda sanyin muma a nan ba wasu mutane a wajen don kowa ya rufawa kan sa asiri an she gida muna dan dakin mu da yafi ko wani sanyi a gidan saboda rufin shi babu silin kwano ne zalla a sama kawai.
Daga can cikin gida muke jin muryan umma na kwalla min kira ke fatima fatima fa, ko sai nace a ruwa zaki gane dake nake yi inda ta karaso har kofan dakin mu.
Zubur na amsa daga barcin daya dan dauke ni na safe wanda ban dade da farashi ba donndan hiran da mukayi da manjo lokacin da na gama sallah.
Ga manjo na fadin tana barci amma umma sai kwala min kira take kamar da gaiya.
Fitowa nayi don jin kiran kamar ba na lafiya bane sai fadin take da na leko kifito rana yayi baki wanke muna kwanonin abinci ba ko kin aje wanine da zai wanke su.
Nace umma sanyin nan nake jira ya rage in fito sanyi nake ji sosai yau tace zaki shige ki dauraye kwanonin nan ko sai na bata maki ranki.
Umma nifa ko abincin daren jiya ba a bamu ba don an ga na dafa taliya da yamma tace eyyeh ke nan ba zaki wanke ba tunda bakici abincin ba ?.
Na turo baki ba tare da nayi magana ba sai dai kuma ban gusa ba ta sake fadin zaki gusa ko sai na falla maki mari na sake fadin umma ai zan wanke bance ba zan wanke ba.
Ban kai ga karasa magana ba naji saukan mari a fuskana halin nawa nayi na ihu Manjo tayo waje a gigice tana gyara daurin dan kwalin kanta.
Tana fadin may yar nan tai maki da safen nan kika duke ta haka safiya sunan da take kiran ta dashi ke nan.
Muryan yaya dan tantirin gidan mukaji yana fadin dallah ji wanan tsohuwar kamar an wani duke ta sosai umma saude da ta leko tace dama ai don ta fito tai wanan ihun.
Kai kuji tsoron Allah may wanan yar marainiyar Allah ta tsare maku a gidan nan ne wai yarinya bata da daman magana sai duka ina nan diyan ku ke maku abinda suka ga dama wana na taba ganin kun duka a cikin su.
Sai kuka nake wi wi wi wanda ke kara zuga zuciyar manjo tana sababi dasu yace ke dallah ki ruwa mutane baki karna zo wirin nan in lalatsaki yanzu.
Manjo tace in ka iso zo ka lalatsata din dan banza mara kunya kawai yace idan batayi shiru ba yanzun nan kuwa zan mata dukan banza idan yaso tayi kukan da tushe .
Jin abinda yake fada baisa na daina kuka ba don manjo na gurin nasan ba zata bari ya duke ni ba sai dai da biyu nake kukan don kar nayi wanke wanken kwanonin da sasfe safen nan.
Ganin nama kara volume din kukan ne bata san lokacin da ya zagayo inda nake ba ya fara kai min duka ta ko ina ya samu a jikina har sai da uwayen nasa suka tsorata sukai mai magana.
Manjo tayo kanshi da icen girki dats gani a wuta ta dinga kwala mai a jiki iya karfin da Allah ya bata shima sai da yaji jiki ranan haka manjo ta haukace masu a cikin gidan ranan sai da a ka kira baffa ya dawo gida kafin ta lafa.
Baffa yaga irin ta,a san da yaya hashimu yai min yayi fada sosai shima ya kafa dokan kada wanda ya kara duka na ko harara manjo tace har aiki.
Lokacin umma safiya tasa baki tace wanan kan bata isa ba muddin zamu dafa mu bata taci sai tayi muna wanke wanke da shara.
Manjo tace ai sauran yaran basayi ba kunya umma safiya tace ai itace karaman su a gidan yanzu dole ita zata dinga yin wanan.
Baffa sale na tsaye sororo bai iya tsawata mata komai ba a lokacin manjo ta juya gare shi tana fafin kana tsaye matar ka ke ci mun mutunci a gidan nan baka iya daukan mataki ba a kai.
Sai lokacin yace ke safiya ya isa hakan kin dai ji abinda nace yana kokarin juyawa ya fita daga inda manjo take ta sake kuka wi wi wi.
Abinda ya kashe mashi jiki ke nan ya kasa fitan da yai niyar yi da farko ya juya zuwa wurin ta yakai kasa tsugun ne yana bata hakkuri.
Nan su umma suka hau zagina suna fadin na kai ga yadda na keso ai yanzu mukan zaman ki a gidan bai haifa muna alheri ba.
Gidan wan mahaifinta ne sai dai ku ku fita ku barta a nan amma ba inda zata tafi daya fi nan din dama abinda mahaifiyar ta tagani ke nan ta barta anan kada ta kashe mata auren ta a can.
Ai babu uwar da zata bar ya kamanki ko waige ta batayi dake ta kwaraice da tuni ta dauke gurin ta ai.
Amma da tasan abinda ke nan tazo ta watsar dake ko waiwaye babu an kwaso jangwan gwan aka kawo muna gida da rana tsaka .
Duk wahalan da muke dake ba a gani a gidan nan don kina makira uban naki ai da yake da rai kan shi ya sani da uwarki sai ke wa yake taimakawa da yanzu wallah zai ganmu ?
Salati manjo ta kara sakewa ta aza hannu a kai tana masu kururuwa a cikin gida daya kara tayar da hankalin baffa don baffa shiru shirun shi har yasa iyalin shi kaf sun raina shi.
Da kyat wanan fitinan ya mutu suka shige part din su baya fitan baffa suna surfa min zagi da aibanta ni iri iri da mugun fata a kaina.
Zagi dai iya zagi na sha shi ranan a gurin su sai dai Allah ya kyauta kawai don kiri kiri suke goyon bayan diyan su suna nuna min banbanci a gidan.

Ta shirya tsab ta dauki yaran zuwa part din Amma don ba bazata tafi da yaro ko daya ba tunda ranan zasu dawo garin.
Bayan ta rufo kofan ta ne ta juya tare da yaran suka nufi can a daidai lokacin da maigidan su ya fito daga part din shi ya nufi part din hjy jummai don su gaisa.
Hjy maryam da ta fito gaida Amma ce suka hade tun daga nisa take kare mata kallo irin shigar da tayi alama ya nuna mata fita zatayi a lokacin.
Dan murmushi ta sake mata don samun fuska taji inda zata tafi suna hadewa hjy maimuna tace ina kwana anty maryam.
Lafiya kalau maman biyu yau sai ina haka kuma ta dan sake murmushi itama tare da fadin zamu shiga wurin gwago ne ta saka ta a kwana itama tace to a fito lafiya.
Alh na shiga part din jummai dake hake dashi kan kudin da yarta ta fada mata jiya taga yana ba hjy maimuna a kofan Amma.
Bayan sun gaisa sama sama da sune yake fadin zanyi tafiya yau tare da maimuna zamu tafi bauchi gurin yarta.
Kamar bata ji shi ba tace dama ina son ka shigo ka bada kudin yaran nan su samu su tafi duba takardun su.
Kallon mamaki yai mata tare da fadin shi duban takardun har sai da kudi akeyin shi yanzu kuma in kuma na trasport kike magana ina dai diver ne zai kaisu.
Amma kaima kasan dole sai sun rika wani abu dai ko don ba za a sake su haka su kama hanya ba wani abu a hannun su ba ?
Yace to ki basu yau dai kan ban yi niya ba ni tace eh ai ba abin mamaki bane don ka hana su kudi yanzu amma kana iya ba wa yanda ka mayar mutane a gidan dul sanda suka bukata su.
Wani kallon mamaki yayi mata tare da girgiza kan shi ya juya zai fita ta kara fadin duk dai abinda mutum keyi Allah na ganin sa ai.
Idan na cuce ki sai ki barni da Allah yana fadin haka ya sa kai ya fita ranshi bace da al,amarin ta yanzu ko wurin hjy maryam da ya shiga itama basu kwashe da dadi ba da ita.
Don duk wace yacewa da hjy maimuna zasuyi tafiya wurin yar ta sai ran maishi ya baci itama hjy maryam din korafin tayi mai wai kiri kiri ita ya hanata karbo maganin ta da takeyi amma gashi zai tafi da maimuna da kanshi wurin yar ta ai.
Cewa yayi mata da bake zuwa dake da farko amsan magani sani akayi ko wani ya gune maki a gidan nan koda maimuna muke zuwa na hana din in kin isa sai ki tafi mu gani.
Ita ko hjy maimuna bata fito ba sai da ta bisu daya bayan daya tayi masu sallama duk da ba wani Allah ya tsare janya mai kyau data samu a wurin illa sai kun dawo.
A haka suka kama hanya sai bauchin yakubu sammakon da sukayi ga kuma lafiyar yayyar mota suka isa da wuri.
Ta san gidan don haka ne basu wani sha wahala ba gurin neman gida sun iso da karfe daya saura garin misau din lokacin na gama kukan wahala ina barci jikina duk yayi min tsami sosai ga zazzabi na son kamani Allah ya taimaka baffa ya aiko min da magani in sha.
Mutanen gidan suna zaune suja dinga jin sallama daga kofa sai wani yarone ya fito daga falon su inda suke yawan zama babu komai a cikin falon sai kwamatsen su da kayan dauda da suke tarawa a ciki don dakuna sun masu kanana yan matan kuma a falon suma suke kwana amma hakan baisa sun gyarashi ba.
Yana amsa sallaman ya juta don fadawa iyayyen don bai san ta ba sai umma saude ta leko da farko bata gane ta ba sai da tace yaya baki gane ni bane maimuna ce fa daga kano.
Tace Lah maimuna kece hakan ban sheda ki ba sa;un ku da zuwa yanzun kuke tafe ne sai ta hau kamay kamy da sabarin baki.
Saude ke da wacece a gurin wai umma safiya ke tambaya tace wallahi yaya kinga maimuna ce uwar fatima a garin namu yau.
Wace fatiman kuma tana fitowa take tambaya ganin maimuna a tsaye cikin shiga ta alfarma babu inda zaka ganta ka kushe mata ta waye ta zama babban mace sosai kamanin ta na asali ya kara fitowa fili.
Turus tayi tana fadin maimunan Abubakar ce haka ta zama wata yar gayu da ita ikon Allah lalai duniya mai canza kama.
Iso sukai mata da ta shigo falon nasu mai kama da dakin mahaukaciya don ko tsohuwa ba zata bar guri ta haka ba.
Bayan sun gaisa da ita ne suna dan kamay kamay take fadin babba fa ko sun koma azare ne ?
Babba na nan suna shiyan su bara a kai ki saude tace tana mikewa bata zaci a gidan part din yake ba sai da taga an nufi dan dakin da take zaton ko akulkine da ita a ranta tace ikon Allah tare da rashin jin dadi cikin zuciyar ta.
Daga kofa suke sallama sau uki suna yi can manjo ta karba masu sallaman tare da fadin iso daga ciki suka daga labulen tsohon zanin manjo da muka sa a kofan suka shiga.
Babba maimuna ce a garin namu yau ta zo tace wace maimuna fake nan tana tambaya hjyn ta kutso kai cikin dakin.
Suna arba da manjo sai tsohuwar ta sa kuka dan gurin ta samu daga gefen da nake kwance ta kai zaune itama tana share nata hawayen .
Maimuna ashe kina tafe manjo tace bayan gama kukan ta datayi tana kara dan gyara mata wurin da take zaune sai saude ne tace wanan barci take ne ?
Yomar ai dole tayi barcin wahala tasha duka haka da sauri saude dake jin tsohuwar na shirin masu tonon sila ta juya tare da fadin bara na kawo maki ruwa dai .
Hjy ta kalli tsohuwar tace tare da maigida na muke yana waje ko za, a kai mai abin zama a wajen .
Sauden tace barin tura yaro yanzun ya kira shi a shago don kada a barshi shi kadai a waje nan ta bar hjy da manjo.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
16/11/2021, 22:39 - ??5惙5惙5?: ALHAMDULLAHI ALAH

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login