Showing 315001 words to 318000 words out of 419207 words

Chapter 106 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1394

Har layin kin nan mun bata ashe an sace wayan ki a lokacin bai shiga ba ban sake tuna maganan ba sai yau danaji wanan zancen a bakin hjy gamay dake.
Sayadi shine baki fada min ba duk dadewan nan da kikayi a kasan nan nace wallahi mamu na shafane tun lokacin da zancen sai naga ta fara hawaye masu zafi suna zuba mata a idanun ta.
Mamu ki bar kuka nasan har shagon matarnan idan har ban samu layin ta ya shiga ba zamu iya neman ta a can London din.
Sayadi tsoro nakeji a raina a yadda gwaggo ke ban labarin mahaifiyata tun lokacin da ta barni tabi iyayyen ta har lokacin basu karajin komai daga bangaren taba.
Idan ya kasance wanan matar basu bane yan uwan mahaifiyata zan kara shan zunde a gidan nan ke nan.
Wa zai san wanan zancen mamu ko Amma ba zan fadawa ba sai na tabbatar da komai yanzu dai ki tambaya ki san sunan mahaifiyar taki da kasan su mu sani a gurin Amma .
Gwaggo bata son ina mata zancen nan ko kadan sai nake gani kamar basuyi rabuwan lafiya da ita bane a lokacin.
Idan kin ban baki zan tambaya a cikin hikima muji ko tasan sunan ta kafin in kira matan in samu hujjan da zan bata kan tambayoyin da zasu yi mun a kanki.
Idan zaki iya tambayan ta sai ki gwada muji nace shike nan zan gwada in gani ban bar dakin ba saida naga hankalin ta yadan kwanta ina bata labarin komai akan haduwarmu da matar.
Bayan la,asar na shiga dakin Amma kamar yadda na mayar da part din ta wurin hirana da shan iska tundai idan in murja tana gidan.
Nan muke zubewa muyi hiran mu muna mata shewa tana zagin mu don na kwatar da hankalina ban nuna damuwan rabuwa da yaya yana cin zuciyana ba ko kadan a gidan ba har wani ya gane hakan kamar yadda mamu ta lurar dani.
Sai kuma yin hakan ya koma yiwa hjy zafi har bata iya boyewa a ranta din nasa an kara gyarawa mamu part din ta danta ya turo kudi mai yawa an muna gyaran an saka sabbin AC don nace zafi yana damuna.
Sam bata ganin mu cikin kunci ko rashin walwala sai kuma ta koma cewa mun asirce mata da da asiri baya kallon kowa yanzu idan bani ba da yayana da uwata.
Ammace ita kadai na samu a falo babu kowa a part din don shirun da falon yayi ta kalleni tana fadin ai na dauka kinyi fushi ne da kin tafi.
Dawa zanyi fushi Amma na zauna ina fadi tace yo ni na sani yar nan tunda abin gidan nan baya karewa kullun da kalar fitinan da ake tashi dashi a gidan nan.
Nace komai yai farko yana da karshe Amma idan Allah yayu mamu zata hadu da dangin mahaifiyar ta koda tsufa sai su hadu idan kuma Allah baiyi haduwan su ba sai a lahira Allah ya hadasu.
Ina kaiwa kwance don yanzu sam banda jimirin dadewa zaune ko kada nace waini mamu may ye sunan kakana da ta haifi mamune kuma ita mutumiyar inane wai ?
Sai naga Amma ta bata fuska tana fadin siyama naji iyayyen ta na fadi amma mu da halimatu muke kiran ta wurin mu.
Zancen mutumiyar inane ba zanje ga garun suba na takamaimai saidai nasan su din jinsin labawane dake makwabtaka da kasashen bakar fata a lokacin.
Karatu mahaifinta yazo yi a maiduguri da matar shi har ya fara sana,a anan kakan ki Amadu yana aikin kada a lokaci a nan suka hadu da ita haliman .
Anyi rikici sosai kafin su yarda su aura mai ita don yarinyar ta nace sai shi a lokacin bamu da hali nice nayi mai jagora lokacin kakan ku mijina yana raye da taimakon shi komai ya kammala.
Basu kai shekara biyu ba da aure kwatsam sai ga yanuwan su sunzo daukan shi ashe shidin wani dan babban gidane fushin zuciya yayi ya bargida ya dawo maiduguri ya zauna.
Zuwan yan uwanshi shi ya bata komai don sunce har halima ba zasu bari a nan ba tare zasu tafi saidai mahaifin ki ya rubuta mata takarda.
Magana har ta kaimu fadan sarkin barno a lokacin nan dai dole hukuma tace ya bata takardan ta su tafi da yarsu ya samu wata ya aura a nan.
Fushin haka lokacin mahaifiyar ki nada shekara daya da haihuwa nace su bamu yarmu muma dana san yin hakan zai jawowa mahaifiyar ki gori nan gaba haka da ban nemi su bamu ita ba A ruwa.
Baki tabajin sunan kasan ba a bakin kinta amma tace ni dai tana ce min su din bakaken larabawane ko yaushe ban tsamanin tasan komai ba game da iyayyen ta din.
Halimatu sadiya kenan take amma tace iyayyen ta kuma suna kiranta da siyama mudai a wuri mu halima muke kiranta.
Itama yanzu nasan tana cikin kewar yarta da mararin rashin ta a kusa da ita saidai nisa zai hanata zuwa don da ba wasa bane.
Saidai kuma nakanyi tunanen koda tazo din ma mu mubarcan tun bayan rasuwan kakan ku kawun ki ya dawo dani nan gida kusa dasu.
Don haka ba wanda zai fada mata a inda muke yanzu da zama koda tazo din neman mu.
Shiru nayi ina nazarin maganganun Amma a cikin raina yayin da ita bata kula da halin da nake ciki ba.
Ina nan zaune wurin Amma har bayan isha,i a daidai lokacin da nake shirin tashi na koma part din mahaifiyata ne mukaji ihu a cikin gidan wanda yasa mu fito ga baki dayan mu gidan waje.
Nafisa ce suka samu matsala da sauriyin da zai aure ta wanda murja tasha min korafi akan basu dace da juna ba nakan ce ina ruwan ta ba ita ke son shi ba hakana.
Sai gasu yau dan magana ya hadusu yayi mata dan karen duka a kofan gidan mahaifin ta kuma ya shigo har ta cikin get ya jefo mata zagi da tonon asiri a tsakanin su.
Wanda babu dadin ji kowa na gidan yana waje an kasa wanda zaiyi mai magana a gidan sai saurare akeyi abinda yake fadi din.
Kai amma dai baka da mutunci da kima aikai ka fita rashin tarbiya da zakazo har cikin gidan mahaifinta kanawa mutane rashin mutunci haka.
Ka koma gida a baka tarbiya zai fi don kai baka san darajan mace ba ko a gidan ku na fada a hasale.
Don raina ya baci da rainin wayau daya kawo muna har gida yana ciwa iyayyen mu mutunci.
Yace naji banda mutunci din ita tana da shine sau nawa ni kaina ina zubar mata da ciki shine yanzu zata koma bin wani dan iska kuma wai a haka akeson lakaka min ita in aura.
Salati aka dauka ga baki daya nace fita gidan nan mara mutunci da sanin yakamata har in kuyi hakan ai tare kuka aikata zunubin ku.
Asalima kaine wanda ka lalata har taji bata iya hakkuri dakai ta fara bin wasu mazan kajira kaga naka sakamakon dan iska kawai mara tarbiya.
Jin ina fada dashi yasa murja saka baki itama ta shiga tona mai asiri tana fadin kai waye baisan abinda kakeyi ba garin nan.
Kana sato kudin mahaifin ka kana rudin yan mata dashi har giya da karuwai kake kwasa kuma mun sani.
Yace ni kikewa kazafi babu kazafi a zance na don bakin da bai karya ya fada min daga gidan ku na samu labarin komai ka fita zakka a gidan uban ka kakaiwa mahaifin ka ko ina a duniya.
Ya nuna mu yana fadin you see karan ku zanyi don wanan sherin da kai muna Allah ya kaika dan iska kaji tonon asirin da baka taba zato ba na bashi amsa.
Ke Fatima ku kyaleshi yayi abinshi ga mara kunyar da ta ja min wanan abin har gidana ya juya wurin hjy data daskare a wuri daya yana fadin kin daiji halin yarki yau da kunnuwan ki.
Abinda take aikatawa a gidana sai kuma ya kasa karasa maganan ya juya ya koma part din shi.
Daya bayan daya muka dinga watsewa a gurin don maganan ya girmi kunnuwan mu da ji.
Dagani har mamu ba wanda yabi ta maganan balle mu zauna muyi zancen a dakin kowa yayi shirin kwanciya ya kwanta abinshi.
Washe gari ma da wani sabon rigiman muka tashi don iyayyen yaron ne suka zo gidan tunda safe wai anciwa dansu mutunci sun fasa auren a basu kaya su da suka kawo na aure.
Da lissafin kudi mai yawa da wai za a bashi wanda taci nasa tun anayi dasu da hjy a daki har suka fito waje suna cacan baki .
Hakan yasa aka fito don jin me kuma ya faru yau din ma daya daga cikin matan ke fadi munzo ne mu karbi kayan da aka kawo na auren dan mu yace ya fasa.
Ina tsaye daga kofan mu nace hjy ku koma kuce mai ba za,a bayar ba duk abinda yakeji a shirye muke dashi.
Shida bakin shi ai yace sau uku suna zbar da ciki shi shida ita don haka an rike kayan a matsayin kayan jegon ta na diyan da yake fitar mata.
Ban taba sanin akwai abinda zai girgiza hjy ba haka matan na fita get sai hjy ta sake wani irin kuka a wurin.
Gwanin ban tausayi tana fadin Nafisa kin gama dani kinja mun abin fade a gidan nan kin tozartani a idon jama,a.
Amma ta karbe da fadin kada kiga laifin yarki ita kadai kece mai babban laifi a gidan nan kowa yace ruwan wani bai tafasa nasa ko dumi baiyi.
Jummai kin cuceni kin bata min zuria ta ba zan taba yafe maki ba a rayuwa sai Amma ta fashe da wani irin kuka itama mai ban tausayi.
Da sauri su mamu da mama hadiye suka isa wurin ta suka kamata suna fadin tazo ta bar wanan maganan don Allah wanda ta fada ya isa.
Nikan kafana naja na koma cikin part din mu ina jin babu dadi a raina don abubuwan da suka faru babu wanda zaiso ace nasa ya sama yau.
Ko banza Nafisa yar uwatace kuma kaunar uban diyana bako zanso ace wani abu mai muni irin haka ya faru da ita ba.
Mamu ta dawo part din ta tana kitchen sai jin sallaman hjy maryam mukayi tashigo gaida ita nayi ina mamakin shigowan ta shiyan mu don ba kasafai take shigo muna ba sam na shafa da zancen daya faru ne yakawo ta.
Mamu ra fito tana fadin a,a hjy ce tace kedai nice maimuna magana ya isheni a zuciya nace bara na dan zo nan in rage.
Ke kinji mun yarinya da abin kunya haka ana cewa namu sune lalattu ana muna gori ya tayi goshi kaya har sait uku da sauran tarkace ashe ashe ba alheri suke aikatawa ba da yaron nan shiyasa dare da rana suna makale da junan su.
Hjy wanan magana ai ya shafi kowan mu nake gani ko kin mata da cewa Nafisa yar dan uwane ne wai ?
Kekuma ai diyar mijin kine idan sunan gidan nan ya baci ba Nafisa kawai za a zarga ba duk ya shafi yayan gidan nan ga baki daya.
Hakane kuma ta fada cikin wani yanayi sai kuma tace amma dai idan da dayan mu wanan magana ya shafa da yau munji hjy a gidan nan.
Ko itace ya shafe mu ai tasan gaskiya don babu musulmin kwarai da sheri zai samu dan uwan shi har yaji dadi a ranshi.
Bata dai gane komai ba haka yasa ta fita bayan ta gama yan surantanta a wurin nikan kamar bana falin zaune a lokacin don ko kallon ta banyi ba.
Tana fita nace mamu wanan matar har yanzu halinta yana nan ashe tace Allah dai ya rabata da wana halin yanzu ita har taga abin gulma a nan.
Can kuma ta juyo tana fadin wai nikan kunyi maganan da kikace da gwaggo ko bakuyi ba har yanzu.
Nace munyi mamu ta fada min komai har auren su duk ta ban labarin komai nace amma ai bata da laifin wucewa ta barki don su Amma su suka hana ta wuce dake a lokacin wanda a yanzu take da ta sanin yin hakan.
Haka dama Allah ya nufa damu haka ya tsaro min nawa rayuwan kuma nace hakane kuma.
Ina son zan kirata yanzu idan na gama abinda nakeyi sai muji ko za,a sameta muyi magana.
Ganin hankalin mamu ba zai kwanta ba yasa na dauko wayan na kira layin nayi sa,a ya shiga sai dai ba dauka ba har ya katse.
Kira biyu nayi ba a daga ba na fahinci mai wayan bata kusa da waya a lokacin.
Tana zaune ta tasani a gaba har na aje wayan ina fadin idan taga kiran zata kira kila daga baya.
Mamu ta sauke ajiyan zuciya tana fadin Allah yasa nace idan bata kiraba zan kara kira kafin dare yayi.
Har na aje wayan sai naga ya kamata in kira yaya inji lafiyan shi da yaran don yanzu ban san takamaiman ida suke ba dakai.
Kira biyu ya daga da sallama na amsa mai yana fadin yau kin tuna damu ke nan nace ai kullun ina tunawa daku.
Allah yasa yace nace baka yarda ba ke nan yace ina zan yarda tunda kina son dagwara min laifin da kinfi kowa sanin banawa bane.
Akan me zan dagwara ma laifi yaya Allah yasa hakan shine alheri a gare muna fada sai naji yace hakan kamar yaya ?.
Nayi saurin gyara zance na da fadin na zama ba kusa dakuba mana yanzu yace gara da kika gyara lafazin ki.
Ina sultana gata a hannun mamu tana jin ka bata wayan yace nace sultana din ko mamu yace sultana dai.
Na yunkura na kara ma yarinyar waya a kunnen ta magana yake mata tana dariya ba bakin da zata bashi amsa a lokacin.
Na cire wayan a kunnen yarinyar ina fadin bari in barka kayi aikin ka yace aiki yafi jinku a yanzu da nakeyi.
Yaushe zaku dawo ne ya tambayeni nace babu rana gaskiya kenan baki tausaya muna zahra dan murmushi nayi nace ina tausayin ku mana.
Saidai banda yadda zanyi ne a yanzu ka sani ina dai kwantar mai da hankali kada ya fusata in samu mu rabu lafiya dashi a lokacin.
Mun dauki lokaci muna wayan saida na tambaye shi queen fa yaya wajen su suna lafiya ko yace ban koma Europe ba har yanzu muna nan landin labawa tukun .
Mukai sallama na kashe wayan na zauna ina tunane a gurin yadda wanan al,amari zai kasance muna nan gaba.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:34 - ??5惙5惙5?: Ina zaune a inda nake ina tunane naji muryan mamu tana fadin kina son tayar da hankali kan auren da mijin ki zai kara ko ?
Na dago kai nace mamu auren shi bai damay ni ba sai dai nasan auren gaiyya ake son mashi a kaina.
Don murja ta gano ko wace yarinyar ce ashe diyar hjy sabuwace da sukai zama lagos ance idanun yarinyar a bude yake sosai zata girmi anty salma na a wurin haihuwa sosai.
Sayadi ba zaman lagos ba ko zaman turai tayi karewan bude ido mai zai dameki indai kin rike gaskiyar ki da amanan mijin ki a ranki kina kuma aiki da hankalin ki aiko tsakiyan faransa ta tashi karewan bude ido zata barki ne.
A yadda Murja ke fada min taji wai ashe zancen nasu ya dade sosai yarinyar taki da farko da hjy taso ayi hadin sai yanzune suka aminta da ayi suna bin hjy sauda kafa har ta yarda.
Mumu tace kamar nasan da zancen nan a baya saidai aikin mantuwa kawai ashe zancen nasu yana nan har yanzu ai da farko na dauka diyar Rakiya ce ko Ramatu dan suma suna son auren shi naji wurin hjy maryam.
Ashe yar wurin hjy sabuwa ce kuma yanzu idan wanan ce aiki barsu kawai zai fita a tsakanin su don bata da hakkuri ko kadan kowa yasani.
Ba mutunci ne da wanan matar ba su kansu suna tsoron masifan ta shine kuma yana zaune zaman zaman shi zasu dauko yarta su bashi kai hjy bata lissafi kafi ta aikata abu wallahi.
Mamu ai duk saboda nine nake gani zasuyi wanan hadin .
Tace a wurin hjyn gidan nan ba amma su wurin su aiba hakana bane mijin ki kamilin mutum ne da yasan kansa ga zati da kyau da cikkaken ilimi uwa uba arziki wanda ko wace mace yanzu take gurin samun mijin irin shi.
Haka ya tashi da farin jinin mata tun muna yara duk da koda yaushe fuskanshi shi a daure yake bai hana mata suce suna son shi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login