Showing 339001 words to 342000 words out of 419207 words

Chapter 114 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1395

bukatan taimako a duniya sun daukeni tankar yar su ta jini a cikin su.
Da taimakon su na fara zama mutum a duniya har na fara mayar da hankali ga karatuna both boko da arabiyan dana samu a yanzu.
Ta yaya zan manta da wa yan nan mutane a rayuwana kuwa sai dai abinda banda shi don sune yanzu abin taimakawa a gare ni don yaya ya tsare min komai daga bangaren yan uwana da nake tunane a baya gaskiya yanzu basu cikin matsala sosai yadda na zata zanzo in same kamar yadda na barsu a baya.
Saida nayi sallah na shiga gaida su mama a part din su har yanzu na hango kiyayyana a idanun mama uwar gidan baffana sai dai tana kokarin dane hakan a fili bata nunawa duk ta hakan sai data baiyana din.
Don cewa tayi min wasu mata sun iya shige shige a duniya sai kaga suna samun sa,a wurin malamai kamar kamun yuka.
Da farko ban san inda zancen nata ya dosa ba akaci gaba da hira ana dan dararaku a dakin ta kara fadin ai ita maimuna yanzu sune kano.
Wace ta kama miji har danshi a hannun ta mezai dame ku a rayuwa dama ance kano haka suke da malamai kamar yankar yuka ga aiki sai dai idan baka da kudi a hannun ka.
Shiru dakin yayi lokaci guda kamar babu kowa a cikin sa sai yartane tace mama wanan magana fa kuma babu dadin ji.
Tace gaskiya na fada safiya yanzu nawane ban kashewa a garin nan ku samu ko auren farko kuyi hakan bai yuyu ba.
Baga yar uwanku ba da uwarta tai mata tsaye kamar yadda itama ta tsayawa kanta rayuwan ta yanzu ya koma abin kwatance a cikin ku.
Wa yaki yau ace nasa ne a hakan yake jin dadi yadda fatima keji a yanzu ki duba wa yan nan yaran nata kosu kadai abin alfahari ne ga bawa ai.
Mama Lami ke nan dani dasu duk daya muke a gare ki kin san kuma ance duk wanda ya dogara ga Allah baya tabewa a duniyan nan.
Uwata dani tun farko ga Allah muka mika al,amarin mu abinda kike tunane ni a sani na mamu bata taba bani wani abu a duniyan nan da sunan mallakan mijina ba.
Tace Affa ke me kika ani Fatima ai wanan aikin sai anayi ana tushi bawai dole sai ta sanar dake komai ba da takeyi.
A,uzzubillahi mina shaitanin rajin nace kafin ince lala mama babu wanan rayuwan a zuciyar mu gaskiya.
Sa,ane dai daga ubangiji da rahama irin na Allah muka samu daga ubangijin mu tare da taimakon kawuna da kakata Amma.
Shiru dakin ya karayi a lokaci guda babu wanda ke furta wani abu ko ita mama lami taja bakinta tayi shiru don kwabarta da yarta tayi a fakaice lokacin.
Mikewa nayi na fita ina masu saida safe don ba lalai ne in dawo part din ba ranan don mama ta gama bani mamaki yau din.
Da mamakin ta na koma dakin Amma inda na samu har murja ta gyara shifida gadon Amma da kasa inda zasu kwanta gadon kuma ta barwa yara dani wai.
Nace a, a murja ku hau sama ku kwata ke da Fauziya sai mu mu kwanta a kasa.
Rufa min asiri yau kin san fadan da kawu yayi da yaya da hjy ne tunda safe kan yaran nan wai ita sam bata yarda azo dasu ba garin nan.
Fauziya na kalla nace Fauziya idan ki kara cin abinci ki hau gado tare da yaran nan ku kwanta dasu ni da murja a kasa sai mu kwanta ko murja ta hau wanan dogon kujeran idan zai mata zaifi.
Murja tace nan ma ai zai muna mu kwanta a raina nace dama nasan hjy ce zatace bata yarda azo da yaran nan ba don kawai ta kuntata min ga hakan.
Ranan bamuyi barci da wuri ba muna hira da Murja da Manjo har murja tayi barci ta barmu muna hiran yaushe rabo.
Inda na fahinci cewa har yanzu kakartawa zaman takura da hakuri takeyi da mutanen gidan namu.
Washe gari muka tashi dan gyare gyare mukayi kafin yaro yayi sallama da kulan abinci niki niki wai ummace ta bayar a kawo muna abin karyawa.
Manjo sai fada takeyi don me umma zatayi wanan wahalan ita da take fama da kanta ga kawu yayi iya nasa kokarin.
Wurin sakawa ai muna abin karyawa lafiyayye don girmamawa wanka nayi na fito na shirya cikin wasu kara redimed daga dubai ya sayo min su sai walkiya suke ko ina.
Kai Fatima wanan kayan sun sha jinina gaba daya ke ko wani shiga kikayi sai ya karbi jikin ki.
Nace ko tace wallahi ba karya kema kin sani ai basai na fada ba kin ko ga duk wa yan nan kayan yawanci a nan zan barsu ba zan tafi da ko dayan suba kila.
Da sauri tace ashe zamu samu nace niyata ke nan dama idan zan tafi in raba maku shi sai kizo ki zaba kafin kowa ya dauka.
Saidana shirya na shiga wurin su mama na gaida su da kwana daki daki can ma a dakin mama lami saida ta sake sake min magana na haibaici kafin in fito.
Gidan su Atika muka shiga muka gaida umma kafin mu fito ta hadamu da yaro zuwa gidan da Atika ke aure a wani unguwa.
Atika tayi murna ta rasa yadda zatiyi saita fashe da kuka lokaci daya nima kukan ne yazo min a lokacin muka hade kai muna kuka gwanin ban tausayi sau bayan mun dan lafane ta fara bani labarin halin da take ciki bata boye min komai ba har abinda umma bata taba sani ba.
Muna nan mijin nata ya shigo yana fadin yau baki mukayi ne tun a waje na hango mota a kofan mu.
Da ganin shi dan duniyane sosai irin yan karyan nan don gashi fes dashi zakace mutumin kirkine shi din.
Hjy Fatima ko yace yana zama yana kallon yadda muka zauna a tare da Atika a lokacin.
Dariya mukayi nace malam hafiz ke nan ashe ka iya canka daidai mun dame ku lafiya ko yace lafiya nan muk hiran dashi idan na fahinci shi mutum ne mai son nuna ilimin da yake dashi da yawan son nuna turanci a bakin shi.
Nace malam Hafiz aiki fa a ina kake aikine halan sai ya dan canza yanayin shi yace hjy kin san halin kasan nan tamu.
Ganin canjin yanayin nasa yasa na fahinci akwai matsala rashin jigo a rayuwan shi.
Nan dai muka dan taba hira dashi ya mike yana fadin barin dan fita in dawo anan zaku wuni ko nace muna nan da mutumiyar tawa sai dare yau manjo zata gan mu ai.
Saida ya fita ya kira Atika sun dan dade tare suna shawara kafin ta dawo dakin tayi dan tone tone ta fita da abu a dunkule cikin jikin ta.
Bayan ta dawo ne take fadin wai ni zaiwa wayau ya burge ku nace ina laifin sa har yana kokarin burge mutanen ki na fahinci Hafiz Atika.
Bawai yana maki haka bane da gangan umma tayi gaskiya da bata bari auren ki ya mutu da bawan Allah nan ba.
Duk mutumin dayasan ya mutanta maka bakon ka ai idan ya samu nan gaba zai maki alherin daya dace .
Muna nan ya dawo da ledoji yana kiranta daga waje ta mike ta fita ta dan jima kafin ta dawo dakin ya leko yana gaishe mu da zama zai fita na ba fauziya abinda na tanada masa in bashi.
Yarinyar tana kaimashi sai gashi a dakin ya cire hulan kanshi yana fifita dashi yana fadin hjy Fatima sai kuma ya kasa magana a lokacin ya dukar da kan shi kasa na dan lokaci.
Ya dago yana fadin na gode hjy nagode yana dan jujuya kudin dake hannun sa nace ka hada ta kardun ka idan zan tafi na wuce dashi .
Shiru yayi na dan lokaci kafin ya fara magana a cikin sanyin rai yana fadin Fatima na gode nagode Atika kinga Abinda kawarki ta bani yau,


ZAINAB IDRIS MAKAWA
17/11/2021, 07:16 - ??5惙5惙5?: Bamu bar gidan Atika ba sai dare muka koma gida mun dawo mun samu abincin da babbafa ya saka ai muna yana jiran mu a dakin manjo.
Mukace mun koshi ba zamuci ba munci abinci a gidan Atika sai yaran gidan, ana fita dashi yaran shi suka zauna sukaci .
A daidai lokacin Umma lami ta dawo daga unguwar da ta fita tun da magariba tana arba da yaran zaune suna cin abincin ta doka wani uban salati lokaci daya.
Hankalin kowa ya koma gareta suna mamakin ta nan ta fara fada dasu tana fadin abincin dana dafawa Fatima da yaran ta kuka zauna kuna ci shike nan.
Umma tace ba zasuci ba kada ya lalace ta fito muna dashi fada take wanda duk mai hankali zai fahinci akwai wani abu a kasa.
Jin sababin nata yayi yawa har muka gaji muka fito daga dakin manjo a lokacin.
Lami wanan fadan haka halan wani sheri kika karbo kika zubawa wanan yar marainiyar Allah da iyalin ta manjo ke tambayan umma Lami a hasale.
Ganin kowa yana kallon ta taci gaba da fadin wanan fada naki duk mai hankali yasan bana lafiya bane .
Gabana ne yayi wani irin mugun faduwa tsikan jikina ya tashi don sam wanan tunanen baizo min a raina ba da farko.
Tsohuwa wanan wani irin magana kikeyi haka kuma gaskiya na fada ina dai wanan abincin na yarnan ne.
Kuma tace akoshe suke yan uwanta su dauka suci kada ya lalace kinzo daga baya kina wanan fada anya lami ba wani sheri kikai niyar yiwa yarinyar nan ba kuwa Allah ya kamaki da hannun ki.
Ai dama bana abin kwarai a gidan nan sai a dauko sheri a sakawa mutum don kawai kiyayya.
Allah ya kyauta manjo tace tare da duban inda muke a tsaye cirko cirko tana fadin maji ma gani ita dai ramin karya kurarane dama sheri karene mai shi yake bi.
Har muka koma dakin mu jikina bai dawo daidai ba sai maganan manjo nake ji a kunnuwana lokacin da take tambayan umma lami kan abinda yasa take fada haka tana kumfan baki don kawai diyan ta sunci abincin data girka muna da rana.
Jikin kowa a cikin mu yayi sanyi a lokacin don haka muka nemi wuein kwanciyar mu muka kwanta saidai barci bai daukeni ba a lokacin sai zuwa dare sosai.
Don nayi iya tunanena banga laifin da nayiwa wa yan nan mutanen biyu ba a duniya watau umma da hjyn su yaya da suke nuna min kiyayya irin haka.
Yanzu da munci abincin wani abu ya samemu ko ya samu yaran mutane yaya zanyi da kakar su da mahaifin su nake nanatawa a raina.
Can barci ya dan figeni nake jin motsi sama sama a gidan tunda na bude idanuwana na kasa rufe su tun ana wanan motsin kadan kadan har abin yayi yawa sosai ina jiwo hayaniya.
Da kuka manjo ne ta mike tana fadin dama na san za a rina akwai abinda ke faruwa a gidan nan duk yadda akayi.
Nace ashe baki barci ba kina jin su manjo tace najisu ai kokarin tashi zaune takeyi tana fadin hakan.
Kofa ta nufa tana budewa zuwa waje inda na taso na mara mata baya muka fito tare bayan na saka hijabi a jikina.
Dan gidan umma lami ne dan matashi sanusi ke faman wulle wulle a kasa ciwon ciki ya turnike shi lokaci guda.
Salatin da manjo ta saka tana fadin dama nasan fadan nan Lami dazun ba a banza kikeyin shi ba.
Dama yar nan kika so ki kashe da yan uwanta da yaran ta ko me Baffa yace haba babba wanan wani magana ne haka kuma ?
Gatanan tsaye ka tambayeta ta baka amsa nan dai cikin fada fada take mayar mai da abinda ya faru.
Mutuwan tsaye babffa yayi a gurin tare da nazari a ranshi yace tabbas akwai kamshin gaskiya a maganan nan naki babba.
Ihun da Sanusi ya yanka ne lokaci guda yasa mukayi kanshi a gigice dukawa nayi ina kallon shi kafin in ce da sauri mama akwai manja a gidan nan a bani da sauri.
Da sauri mama ta wuce zuwa dauko manja zuwa lokacin har ya fara zubar da wani kumfa a bakin shi mai kauri.
Tana kawowa na bude bakin shi na dura mai manjan sosai a ciki kafin in ce madara fa akwai madaran ruwa a gidan nan a bani.
Akwashi yana nan cikin kayan shayin dana shigo dashi dazun yake cewa mama ta juya da sauri zuwa dakin shi.
Madaran na bashi sai kuma ga amai ya biyo baya nace Alhamdullahi yazo akaishi asibiti insha Allahu ba abinda zai same shi sai dai don Allah duk wanda yaci abincin nan a bashi manja da madara yasha.
Ruwa ruwa aka kwashe shi sai asibiti ranan umma tasha tsina da zagi wurin manjo da babffa .
Nikan ban bisu asibitin ba daki na koma mukayi zugun ni da murja kowa da abinda yake rayawa a zuciyar shi.
Can murja ta nisa tana fadin Fatima kina tare da kariyan Allah wallahi duk sanda wani sheri yake tunkaroki sai ubangiji ya kareki daga gare shi.
Yau da badon Allah ya tsare mu ba baza,ayi wanan tunanen ba sai ace kwanan mu ne ya kare a nan ai.
Murja kin san plain din wanan matar idan anyi magana sai tace unguwar da muka fitane dai mukaci wani mugun abin don ba za a taba dora mata laifin ba.
Kiran sallah ne ya tayar damu daga zaman da mukayi son muna zaune mun kasa komawa mu kwanta barci.
Bayan mun idar muka ja kofa muka rufe barci sosai mukayi sai hayaniyar mutane dake shigowa ne ya tayar damu daga barcin.
Ban bude kofan dakin manjo ba don kada yarana su fita tsakar gida muna dakin don ban bar kowa a cikin mu ya fito waje ba saboda tsaro duk da nasan Allah yana tare damu.
Bugun kofan da akeyi tare da sallamane yasa na mike na bude kofan umman Atikace take buga kofan .
Ina budewa tana fadin Fatima barka da arziki ashe wanan matar tana nan a bakan ta akanki har yanzu.
Umma na rasa mena tare wa umma take bina da wanan nufin haka ko yaushe idan nazo garin nan.
Baki mata komai ba Fatima illa hassada da kyashine irin na dan adam idan bashi ba ya kamata yanzu ace matar nan ta saduda da wanan abun a kanki.
Muna tsaka da hira wayana yayi kara na dauka ina dubawa wanan matar daine ta sudan take kirana inda take kara tambayana address din dana basu na kara maimaita mata shi yadda ya dace.
Murja na dan kalla ina fadin ina ganin yau zamu koma kano don muna da baki a gida zuwa gobe ko jibi.
Da sauri murja tace nima tun dazun naso in sheda maki haka mu koma gida kawai zai fi don wanan abin ya firgitani wallahi.
Umma dake zaune tana jin mu tayi saurin cewa a, a kada kuyi haka don Baffan ki bazai ji dadi ba a ransa.
Ku bari zuwa gobe idan Allah ya kaimu sai kuyi sammako ku tafi abin ku shike nan nace ba tare da nuna wani damuwa to umma.
A gidan ta mukai wanka muka shirya don ban yarda yarana su matsa kusa dani ba a nan Atika ta same mu gidan nasu ranan dai wuni mukayi muna magana kan abu daya a gidan.
Sai dare sosai muka dawo dakin manjo don mu kwanta tare da shirya kayan mu ba wanda yasan cewa zamu koma a washe gari sai umman Atika da Atika din suka sani.
Washe gari tunda nayi sallah na fito dakin babffa na nufa nayi sallama daga bayana ya amsa min yana dawowa daga masalaci.
Har kasa nakai ina mashi ina kwana yana amsa min yanayin shi kawai ya nuna yana cikin damuwa sosai a lokacin.
Na dan kara kwantar da murya ina fadin baffa yau muke son mu koma din an bugo min waya zamuyi baki daga kasan waje a yau din nan ko gobe .
Yace Fatima kada ince wanan abinda ya farune ya daga maki hankali kike son komawa kano yau.
Da sauri nace a, a baffa wallahi dalilin ke nan na fadama idan bado baki ba ai kwanakin daya bani zancika a nan.
Wuri kawo ya samu ya dan tsuguna yana fadin Fatima bansan irin kalamin da zanyi maki amfani dashi ba wurin baki hakkurin abinda ya faru.
Da sauri nace baffa akan me zaka bani hakkuri akan laifin da bakai ka aikata min shi ba ya nisa tare da fadin ba zanso ki rike wanan

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login