Showing 189001 words to 192000 words out of 419207 words

Chapter 64 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1516

masu rufe tsiraici yace wana ke nan ki sani ba a fita ba tare da izinina ba ko nan da kofan gidane.
Ki tabbatar da bakin da bn aminta dasu ba kada in gansu a gidan nan don ban zama mutumin banza a gari.
Ban son barnan abinci zaki iya dafa duk abinda zuciyar ki ke so a gidan nan muci haka kuma idan kina da ra,ayin wani abu zaki iya fada min kafin lokacin fitana ban son sai abu ya kare ace za a fada min.
Ban yarda da yada sirin gidana a gurin wani na wajeba ko waye sirin mu sirin mune iyamu duk ranan da naji wani zance gidan nan a waje ki kuka da kanki don banda dadi idan an taka min doka.
Idan kinbi tsarina mu zauna lafiya dake a gidan nan zaki iya zuwa ki kwata don dare yayi yanzu Allah ya bamu alheri ya mike yana kokarin kashe kayan wutan dake falon.

Gidan ikilima yan uwa da abokan arziki sun watse kamar yadda al,adan buki ya tanada gida ya rage saura ita da kanwar ta.
Ana sallamay isha,i abokan nan shi suka rako shi gidan sun samay su a falo suna hira don ba wani wayewa sukayi dashi ba sosai.
Daki suka koma da sukaji hayaniyar su tafe shida kanshi ya shiga ya kira su don suyi sallama da abokan shi dake son ganin ta.
Ba laifi don ta dauki dan haske kawu sun dan masu nasiha da shawarwari yadda ya dace da zasu tafi suka aje mata alherin da sukazo mata dashi.
Mikewa sadiya tayi tace itama zata tafi yace su sauke ta a gidan su ya dan jima bai shigo ba sai can ya shigo ya rufe gidan.
Ledadojin daya shigo dasu ya mika mata fuskanshi a daure tamau don shi mutumne da baida fara,a ko kadan baida yawan surutu.
Yana mika mata ya fice dakin tun lokacin bata kara ganin sa ba sai safe da zai tafi masalaci ya tayar da ita ta hanyar bubuga mata kofa.
Ya wuce bai shiga gidan ba sai dai har ya dawo baiga alaman ta tashi tayi sallah ba balle ta fito gyara gidan .
Har karfe takwas saura ya nufi dakin ya buga ta taso da kyar tana ya mutsa fuska ta bude kofan shi ta gani tsaye ciki hade fuska yace ke kinyi sallah kuwa ?
Bansan gari ya waye haka ba ta bashi amsa cikin rashin damuwa da abinda ta fada yace a dan hasale ke wata irin mara hankali ne ?
Sallah asuba kice baki san lokacin yinsa yayi ba bari kiji ban daukan wanan shashan a gidan nan ya zama maki na karshe duk lokacin sallah yayi bakiyi sa a lokaci ba sai na saba maki.
Ki shige kije kiyi sallah tun kan na saba maki ya juya yana tunane a ranshi lalai mahaifinsu ya fadi gaskiya suna da aiki sosai a gare su gamay da amaren nasu.
Bai yarda ya sake mata fuska ba ko kadan hakan yasa ta shiga tsoron shi don umurni yake bata gashi gidan shiru ita data saba da yawan surutu a part din su suna hayaniya da uwarsu da yan uwanta ko yaushe.
Wanan zaman shiru din ya fara damuwan ta da zaran ya shigo zata fito daga dakinta tazo ta zauna falon saidai suyi zama kaman kuramay ita dashi bai mata maganan komai har sai ta gaji tayi magana ya basar da ita ba amsa don haka halin shi yake shi a rayuwan shi.

Gida;rakiya da habbib an gama komai kamar yadda ya dace gidan ya koma shiru dama shi bawai yasan rakiya bane don da dare suka taba haduwa da daddy ya matsa masu sai sunje sun gana din.
Ko yanzu a gajiye ya shigo gidan ga haushin da takaicin abubuwan dake faruwa a tsakanin iyayyen nasu a lokacin tare da tunanen wai yau shine da aje macen da baiso a gidan shi.
Ya shigo ba tare da sallama ba don gidan ba kowa ita kadaice a zaune a falo tana kallo cike da tsoro don babu alaman motsin kowa a gidan.
Ganin shi tayi murtun da fuska haka ta daure tare da dan mikewa tsaye tana fadin sannu da zuwa yaya tana dan dariyan yake .
A dakile ya kalle ta sai dai bai taba tsamanin haka rakiyan take ba a fili yadda ya ganta yanzu tasha kwalliya kyawon ta na diya mace ya fito sosai a fili.
Duk da haka yayi kokarin hade mamakin shi wurin amsa mata ciki ciki ya nufi hanyar daki shi ta bishi da dan kallo tana murmushi kasa kasa don tasan abinda suka shirya da mahaifiyar ta.
Ya jima a dakin shi tana zaune bata shiga daga ciki ba sai can gashi ya fito da alama wanka yayi duk dadewan da yayi a dakin.
Yana saye da three quater wanda da yar riga armless yayi mamakin ganin ta a inda ya barta zaune har lokacin.
Yana fitowa ta sake fadin barka da fitowa yaya ya gajiyan taro wanan karon da mamaki ya amsa mata rashin zuciya irin nata.
Zama sukayi gaba daya falon ba wanda yai magana a cikin su sai habbib da yazaro wayan shi yana kiran dan uwan shi yaji ko sun sauka lafiya ?
Sai dai layin bai shiga ba a lokacin haka yasa shi jan guntun tsuki yana wani layin ya kira saidai wanan karon mace ce yakira da wayan nasa.
A yadda take jin suna magana cikin tausassa murya ta fahinci akwai soyayya duk da da harshen turanci suke magana.
Rakiya dake zaune duk da taji haushin cin fuskan dayai mata din bata yarda ta nuna hakan ba gare shi.
Tasan dama don ya musguna matane yake waya da wata mace a gabanta don taji haushi kuma gurin shi ya cika taji haushin saidai ta yi kokarin shanyewa.
Sai da ta bari ya gama ya dauki remote yana chanza chanel ta kalle shi ta mike tana fadin sai da safe yaya .
Ya kalle ta cike da gadara yace ke a gidan ku ba a koya maki tarbiyan ba miji ko ruwa bane ?
Ta dan murmusa tana gyara gyalen ta kamar bata damu ba tace kayi hakkuri yaya na dauka ai ba zaka sha ruwa yanzu da dare bane ?.
Cikin takama yace kinga inba zaki debo min ba kada ki cikani da surutun tsiya don Allah doluwa kawai dakikiya .
Allah ya baka hakkuri tace ta nufi gurin da fridge din yake ta dauko goran ruwan da yayi raba har ya gaji don sanyi tare cup a saman fridge din ta kawo mashi.
Kallon cup din yayi yace ashe ke sokuwace kasheni kike so yi tun yanzu ba zaki dauraye kofin kafin ki bani ba don cuta zaki bani shi a haka da datti ?
Dauka tayi ta nufi kitchen ta dauraye saida ya tsane ta fito ta kawo mashi ya dauka yana wani juya cup din a yatsune ya tsiyaya dan ruwa kadan ya kurba ya aje da gani dama ba shan ruwan zaiyi ba.
Dauka tayi zata mayar bayan ya gama habbib ya kalleta cikin kallon tsana yace wama sunan ki kamar wata tsohuwa da suna mutanen da can.
Tace sunan kakan mu aka saka min amaryan Amma ance bata taba haihuwa ba har ta rasu ban tabaye ki jin tarihi ba.
Idan ina son ji ba kece zaki fada min ba don Amma na da ranta a gurin ta zan iya jin komai ya fada yana mata kallon mugunta.
Kina son zama dani a gidan nan ya fada cikin tsare ta da idanuwan shi masu bata tsoro ta bude baki da kyat tace.
Yaya kaman yaya ina son zama dakai bayan kuma kaga gani gidan a yanzu tunda , , ,
Ke ki bani amsa tambayan ki nayi kin amince da wanan hadin da akai muna na aurena dake ?
Ta danyi murmushi kafin tace mai zai hana yaya tunda kana dan uwana kuma musulmi kuma iyayyen mu sukai wanan hadin don cikan wani burin su .
Tunda ba mu kadai akaiwa wanan hadin ba kowa kuma ya hakkura sai mune zamu nuna masu gazawan su.
Ya kura mata ido yana kallon yadda take fitar da lafuza a bakinta karamar yarinya da ita ta iya kinibibi yace a ranshi.
Amma a fili sai data gama magana yace good yana kallon ta tare da kasheta da ido saida ta dukar da kanta kasa.
To tunda hakane ina son ki sani kin shigo gidan da sai kinyi hakkuri da zaki zauna a gidan nan tare dani don kin taro wa kanki kunci da bakin ciki a rayuwan ki yarinya habbib ba mijin mace bakauya irin ki bane .
Yana fadin haka ya mike ta bishi da kallon mamaki ta juya ta mayar da ruwan ta shige dakin ta take ta kira uwarta ta labarta mata abinda ya faru a tsakanin su.
Uwar tayi dariya tace haka yace tace wallahi mama tace ki barshi baisan shi karamin dan iska bane sai ya shigo hannu zai gane kuren sa.
Shiko daki ya koma yana cika yana batsewa har ya kwanta yana tunanen irin ukuban da zai gana mata a gidan.

Aisha da Aliyu basu samu wani matsala sosai ba don da ya dawo gida dakinta ya nufa ya samayta a kwance ganin tana barci ya jawo mata kofan bayan ya gyara mata rufa ya koma dakin shi.
Washe gari koda suka tashi ta samu har ya dora masu girki abinda zasu karya dashi a gidan da mamaki take kallon shi tare da rabewa kofan falon tana fadin yaya ina kwana ya amsa a sake yana fadin yan mata kin tashi.
Ya dare ya gajiyan buki na shigo jiya na samu kinyi barci harda mafalki kikeyi kina harbin iska.
Dan kunya taji ta noke kai cikin hijjabinta tace a shagwabe yaya shine ka fara aiki baka tashe ni ba yace ke rufa min asiri kada su gwaggo su zo suganki da safen nan kina aiki su zarge ni don haka su zaman su yazo da rashin akasi.

ZAINAB IDRiS MAKAWA
16/11/2021, 23:14 - ??5惙5惙5?: JUMMA,AT MUBARAK YA UMMAH MUSLIMIN

Dakin yana da dan girma sosai sanyin garin kawai ya wadatar da mutum balle na dakin kuma haka yasa ni takurewa a wuri daya.
Tunawa nayi da sallah nayi zubur na mike da lalube na gano bandakin kallon tsaruwan shi na dan tsayayi kafin in karanbanin taba wani wuri da nike zaton nan ne makunnin ruwan sai ga ruwa ya zubu daga dan wayan dake makale a wurin.
Wanka na fara tare da dorawa da alwala na fito ban san satin gabas ba dan tunane na tsayayi sai na tuno na fara ina cikin sallah merry ta shigo dakin ganin yanayin da nake yasa ta juyawa ta koma zuciyar ta cike da tunanen irin akidar mu.
Sai lokacin na bude kayan troller dina na dauko wani bakin dogon riga mai shap na saka tare da hijjab dina fari na tayar da sallah.
Na dade zaune a gutin ba zance banjin barci ba don nayi a jirgi haka kuma bai hanani jin wani barcin ba.
Mikewa nayi zuwa gadon na kwanta banjima ba barci ya daukeni kuma na jima ina barci ban falkaba sai sha dayan rana jin motsin mutum kusa dani yasani bude idanuwana.
Merry ne zaune a bakin gadon tana sake murmushi a fuskanta haka yasa na yunkura na tashi zaune ina gaida ita.
Tace kinsha barci tashi kici abinci rana yayi a hankali na yunkura ina kokarin saukowa saman gadon.
Kusan a tare muka fita falon tun fitowan mu na hangoshi zaune yana cin abincin shi hankali kwance.
Yana saye da yar rigan da kamar yana dasu da yawane don kala kala yakan saka wani lokaci.
Yauma sin saye yake da bakarta a jikin shi sai wando milk color a kasan shi ya zauna yana cin abinci a hankali.
Saida na karaso inda yake na kai rusunne nace yaya ina kwana ya amsa min ba tare daya juyo inda nake ba yaci gaba da cin abincin shi.
Wuri ta nuna min in zauna itama ta jawo kujera ta zauna tanacewa yarta oya come and pray before eat.
Sai yarinyar dake wurin mahaifin nata tana mashi gwalanci umm kawai yake amsa mata dashi da alaman ko cikin iyalin nasa haka yake bai da sakewa.
Uwar tace oya close your eyes sai yarinyar ta rufe idanuwan ta uwar nata gwalanci adduan su yarinyar nacewa Ameen kamar yadda uwar tace ta amsa.
Sun gama ina zaune ina kallon su tace fatema eat now dan murmushi nayi na kai hannuna ina diban abincin a hankali sai dai na kasacin don kawai abincin ban ma taba ganin irin shi ba.
Da dai ta matsa min dole na dan kai abakina ina taunawa a hankali kamar ansani ci dole.
Shi ya fara mikewa har ya dan taka ya juyo yana fadi da hausa idan kin hda takardun ki kiba merry a san inda za,a saki.
Ya juya wurin merry yana mata bayani ina dan tsuntan abinda suke fadi saboda turancin su jin shi nakeyi kamar na turawan gaskiya dan kwaraiwan da sukayi dashi.
Ina gamawa na mike don merry tana waya a lokacin yar tasu ta kura min ido hannu na mika mata alaman tazo sai ta noke jikin uwarta.
Juyawa nayi na fara tafiya ta katse wayan tana fadin Ina zanje nace zuwa zanyi in dauko takardun nawa .
Ki dawo ki zauna wanan barcin gajiyan yayi yawa haka nayi dan murmushi na juya zuwa kujerun falon na zauna saman daya.
Ta taso itama zuwa wurin kujerun tana fadin ina that your grandma da step mother nace sunce a gaida ke.
Tace ki sake jikin ki yayan ki ya fada min baki so zuwa ba shiyasa na ganki haka ki kwantar da hankalin ki you should feel free here nan ba mai takurawa wani ko kadan irin can.
Kowa yana da incin kansa a nan zaki iya yin duk abinda ranki ke so kiyi babu takura zaki san duniya idon ki zai bude sosai.
Dan murmushin yake na karayi don jin abinda take fadi din haka hiran namu dai sama sama mukayi shi don ita ba hausa take jiba ni kuma ba wani turanci sosai nake ji din ba.
Abincin rana ba wani abinci bane don da safe sai dare sukafi ba abinci muhinmanci koda ta dire min snack da tarkacen kwalama a gabana .
Kallon abincin nayi ina bata rai tare da kai bayaba a saman makarin kujeran da nake zaune.
Curious tace may ke damun ki gajiya ko yunwa tana kallona tace you can cook any delicious you want.
Da mamaki na dago kai ina kallon ta ta daga min gira ta daga min tana fadin kin san ku yan nigeria kun saba da cin abinci sosai.
Ban san lokacin da murmushi ya subuce mun ba a fuskana don ji abinda ta fadi din.
Tace yes haka kuke cin abinci matan ku na zama manya da sun fara shekaru mana may kuke kiran sunan wanan abincin da step mum ta ke yawa muna ?
Na gaji da zama na mike zuwa ciki sallah nayi dan da lokaci nake amfani don ba kiran sallah ba komai a garin .
Gashi tun safiyan zuwan mu ban sake saka shi a idona ba sai da merry ke waya nake jin wai ashe yayi tafiyane bai garin.
Duk zaman garin babu dadi duk son sanin wanan kasan da nakeyi yanzu da nake cikin shi sai naji duk garin ya isheni shiru ba abokin hira ba wani motsa jiki ko kadan.
Yau tun safe dana tashi naji ina son zagaya gidan har girkin abinda zanci nake son yi a ranan.
Bayan na gama shiryawa na fito a hankali nake dan takawa ina bin ko ina na gidan da kallo sai dai inda nagani a rufe ban gigin shiga gurin.
Hankalina ya dauku ga kallon wasu gumakan dake zubo ruwa a tsakiyan gidan jin muryoyin su ya dawo da hankalina daga kallon da nakeyi.
Merry ce ke magana kamar a fada yana tafiya tana fadin don may zaka kaita wanan school din na fadama wanda na zaba mata yafi dacewa da ita.
Ka tuna yarinyar tana da kamar baiwa a tare da ita ya kamata ace baka damu da akida ba ko wani abu tunda karatu ne ya kawota nan dama ai wanan rashin adalci ne ta karasa fadi.
Why merry why zance ga abinda za ayi kina kawo naki ra,ayin akai yarinyar nan fa yar uwatace ina da right din zaba mata abinda nake so daidai da ita.
Tace ok yanzu na fahince ka ra,ayin ka kake so kai bana wani ba ka nuna min cewa yar uwankace kai kadai.
Merry stay away from my family issue nina san mutanen mu nasan halin su fiye da sanin ki.
Tace a fusace Am

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login