Showing 360001 words to 363000 words out of 419207 words

Chapter 121 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1496

ga baki daya.
Haka dai uwar tayi ta zugata da mugayen shawara har taji wani karfin gwiwa yazo mata lokaci guda .
Suna gama waya da uwar ta mike cikin karfin gwiwa ta nufi hanyar fita daga part din ta suka hade da yarinyar data turo din.
Da sauri yarinyar ke fadin wallahi anty ins ganin maigidan ne don naga yan aikin gida suna ta shiga gaidashi.

Babu abinda nakeyi sai juyi nake a gado tsakiyan yarana dake kwance suna ta barcin su hankali kwance.
Kallon fauziya dake kasa kwance nayi don gadon bai isar mu ta kwanta a kasa ita.
Itama sai barcin ta takeyi hankalu kwance abinta gyara kwanciya nayi inaci gaba da tunane a raina.
Yanzu yaya yana can yana morewa rayuwan shi da amarya ni gani nan da yara ina jinyar jikina.
Wasu hawaye ne suka zo min lokaci guda masu zafi sai dan jaririna ya motsa ina jin yana kuka na kasa tashi in kamashi a lokacin .
Zubur naga Fauziya ta mike daga batcin da takeyi tana fadin anty yaro yana kuka bakiji bane.
A hankali nace ina jin sa Fauziya tashi ne ban iyawa kawai da sauri ta mike takai gareshi lokaci guda ta dauko shi tana dan jijigawa.
Yaron yaki shiru ta nufoni dashi tana mika min dole na gyara na karbe shi na fara bashi nono yana ja.
Zama Fauziya tayi a bakin gadon tana fadin naso in dauko littafina a daki sai dai ban son komawa dakin don lokacin Anty Nafisa batayi barci ba.
Wanan ai na rasa me take nufi daku haka a gidan nan na bata amsa tace dazun naji tana waya da maman su harda kukanta tana fadin mama ya sakeki fa ?
Fauziya karde ince kawu ne ya saki hjyn su don dama ya fadi haka idan ta matsa da zancen auren nan .
Ke nan hakan ya tabbata ke nan ko dama ai sheri karene maishi yake bi akace idan tayi don ni tun yanzu ta fara girban abinta ai.
Saidai duk abinda ya faru zamuji ne muna zaune ai maganan duniya baya boyuwa yanzu.
Mun dauki lokaci muna hira sosai da Fauziya yarinya mai wayau tana kwantar min da hankali a matsayina na yar uwanta.
Washe garine da safe bayan yara sun tafi makaranta mun karaya na koma dakina don ban son yawan hayani ga Nafisa ta sake volume din tv dake aiki ya karade falon da kara lokacin.
Nayi barci na tashi sai ga kiran yaya a wayata banyi saurin daga wayan ba har ya katse ba a jima ba saiga wani kiran ya kara shigowa shine kuma again.
Na dauka cikin basarwa ina kokarin nuna mashi ba komai a bangarena nace ina kwana yaya don nasan safiyace can a lokacin.
A daidai lokacin da Samira ke shigowa ke nan daga part din ta taji yana fadin Zahra ya kuka tashi ya yaran.
Ja tayi ta tsaya tana sauraren shi har lokaci bai dago kai ya kalle ta kamar baisan mutum yana gurin ba a lokacin.
Har muka gama waya tana tsaye a kanshi sai zafi takeji a zuciyar ta na yarda taga yana hira dani a cikin dadin rai duk da a waya muke maganan.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
17/11/2021, 07:20 - ??5惙5惙5?: Yana gama waya dani ya dago kai a hankali yana duban wanda ke tsaye a kanshi lokaci ganin Samira da take tsayen cikin yanayin damuwa tana sauraren shi ta, sauke ajiyan zuciya tana fadin ashe ka iso garin bamu da labari.
Ke haka aka koya maki a gidan ku idan zaki shiga wuri kada kiyi sallama ko gaida mutane ya fadi yana kallon ta ido cikin ido na dan lokaci.
Kafin ya mike da zumar barin falon don hankalin shi yana gun nahaifin su tun daren jiya da yasamu labarin abinda ke faruwa tsakanin shi da mahaifiyar su wanda baiji dadin hakan ba.
Don yanzu abin kunyane a garesu ace da girmasa iyayyen su zasu kashe auren dake tsakanin su shekara da shekaru suna tare ana hakkuri da juna.
Balle yanzu data dalilin shi duk yake ganin wanan abin ya faru haka a tsakanin su don hjy ta kasa yiwa mahaifin shi biyaya kamar yadda akeson ko wace mace ta kasance da yiwa mijin ta biyaya koda ya kasance itace da gaskiya ga magana.
Dolene na miji ya kasance shine mai juya gidan sa da iyalin sa ba wai mace daya aje tace sai abinda ranta ke so dole za,ayi ba.
Ya rasa mai yasa hakan yake kasancewa a tsakanin iyayyen nasu ko wani lokaci irin hakan baka taba jin fitina tsakanin shi da hjy maryam ko maman twin's irin haka mai karfi saidai a tsakanin iyayyen nasu biyu kawai akeda wanan matsalan a gidan.
Ko dai sunayi dashi ba mai karfi irin hakan da yake yawan faruwa a tsakanin mahaifan nasu ba .
Dear bansan ka shigo ba sai yanzu shine abin ya bani mamaki har na manta da ban maka sallama ba ashe tana magana tana wani kashe mai idanu irin na goggagun mata yan bariki.
Zai bude baki ke nan yayi magana sukaji sallaman hjy daga kofa wace itama sai lokacin ta san da isowan shi garin ashe itama ?
Wani irin bacin rai ya saukama Samira a rai lokaci guda tana fadin me kuma ya kawo wanan matar nan yanzu a daidai lokacin da zan fara dana tarkona gunshi ?
Cikin kula da ladabi yake fadin mama yanzu nake shirin zuwa inda kike ai don jiya da dare Habbib ya kirani yana fada min matsalan da kuka samu da daddy.
Da sauri hjy tace amma shi habbib din ya kasa kirana muyi maganan sai kuma yake iya fadawa wani ko idan ka fito ina jiran ka a waje tace tana juyawa.
No mama ki zauna muyi magana wanan ai tasan nan din ba part din ta bane so zata iya fita ta bamu wuri mu gama.
A take Samira ta kwabe fuska tana mashi kallon mamaki tare da fadin zaka zo hannu sai ka rena kanka a wurina idan nice.
Ta juya da karfi ta bar falon alaman bata so hakan da yai mata a gaban hjyn ba ai wanan sallon har hjyn taga wallentane a gidan.
Tana fadi a ranta kaida kanka zaka sameni har dakina mu zuba ni dakai sai lokacin take jin bakin cikin rashin jan ajin da batayiwa kanta ba don ko wace amarya ai angone mai binta har dakin ta.
Samira na fita hjyn ta sauke ajiyan zuciyan tana kallon dan nata tare da fadin zanso kabi wanan yarinyar a sannu don Allah.
Baiyi magana ba sai cewa yayi mama me yakawo haka har daddy ya rufe maki kofa da girman ki aka tozarta ki a garin nan haka ?
Kaima ka sani ai zancen wanan auren naka danayi tsaye akayi shine mafarin zancen da sauri ya dago kai yana fadin aurena kuma mama garin ya har haka ya faru kuma ?
Dama ai ya fadi idan har na matsa aikai wanan auren in san da sanin na bar nawa dakin ke nan sai dai idan ka manta hakan daya fada a baya.
Mama kin san da wanan maganan kika yarda har akai wannan auren da yarinyar nan ?
Kin kwammace ki bar dakin ki saboda ki farauta ran su ko ki batawa wasu rai kawai ?
Wanan wani zance kakeyi haka idan badon kana auren yarinyar nan ba har Alh ya isa yace kada ka auri yar sabuwa a gidan nan.
Mama ya isa har ya wuce duk abinda kaji daddy yai magana a kasan sa wanan abin abin dubawane ga mutum.
Ba wai don ina auren Zahra daddy zaice kada na auri wanan yarinyar ba sai dai don abinda ya hango a auren.
Da zaice don ina auren zahra kada in kara matane ai da yace in rabu da merry don bata dace dani da addini na ba .
Nafika sanin halin mahaifin ku babawo banda wanan abin baida wani abinda yake da hujja dashi kan auren nan.
Tunda sun riga da sun gama dashi ko baida tacewa kan maimuna da diyan ta yanzu ga kowa.
Har da maimunan bata kasan nan tana da laifi kan wanan maganan naku ke nan don Allah mama ki daina wasu abubuwa yanzu don girma dada shigan ki yakeyi a kullun .
Bamu jin dadin irin wanan abinda ke faruwa a tsakanin ku da daddy ko da yaushe.
Zanje wurin daddy mu zauna dashi don girman Allah mama kibi wanan maganan a sannu a samu a sasanta wanan maganan hakana din ba zamu so har mutane sukai ga fahintar hanlin nan da kuke ciki ba keda shi.
Na dade da fahintar laifina kuke gani kan matsalan dake faruwa atsakanina da Alh a yanzu.
Shiyasa banjin zafi idan wani yaji zafina kan haka tunda ance ita mace ba zata kwaci yancin ta ba don tana mace.
Mama kiyi hakkuri ba hakan nake nufi ba nidai rokona shine ki don Allah ki kwanta kibi daddy a samu a sasantaku ki koma dakin ki ya janye sakin daya furta a tsakanin ku.
Don kinga ita kanta maman twins da suka samu matsala kan gidan da iyayyen ta suka sai mata zata zauna a ciki yace bai yarda ba.
Da sauri tace gida fa kace aka sayawa maimuna koka saya mata dai.
Da sauri yace subbahanallahi mama ko banson albarka ai zan so fita kunyan jama,a ban sai maki gida ba zanje sayawa uwar matana saboda neman me zanyi hakan mama ?
Na sanan maka din komai zaka iya kan wanan shu,umar yarinyar a yanzu da take ganin ta daure ka gaba daya.
Murmushi yayi yana girgiza kanshi a hankali yana fadin haka dai kike gani mama amma ni ban yarda mace ta shige min gaba ba ko kadan.
Ban dai yarda in tauye hakkin mutum da yake a kaina matukar ina tare da mace bana tauyeta ko shiga hakkin ta.
Hjy tace yanzu yaya zancen gidan ita maimuna ake ciki Alhn ya yarda da zancen ne ko yaya ?
Bai yarda ba ita kuma ta kafe akan ba zata yarda ta dawo wanan gidan ba kuma suma iyeyen nata suka biye mata.
Shine yar nata ta kirani tana fada min abinda ke faruwa a tsakanin su wallahi mama kira daya nayi masu na basu hakkuri suka amince min da hakan.
Yanzu babu zancen gidan ke nan ko yace gida na nan a matsayin nata za,a zuba mata yan haya a bangare daya don su dinga kula mata da gidan.
Wani irin bakin ciki da hassada ne a lokaci daya ya rufewa hjy zuciya tana kara jin tsanan mamu har kasan ranta sai anyanawa take a ranta idan ba tayi da gaske ba wanan matar zata bata mamaki nan gaba.
Muryan dantane ke fadin don haka mama kamar yadda taga darajana tabi abinda na roketa kema ina rokon ki da duk abinda daddy zai fada kiyi hakkuri dashi a zauna lafiya .
Bata samu furta mai komai sai hakkuri yake bata cikin kwantar da hankali da taushin murya yadda zata samu fahintar shi.

Zama nayi yau na dauki kwalliya mai daukan hankali don yau ina son kaiwa yan uwan mamu ziyara tunda na haihu ban fita daga gidan ba sai yau duk dako yaya bai hanani fita inda nakeson zuwa.
Nafisa na zaune muka fito falon tun ina saman steps take bina da wani irin kallo har na sauko kasan inda suke zaune.
Da sauri fauziya dake fitowa daga dakin su ta zo ta karbe Abbati a hannuna tana fadin wai anty yaron nan fa girma yake karawa a kullun.
Tana zama a gefena da yaron a hannun ta take fadin hakan lokacin duban yaron Nafisa tayi take fadin na rasa wa yaran nan ke kwasowa da kyau haka kamar diyan larabawa dasu.
Kallonta nayi ina fadin Nafisa ke nan gashi kin fada dole suyi kama da su tunda suna da jinin su a gauraye dasu.
A daidai lokacin ne maria ta fito da sauran a cikin shirin su tsab suma ta bisu da kallo tana fadin wallahi dole yaya yaji dake har ransa ko don wa yan nan yaran Fatima.
Yara haka sai daukan ido a duk inda suke shiyasa nake fadawa shiyasa nake fadawa hjy ta bar yaya da iyalin su a kullun ko wani ahali ba a son rasu sukan rabu ba indan kaddara ta gitta masu.
Yanzu gashi ke baku rabu da yaya a yadda take so ba yanzu gashi batayi nasaran rabaku din ba ita da shekarun ta daddy ya hasale mata auren shi a kanta.
Na dago kai ina fadin Nafisa kin san abinda kike fadi kuwa yaushe wanan magansn ya faru kike furta hakan yanzu.
Wallahi Fatima anty salma ta dade tana min nasiha kan mu bar biyewa halin mama don shi kanshi yayan mu ba zaiji dadin halin da mama take sa muna nuna maku ba tare da laifin komai a garemu ba.
Ita dai anty salma ai ta huta da bata tsaya bin halin mama yanzu kinko ga ta zauna a dakinta lafiya ba wani tsangwama a yanzu.
Ga yaya ya ttaimakawa rayuwanta yanzu idan nayi magana ko ina son yayi min wani abin sai yace dani inyi aure kamar yadda yan uwana sukayi.
Fatima yanzu ta ina zan fara neman wani mijin Manir ne mun bata dashi kin sani tun kuna can ya dawo mu shirya mama tace bata yarda ba don ba zata bari taji kunyan mutane ba tunda har ya iya bata min suna a gaban kowa.
Amma har idan kina son shi har yanzu Nafisa mai zai hana ki fadawa yayan ki don nasan yaya zai fahince ki idan kin fahintar dashi gaskiyar maganan.
Shine kawai zai iya shawo kan wanan maganan har kowa ya yarda da shawaran shi in Allah ya yarda don yaso ace an hada auren ki dana Murja a lokaci guda.
Tun wanan dan hiran da mukayi da Nafisa dana lura abin duniyane ranan ya dameta tana neman abokin sha??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????wara har ta dan sake layin hjyn su garebi.
Munje gida anty don gaida ita tunda ta dawo daga kasan su bamu samu zuwa ba sai itace ma tazo inda nake dana haihu ta duba jikina.
Ina tambayanta yaushe su mamu zasu koma Nigeria ne take fadin suna son sai sunyi aikin hajjin banan nan a tare da ita zasu mayar da ita gida.
Nafisa kan sai mamakin irin arzikin su takeyi ga gidan babba ko ina yan aiki ne birjit a gidan kamar suna zaune a kasan su .
Ni kaina lokacin dana fara ganin su haka nayi mamakin abinda yasa har ta bude saloon ake mata aiki.
Take ce min ai ba a son mace ta zauna ba dan inda kudi yake shigo mata ko yayane ya kamata ace mutum yana da dan sana,an rufin asirin shi don ba komai ne zaka roki namiji ba ka samu kai tsaye.
Yini mukayi sosai a gidan mun sake jiki don irin yadda matar gidan take jan mu a jiki gaba dayan mu har Nafisa.
Da yamma muka dawo gida bayan mun dan kebe da anty ta van sakon da dama nazo karba wanda kakata ta bayar a kawo min ta hannun su.
Baya nayi wanka na kwanta ne sai kuma tunane ya dameni don yau kusan kwana biyu ke nan banji kira daga yaya ba.
A take zuciya mai nashe nashe ta nasa min cewa ina zai kiramu yana can yana cin amarci da amaryan shi shike nan ya gama da mu nan ke nan .
Naji wani irin kishi ya rufe min zuciyana kamar yadda ko wace mace take jin wanan yayin da mijin ta yai aure.
Da kyat na samu na yaki zuciyana kan irin yadda nakeji din a raina na samu har barci ya dauke ni hakana.
Haka yasa washe gari na tashi da wani itin bakin rai a zuciyana kin ma fitowa nayi daga dakin ga baki daya ina kwance inata faman tunane a raina.
Ina kwance a hakana wayana ya dauki ringing ina kallo yai ringing har ka katse ban dauka kira kusan uku yai min naki daga wayana a lokacin.
Sai ga Nafisa na doka sallama a kofan dakin nawa wanda tun zuwan ta ban taba yarda ta shigo min dakin ba sai yau da dan uwanta yace a bani waya muyi magana dashi ta wayan ta tunda ya kira ban dauki wayan ba.
Bayan ta shigo da sallama na karba mata take fadin barci kikeyi ne dama nace ma yaya ina zaton hakan ai.
Tana magana take miko min waya idanuwan ta kuma yana yawo a kusurwan dakin da take bi da kallon mamaki sosai.
Dama tayi zaton hakan don ganin yadda aka tsara dakin yaran dana su maria tasan namu abin kallone shi.
Na duba wayan har lokacin yana kunne bai kashe ba nayi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login