Showing 405001 words to 408000 words out of 419207 words

Chapter 136 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1524

har zuciyan su yake.
Ashe merry ta dawo ne Nafisa ta fada yanzu na tashi na ganta nima na bata amsa a takaice muka daga muka bar dakin.
Karfe biyar bayan Atika ta tafi ne sai gashi ya dawo wanan karon su ukunsu suka shigo gidan inda suka yada zango a dakin da mahaifiyar su take.
Sun dan jima a dakin shi ya fara fitowa ya same ni a daki tare da fauziya muna ba Abba magani don jikin shi da ya kara zafi lokacin..
Har yanzu jikin nasa da zafi ke nan ya fada lokacin daya shigo yana karasowa inda muke .
Na dan dago kai ina fadin yanzu ya kara zafi kuma shine nake bashi magani .
Dukawa yayi ya karbi yaron a hannu na yana fadin bari ayi sallah mu kaishi asibiti a dubashi bandai yi magana ba har ya gama da yaron zai fita nake fadin ashe merry tana tafe ne ?
Merry ya juyo da mamaki yana tambaya fuskan shi dauke da mamakin jin haka.
Tazo ne ya tambaya yana kallon fuskana da mamaki sai kuma ya juya yana fadin humm ya fita.
Nikan sai ban san dalilin jin zuwanta bai kwantar min da hankalina ba don haka nake faman kafa kafa da yarana a gidan na saka ido ga duk wani motsi nasu.
Zuwan ta da kamar sati biyu a gidan kowa na zaman sa ba ruwan wani a tsakanin mu don baka sanin ma tana gidan sai idan ta fito za a ganta.
Gashi ta rame ta kara duhu sosai da gani bata cikin yanayin dadin rai yanzu.
Kai ranan dai yawan mafalkin da nakeyi marasa dadi yasa na yanke hukunci fadawa mamu cikin daren nake waya da mamu ina fada mata nifa hankalina bai kwanta da zuwan merry din nan ba, .
Don haka kawai nake jin faduwan gaba tunda na ganta garin nan ga yawan mafarki da nakeyi mara dadi.
Mamu ta tambayeni da ita kike yawan mafalkin kodawa nace hankalina daine bai kwanta ba mamu.
Nasan halin bakaken fatan America wurin daukan famsa sai nake ganin kamar shi tazo yi a kan yarana da sauri mamu tace
Don me zaki fadi haka sayadi ina ruwanki da maganan su da zata dauki fansa gun yaran ki kuma.
Mamu nidai hankalina bai kwanta ba da wanan matar tunda har naji gabana yana faduwa haka tunzun ta gaskiya a cikin daren nan zan kawo su yanzu daya shiga sallah.
Ki bari zanzo da kaina tare da Nura mu dauko su a daidai lokacin ta yadda ba wanda zai gane hakan zan ma kawun ki bayanin komai yanzu.
Inji mai zai fada kada in kwaso yaran bada sanin shi ba.
Haka kuwa ya faru don ba wanda yasan fitan su gidan har da maria suka fice gidan koda ya dawo yana tambaya cewa nayi kawu ya aiko aka kwashe su dazun bayan fitan shi.
Don me aka dauke su da yamman nan nace ban sani ba ya dai aiko yana son yaran su zo mai ne kawai yace.
To amma kuma idan daddy zai kwashi yaran zai kira ko ya fada amma haka ka, , , sai kuma yai shiru ya juya ya fice daga dakin.
Nikan ganin merry tana gari yasa nake rufe kofana da wuri na shige abina daki in kwanta.
Da kyat na samu Abbana yayi barci ranan sai fitina yake min bayan na samu yayi barci, bayan dan fitinan daya taba shiga barcin can cikin barcina nake jin hayani ana dukan kofana da karfi kafin in bude idona da kyau ina saurare kofan aka kara duka da karfi sosai na mike zaune ina kokatin kunna autan dakin don inga haske.
17/11/2021, 07:26 - ??5惙5惙5?: Jin bugun kofan yayi yawa yasa na fara addua, can naji murya da alama ba hausawa ke magana ba a yadda nake jin muryoyin su a lokacin.
Suna fadi a cikin turancin lagos dana kwarai meke na break d fucking door now.
Wanda aka ba umurnin karya kofan ya fara kokarin dukan kofan da karfi yana son balla kofan kota karfin tsiya.
Ina tsaye kuryan daki ina jero duk addu,an daya zo min a bakina a lokacin can naji dayan yayi wani kara yana fadin shit he don't shoot me wooo.
Jin hakan yasa na kara matse yarona gam a bayana ina jero adduan ina ji ina gani ga kofan ya kusa budewa don ba karamin duka sukewa kofan ba lokacin.
Wani karan na kara ji mai karfi wanda ya tayar min da hankali sosai don ina jin sautin tankar na yaya umar a lokaci.
Ina saman bakina ga hawaye yana zubo min wanda bansan inda suke fitowa ba a lokacin.
Shiru naji a lokaci guda a daidai lokacin da Abbana yaji matsan da nayi mai yaiwa hadi da karan dukan kofan ya tayar dashi a lokaci guda.
Ya fara kuka babu kakautawa a lokaci daya ina kokatin rufe mai baki yanayi kamar zai shude a lokaci daya.
Kukan nasa yai min yawa yasa na sauke shi ina kokarin bashi nono ko zaiyi shiru .
Sai dai ina zuciya irin ta yara yazo mai a lokacin sai kuwa yake don ya tsorace ga baki daya.
Shawara nayi na shage ban daki dashi in lalashe shi a hankali na tura kofan ban dakin na rufo na fara lalashin yaron da kyat na samu ya kama nonon sai faman ajiyan zuciya da yake saukewa lokaci guda .
Ina cikin bathroom din cike da tsoro don ba komai nake jawa ba sai wullakancin da sukewa mata a yadda nake jin labari shi nafi kawowa a raina.
Can gabanin asuba naji ana sake dukan kofan dakin tare da kiran sunana inda na tabbatar da muryan yaya habbib ne dana su kawu.
Sai wasu muryoyi danake ji na daban suna fadin a karya kofan mana aga halin da take ciki idan basu harbe ta ba.
Tunda ga shedan harbi a kofan kuna gani sai naji an kara kiran sunana da karfi haka yasa na taso a inda nake da sauri zuwa wurin kofan na fara budewa.
Da kawu balarabe na fara arba haka ya kwantar min da hankali na nufesu ina kuka sosai naji muryan mama hadiye na fadin a kama yaron kada ya fadi kawu kuma yana fadin bakidai ji ciwo ba ko Fatima ?
Kai kawai na iya girgiza masu ina kwantawa a jikin mama hadiyen cikin tashin hankali.
Can kuma na dago da sauri ina fadin yaya fa mama ina yaya yake don ban ganshi a cikin su ba yasa nake tambayan shi.
Ya na nan naji kawu balarabe ya bada amsa yana kawar da kai da sauri tare da fadin hadiye ku zauna da ita a nan zamu koma asibitin yanzu.
Mama wake asibiti don Allah ku fada min ina yaya yake ko shine ke asibitin ne mama ina tambayan ta wasu hawaye na kara zubo min lokacin.
Kwantar da hankalin ki ki kama yaron nan dake kuka yanzu idan gari ya kara wayewa zai dawo ai.
To nace ina kaiwa zaune har lokacin ina raba ido ga mutanen dake tsaye a kaina fuskokinsu babu dadi a yanayin su suna tsaye kowa ya kura min idanu suna kallona.
Dan dukawa nayi ina kallon yatlron dake shan nono don ajiyan zuciyan danaji yayi da karfi lokaci guda saboda kukan daya sha din.
Wani sautin kuka naji an sake wanda yasa na mike tsaye zubur da yaron dake makale da nono a bakin shi yana sha kamar ba gobe.
Sai lokacin nasan da hjy maryam a wurin don jin muryanta da nayi tana fadin don Allah ku bata hakkuri karta koma daga muna hankalin Fatiman kuma.
Lokacin har nakai tsayeni na nufi hanyar dakin hjy inda nake jiyo koke koke a dakin hjy ce ke fadin na shiga uku na lalace sun kashe min jigon dakin nawa yau.
Wa aka kashe na jiyo ina tambayan mama hadiye danaji ta dafani da sauri mama tace ba a kashe kowa ba fatima rudun hjy ne kawai.
Yanzu me aka dauki ran mutum ne sai akashe mutum akashe banza don kawai imani ya kawo a zukatan jama,a.
Allah ya jikan ka umar Allah yabi maka hakkin ka ga duk wanda ke da hannu a cikin aikin nan.
Idona naji ya fara rufewa a lokaci guda daga haka ban kara sanin inda nake ba sai falkawa nayi nagani daure da ruwa karin ruwa a hannu na ana kara min.
Bude idona da sukai min nauyi nayi har wani yaji suke min saboda halin masifan da muke fuskanta a ranan.
Kallon dakin nayi na fahinci a asibiti nake kwance har lokacin ban san karin ruwa ake min ba saida na daga hannu na a lokacin naji karin ruwan da ake min din.
Zubur nayi kokarin mikewa zaune don tuna abinda ya faru damu da zancen hjy danaji har nakai ga sumewa sai yanzu na farfado daga suman danayi din.
Muryan su Amma naji suna fadin subbahanallahi hadiye ku kamata don Allah kada ta fama ciwon ta.
Sauke idona nayi kan Amma dake magana ina fadin don Allah Amma ku bari in tashi ina son ganin yaya umar yanzu don Allah Amma ki taimakeni in ganshi kofa sau gudane zan natsu wallahi.
Umar yana nan A ruwa saidai shima a kwance yake yana jin jikin shi don sun mashi rauni a lokacin da suka shigo gidan.
Innalillahi wa ina alaihim raji,un Amma sun jinwa yaya ciwo wa yan nan mutanen wasu irin mutane ne su marasa imani.
May mukai masu suka zo muna a wanan dare haka harda bindiga suna harbi kamar munyi masu wani laifi a rayuwan mu.
Shigowan yaya habbib tare da wani likita yasa na mayar da kallona garesu ina fadin din Allah yaya habbib ka kaini wurin yaya ina son ganin yaya insan halin da yake ciki don Allah.
Za a kaiki zahra ki kwanta ki huta shima din yana dakin hutu a yanzu haka ba a son a dame shi.
Tau tau yaya don Allah a kula dashi da kyau tunda kana wurin nan kada wani abu ya same shi.
Za a kula dashi insha Allahu ai ya samu sauki sosai yanzu barci kawai yakeyi daya samu.
Idona na mayar na lumshe hakan bai hana hawaye biyo gefen idanuwana ba a hankali suke gangarowa daga cikin idanuwana.
Barci ne ya kara daukeni a hakan sai lokacin yaya habbib suka fice daga dakin shida likitan da suka shigo a tare.
Yana ganin nayi barci yasa shi fita dakin ranshi babu dadi a lokacin muryan mama hadiye ne yaji a bayan shi ya dakatar dashi daga tafiyan da yakeyi.
Ya juyo yana fadin mama ana kan bincikin har yanzu ba a gane komai ba don kin san suma a bangaren su ai ba karamin shiri sukayi ba kafin su diro masu din gidan.
Allah dai ya tona asirin kowaye ke da alhakin wanan abin da gagawa mama hadiye tace tana hawaye.
Yanzu yaya ake ciki zancen shi umar din kai ya girgiza yana fadin har yanzu dai bai farfado ba sai dai yana numfashi kamar yadda yakeyi tun dazun.
Nan dai zuwa safe idan munga halin da yake ciki zamu nemi transafer zuwa Abuja mu gwada can mu gani.
Allah dai ya tada kafa ya bashi lafiya ita Fatima din sai zuwa yaushe za a sallameta ne don naga kamar dan damuwa ne kawai ke damun ta da firgici.
Eh to yanzu dai likita ke fada min cewa sai nan zuwa safe itama idan anga yadda jikin nata ya kasance.
To Allah ya kaimu mama tace tana juyawa zuwa dakin da nake kwance a ciki ta samu amma ta shiga yin alwala don yin sallah la,asar da yayi.
Tana fitowa itama mama din ta shiga don dauro alwalan tayi sallah fitowan ta yayi daidai da zuwan mamu da hjy maryam tare da kawu.
Abincin dake hannun Nura ya aje yana kallona suma din hankalin su a kaina yake mama ta fito take masu sannu da zuwa.
Suka karba tare da tambayan ta yaya mai jikin tace da sauki don ta farfado dazun sai dai damuwanta shine a kaita tana mijin ta don Allah.
Innalillahi suka furta Hjy maryam tace wanan daukan alhakin dame yai kama don Allah mutum a gidansa yanzu bai tsira ba wanda ke kan tafiyan ma haka ba a barshi ba.
Imani da tausayi ya fice a zukatan mutane sai son kai da son duniya shine abinyi a yanzu ido rufe.
Umar dai ba wani mai rigima bane balle ace wani abu ya hadashi da wani akai mai haka.
Yanzu ai ba sai kayiwa mutum komai ba zaiyi kokarin rabaka da duniya kawai lokacin muke da Allah ya fada shine ya fara gabato muna ubangiji yasa mufi karfin zuciyan mu dai suka karba da amin.
Dakin yai shiru sai kukan Abbana dake tashi kawai wanda su mamu suka shigo dashi don yadan sha nono idan na falka.
Don tunda na fadi aka daukoni sai aka mikawa mamu shi a can ya wuni gidan mu wurin su mama din duk da kowa ranan ranshi babu dadi kowa babba da yaro daya shafe mu yana cikin tashin hankaline.
Asibitin kuma yana cike da yan uwa da abokan arziki har ma da wa yanda ba,a sani ba a lokacin.
Kawune ya kawar da shiru ta hanyar tambaya wai shi fa tun safe da abin nan ya faru baiga wanan yarinyar ba da akace itama tana kasan kuma ai dole tana cikin gidan ai da abin ya faru ko ?
Wa ke nan Alh hjy maryam ta tambaya tana kallon kawu din yace dayan matar tashi mana ai naji ana fadan tana kasan nan ko ?
Laila kuwa merry din tun ganin safe da nayi mata a gidan ban kara ganin ta ba mama hadiye ta fada.
A jiyan zuciya mamu tayi tana fadin yarinyar nan sayadi kamar mai duba a jiyan fa ta kirani muna waya da yamma take fada min.
Cewa ita dai gabanta sai faduwa yakeyi tun zuwan merry din kasan nan danayi mata fada kan hakan .
Sai cewa tayi ita tasan ko waye merry din don halin black American da nakeji merry din tana dashi sak.
Don haka ita dai bata yarda yaran nan su zauna a gidan ba dole Allah zata kawo min su su kwana biyu a waje na.
Nace ta bari sai Alh ya dawo zan fada mai zuwa dare kuma ta sake kira tana fadin taji shiru shine ta bugo min don gaba daya ta kasa natsuwa da hakan .
Nace ban fada ma Alh ba do bai dade da dawowa gida ba a lokacin shine fa tace gasu nan yanzu zata saka akawo su idan daga baya zanwa Alh bayanin zuwan nasu.
To zuwan nasu ne yasa na manta in fada ma Alh don yaran sun shagalar dani wallahi sai gashi kuma mun tashi da wanan maganan yau na tashin hankali haka.
Lalai akwai ayan tambaya a nan don wanan magana yayi kama da batar ita merry din su hjy ya kamata a tambaya ina ita merry take aji ko a gidan ta kwana itama jiyan da abin ya faru.
Gidan ta kwana yaya don na ganta da mukazo da idona sai hjy maryam tace tabbas tana gidan don itace ma ta ke kururuwan da Alh balarabe yace a daina kuka haka.
To ina wanan yarinyar ta shiga yanzu ko dai tana gidan ne don taga kowa hankalin shi yana ga wa yan nan kamar an fita batunta an ware ta daban.
Bani tunanen haka Alh inji hjy maryam yanzu dai habbib ya kamata ka sanarwa komai don a bincika inda take din ko ya sani shi.
Ina zai sani tunda shine tsaye a kan komai tunda aka wuto da umar asibitin nan yake nan ban sa ya koma gida ba har yanzu ma mama hadiye ta fada.
Kawu yace to amma dai kun san wanan maganan ba abin kyalewa bane don dole ne mu san halin da yar mutane take ciki kasa ta salwanta kuma.
Ko tana daki don bakin ciki ta kulle kanta don shi kafiri bai san yarda da kaddara ba idan tazo mashi.
Waya kawu ya dauko daga aljihun shi yana neman layin habbib din ya fara kira sai kiran ya shiga.
A daidai lokacin ne kukan da Abbana keyi ya falkar dani daga barcin na bude idona sai akan su kawu din da matan shi dake tsaye a kaina lokacin.
Kallon yaron dake miko min hannu zuwa wurina don ya karbi abincin shi sam yaki sakewa a gidan mamu dukda mariya da fauziya dake gidan tare da yan uwan shi a lokacin.
Kawu yace min sannu Fatima ya karfin jikin kuma da sauki

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login