Showing 102001 words to 105000 words out of 419207 words

Chapter 35 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1438

ta kwanta da kyau.
Dama a gajiye take abinka da mai ciki bata ki ba ta bi mamu zuwa kuryan dakin ta a can ta haye gado ta kwanta sai barci.
Zai fita ya hadu da mahaifinsu a waje yaje su gaisa dashi sun gaisa kamar kullun har lokacin akwai dan sauran fushi a fuskan mahaifin nasa har lokacin.
Ya dan dubi mahaifin da ke tsaye yana fadin daddy nazo tun dazin akace kafita yace eh yanzu ma dawowa nayi in sha maganina dana manta ban sha ba kafin in fita.
Daddy mai zai hana aje asibiti sai nake ganin zaifi da shan magani haka a gida ko yaushe sai kawu yadanyi murmushi kadan yace.
Asibiti ai munje su suka dorani akan maganin kasan yanzu idan girma ya fara kama mutum sai a hankali.
Yana fadin haka ya juya yana kokatin barin wurin don tafiya yace to daddy Allah ya sauwa sai ka dawo ke nan ya gyada kai yana kokarin shiga mota yace Amin Umar fuskan shi a matse ya ja mota ya wuce ya barshi a gurin har ya fita get din gidan yana tsaye yana kallin mahaifin nasa.
A hankali ya rufe idanun shi yana tunanen sauyawan daddy nasu gare su kamar ba sune suke kamar abokai dashi ba.
Can ya bude idon ya sauke numfashi ya fara takawa zuwa inda ya aje motar shi ya shiga ya fara tokawa a hankali.
Lokacin zuwa islamiya yayi na fito na fara kiran kanne na don mu wuce don Ahmed yayi tafiya kwana biyun nan da kafa muke zuwa islamiyan.
Ban tsayawa jiran kowa yanzu don bata muna lokaci suke idan mun makara kuma a duke mu ni nawa bai damuna sai na kanne na da ake tsala suna kuka yasa nake saurin zuwa islamiyan kada mu makara.
A hanya mun dan taka kadan da gida a wurin wani gida da ake aikin sa ba dare ba rana dan nisa kadan da gidan kawu naga wani a tsaye ya bada baya kamar ya umar.
Faduwan da kanina yayi yasani dakatawa da tafiyan da nake ina gulma na tsaya ina fada dashi ya daga yana kuka.
Jin muryan mu dayayi yasa juyowa inda muke yana fadin ba zaki daga shi ba kin tsaya kina fada wawiya kawai.
Yana takowa zuwa inda muke ya karbi yaron dake kuka a hannu na ya jashi haka yasa dole muka tsaya yana tambayan shi ina zamu tafi haka da wanan ranan lokacin uku da wani abu na rana hudu batayi ba ko.
Yaron yace yana bata fuska islamiya zamu baiyi magana ba yaja hannun yaron zuwa wurin motar shi kawai sai da yasa shi a motar ya juyo inda muke yana fadin kuzo in sauke ku inane islamiyan naku yake ?
Ganina a tsaye ya kara fadin ke ba zaki zo ki nuna min gurin ba kin tsaya kina shagen kallon tsiya da sauri na daga kafata zuwa inda suke ya bude mota muka shiga da kwatance na nuna mai wurin .
Zan iya cewa ban taba shiga mota mai kyau da haduwa ba irin wanan ga kamshi da sanyin AC dake tashi a ciki sa.
Tunda muka shiga baiwa kowan mu magana ba har ya sauke mu nima ban samu bakin masa godiya ba yaja motar shi ya tafi.
A gajiye na shigo gida don yunwar da nakeji wanda rashin tsayawa inci abinci rana da zan fita ya haifa min jin wanan yunwan da nakeji.
Nayi sallama na shiga falin namu suna zaune a falo yana bata fruit a baki na fado falon.
Sai kuma na dan ja na tsaya daga kofan a juyo yana kallo na tare da fadin may kika tsayawa mutane akai kina kallo tsaban gulma kuma.
A hankali na taka zuwa ciki ina fadin ni nasan kuna ciki ne har yanzu kawai anzo an takurawa mutane na karasa fadi ciki ciki dakin mu na nufa ina cire hijjab din jikina da nikaf .
Ban kara fitowa ba duk da uban yunwan da nakeji sai da na daidaici sun bar gidan na fito lokacin har sallah isha,i nayi a cikin don kada in fito in samay su a falon.
Na samu kanne na suna cin abinci suna ba mamu labarin kaimu islamiyan dayayi dazun sai dai mamu bata gane wa suke nufi ba a cikin su.
Na gaida mamu tun kan in zauna ta amsa da fadin badai sai yanzu kika tashi ba nace har nayi sallah ko mamu tace kin kyauta.
Tace yaran nan ke fada min wai yayan ku dazun ya sauke ku islamiya wanne daga cikin su ta tambaya tana kallin fuskana.
Wanan daya shigo nan dazun ne ya kaimu na bata amsa tare da fadin mamu akwai abincin rana kuwa don dazun ban tsaya naci ba.
Tace ban ma girka wani ba don da yawa nayi dama don bakina sai kuma ta kasa cin abincin sosai nasan bata saba da irin shi bane.
Mamu may yasa bata zuwa part din maman su nafisa take zama muna a nan ko yaushe wallahi mamu ni ban son zamanta anan sam.
Ke ki rufa min baki anya Sayadi kina da tausayi kuwa yanzu ko ban jata a jiki ba ke ba mai min fada bane injawota a jiki yadda ake mata a gidan nan.
Ko haka kika koya ga karatun naki da kike fita dare da rana daukan darasi rashin tausayi ga wani.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:02 - ??5惙5惙5?: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM YA ALLAHU YA KAIYUMMU, , , ,


Ranan lahadi da yammaci kawu suna zaune da mamu a falon shi tana hada mashi abincin sa da idan yadawo yake ci sai kuma dare idan zai kwanta yasha yayan itacen da akullun baya katsewa gun matan shi don sun san shine abincin shi.
Umar da merry ne suka shigo gidan tun a waje ya san daddy su na gida don motan daddy daya gani a waje.
Don haka kai tsaye part din daddy ya nufa da matar nasa dake cikin atamafa buje da riga sai dai kanta babu dan kwali ko hula balle hijjab sai dan kwalin kayan ta dan dora a saman kafadan ta daga gefe.
Daga kofan falon ya tsaya yana sallama aka amsa mashi kawu da ya sheda muryan dn nasa tunkan su shigo ya kalli kofan yana kokarin kawar da kanshi gefe daya.
Yana gaba tana bin shi a baya suks shigo falon mamu dake gefe zaune tana ganin tare da merry suke ta dan sake murmushi a fuskanta tana tashi a inda take zaune kusa da kawu din tana fadin.
A cikin murna yau inlaw dina ce haka ban sheda ta ba kin fito yar African ki tsab wallahi suka dara gaba dayan su banda kawu daya kara tsuke fuskanshi a lokacin.
Ta kamo hannun ta tana dan rada mata tayi yadda taga mijin ta yayiwa mahaifin nasa ta amsa da thank you ma.
Cike da fargaban abinda zai biyo bayan shigowan nasu umar yake, don bai san irin karban da daddy zai masu ba a lokacin .
Sai dai samun mamu dayayi a gurin yasa ya danji sanyi a rashi don yasan komai zai faru kasancewar mamu gurin abin zai zo mai da sauki.
Ya karaso har inda kawu yake zaune ya zube bisa gwiwoyin shi tare da dukar da kanshi yace daddy barka da wuni an dawo lafiya ya kasuwa ?
Merry da takai kasa da kyat don bujen jikin ta da nauyin ciki tace good afternoon dad.
Umar da kirjin sai bugawa yake a lokacin don sauraron amsa kawu din zuwa gare su.
Kawu ya dan dago kai yana kallon umar din yace cikin dakiya Alhamdullahi umaru kasuwa ma masha Allahu.
Mamu dake gefe ke fadin marry ta zauna da kyau don taji dadin zama mana sai tace a a hakan ma yayi tana son daddy bless on her.
Lokacin kawu ya dago ya dan kalle ta yace thank you iam fine fuskan ahi ba yabo ba fallasa gare ta.
Dan shiru ya biyo baya falon kafin ya juya wurin mamu ya ce a shiga da ita wai kunu take son sha yanzu.
Mamu dai tace to bari aje a dama mata yanzu Allah sarki abu ga mai ciki ita yanzu kunun kawai ya biyo mata a rai ?
Dan juyawa yayi gurin ta ya danyi magana da ita ta mike ta bi bayan mamu zuwa part din suka barshi nan tare da mahaifin nasu a falon.
Shiru ne ya dan kara wanzuwa a falon sai karan na,uran dake aiki a falon lokacin uma??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????r ya rasa ta inda zai fara bayani wa mahaifin nasa don yana tsoron ya sake wani laifi a gurin shi.
Kawu ya kula umar magana yake son yi dashi lokacin sai dai da alama yana jin nautin fadin maganan da yazo mai dashi ne.
Kawu ya dan kai kishin gide yana fadin umar may ke tafe da kaine don da alama wani magana ya kawo ku gare ni yanzu.
Umar din yayi murmushin karfin hali yana gyara nade kafan shi yace eh daddy sai dai ba wani magana bane ina dai son in kara baka hakkuri bisa ga laifin dana aikata maka don Allah ka yafe min.
Kai kawu ya girgiza yace yaro ke nan umar idan banyi hakkuri ba kashe ka zanyi aini na hakkuri muddin dai kabi sharadin dana kindaya maka akai ba tare da kuntatawa marainiyar Allah da na zaba maka ba ni ya wuce a gareni ai.
Umar ya dan sosa keyan shi yace in sha Allahu daddy zaka samay ni da maka biyayya kamar yadda Allah yace a cikin natsuwa yai maganan shi.
Kawu yace daya fima alheri umar yanzu ina dadin wani koda dan uwana yau yazo gidan nan ace wai wanan arniyar ce uwar yayan ka.
Ka kwatanta a kanka yanzu zakaji dadin hakan a rayuwan ka wace irin uwa ka nemawa zurin,an ka da zasuzo duniya nan gaba ?
Umar yaya kake son mu,amulan mu da iyalin ka ya kasance a gidan nan nan gaba ?
Umar a cikin yayana kaf kai nake sa ran rike min zuriata koda bayana ne don hankalina gare ka yafi karkata da hakan sai dai kash ashe ban yi tunane mai zurfi ba da nake wanan shawaran a raina.
Maganar kawu ya saka hankalin umar a wani hali sosai a lokacin don shi sam baiyi tunanen wanan ba a gaba shidai ya biya bukatan kanshi kawai don jin dadin sa.
Sai yanzu da mahaifin nasa ke fadakar dashi yake tuna hakan hankalin shi idan yayi dubu ya tashi da zancen kawuna da yake mai yanzu.
Saboda hakan na yanke shawara akan ku akan abinda ku kuka kasa hangowa nan gaba uwar ku kuma tana goya maku baya kan shirmay da kuke yi din.
Lalai kawu yayi ya tuno mashi abinda shi ya kasa tunowa gaba ake duba ba kusa ba don maganan kawu gaskiyane umar yace a ranshi.
Kawu ya kare da fadin saboda haka ko bayana idan kuka saba alkawarina ban yafe maku ba umar.
Da sauri yace in Allah ya yarda daddy zaka samay ni mai biyayya a gare ka don Allah daddy ka yafe min nayi kuskuren da ba zan sake irin sa ba a rayuwana.
Dan shiru ya kara biyo a falon sai kawu yace akwai wani abin ne bayan wanan don ni kaji magana ta na dade da yafe maka don duk mairai bai wuce kaddaran shi sai dai taka kaddaran tazo muna a kyamace don haka nake maka fatan shirguwan wanan yarinyar nan gaba.
Yace insha Allahu daddy ina kokari a kai yace kamatsa da hakan don yana da kyau gaba akewa gudu ai.
Nagane nufin ka yanzu daddy a gare mu in sha Allahu haka ba zai sake faruwa ba gareni.
Ya gyara zama tare da fadin daddy dama tun dana dawo bamu samu zama da kai munyi magana sosai ba don ina son fadama irin ci gaban dana samu a gun aikina a can.
Ina jinka kawu yace tare da fadin uwarku tana kokarin nisanta ku dani kan wani dalili nata na banza ta yaya zan iya sanin halin da kuke ciki a yanzu.
Yace No daddy ba hakana bane zama ne ban samu yi ba amma ta yaya mama zatace ta nisanta mu da kai.
A can bayan kare karatu mataki na biyu na samu aiki da wani company daga nan na wuce karo ilimi ina aikin kuma da na kamala sai gwaunatin kasan ta dauke ni aiki a ma,aikatansu nacan.
Ganin irin riban da hakan ke dashi yasa na yarda zanyi aiki dasu na dan wani lokaci idan adadin danake ganin
Kawu ya girgiza kai cike da gamsuwa da bayanin dan nashi yace yaro ke nan sai dai ina son ka sani rayuwan mu yau ba a hannun mu yake ba umaru.
Don ko yayane kasanka tafi bukatanka a yanzu don haka ban lamunce ma zaman ka acan ba dindindin kaji na fada maka.
Ya amsa da insha Allahu daddy don nima ba zanso yarana su taso da wani akidan da baishafi al,adana ba a yanzu.
Kayi tunane mai kyau Allah yayi maka albarka yasa a gama da duniya lafiya yace Amin daddy na gode.
Kawu yace zanso ka bani dama in gana da ita matar taka idan ba damuwa don ta fahinci irin gidan da ta shigo.
Cikin dauriya da faduwan gaba yace ba matsala ai daddy sai dai kuma ka gafarce ni don nayi wani karanbanin ba ban shawarce kuba daddy don nasai gida tun ina can a nan unguwar aka rusheshi akai min tsarin da nake so gare shi.
Kawu ya jima shiru ba tare da yai magana ba yana tunanen halin rayuwan dan nasa na zurfin ciki.
Yaya har akai ya sai gida akai masa gina duk basu da labarin hakan sai yanzu yake fada mai ga wanan bakin aure da yayi ace duk yara matan musulmai dake cikin kasan nan da garin kano basuyi mai ba ya jajibo masu kafira a matsayin suruka don yawan zurinfin cikin su bai sanar dasu ba sai da abu yayi nisa haka harda rabo.
Sai dai babu yadda zai da dan nasa tunda ya fahinci halin sane hakan ba wai yin kasa bane illar nisan ta su da kowa da mahaifiyar su tayi tun farko duk yajawo hakan.
Allah ya kyauta yasa albarka ka more kai da iyalin ka lafiya da yawancin rai.
Wani irin dadi ya ziyarci zuciyar umar da wanan adduan da mahaifin shi ke masa a yammacin nnan haka ya bashi daman ci gaba da fadin akwai wasu dana saya a lagos da Abuja sai kanfanin da muke son hadawa ni da wani abokin aikina bayerabe a can kudu.
Umar duk wanan lissafin da kake min a ina ka samu kudin yin su cikin wanan dan shekarun da kayi kana aikin ka ?
Dan murmushi umar yayi tare da fadin daddy ka yarda dani ba abinda kake nufi din nan bane don idan ka duba can kasan ba irin nan bane da ake tauye ma,aikaci shiyasa mutanen mu yanzu basu son yin aiki a kasan nan.
Don albashin can ya nunka na nan nikin baninkin idan kuma kayi duba gani international referner ne na hadin kasa da kasan turai zaka fahinci ta yadda kudi suke zo min a yanzu.
Shiru kawu yayi na dan wani lokaci yana nazarin maganan dan nasa kafin yace Allah ya kyauta a dai riki gaskiya ga duk abinda akasa a gaba.
Ya dora da fadin a dinga kyautatawa yan uwa da mabukata dake a kwai kasa damu don muna da yan uwa a birni da kauye wa yanda ke bukatan kulawan mu.
In Allah ya yarda daddy za a kula zan yi kokarin zagawa a cikin dangi mu kai ziyara kawu yace Allah ya bada iko ya amsa cikin jin dadi da Amin.
Kawu yace kaje kazo min da matar taka kafin lokacin sallah ya gaba to in fita ya amsa da to daddy yana yunkurawa ya tashi.
Ba karamin dadi umar yaji ba na fahintar juna da sukayi da mahaufin wanda ya samay shi a cikin saukin kai a yadda bai zata ba.
A falon mamu ya samay mu zaune ana dariyan merry dake shan kunu tana santin shi don hadin da mamu tayiwa garin kunnun tsamiyan kafin ta dama dama yana aje a ckin fridge din ta don ba kullun ake damawa ba.
Muna ganin shigowan shi kowan mu ya natsu muna gaida shi da shigowa gidan ya dan kalli mamu yana fadin daddy yana son su gana da ita.
Tace masha Allahu hakkuri bai bar komai ba umar dama nasan in anbi Alh zai sauko a sannu a cikin muryan shi kamar mai rowa yace hakan ne nagode maimuna.
Wani kallo na watsa mai da mamakin yadda yake kiran sunan mahaifiyata haka gatsau sai naji ya kara zube min a idona.
Ita ko mamu hakan ko a jikin ta bata damu da yadda nasha toka ba na bata raina sosai sai ji nayi tace sayadi dauko mata dan karamin hijab din

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login