Showing 408001 words to 411000 words out of 419207 words

Chapter 137 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1473

kawu na bashi amsa sai hawaye.
A daidai lokacin ya dauki wayan suka fara magana da yaya habbib a waya kan zancen merry din da ba,a gani ba a lokacin.
Ya juyo yana gab da fita dakin yana fadin ku mikashi mana ta bashi nono tunda ta tashi tun safe yake wanan kukan saboda firgitan da yayi.
Yana fadin haka ya juya ya fita daga dakin ita kuma mamu ta miko min Abba din dake kuka ta hanyat shi fidar dashi saman gadon da nake kwamce din.
Ita ta gyara muna kwanciya da yaron duk su mama d hjy suna kallon mu gwani ban tausayi damu lokacin.
Kawu sunyi magana da yaya habbib yace shima ta fado mai a tai da bai ganta ba asibitin tun dazu.
Dkn Allah ayi kokarin nemo inda take kada yar mutane ta salwanta kuma muna cikin garin nan.
To daddy ya amsa yana dauko wayan shi kake a cikin aljihun yana neman wani ashe hjy yake kira don ya tambayeta ina merry din take ne .
Hjy jiki na rawa ta dauki wayan tana zaton za ace wani abu game da yaya umar don haka tayi saurin daga wayan don gani layin habbib din ke kiranta dan jin halin da umar din ya ke ciki a lokacin.
Saidai sabanin jin bayanin komai daga gareshi da tayi yake tambayan ta ko merry na gidan do bata asibiti tunda suka zo nan.
Ina zan sani tunda ba nan take shigowa ba balle mu sani don Allah idan nafisa na kusa ta duba muna ita a bangaren ta ko tana gidan.
Nafisa ta kalla kafin tace ni ba wanan ba yanzu wani hali dan uwan naka yake cikine wai kun barmu nan a duhu haka babu labari.
Yace mama sai dai addua ga yaya gaskiya don yanzu shi yafi bukata a gare mu tunda har harbi biyu sukai mai da kafa da kirji kinga dole ya shiga wani hali a yanzu.
Shiru tayi ba tare da ta kara furta komai ba sai can ta kalli Nafisa tana fadin wai ki duba mashi wanan yar waje din ko tana gidan nan.
Nafisa tana kunkumi ta mike zuwa part din don dubawa sai dai tana zuwa ta tura kofan ta sameshi a bude babu kowa a ciki ta dan duba har bathroom nan ma bata a ciki ta fito ta bude wardrove din dakin dakin sai dan daidaikun kayan merry din ta gani a ciki.
Alaman dai babu mutum a cikin dakin na dan wani lokaci ke nan ta fito ta fadawa hjy abinda ta gani a dakin.
Hjy dasu mama sukace ta duba waje ta tambayi masu gadi ko sunga fitan ta .
Masu gadin sun tabbatar mata ba, a dade da kai maigidan asibiti ba ta fito wata bakar motace tazo ta dauke ta da yar jakkar kayan ta.
Komawa tayi ta fada masu habbib hjy ta kira take fada mai komai kawu dake gefen shi yace shike ban zancen yarinyar nan ya tabbata kan matar nan da alama fansan yarta tazo dauka gareshi dama.
17/11/2021, 07:26 - ??5惙5惙5?: Bai bata lokaci ba wurin kiran dansandan dake kula da case din yana bashi bayani kan zargin merry da kuma batan da tayi.
Dansandan yace gasu tafi don du kara daukan bayani kowa dake gidan lokacin da abin ya faru.
Cikin yan mintina suka shigo asibitin a nan suka samu yaya habbib don jin karin bayanin kiran da yai masu din.
Kara maimaita masu bayanin dayayi mai a waya yayi suna rubutawa a takarda kafin su ce suna son duk wanda ke gidan a wanan daren zasu gana dasu daya bayan daya.
Wake cikin asibitin nan a cikin su eh akwai matar maigidan wace ke kwance a yanzu da take jin jiki sai kuma dayan maigadin da aka harba dayan kuma ya mutu tun a lokacin da abin ya faru dashi.
Ok ko zamu iya ganin wani daga cikin su a yanzu dansanda yace yana tambayan likitan sai a lokacin likitan ya dan gyara tsayuwa yana fadin.
Da zaku barsu har zuwa gobe don lokacin hankalin su yadan fara kwantawa suna cikin dan hayacin su zaifi sai ku dauki duk bayanin da kuke so a garesu.
Ba matsala dansandan yace ko akwai wasu da zamu iya gani bayan wa yan nan din yaya umar yace eh akwai wani mai kula da duk wani al,amarin gidan tare da matar shi da suke a gidan lokacin da abin ya faru.
Ok yana ina yanzu ya habbib yace zamu iya samun shi a gidan yanzu don ko yaushe shi yana gidan bai faye fita ba.
Zamu iya zuwa yanzu mu ganshi idan ba damuwa ya fada yana kallon habbib din yace No problem zamu iya zuwa mu ganshi ai da haka suka bar asibitin a tare.

A dakin da nake kwance kawu ya shigo bayan sun fito sallah magariba ya samu su mamu a zaune inda suka idar da sallah yake fadin dare ya soma zaku fito ne mu koma gida.
Yaron fa a nan zamu barshi kodashi zamu koma gidan hjy ta tambaya tana kallon mamu don son jin amsan da zata bayar.
Kafin mamu tai magana kawu yace a barshi nan mana tunda an samu tana dan cikin hayacin ta yanzu.
Nima shina gani don ko munje dashi ba zai ci komai ba kamar yadda yayi dazun .
Kawu ya dan matso kusa dani yana fadin fatima mu zamu tafi yanzu dare yayi mun bar yara a gida .
Ina son ki kwantar da hankalin ki insha Allahu mijin ki zai samu lafiya da yardan Allah kuma yan sanda suna nan suna binciken wanda keda alhakin aikata haka .
Da kyat na bude baki ina fadin kawu don Allah kayi magana a cire min ruwan nan inje inga yaya umar din dakon da yake.
Zakije fatima kiyi hakkuri kema yanzu ba dadi kike ji ba har ruwan ya kare sai a rakaki ki ganshi ki mashi addua don yanzu adduan mu yake bukata fiye da komai.
Ina jin hakan na runtse idanuwana ina jin zuciyana kamar zai fashe a lokacin nasan yaya umar yana cikin wani yanayi mai muni ke nan a yadda kawu ke nufi.
Ban kara bude ido ba har barci ya daukeni a hakan yadda nake ina tunanen halin da mijina yake ciki.
Jin an dauki yaron dake manne a jikina yasa na falka firgigit ina bude idanu a tsorace sai nake ganin kamar mutanen ne suka kara dawo min a lokacin.
Ganin mama hadiye tsaye a kaina yasa na maida idanuwana rufe muryan yaya Ahmed naji yana fadin sannu fatima ya jikin naki.
Sake bude idanuwa nayi a hankali ina fadin da sauki salma ne ta matso bakin gadon tana fadin ya jikin fatima kai na gyada mata kawai ina datse bakina don yadda nake ji a lokacin .
Ina jin Ahmed na fadin har yanzu dai ba,a samu bayanin wa yanda sukai wanan abin ba ko ?
An sani ba kowa bane merry ce na bashi amsa don tun lokacin data zo garin nan zuciyana ya bani hakan kuma shi kanshi yaya na fada mai abinda nakeji game da ita akan yarana.
Kowa dake dakin ya dauki salati sai mama ke fadin ki bar fadin haka fatima tunda zato kikeyi don Allah .
Ba ita kadai yanzu ake zargi ba ai har hjy sabuwa da yarta suma ana zargin suna da hannu a cikin wanan abin ai.
Tunda ta fadi sai yaga abinda zatayi mai tunda yai masu haka a gaban kowa kinga ko dole a zarge ta itama.
Allah dai ya tona asirin duk wanda yai wanan abin Ahmed yace aka amsa da amin gaba daya.
Juyowa nayi a hankali na kalli salma ina fadin salma kinga yaya din wani hali yake ciki nace su bari in tafi in ganshi anki bari in tashi.
Fatima kiyi hakkuri kema kina cikin taki laluran ga ciki a jikin ki dake maki wasa sanadin wanan abin ga kuma halin da kike ciki.
Ba zaki fada min halin da yayan ki ke ciki ba kema salma ku fada min mana don Allah idan ya mutu ne in sani.
Wallahi bai mutu ba fatima yana dai cikin wani haline mara dadi don har yanzu baisan a inda yake ba.
Kuma likitoci basu bari a shiga inda yake sai yaya habbib da daddy da akace ya shiga dazun ya ganshi.
Zubur na mike zaune ina kokarun cire karin ruwan da ake min wanda yakici yaki cinyewa har yanzu don rage karfin ruwan da sukayi bai sauka sosai da sauri.
Sai subbahanallahi may kikeyi haka Fatima ina, zaki don Allah, don Allah ki natsu ke kanki baki da lafiya fa.
Shine abinda wa yanda ke cikin dakin suke fada min cikin tashin hankali suna kokarin kamani su kwantar dani.
Ku barni in inje in ganshi ko akwai abinda zan iya mashi a yanzu don Allah na fada ina karasawa da kuka .
Tausayi na basu naji mama na fadin ni banga dalilin da zaisa a hanata ganin shi ba dama don ganin shi shine kwanciyar hankalin ta a yanzu.
Jin abinda mama tace na juya gare ta ina fadin don Allah mama ku barni in ganshi don Allah saka hijab mu tafi inda yake saidai likitocin basa yarda kowa ya shiga dakin da yake ciki gaskiya.
Muma da muka tafi ta taga muka tsaya mukai mai adduan Allah ya bashi lafiya tana gaba ina binta a baya muka karasa har emergycy dakin babu kowa sai shi dake kwance ga na,ura saukan numfashi makale a hancin shi sai ruwa da ake kara mai.
Innalillahi na fara ambata sai dai duk da halin rudun da nake a ciki bai hana inyi nazarin yadda abin yake ba.
Juyawa nayi ina fadin mama ko zan iya ganin likitan dake kula dashi don Allah ?
Eh to habbib ne tare da wani likita abokin shi suke tsaye a kanshi dama ya Ahmed ya fada yana karasowa kusa.
Amma idan kina son ganin shi ai za a iya masu magana a yanzu sai a hadaki dasu ko , ?
Da sauri nace don Allah yaya idan ba damuwa zanso in gansu akwai maganar da nake son yi da likitan a yanzu.
Ya juya tare da fita wurin komawa nayi ina kara nazarin halin da yaya yake a ciki lokacin.
Saiga yaya ya dawo yana fadin likitan yace naje tare dashi da salma muka shiga office din nan ya nuna muna wurin zama yana fadin lafiya dai hjy kike son ganina hope ba wani matsala bane kuma yanzu.
Dago kai nayi ina fadin doctor idan babu damuwa zanso muyi magana insan abinda kukai ma mara lafiya amfani dashi da irin ci gaban da kuke ganin ana samu gareshi yanzu.
Wani kallo likitan yayi min yana kokarin cire glass din dake saye a idon shi.
Amma malama ke din wacece da zaki zo min da wanan maganan ya fada cikin daure fuskan shi aka kwankwasa kofa za a shigo office din.
Hakan ya hanani furta mai komai har wanda ya shigo din danaji yana mai sannu da zuwa amsawan maishi yasa na juyo daga inda nake zaune don ji muryan wanda na sani.
Shima anyi sa,a ya juyo yana kallon mu a cikin mamaki lokaci guda muke ambatan sunan juna.
The guy yace Fatima kece ko gizau idanuwa na ke min don na bincika an fada min kin koma second degree din ki a can London kuma.
Kai na gyada mai ina fadin hakane yanzu ma mun zo kasan nan don duba sarakuwata da bata da lafiya shine wani tsautsayi ya samemu a nan din.
Likitan ne ya karba da fadin kan isue din dana kiraka ke nan yanzu don abin ya shige min a duhu ni kaina.
Innalillahi ya furta tare da fadin how comes hakan ya faru is a long story sai dai da alama kasan ta a yadda naga kun nunawa juna.
Kallo na The guy yayi yana fadin wanan da kake gani aida nasan tana nan da ban baro Abuja nazo nan ba don duk abinda zan iya itama iam sure zata iya fiye dashi ma a yanzu.
Mu daina wanan magana muyi zancen mara lafiyan nan please don i am sure muna gab da rashi a yanzu saboda awowin daya dauka a hakan.
Nan na fara gin ma likitan tambayoyi yana min bayani sai na tuno da wani hikima da aka koya muna indan an harbi mutum.
Nan nayi masu bayani take likitan ya mike yana fadin shaf na manta da wanan idea din da kika kawo kiran doctor habbib yayi yana masa bayani sai yace gashi tafe.
A tare dani muka shiga da yaya dakin theater din aka yi mai duk wani abinda ya dace a lokacin kusan duk wani dan uwa na jiki yana tsaye a gurin an zubawa sarautan Allah ido kawai.
Ni kaina hankalina ba a kwance yake ba alwala nayi na tayar da sallah nakai kukana ga ubanginjin talikai mai jin roko da biyan bukatun bayin shi.
Ina sallamewa na zauna addua a gurin can kuma tunane ya dauke min hankali na yanzu idan yaya ya tafi ya barmu ni yaya rayuna dana yarana zasu kasance daga baya.
Ban kaiga karasa tunanen ba naji ana kiran sallah asuba don haka na mike don yin nafila.
Saida aka tada kabbara a masalacin dake cikin asibitin na mike don gabatar da sallah na idar kenan ina lazimi naga likitoci da sauri sun shiga dakin da yaya din yake kwance.
Da sauri na mike tsaye zuwa dakin saidai na samu sun rufe kofan hakan yasa na tsaya sanin shiga lokacin aikin su dokane.
Tunda ba aiki nake a gurin ba ina tsaye ina shawara naga wani nurse zai shiga dakin da sauri yana rike da kayan aiki a hannun shi.
Ban tsaya ba na jefa kai???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?na a dakin nima a rikice suke su duka suna gani na dayan yace don me na shigo masu daki lokacin aikin su.
Ban damu da tambayan da yake min ba hankalina yana gun yaya da sauri na karasa ina fadin ya miko min spoon ko seazors kada yai mai alluran nan yanzu.
Nawan shi nagani wurin miko min abinda na bukata din da sauri na dauko na bude bakin yaya na saka mai tare da toshe hancin shi sai naji ya ja wani irin ajiyan zuciya lokaci guda a hankali numfashin shi ya fara dawowa .
Dakin yayi tsit kowa na kallin ikon Allah duk idanuwan likitocin yana kanshi har ni a lokacin sai na,uran da aka makala mai ke aiki cikin dakin nima duban na,uran nakeyi a hankali ya koma daidai na zare almakashin dake bakin shi.
Addua na fara jero mai na samun sauki a wurin Allah don yana cikin wani yanayi wanda ba,a son mutum ya kai a lokacin.
Juyawa nayi ina fadin ko za,a samo wani allura na fada don shine daidai aimai a lokacin ba wanda suke niyar mai ba a yadda yaken.
Alluran nan yana da wuyan samu gaskiya a yanzu wani ya fada min yake fadin basu faye sayoshi ba a kasan nan don ba kowane zai iya sayen shi ba.
Dayan likitan ne ke fadin yana ganin yana dashi a gurin shi daya sayo zaiwa wani mutum a lokacin kuma sai mutumin ya rasu.
Likitan mai duba yaya yace yayi sauri ya dauko muna nan ya juya ya fita dakin yayi tsit muna ksllin yadda numfashin shi ke tafiya a hankali har wanan likitan ya dawo da maganun a cikin wani kula don ba, a barin shi inda babu sanyi.
Karba doctor yayi suka fara shawaran mill nawa zasu mai ina jin hakan nace give him five is ok for him now.
Kallona sukayi dukkan su basuyi magana ba don the guy ya riga ya fada masu su yarda dani da duk shawaran da zan basu nasan aikina sosai.
Anyi alluran da kamar minti goma sha sai numshin ya koma normal sosai har zaka iya jin dan hantsari daga gare shi.
Sai lokacin na sauke a jiyan zuciya na juya ina fadin thanks tare da nufar hanyan fita daga dakin don kafafuwana ba zasu iya daukana ba a lokacin.
Na fito daga dakin idanuwan kowa a kaina don na samu har hjyn su tazo an kamota tana wurin da duk yan uwanta da na kawu sai wasu fuskoki da ban sani ba.
Rasa wanda zan amsawa tambayan da suke min nayi don kowa na son jin halin da yake ciki saboda hankalin su gaba daya ya tashi a lokacin.
Da sauki na fada na nufi empty kuran dana hango na zauna don ba zan iya tsayuwa ba a lokacin gashi nima ba lafiya ne a jikina ba.
Abbana mama hadiye

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login