Showing 402001 words to 405000 words out of 419207 words

Chapter 135 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1509

a gabana wallahi.
Wanan idan ba kakai zuciya nesa ba kina ganin mai zai faru a wurin saukin abin ma yaran nata basu dauki wanan halin nata ba a ran su da ai zumunci ta dade da lalacewa ko a family mu.
Gulman me kuke yi haka kuka kashe murya haka don da gani zaman gulma kuke a nan muryan yaya habbib ne yake fada muna haka .
Juyowa mukayi muna kallon shi da dan murmushi a fuskan ko wacen mu sai matar shi ke fadin kai yaya mu hiran abinda ya faru mukeyi ba gulma ba.
Kun gaisa da hjy ne da kuka zo nan kuka zauna ya fada yana tsare mu da idanuwa ma,ana umurni yake basu a lokacin.
Dakin ne baida dadin shiga yanzu yaya ana cikin wanan tashin hankalin haka yasa bamu shiga ba sai dan zuwa anjima idan an rage yawa.
Yadda ya juya yasa ta fadin Aisha tashi mu dubata kada muma namu ya same mu yanzu a gurin shi.
Ni dai ina jin su suna mikewa na mike nabi bayan su zuwa dakin da hjyn ke ciki duk da muna jin hayaniyar yan uwanta a dakin.
Mun samu har su salma sun shigo don labarin abinda ya faru da safen ya isa kunnen yan uwa sai zuwa gidan suke don jin ba,asin zancen.
Sallaman mu ya dawo da hankalin su kofan dakin muka shigo mu uku muna gaida su mama Asabe take fadin au a tare kuke da maigidan ashe ?
Tare muke mama Rukaiya ta fada tana neman wurin da zata tsuguna a dakin don ba wani fili a dakin don tarkacen hjy dake dakin yanzu.
Sun gaida hjy tana amsa masi cikin yanayin rashin dadin zuciyan da take a lokacin take tambaya da ina yaran suka barsu ne ?
Aisha tace suna gida wurin mama muka barsu da zamu zo mun biya can suka ce zasu tsaya a nan da cewa gidan kawu ke nan.
A dan dakile ta amsa don jin abinda Aisha ta fada din da alaman hakan bai mata dadi ba kasan ranta.
Fatima sannu da kokari fa muna ta jin kokarin da kikeyi da jikin hjy wurin asabe Allah ya saka da alheri ya baku masu rama maku hakan.
Dakin ne ya amsa da amin ina fadin hjy dazun ko kin sha wanan maganin dana hada sai mama asabene tace .
Ina fa yan nan ta dauko ke nan zata sha wanan bala,in yazo muna tunda safen nan ai sabuwa batayi ba wallahi.
Don Allah Asabe ku daina ganin laifin su nifa har gobe inda gaskiya yake nake fada sam sabuwa wuri ta samu a nan .
Allah dai ya kare komai bai kai ga faruwa ba a tsakanin su amma mama komai gaskiya ai hjy sabuwa tafi mama laifin don ta boye mata gaskiyan halin da yarta ke ciki don cuta da zalunci kawai salma ke fada.
Magani na hada na kara bawa mama Asabe don taba hjy din a wanan lokacin na fita zuwa dakin yaya don na samu yaya habbib shi kadai a zaune falon shi bai fito ba.
Dakin na tura na shiga da sallama na hango shi kwance yana rigingine fuskan shi yana kallon saman dakin.
Dan juyowa yayi ya kalli kofan kafin ya kawar da kai ya koma a yadda yake da farko na karaso ina fadin yaya ka kwanta kabar yaya habbib a falon shi kadai zaune.
Yana gidan nan ne har yanzu ya tambaya har lokacin kamar bason mu hada idanuwa dashi ne.
Zama nayi a gefen shi ina fadin lafiya na gabka haka yaya ina tambaya tare da kallon shi a yadda yake din kwance.
Yace da kyat No ba komai sai yai shiru nima dai shirun nayi na dan lokacin kafin yace Zahra na amsa da na,am ina kallin shi.
Kada ki dauki wanan abin daya faru da zafi kice zaki rike shi a ranki don Allah .
Da sauri nace haba yaya a kan me zan dauki wanan zancen da zafi bayan Allah ya karemu daga sherin hjy da yarta.
Hannu ya daga min yana mikewa daga kwancen yake fadin nasan kalaman hjy sabuwa da mama ta fada a kanki suna da zafi sosai.
Don haka nake rokon ki kan kiyi hakkuri da duk abinda hjy tayi maki kada kice zaki dauki wanan abinda zafi a ranki.
Yanzu bada bane yaya hjy nasan uwatake a gareni kuma sarakuwata don haka don mahaifiya taiwa yarta abu saita dauki zafi da ita.
Ajiyan zuciya naji ya sauke mai dan sauti yana fadin idan kin min hakan kin kyauta min matuka kuma ina alfahari dake akoda yaushe don nasan daddy bai min zaben tumun dare ba.
Ko nace ina dan kallon shi ina murshi yace kinfi kowa sanin wanan hadin namu ai daga Allah yake kawun ki idda sunna yayi kawai .
Au goron da zaka ba kawu a yanzu ke nan yace gaskiya na fada yana kokari tashi tsaye ta hanyar dafani ya mike tsaye.
A tare muka fito dakin har lokacin yaya habbib yana gurin zaune wanan katon tare da yaran yake fira jin fitowan mu yasa ya dago kai yana kallon mu.
17/11/2021, 07:26 - ??5惙5惙5?: Sun dade tare a falon bansan may suke zance a kai ba don ina daki tare dasu Aisha muna hira inda suke ban hiran abubuwan da hjy take yi masu na rashin dacewa gare su.
Ban furta komai ba sai kara kwantar masu da hankali a kanta kamar yadda nima mamu take yawan yi min nasiha da kada na nuna abun yana damuna don dan ta bazai ji dadin hakan ba idan na nuna.
Rukkaiya kan cewa take ita kan gaskiya ba zata iya shanye wani abu a ranta ba don da gangan ake maka cin fuska don kawai danta yana auren ka sai ka zama abin ki ga mutum ?
Sai bayan la,asar yaya habbib ya bugo waya yana fadawa matar shi ga driver nan a waje yana jiran su don yaran sun fara damuwa lokacin.
Sai da suka shirya sun dadauki abinda suke so a dakin nawa ban hanasu don sun nuna ra,ayi akan abina nasan Allah zai musaya min da wanda ya fishi idan na basu da zuciya daya.
Muka fito zuwa dakin hjy don su sallameta a zaune take lokacin tana shan ferfesun kaysn cikin rago.
Nafisa tana tsaye a kanta da ruwa rike a hannun ta tana bata jin sallaman mu shigowa yasa suka mayar da hankalin su gare mu.
Mun mata yaya jiki yayinda take dan dago kai tans fadin ashe kuna gidan nan har yanzu eh yanzu zamu koma don yaran nacan su damu mu dawo.
Ke nan ba za,a kawo su su ganin basu ko don kuna gudana da yayan ko hjy ta fada tana kai cibin da take shan ruwan miyan a bakin ta.
Can muka fara zuwa gaida daddy shine suka lekawa mama don sun saba da ita yasa muka barsu can tare da ita don lokacin an bugo waya ana wanan fitinan da safe.
Na fahinci may Rukkaiya take nufi yasa nayi saurin fadin hjy Nafisa ashe kin shigo ban sani ba ?
Tace ummm ke dai fatima na shigo dazun bayan azahar da nake jin abinda wayan nan marasa mutuncin sukayi yau .
Don ni ina kuryan Amma ina barci banji me ke faruwa ba sai dana tashi Amma ke labarta min hakan.
Wallahi naso na shigo a lokacin da yau sun kara raina kansu wallahi don wana karon ba zan kyalesu ba Allah.
Umm tashi mu tafi Rukkaiya tace tana hararan gefen da Nafisa din take .
Jin hakan nace Nafisa ke nan wa yan nan ai sai irin su yan duniya don babu mutunci a tare dasu ko kadan.
Na fahinci babu shiri a tsakanun su da samira do haka nake kokarin a rabu lafiya a dakin don yanzu sam bansan me yasa bana son tashin hankali ba ni.
Ganin sun fara fita daga dakin yasa nace barin dawo Nafisa in baki labari ta amsa da ai ina nan don kilama a gidan nan zan kwana yau.
Nace kice dai yau mune da bakuwa a gidan nan ashe mara masu Aisha baya nayi ina fadin sai yaushe kuma zan ganku ?
Muna nan ai tunda an kawo mu jiya ne don haka sai kin gaji da ganin mu har bakin mota na raka su suka tafi ni kuma na koma ciki.
Dakin nayi niyar shiga zancen dana sama sunayi ya hanani shiga dakin Nafisa ce ke fadin ai nasha fada maki wallahi fatima tafi su kirki dan dama Aisha don ita bata fitowa fili ta tsulawa mutum tsiya kai tsaye.
Uhumm ni kaina canzawan yarinyar nan yana ban mamaki don da farko na dauka makircin sune take min don mijin nata ya gani.
Amma yanzu na fara sarewa da al,amarinta don yadda akai wanan maganan sabuwa ta tona min asirin duk abinda mukayi tare da ita amma bata canza min fuska ba saima goyon bayana da tayi a gurin.
Jin hakan yasa na fasa shiga dakin naja kafana?????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????? nabar kofan dakin zuwa part din mu zuciyana cike da tunanen maganan nasu.
Lalai mamu tayi gaskiya da take fadin duk abinda zataiwa hjy bazata taba son mu a ranta ba don kiyayyan mu ya riga da ya shiga ranta ko mai kankare shi sai Allah.
Tunanen ba zai kare ba na tashi zuwa gun maria don ganin halin da suke ciki don yinin ranan na barta da yaran tana dawainiya dasu.
Na sameta tana goye da babana da yai barci a bayanta sai sultana da take shiryawa don fauziya tana bayi tanawa yaran wanka lokacin saboda yamma dayayi.
Har zuwa lokacin da yaya ya dawo gida baya cikin walwala tare dashi na fahunci hakan ne ta hanyan rashin cin abincin dare da baiyi ba sai ruwan shayin daya sha ya kwanta a lokacin.
Ban matsa da tambayan shi haka nazo na kwanta na tashi don da safe ma muryan shine a inda yake karatun kur,ani ya tayar dani .
Kallon shi nake da mamaki da bai tayar dani inyi sallah ba a ranan haka kuma banji lokacin da akai sallah asuba ba a ranan .
Ki tashi kiyi sallah lokaci yana kurewa sanyin ruwan sama ya hanaki tashi kiyi sallah akan lokaci.
Ban iya magana ba lokacin don raina da nake jin babu dadi saboda rasa sallah asuba danayi a ranan.
Ban tsaya dakin ba fita nayi zuwa dakina na shiga bandaki kodana idar da sallah ban daga ba wurin ina zaune sai faman tunanen rayuwa nake a raina.
Merry ce ta fado min a rai tausayin ta ya kamani don raba da da mahaifi sai Allah nasan kuma wucen merry ta bar queen a kasan nan bawai ta bar zancen bane.
Saidai matakin da zata dauka ne ban san yadda zasu kaya karshe ita da mijin nata ba a karshe.
Mikewa nayi don jin ruwa ya kara saukowa a lokacin hakan yasani fita daga dakin zuwa wurin maria don in duba halin da suke ciki.
A daki na same su bata yarda tabar yaran sun fito koda falo ba don ruwan da ake shekawa a safiyan .
Tana ganina ta fara gaidani kamar yadda nake kiranta da maman kid's haka na ambata mata ina zama nake tambayan ta ya suka kwana tace lafiya sai dai Abbanane jikin shi da dare ya danyi zafi kadan.
Tabashi magani da safen nan taji zazzabin ya sauka nace a jikin shi nace ai da bakuyi mai wanka ba yanzu.
Ina daki har ta shirya yaran suka fito cin abincin sai lokacin na tuna ban leka hjy ba ranan .
Koda naje na same shi dakin suna hira nayi sallama na shigo Nafisa tana kwance saman dogon kujera har lokacin tana barci bata tashi ba.
Mama Asabe ne ke fadi ai nace hjy yau bamu ganki ba tun dazun dan murmushi na sake a fuskana ina fadin Abbana ne baida lafiya yau na dan tsaya dubashi.
May ya samu yaron kuma ta sake tambayana, hjy kuma tana fadin waye ake kira haka cikin yaran ?
Bani kadai ba har yaya saida ya dan kalli mahaifiyar tashi don jin tambayan da tayi a lokacin.
Kafin wani cikin mu ya bada amsa sai mama Asabe tace karamin wanda ake goyo shine da wanan sunan.
Ikon Allah sunan shi wa ke nan ake kiran sa da Abba shiru nayi ina mamakin ta a raine sai shine ya bata amsa da Abubakar yake ai.
Sunan mahaifinta ke nan ka sakawa yaron ashe ai na fada maki tun lokacin da aka haifeshi Abubakar na saka mai.
Amma ai baka fada min sunan mahaifinta bane ka saka mai ko zaiyi magana mama Asabe ta amsa da fadin ko ba sunan shi bane tunda haka sunan yake sai ta kirashi da Abbanta don sunan mahaifintane haka ?
Umhumm kawai hjy tace tana kawar da kai gefe daya ganin haka yasa na mike don barin dakin sai mama Asabe ke fadin.
Allah dai ya bashi lafiya da dukkan musulmi baki daya muka amsa da amin ina barin dakin.
Wanka na shiga na fito na tsaya shiryawa hakan ne ya dan daukeni lokaci har yakai ga shigowa dakin ban gama shiriba.
Fuskana babu walwala ina mai jin zafin maganan hjy datayi kan yarona ko adduan samun lafiya bai samu ba a gurin ta.
Yana shigowa ya kalleni ganin yanayi na yake fadin ni zan fita akwai inda zamu tafi da Nasir yau.
Kayi break ne na tambaya daga inda nake zaune a gaban mirrow na yace yanzu dai zan fita nayi ina son zanje gida yau in gaida kawu na fada.
Ki bari sai idan na samu lokaci mu shiga tare don ina son zuwa mu zauna dashi nima amma kasan mamu bataji dadi ba tun shekaran jiya ban lekasu ba .
Kina magana kamar wace ke cikin bacin rai mana ta fada a daidai lokacin daya kai kofan dakin .
A kan me raina zai baci zancen mama kikewa wanab daure fuskan kaima a kanshi zaka hanani zuwa gida na tambaya.
Kafin ya bada amsa nace akan me zan daure fuska tunda bani tayiwa maganan haka ba kuma ai da zaka saka sunan bakai shawara dani ba da sai ince a saka na kawuna.
To ni na saka na surikina amma ai ba aso ka saka din ba ya dan kalleni ya girgiza kai yana fadin Allah dai ya raya min yarana yasaka masu albarka.
Ya juya ya fita bin bayan shi nayi da kallo tare da jin wani takaici a raina naso yau in je gida in duba su mu dan kebe da mamu kan abubuwan da suka faru.
Ban fito ba don na karbi dana muka kwance tare a dakin haka yasa ban fito ba sai wajajen sha biyun rana ko shi sultana ce ta shigo da kuka dakin na falka.
Muka fito tare zuwa falon lokacin ne maria ke fada min kamar taga merry ta shigo gidan nan don taga wasu mata sun fito part din ta dazun.
A raina nace nasan za a rina shigowan Atika ya dauke min hankali ban kara bi ta kan zancen merry din ba koda gaske ne ita din ce.
Don Atika dana gani saboda koda mukazo kasan tun lokacin mun samu tana bauchi sunyi bukin kanen mijin ta su biyu a can.
Mun jima da Atika a dakin muna hira kafin mu fito zuwa cin abinci a falo sai lokacin na tabbatar da zuwan merry din da muke kwankwanton zuwan ta garin.
Da fara, a a fuskana na yi mata sannu da zuwa ta amsa min da kyat ganin haka yasa na share ta don ni ba lokacin ta nake dashi ba yanzu.
Ban kuma koma dakin su hjy ba don saboda cin fuskan da tayi min saboda kawai sunan mahaifina dataji yaron dashi.
Bayan mun gama cin abinci na kai Atika dakin don ta gaida ita da jiki suna zaune sunyi shiru a dakin da gani kowan su yayi zurfi a tunanen wani zance ne muka shigo dakin.
Sai mama Asabe ke fadin kai bukar ya jikin naje dubashi akace kuna barci tare dashi a dakin.
Na dan juya ina kallon ta tare da fadin yaji sauki ai mama nagode komay hjy ta gani can tace an fada ma maza na rakin ciwo ne halan mai rakin ciwo.
Dan murmushi nayi kawai ina fadin wanan kawatace tun na yarinta yanzu suna garin nan ne da mijin ta zaune.
Ohh itama yar bauchin kuce ashe Nafisa da tunda muka shigo sai a lokacin tayi magana take fadan haka.
Na dan juya inda take ina fadin kin tashi ke nan don iyakata da ita dan guntun murmushi kawai tunda na fahinci tsanata a garesu

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login