Showing 186001 words to 189000 words out of 419207 words

Chapter 63 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1410

ta bangaren ki ita taje ta zauna da yaran nan a madadin ki gidan.
Hawaye ta soma tana fadin da wani zanji yanzu da yaran da na kasa fahintar su ko da Alh da ya nuna min dani da babu duk dayane a gidan sa ko da abinda ku yan uwana kukai min ?
Yanzun dai a bar wanan zancen mu samu ki koma dakin ki ki zauna cikin iyalin ki shine mafita a garemu yanzu.
Ita gurin ta yanzu bai wuce taga ta koma dakin ta ba kamar yadda kawun nasu ya fada in yaso daga baya sai ta san inda ta bulowa zancen.
Don har yanzu bawai ta yarda da auren umar da salma bane a cikin ranta don ba zata yarda ta hada zuri,a da fakirai ba tana ji tana gani.
In ma auren zaiwa salma ai bata rasa masu sonta ba da aure amma ace wai yau almajirin su shine a matsayin surukin ta haba dai damay duniya yai kama ?
Hakama ba zata taba yarda da saka fatima a cikin dakinta ba nan gaba ta zamo mata annoba kamar yadda uwarta ta zamo masu yanzu.
Yadda kawun nasu yace haka ya faru sun samu Alh da sun bashi hakkuri yace shi baida matsala fa indai ta amince da bukatan shi a zauna lafiya.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:13 - ??5惙5惙5?: INA WA YAN UWA DA ABOKAN ARZIKI MURNA SALLAH UBANGIJI YA SADA MU DA RAHAMOMIN SA ALLAH YASA MU DACE AMIN HAPPY EID MUBARAK TO ALL MUSLIMS UMMAH ???a???a???a


Tun fitan su hjy ban daina kukan da nakeyi ba sai manjo itama ta dauka tana fadin yau yar marainiyar Allah akewa haka ?
Idan sun san ba zasu rike muna ita amana ba su bamu ita mu tafi da abin mu don mu bamu gazawa da ita.
Su umma suna bata hakkuri ganin haka yasa Addah yi mun fada na daina wanan kukan da nake kada injawa kaina ciwo kokuma so nake manjo ciwon ta ya tashi ne ?
Sai kuma ta koma fadin kina wanan kukan haka anya kuwa fatima zaki iya kwatarwa kanki yanci a gidan miji da wanan shegen kukan da kike yi haka.
Rarashina suka dinga yi har na lafe na daina kuka suka koma hiran hjy da yan uwanta da suka zo suka kare haukan su sai da suka gaji.
Mama saude tace godiya ga Allah yau da bada yaya akazo garin nan ba da munji zance a gurin ta yadda take hassada kan wanan zancen.
Umma tace saidai ta mutu don da yardan Allah fatima taci gaba ke nan a rayuwan ta manjo tace Allah yasa, Allah yasa umman Atika.
Daga nesa ya tsaya ya kira Murja dax muke tare don itada Atika sune a wurina bata ko leka gidan Aisha ba tunda aka kaimu.
A falo ta samay shi tsaye yana jiran fitowan ta, yace kira mun wanan yarinyar da wani babba nata tace fatima yace mata eh a dake kice ina jiran su a falo ya fada fuska a daure.
Gabana ya fadi dam da murja ta shigo tana fadin sakon nan dai Addah ta shiruani muka fito tare daga dakin.
Yana zaune ya hade hanayen shi guri daya ya dora saman cinyoyin shi tare da dan zakudowa gaban kujeran kadan .
Da ganin sa kasan yana cikin damuwan a rayuwan shi ba sai ka tambaya ba ya fada sosao don tashin hankali da yake fuskanta.
Yana ganin yace mama sannun ku da kokari ku zauna magana nake son yi daku nace a kiraku samun wuri mukayi muka zauna ina a takure naji yana gaida Addah a mutunce yace bayan sun gama gaisawa.
Mama dama nace ai mun magana daku ne don ina son zuwa gobe karfe takwas na safe zamu bar garin nan don gujewa fitutunun da suke tasowa a tsakankanin iyayyen mu.
Zan koma bakin aiki na a can inda nake zamu tafi a gobe idan Allah ya yarda don haka a hada mata duk wani abinda take bukata a tare da ita musanman takardun ta na karatu.
Sai dai bayan shi ba zamu tafi da komai ba duk a nan zamu barshi idan akwai abinda take bukata za a iya aje mata nan gidan idan watarana mu shigo tayi amfani dashi.
Addah tace amma dai za a hada mata tufafinta ko yace har su mama idan munje can zan saya mata wasu sai dai tana iya diban kadan ta tafi dasu din .
Gobe karfe takwasa na safe jirgin mu zai daga daga kano zuwa can don haka sai ayi duk wani abinda ya dace don Allah da wuri.
Sai in akwai wani abinda kuke bukata a yanzu sai a sanar min a sawo don amfanin ku ko ya fada karshe.
Da sauri Addah tace wallahi babu komai sam barka mun gode kwarai a dai rike muna yar marainiyar Allah amana idan kuje can ita kadai muke gani mu tuna da mahaifin ta a yanzu.
Insha Allahu kada kuji komai kudai yi muna addu,a don shi muke bukata a gare ku tace insha Allahu.
Ya kara mata godiya yana mikewa ya fita a nan ya barmu saida ya fice daga falon muka koma daki mun samu suna jiran dawowan mu suji abinda ke faruwa don hankalin kowa a tashe yake da farko.
Bayan mun zauna ne take labarta masu yadda sukayi sai murja tace wai ana nufin har kayan ki a nan zaki barsu ba zakije da komai ba ?
Addah tace harsu yace a diba kadan don Allah kada a dauki masu yawa idan sunje can zasu saya sai umma Atika tace a dai saka mata hijjab da zani don sallah a can .
A cikin daren nan suka kira mamu suna sheda mata don haka ta shirya mun duk wani abinda zan bukata na tafiya a cikin daren nan.
Mamu ta nuna bata san da zancen ba sai dai batayi sanyi a gwiwa ba wurin daukan duk abin da tasa zan bukata a can ta cusa mun su a dan karamin jakkan trolley .
Karfe hudu suka tashi kafin a tayar da sallah duk anyi wanka an shirya yana fitowa sallah sukace ya kaimu cikin gida don inyi sallama da mahaifiyana.
Wani yasa ya kaimu sai ganin mu akayi mun shigo ashe mamu bata fadawa kowa ba nan dai muka samu kebewa da mamu tace to sayadi zaki shiga sabon rayuwan mai kama da incin kai kamar kuma bauta.
Kiji tsoron Allah a duk inda kika samu kanki ki sani aure bautane na ubangiji don Allah sayadi kibi mijin ki sauda kafa ki girmamashi ki bashi hakkin ki daya rataya a kanki a duk lokacin daya bukaci hakan.
Ki kula da ibada kada ki sakaci da rikon ibandan ki komai ritsi komai wahala ki rike ibadan ki kada naji wani abu akasin haka daga gare ki .
Sauran magana zamuyi a waya idan kun isa don nasan ba zai barki ki zauna haka ba waya ba ubangiji Allah yai maki albarka ya baki zuria masu albarka.
Kuka na fashe dashi duk da muryana daya dakushe don kukan dana sha kaina kamar zai tsage gida biyu Addah ce ta shigo dakin ta samay mu har mamu kuka mukeyi tace haba maimuna maimakon ki bata karfin gwiwa sai kuma kema ki zauna kinawa yarinya kuka haka ?
Nan ta tsaya tana fadin ai da alama yaron arziki ne don jiya yadda ya nunawa mahaifiyar shi cewa amana yar nan take wirin shi ya isa a gamsu dashi mu dai fatan mu Allah yasa muce gwamma da akayi .
Yanzu taje ta sallami wanan tsohuwar idan ta dawo taci wani abu kada tabar gida bataci komai ba ita ta riko hannu na zuwa part din Amma da mamaki muke kallon shi don ba wanda yasan yazo gidan .
Kasa na zube kamar bani ba gaban Amma ina hawaye tau A ruwa Allah yayi yau umar zai rabamu dake.
Kije kiyi hakkuri kinji a zauna lafiya yi nayi bari na bari manya sukace dashi ake kama miji kada inji ko in gani kin canza ga tarbiyan da muka sanki dashi.
Shi dai yana zaune yana shan tea din dake hannu shi ta juya gurin shi tana fadin sadsuki Allah ya baka ikon rikon Amana kaji .
A kwatanta adalci ya mike ba tare da yati magana ba yana aje cup din tea din data hada mai a gaban ta yace zamuje mu sallami daddy lokaci yana kurewa.
Ya fara fita ya barni a gaban Amma saida Amma taga fitan shi tace ke ki zage kada ki zama raguwa komai ya saki kiyi yadda ya dace idan ya haneki da abu kada ki yarda kiyi shi .
Idan kinyi haka kin gama samun kan mijin ki sadauki mutum ne mai saukin kai ga wanda ya fahince shi.
Ta miko mi cup din tea din da take sha tace karbi nan ki kurbe duka ki bani kofin shima haka nai masa yanzu don da haka yayi niyar tafiya baici komai ba kada ki yarda kina barin sa da yunwa kinji ko ?
Karban cup din nayi na sha ruwan tea din na mika mata kofin ta karrba mikewa tati muka fito tare a kofan falon muka hangoshi yana jiran isowan mu.
Tare dashi muka shiga yana gaba ina binsa a baya kawu yana ganin mu ya fadada fara,an shi yana fadin.
Har kun fito na gode ma Allah daya nuna min wanan ranan ko yanzu burina ya cika a kanku sadauki ka rike amana kamar yadda kaimun alkawarin rikewa.
Yace insha Allahu daddy zan rike ta dauki takardun ta kawu ya tambaya ?
Kallona ya danyi nace cikin muryan daya dushe mamu ta hada min duka to Allah yaba da sa,a yasa a dace mukace amin sai ga waya an kirashi ya dauka yana fadin gani tafe Nasir.
Nan muka fito sai Amma tace mu sallami hjy maryam haka yasa muka je kofan nata ni kadai na shiga suna zaune da wasu mata da basu tafi ba da gani a nan suka kwana matan.
Tana ganina tace fatima lafiya na ganki da sassafen nan haka tare da kashe ni da idanuwan ta duka..
Cikin wani irin murya nace nazo muyi sallama ne maman ikilima zamu tafi tace ina cikin kara fito da idanuwan ta waje don mamaki.
Zamu tafi tare da yaya can inda yake aiki gabanta ne yai wani mugun faduwa tace england Fatima kina nufin dake zai tafi ko mai ?
Muryan Amma ne daga kofa tana fadin ki fito yarnan jiransa akeyi da kyat hjy maryam ta iya controling din kanta ta fito daga part din ta sai ganin mutane tayi sun cika an rakomu dole ta wayance a furin har bakin mota aka raka mu ina kallo muka shiga baya har kawu yana wurin da kowa na gidan.
Ban san Aliyu yana cikin motan ba sai muryan shi naji yana fadin kai amarya kukan ya isa haka mana kamar mun dauko amaryan kwace.
Kada tayi shiru mana tayi tayi ta gaji ta kyale a can wa zatayiwa kukan munafunci a nan habbib ne yake fadin haka daga gaban mota inda yake ja.
A,a a bros kana jin shi fa ya fara fada maka da mata tun yanzu ?
Dan murmushi naji ya sauke tare da dora hannayen shi saman nawa yana fadin ina jin shi ka kyale shi na bashi bashin na yau.
A hankali yake murza yan yatsuna alaman yana rarashina ke nan sai dai miskilanci bai barshi yayi magana ba.
Wani itin yarrr nake ji har cikin raina yaushe rabo da wani namji ya rikeni haka tun ina yawo da dan buje a cikin unguwa a misau.
Mun so makara muna zuwa bami tsaya jiran komai ba a gurguje mukai sallama dasu inda yaya Aliyu yake ce min zanganshi bada dadewa ba zai shigo haka yasa na danji sanyi a raina.

Salma bata samu ganin mijin ta ba sai washe gari da baki suka watse a gidan, gidan ya rage sai ita da kawayen ta biyu da suka shigo mata su suka tayata gyara ko ina na gidan bayan tafiyan bakin .
Har suka tafi Ahmed bai shigo gidan ba sai wajajen sha biyu saura na dare tana zaune a dakin ta taji motsin shi ya dawo yana rufe gida.
Dakin shi ya nufa saida ya watsa ruwa ya fito ya dade a falo tana jin motsin shi sai can ya nufo dakin nata.
Kamar yadda yai tsamani zai samay ta hakan ya samay ta kwance a takure a guti daya ya tsaya daga kofa ya karewa yadda take kwance kallo.
Har zai juya ya fita daga dakin ganin tayi motsi yasa shi dan dakatawa yana fadin baki barci ba ke nan ki tashi ina falo ki samay ni.
Ya dan jima da fitowa sai gata ta fito tasha uban kwaliya sosai kallon ta yayi ya kawar da kanshi gefe daya.
Karsowa tayi cikin falon ta dan tsaya nisa dashi kadan ya nuna mata kujera da hannu shi alaman ta zauna.
A takure ta zauna din ya dan dauki lokaci kafin yace salma kike ko don ni kin san ba sanin sunan ku nayi ba sosai musaman yaran dakiku din.
Dago kai tayi tana kallon shi da mamaki yau ita Ahmed zaice bai sani ba mutum da kusan ko wani sati yana gidan su do yin wani abinda ya shafi gidan.
Yace kina mamaki na ko kada kiyi mamakin hakan don ba abin mamaki bane.
Tun lokacin da hjyn ku ta nuna bata sona tare da Alh na tsani duk wani dan dakin naku.
Din na lura kuma baku son kowa ya rabi Alh don wani tunane naku can na daban yanzu dai va wanan ba don kinci albarkacin mai albarka a wurin na.
Ina fatan kin san gidan wanda kika shigo ma,ana kin san ko waye Ahmed dan almajiri kamar yadda hjyn ku take fada ko yaushe.
Kamar yadda kika sani sunana dai Ahmed din idan kinga dama zaki iya kirana da Ado Almajiri kamar yadda kuka saba da shi bai taba damuwana ko kadan.
Don Almajiri ma mutum ne mafi daraja a wurin mutanen da suka san hakan irin su Alh namu don yasan daraja da mutuncin amajiti kai ba almajiri kawai ba Alh yasan darajan dan adam da ace yaran shi zaku kwaso halayen shi da gidan ku ya zama gidan kwatance a gurin tausayi.
Naso ace fatima na aura kamar yadda naso ta tun farkon ganina da ita a gidan Alh badon saboda komai ba don halin mahaifiyar ta dana sani kyawawa.
Hjy maimuna mutum ce da tasan yakamata da badon nasan kan gidan Alh ba sai ince uwa daya uba daya ya haifesu ita da Alh din.
Dago kai tayi ta kalle shi a karo na biyu yace yes nasan zakiji zafin magana na sai dai yana da nasaba da abinda yasa na zaunar dake nan yanzu.
Da farko naso yi watsi da zance auren ki dayazo min a bazata lokacin da nake jinyan rashin fatima a gare ni sai zancen auren ki yazo min kwatsam da rana tsaka banda labarin hakan.
Da ace wurin da zan iya gardama ne da na hutar da hjyn ku da tazo gida tana min cin mutumci data san abinda ke raina da batazo ba a lokacin.
Hawaye ta fara don tasan komay ya fada mata taci hakan agare shi don ita kanta kafin hankali yazo mata hjy tasha turata tai mashi rashin mutunci.
Dan murmushi ya sauke dayaga tana hawaye yace a yanzu kan zaki iya fidda hawaye son ranki sai dai ki kwatar da hankalinki don Ahmed ba maci amana bane ko maimanta alheri don kinci albarkacin Alh da darajan shi a gurina.
Ba zan taba kallo ki da ido cin amana ba saudai ina fada maki abindake zuciyana ne a yanzu don ki fake sharudan da zan fada maki.
Dan sanyi salma taji a ranta don jin kalamshi yace na karshe yace ki saurareni da kyau kiji abinda zan fada maki idan kin kiyaye mu zauna lafiya idan baki kiyayye ba mu saka kafan.wando daya dake don dai kin san auren mu babu zancen saki a aure mu.
Ns farko dole ne gare ki ki tsabatace gidan nan tunda safe idan gari ya waye haka kuma zaki hada mana abin karyawa kafin in fita karfe tara na safe.
A ka,idan gidana ban daukan yar aiki matata itace zatayi mun komai daya shafi rayuwan mu don ta dorawa yarana tarbiyan daya dace.
Fuska ta bata don antabota soai yayin da tabi fadin gidan da kallo yace yes haka ra,ayina yake don kinsan ni da kauye ne..
Haka kuma ya zama wajibi gareki ki kare min mutuncin ki yayin da zaki fita ko wani bakon namiji zai shigo a gidan nan ko wanene kuwa.
Yasan halinta na rashin son saka sutura

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login