Showing 381001 words to 384000 words out of 419207 words

Chapter 128 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1461

IDRIS MAKAWA
17/11/2021, 07:22 - ??5惙5惙5?: Mahaifiyar ta ta kira cikin kuka tana fada mata yadda sukayi dashi irin koran wullakancin da yai mata ya hankado ta daga part din.
Har ta kare fadi hjy sabuwa bata samu bakin magana ba sai da taji yar nata tayi shiru tace.
Amma samira anyi yar banza kikaki yi mai koda karfin tsiya ba namiji bane idan kin masa tsirara ki ka hayesa ai dole ya baki hadin kai ko baiso ba daga nan komai ya kankama a tsakanin ku.
Umma baki ga yadda yai min bane kike fadin haka wallahi ya rike mu sosai daga shi har yan uwan shi kan maganan wanan matan mahaifiyar su.
Umma shiyasa naso ki bari tun farko mubi wanan abin a sannu har ya sauko amma kika zo da rigima da uwarshi gashi yanzu komai ya kara lalacewa kuma.
Rufa min baki danazo da rigima don wa nazo ina don kine don abu ya kwabe yanzu zakina ganin laifina ni kadai.
Duk wa yaja wanan abin haka idan bake ba ni yanzu kin fara ban haushi wallahi ace yarinya kamar ba mace ba tana fadin hakan ta kashe waya a cikin haushe.
Samira hankali tashe ta kara kiran uwar bata daga wayan ba don takaicin yarinyar da take ji saida tayi mata kira uku gana hudu ta dauka a hasale tana fadin ki ban lokaci mu san abinyi nan gaba.
Don wanan ne daman da muke dashi a yanzu kafin ya kubce muna don idan ya koma bamu san ranan dawowan shi kasan nan ba kuma.
Ta amsa da don Allah umma ki san abin yi do nima ban son ya kubce min a yanzu ba tare da mun shirya ba.
Da wanan sukai sallama ta dan kwantarwa yar nata da hankali hakan yasa tadan ji sanyi a zuciyar ta.
Ana cikin hakan Nafisa ta samu sallama don jikin ta yayi sauki habbib yana dauko ta daga asibiti gidan kawu ya nufo da ita.
Tana ta turo baki gaba alaman bata son zuwa can tunda taga sun dauki hanyar gidan kawu din.
Yana kulla da ita saidai bai bata fuskan da zatai mai korafi ba kan hakan don dole ta kyale ba don taso ba.
Koda suka shiga gidan kawu din part din Amma ya nufa da ita bayan sallama suka gaisa ana mata sannu da jiki tana amsawa da kyat ta hanyan nuna hakan bai mata ba a lokacin.
Muryan habbib ne ke fadin tsohuwa ga Nafisa nan an sallamota daga asibiti zata zauna a gurin ki nan har abubuwa su koma daidai ta koma part din su.
Amma ta dan murmusa tana fadin banda abinka ba don abubuwa suna zuwa haka a gidan nan ba har sai ka kawo Nafisa nan da kan ka ai nan din na kowa ne a gidan nan.
Hakane Amma a daita hakkuri damu don Allah ya fada yana mikewa don barin su a lokacin don a ranan yake son komawa abuja.
Yana fita Nafisa na inda take a rakube cikin rashin sake jiki don ita bata jin zata iya zama a wanan part din yadda suke nufi ta zauna a wurin Amma din don su a ganin su hakan shine daidai.
Fitowan murja a daidai lokacin Amma take fadin yauwa yar albarka kinga dauki kayan yar uwan ki ki shiga mata dashi daga ciki don a nan zata zauna har komai ya daidaita.
Duk da suna maganan a dunkule ta gane me suke nufi da hakan wai a nufin su sai lokacin da har komai ya daidaita tsakanin iyayyen su mahaifiyar su ta dawo duk tana zaune a gurin Amma din.
Ba yadda ta iya dole haka ta mike tabi bayan Murja kamar yadda Amma ta umurce ta zuwa ciki.

Ya kasance hutun da aka samu yana dan tsowo don hakane muna waya mamu ke fada min cewa ya kamata mu shigo mu duba hjy don jikin nata a lokacin babu dadi gaskiya.
Nace mamu naso hakan saidai yaya din ne nasan a yanzu yana da wuya ya barmu mu shigo Nigeria zan dai gwada tambayan shi mu gani.
Ki daiyi kokarin hakan koda bazai bari kizo din ba don yasan kin damu da al,amarin kema.
Don duk iyalan su Aliyu sunzo har na habbib dubata kinga ya kamata ace kuma din kunzo idan da halin hakan ai.
Hakan da mukayi da mamu yasa na buga mai waya bayan mun gaisai ne ya tambayi yaran da kowa nake rokon sa akan ya barmu mu shigo tunda muna hutu mai tsawo mu duba hjy da jikin.
Tunda naji yace zahra ina kike son zuwa da yaran nan yanzu tafiyan ku a yanzu haka kinsan abune mai wahala gareku dani ma.
Yaushe zan dawo nan bayan kin san abubuwa sun min yawa a nan nace na bar aiyuka na zo daukan ku zai zama wani matsalan kuma.
Nace sai inzo dagani sai Abbana sauran in barsu da maria a nan har in dawo .
Da sauri yace kina da hankali kuwa zahra yaran ne zaki bari da yar aiki harsu hudu zahra kina da tunane kuwa ?
Yaya kayi hakkuri don Allah nima banyi wanan tunanen ba na fada gani nayi dai hakan bai kamata ba ace komai nisan wuri hjy tana cikin wanan halin kuma ace kai naka iyalin basu zo ba .
Wanan zahra matsalanane ban son zuwan ku kasan nan don irin abubuwan dake tasowa daga baya idan kunzo tunda har yanzu bawai hjy ta fasa halin ta bane kema kin sani.
Shiru nayi ban iya magana sai can nake fadi a sanyayye a gaida kowa a gida ya amsa shima cikin wani yanayi da zasuji.
Wayan na kalla jin ta kashe ina sauke ajiyan zuciya a hankali tare da furta kai ni wanan lamarin Allah dai yai muna mafita akansa .
Don wani fannin idan na duba gaskiya yaya ya fada kan matsalolin dakan taso daga wurin hjy din idan ta ganmu a kasan.
Koda mamu ta tuntubeni da maganan fada mata yadda mukayi dashi nayi tace kuma ya fadi gaskiya don hjy bata fasa halin nata ba gaskiya.
Ko tana asibitin nan mun tafi gaida ita bamu dawo a cikin dadin raiba don sai da suka taba fitina da hjy maryam a can.
Cewa tayi maryam din tana farin cikin barinta gidan har tana gallazawa danta don taga bata nan tana wullakanta mata da dacewa Nura.
Nace kin gani mamu balle nida suke hake dani kan wanan amaryan tasa suna fadan wai muke asiri muka shiga tsakanin su .
Salma ke fada min hakan wai hjy sabuwa taje asibitin gaida ita ranan kuma da bata hakkuri kan abinda ya faru a tsakanin su shine suke maganan wai sun fahinci aiki saka hannun ne akai masu har hakan ya faru.
Kaji kuma wai sai yaushe ne hjy zata daina irin wanan halin na daukan wani ne yake jufanta da zaman lafiyan data kasa nemawa kanta a gidan tane ?
Mamu ai kinsan wanda bai barwa Allah lamarin sa a kullun ganin yake kowa yana aikata irin abinda yake aikatawane a kanshi.
Tace hakane baida kin nuna mai sha,awan son zuwan dubata din ba kuma yanzu yasan da hakan bawai laifin ki bane.
Mun bar wanan zancen shima bai sake maganan kan hakan ba dani har aka sallamo hjy bawai don taji sauki din ba suka dawo gida da ita don zaman asibitin babu dadi.
Jin hakan yasa su gaba daya dawowa a lokacin don sanin halin hjyn dana hjy sabuwa dayayi saboda hakan ne ya dawo garin.
Suna dawowa gida da ita ya bude part din mu suka shiga a nan aka gyara mata dakin da zata zauna a ciki.
Gaba daya kowa ya fita zancen wata samira da yanzu suka kara ganin bbakinta sosai a gidan suna ganin itace mussababin jefa mahaifiyarsu a wanan halin duk da yawan kula da hjy sabuwa keyiwahjyn a yanzu .
Na kokarin ganin ta wanke yarta daga wurin su da mahaifiyar su din ko abubuwa zasu zo da sauki a garesu.
Washe gari da dawowan hjyn gida daga asibiti merry ta sauka kasan ita da yarta Queen wace tazo masu a bazata.
Basu ba harshi yayi mamaki matuka da ganin merry din Nageria a wanan lokacin don baisan da cewa zasu zo kasan ba shima.
Itako merry da biyu ta zo garin don ta sada Queen data dameta da son sanin dangin mahaifinta wanda a yanzu taga dacewan yin hakan a garesu.
Sai gashi kuma wani abokin karatun su daya san yaya umar din yana fada mata irin masana,antar dashi umar din ya buda yanzu a Nageria.
Wanan abinda taji ne ya tayar masu da hankali sosai ta gane yanzu umar din yana boye mata wasu abubuwa daya dangance shi.
Idan bata dauki mataki ba sannu a hankali zai gujesu daga ita har yar tasu nan gaba idan ta kyale hakan zai iya haifar masu da matsala.
Duk da yanzu tasan umar din yana da wasu yaran da ya haifa bayan nata yar wanda hakan yana matukar kara bakanta mata rai sosai.
Da zata shigo gidan gaba daya ko ina na gidan gaba daya ya canza mata sai bin dayan part din dats ga an gina takeyi da kallo wanda ita a ganin ta ginan da akayi din take ganin bai dace ayisa a cikin gidan ba ma.
Da tako dadaya suka shigo gidan a daidai lokacin da umar din yake zaune da yan uwan shi suna karyawa da safe tare da yin magana kan matsalan mahaifiyar su din don samun mafita.
Takon da sukaji din ne ya shagaltar dasu kallon mai shigowa a lokacin sai merry din suka gani tare da yarta kamar a mafalki a lokacin.
Gaba daya kallon su da mamaki ya koma gareta ga wani shegen shigar banza da tayi dan bujen data sako iya cinyarta ya tsaya mata.
Sai Queen itama shigen shigar mahaifiyan nata tayi ga kansu dake nuna suna cikin halin takaban mahaifin ta da aka aske shi gaba dayan su suna kuma saye da bakaken kaya a jikin su.
Kunya da nauyi suka lulube yaya umar a lokaci guda na wayan shigar banzan da merry din har yarsu suka shigo dashi a lokacin.
You are wellcome Aliyu dake washe baki yanace masu sannun su da zuwa a lokacin.
Hannu ta dan daga mai mai alaman amsawa tana nufin gurin mijin nasu takai mai hug itako Queen ja tayi ta tsaya tana binsu da kallon mamakin kamanin su da ubanta a lokacin.
Dan hannu habbib ya daga mata tare da fadin zo nan yar mu kece kika girma hakan bamu sani ba yana dan murmushi.
Jin umar bai mayar mata da martanin huging din ta ba har lokacin yana zaune a guri daya.
Dan dagowa tayi da mamaki a idon ta tana kallon shi yace daga ina suke haka ne ?
Tambayan ya bata mamaki yace eh dole in tambaye ki don bayi dake kan zuwan naki ba.
Maganan nasa ya bata mata rai sosai saidai ganin yan uwan shi a gurin yasa ta dake tana fadin mamaki muke son baka ai.
Kayan su da driver gidan yake jawowa zuwa ciki yasa suka maida hanka???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?li a banda umar da yake jin har yanzu a ranshi ya muzants sosai da hakan.
Mikewa yayi zuwa cikin dakin shi har lokacin merry tana duke ta da dafa kujera tana mamakin sauyawan komai a ranta.
Key din dakunan gidan ya fito dasu a hannun shi ya nufi wani daki yana kokarin budewa don a saka kayan a ciki dasuka zo dashi.
Yana budewa ya dawo falon sai lokacin ya samu daman rungumar yarsa Queen a jikin shi yana maijin dadin zuwanta nan kasan shi na haihuwa.
Jan Queen din yayi zuwa wanan dakin yana fadin tazo suje taga dakin da zata sauka a cikin har lokacin yana makale da yar tashi a jiki yayin da merry da kowa na falon ke binsu da kallo.
Ko wani tunane yayi a lokacin har sun kai kofan dakin sai ya juyo yana kallon merry din tare da miko mata hannu alaman tazo mana garesu.
Hakan yasa ta dan sauke ajiyan zuciya kadan ta tako a hankali zuwa gare su ya hada ya rungume su zuwa cikin dakin.
Daya bayan daya su Aliyu suka watse a falin cike da takaicin auren wanan zurian da dan uwansu yayi a rayukan su saidai ba wanda ya iya yiwa dan uwanshi maganan hakan.
Ya dan jima a dakin yana nuna mata bacin rai kan irin shigar da tayi zuwa nan din wanda bai boye mata jin haushin ta ba.
Koda ya fito ya samu babu su umar din a lokacin falon gidan haka yasa ya san sun tafine wurun masu aikin shi ya nufa yana fadin a shirya masu abinda zasuci a lokacin.
Wanka tayi ita da yarta bayan sun daidaita da mijin nata ko yanzuma bata sauya zani ba wani tsinanen rigan ta kara sakawa a jiki shima dai bakin ne kamat wancan din na farko.
Falo suka fito harshi zuwa dining don karyawa tunda tafiyan safe sukayi zuwa garin kano din.
Saida suka karya ne ya kaisu gurin hjy dake zaune a dakin ta bata san ma da zuwan su kasan ba a lokacin.
Hjy da ke zaune shigowan su saida ta dan zabura don kaduwan da tayi da ganin nasu kamar wasu babbakun aljannu take ganin su a hakan kai aske.
Shima kanshi ya zama mai dole ne tunda sunzo din a hakan ba yadda ya iya dasu don bai taba yin nadama irin na wanan ranan ba a rayuwan shi a kan auren merry din.
Yanzu ga abin har ya shafi yarshi na wanan akidar tata na shigan arnan da suka gawurta sosai itako merry din ko a jikin ta .
Wani kallo sukewa juna da hjyn duk da ya fada masu irin matsalan daya samu hjyn a lokacin saidai hakan baisa merry din ta nuna wani kulawa a gareta ba.
A tsaye kamar dokin dake ciwon ciki suka gaishe ta babu alaman wani girmamawa irin na al,adan mu ga sarakuwar nata a lokacin.
Yayin da yar jikan nata da aka tsorata da kowa tun kan tazo ta kara makewa cikin jikin mahaifin nata.
Duk da yana kokarin basarwa yana fadin taje yau ga grany din ta ta gani wacce ta haifeshi .
Hakan baisa yarinyar ta yarda taje gun hjyn ba sai ma kara boye kanta da takeyi kan hakan da yake kokatin nuna mata mahaifiyar tashi.
Tunda merry taga baida niyar fita dasu daga dakin ta juya ta fita zuwa falo kallon shi hjy tayi a cikin wani irin yanayi na ban tausayi tana fadin babawo yar nan taka tana da akidar musulunci kuwa a rayuwan ta ?
Yace mama mai kika gani kan hakan kokarin da nakeyi ke nan akoda yaushe don ta fahinci addinin mu.
Ido hjy ta runtse a karo na farko take ganin gaskiyan kawu a yau kan abinda yake shan fada mata koda yaushe game da dan nasu.
Har ya fita da yarshi daga dakin tana zaune saman keken dake taimaka mata da ka sai mata don zuwa ban daki da dan motsa jiki saboda kwanciya kada yai mata yawa.
Falo suka samu merry dake bin ko ina da kallo na gidan wayan shine ya dauki kara ya dauka ya fita don ganin mai kiran nasa.
Bai jima da fita ba hjy sabuwa da yarta suka shigo falon a lokacin don gaida hjyn saidai ganin merry da yarta a falon yasa suka tsaya suna kallonta da mamaki .
Itama merryn ido ta tsura masu tana mamakin dalilin shigowan su gidan haka kai tsaye.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
17/11/2021, 07:22 - ??5惙5惙5?: Suna shiga dakin bayan sun karewa merry da yarta dake zaune falo tana ta waya kallon kwam suka shiga dakin da mamaki da gulman dake cin su a rai.
Don basu samu damar kebewa ba saboda ba lokaci a gurin da zasu samu magana kafin shigan su dakin da hjy take jinya a ciki.
Itama hjy zaune take da imanin ganin merry a hakan daya cika mata zuciyar ta da mamaki da tsana har lokacin da suka shigo dakin.
Amsa masu sallaman su tayi har lokacin tana zaune saman keken da aka tanadar mata don zama da laluran kewayawa a dakin.
Gaisawa sukayi ko karasawa basuyi ba hjy sabuwa ke fadin hjy jummai wanan ta zaune a falon ku da yarta wacece ita.
Naga wata katuwar arniya tayi kane kane zaune a falo tana busan iska a gidan nan kamar wata yar gida har yaya akayi wanan kafirar ta shigo gidan nan haka ?
Dan runtse ido hjy tayi daga

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login