Showing 303001 words to 306000 words out of 419207 words

Chapter 102 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1462

zaune yana jiran mu har muka shiga yaran na surutu bai kula su ba nidai naja bakina nayi shiru ban tanka masu ba.
Muna isa gidan ganin yanayin da yake yasa ban tsaya falo ba na wuce zuwa cikin dakina don nasan halin shi idan yai fushi baison aimai magana lokacin.
Muryashi naji a bayana yana fadin meya hanaki shiga dakin mama ki zauna da yara ?
Na juyo da mamaki jin abinda ya fadi nace waya fada ma ban shiga na gaida ita ba ?
Wani lalataccen kallo ya jefini dashi kafin yace za, ai maki karyane kike son fada min ko may ?
Sai maganan ya bani mamaki kafin kuma ya bata min rai saidai na danne nace hummm wani sabon sheri da munafunci kuma ake kokarin kulla min ko may ?
Ai ba munafunci da sheri ya kamata ai min ba kamata yayi ace ban kai karshen magana naba naji ya kwasheni da wani gigitacen mari a fuskana saida na duka don zafi.
Kafin yace ke har rashin kunyar taki yakai ki kalli idona ki karyata mama a gabana har kina kokarin zagin ta.
Na dago ina dafe da gefen fuskana inda ya mare ni ina watsa mashi kallon tsana karara idona yana fitar da hawaye.
Yaci gaba da fadi a daidai lokacin da Abdulsalam dake bayan shi ya yanka wani irin ihu shi kuma yana fadin .
Don kawai kina dauka ina auren ki yanzu sai ki zagi mahaifiyata a gabana har kina kokarin karyata karya zatai maki komay ?
Jin ihun Abdulsalam ya jawo hankalin sauran gaba daya sukayo kanmu suna kuka lokaci guda sultana ta kankameni tana wani irin ihu.
Nace ka maraini yaya ba tare da ka tsaya kayi bincike kan wanan maganan ba na barka da Allah wallahi dakai da duk wanda ya zugoka a kaina.
Bai tsaya ko kallon yaran ba ya juya ya barmu a gurin tsaye muna kuka muryan maria naji tana fadin madam mai yayi zafi haka yau tsakanin ki da Oga ?
Kallon ta nayi na juya zuwa dakina rike da hannun yarana dake kuka har akai magariba ban fito ba har yaran sai maria dake sintiri don laluran yara a lokacin.
Faisal autan su yaya ya shigo yana sallama ga tv na aiki a falon saidai babu kowa a gidan ganin haka ya juya zai wuce sai ga yaya ya fito daga dakin shi zai tafi masallaci ya ganshi.
Jin motsin fitowa ya juyo yana gannin yayan nasa ya fara gaida shi tare da fadin anty Fatima fa da su Abdul dazu sunce in sayo masu ball na dawo gida shine na samu ance sun wuce shine na kawo masu yanzu.
Kallin yaron da suke da shigen yanayi daya yayi yana fadin suna ciki wurin maman su ina gani daga nan ya tsaya yana kwallawa maria kira ta amsa don tana dakin su dama.
Kafin maria tazo faisal da bai san kaiba yaci gaba da fadin tare suka so muje don kada kai fada yasa ban fita dasu ba sai na barsu nace su bari naje na sayo masu ai.
Don mun dade falon mama tare dasu suna min hira yau ya juyo ya dubi yaron yace falon wa kace yace falon mu muka zauna dasu da maman su.
Mama fa ya tambayi yaron mama kyalesu tayi ita da Nafisa suka shige daki nima banso hakan da mama tayiwa anty Fatiman ba wallahi na bita daki nace sun barsu zaune su kaidai ta koreni.
Muje muyi sallah yace wa yaron yayin da cikin rashi yake maimaita innalliallahi a zuciyar shi.
Amsan ball din maria tayi tana godiya tare sukai sallah a masallacin unguwan inda yaiwa yaron fada yabar kaiwa dare a waje hakana kafin yace driver shi ya kaishi gida bayan yaba yaron kudi da murna yana godiya ya tafi.
Inda na idar da sallah na zauna ina tunane idan har hjy ta fara cin galaba akan danta zata iya fada mai magana ya yarda dashi a yanzu ashe kuwa aiki babba ya ganni a gabana.
Shine ya turo kofan ya shigo udon shi ya sauka kan sultana dake kasa yashe tana barci a gurin tayi kukan in dauketa naki na tayar da sallah lokacin sai tayi barci.
Daukan yarinyar yayi tsab zuwa kan gadona ya ajeta ya dawo saman kujeran dake gefena ya zauna.
Ya dan dauki lokaci kamar ba zaiyi magana ba can ya dago tare da ajiyan zuciya yace cikin natsuwa zarah na fada maki tun bamuzo kasan nan ba .
Na rokeki cewa ki mutunta min kowa nawa da yake nawa kamar yadda nima zan mutunta kowa naki kamar yadda ni kike mutuntani da aurena.
Sai lokacin na dago kai nace wana taba yiwa rashin mutunci a gidan mu kaf ko bayanzu ba sai wanda yaso raina min wayau ko shi sai yara yan uwana zakace na taba wani tashin hankali dasu.
Ya murmusa yace amma dai kin san tun farko inda maganan nan ya fito har zaki tsaya gabana kina kokarin karyata min mahaifiyar data haifeni a gaban idona.
Nace yanzu kuma ai ya saura gare ka don ban zama ko yaushe dan magana kadan ya hadamu ka daga hannu ka mareni ko a gaban waye .
Ni nagaji wallahi na gaji ba zan iya irin wanan zaman ba wallahi da kaje an fada ma magana baka tsayawa kayi bincike sai kawai ka daga hannu ka mareni .
Idan ke kin gaji ni ba zan taba gajiya dake ba raini ne kawai ga kowa ba zan iya dauka ba don gaba ki sani ban raina maki naki mahaifan ba bako zan yarda ki raina min nawa ba.
Raini kuma na nawa ne ba aiwa mahaifiyata ba ina ji ina gani tunda muka zo sau nawa ka shiga ka gaida ita.
Kumani data haifa kana kokarin hanani zumunci da nawa iyayyen .
Yayi murmushi ya mike tare da fadin komai zaki iya fadi yanzu ai saidai dadin abin ita maman taki tasan ban taba rainata ko mata wani abin bacin raiba.
Don haka kema nake rokon ki akan ki kara yin taka tsantsan da duk wani abinda zai jawo mama tace maki kinyi mata laifi ko wani abu da har za a iya tunzurani a kanki
Don nasha fada maki cewa kimin adalci don ni din na mijine namiji kuma yana nufin zan iya juyawa daga matsayina in koma wani matsayi a gareki don haka nake kara fada maki ki bini a sannu.
Ya mike ya fita tare da kallin yaran dake ta barcin su saman gadona hankalin su kwance ya fice daga dakin zuciyar shi tana mashi kuna.
Yana fita nakai kallona ga yaran dake kwance suna barci tausayin su ya kamani a lokaci guda ban san lokacin da wasu hawaye masu dumi suka kara sauko min a idanuwana ba.
Ina kuka ina tunanen sakani gaban da hjy tasha alwashin yi taga bayan aurena da danta yanzu in haka ya tabbata yaya makomar diyana zai koma don nasan karshe dai karbe yaran za,ayi daga hannuna abawa hjy don babu mai rikesu sai ita.
Haka muka zauna kusan kwanaki kowa sai harkan gaban shi yake a cikin mu iyakarshi in ya shigo ko kafin ya fita yaba yaran shi kulawa kamar yadda ya saba basu koda ina zaune bai kulawa da ni kamar yadda nima na dauko share shi din.
Ranan da safe ya shigo dakina ina kwace muna waya da Aisha ina ganin shi na cewa Aisha zan kirata anjima na dan juya wurin shi a gyatsire na gaida shi da kwana ya amsa ba yabo ba fallasa tare da fadin zanje lagos yau ina ganin zan kwana biyu a can .
Don haka ki kula da gida da yaran nan yasa hannu cikin aljihun riganshi ta ciki ya ciro kudi yana miko min tare da fadin wanan ki rike a hannun ki ko wani abin zai iya tasowa bana gida.
Da ka barshi tunda komai muna dashi yace na sani ki dai rike wanan din a wurin ki nace na mika hannu na karba tare da fadin Allah ya tsare.
Har yakai kofa nace yaushe zani bauchine ganin su yanzu muna batun share wata daya da wani abu a kasan nan fa.
Idan na shirya zan fada maki in lokaci yayi ya fada yana fita daga dakin ganin bai gari yasa na kira murja mu zauna tare da ita don bata son zuwa idan yana nan bansan may yasa haka ba.
Da rana muna zaune sai ga salma tazo muka gaisa take tambayan yayan nata nace yai tafiya a ranan.
Sai naga bataji dadin hakan ba bata dai fada min komai ba nan muka zauna da ita mukai hira taci abincin rana tare damu.
Saida tayi sallah tace zata tafi nace ta bari in kira driver gidan ya mayar da ita gida na tashi na shiga daki dubu hamsin na kidaya daga cikin kudin daya barmuna na hada mata da yan abubuwa na saka a leda .
Lokacin dana rakota namika mata kudin da kayan saida naji tayi wani irin ajiyan zuciya tana fadin Fatima nagode yau kin rufa min asiri wallahi don ba karamin dadin wanan kyautar naki naji ba.
Saboda may anty salma na tambaye ta tace kinsan halin mazan nan yanzu buki ake dashi can garin su dama na kannesa shine nake son dama indan rike wani abu kada in tafi hakana hannu sake.
Yanzu kinga zan dan samu na rikewa saura har in samu indanyi dinki a ciki.
Wani irin abu naji ya dira min a zuciyana nace anty salma kina nufin shi yaya Ahmed ba zai maki wa yan nan abubuwan ba ta danyi murmushi tana fadin fatima ke dai Allah ya sauwaka yanzu ko namiji yana maka idan baka dashi ga hannu ai ragagene.
Karatun nan fatima yaya ya tsaya muna saida mukayi shi muka gama aiki dai ne yanzu ya zama fitina kuma don shi na gidana ya rantse ba zai barni inyi aikin gwaunati ba.
Jin hakan shima mijin ikilima yace itama ba zatayi ba nace anty salma haka yaya Ahmed ya koma kuma.
Tace bari kawai Fatima ina da maganganu da yawa danaso mu zauna muyi dake saidai ko wani zuwa nayi bamu samun lokaci.
Kada ki damu anty salma zanzo har gidan in samay ki mu tatauna sai dai yanzu barin zo na koma ciki na kara fitowa da wani ledan turama a hannu na kawo mata tana batun yin godiya nayi saurin bude mata motar ta shiga ina fadin ta bari sai munyi waya da ita.
Nan ta tafi ta barmu cikin tashin hankali ta barni da tunane kala kala a raina ranan


ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:32 - ??5惙5惙5?: Salma ta wuce ta barni cike da tunane haka naja kafa na koma falon na samu murja zaune tana kallon film a falon.
Ta juyo tana fadin ta tafi na amsa a wani yanayi ina zama nace ta wuce taci gaba da kallon ta sai kuma can ta juyo tana fadin .
Yanzu salma rayuwan ta ya sake gaba daya kamar ba salma ba wallahi ta hadu da mijin daya natsa mata daukan kai da izzan nan nata gaba daya.
Gashi tana mutuwan son Ahmed a rayuwan ta da bata son shi da tuni maman su tayi sanadin da ta kashe auren su wallahi.
Murja inda Allah ya tsara ma rayuwan ka idan kana da tunane sai kayi hakkuri da hukucin ubangiji ai.
Dashi Allah yayi zata zauna tace ai gara salma ma in fada maki don ita ikilima raguwace ta karshe ga aukin haihuwa kamar wata akuya.
Haba murja dudu yaran su nawa yanzu ki duba fa diya uku suka haifa fa kike fadin haka .
Nima ba gashi diyan nawa uku bane yanzu tace aike Allah ne yai maki kyauta da kari kowa ya sani kedai murja a fada a hankali kada duk shekara ki taramu gidan dan batta suna da cewan wanda zata aura.
Tace wa ni baki daiji ba da kyau fatima, waneni da rayuwa irin nasu sun mayar da kansu wani iri kowa na fada dasu kan kama jiki kamar ana kara zugasu ne suyi.
Yanzu wa zaice wai salma ta hada takarda don Allah ko karatun saida kawu da mijin ki sukai tsaye suka mayar da hankali ga karatu.
Karatun ko baka aiki yana da amfani sosai na bata amsa ba wai da niya suka bar kansu haka ba murja akwai rashin waddata yana damuwan rayuwan su.
Don kinga yanzu da zasu fara aiki ko wani sana,a mai karfi suna dan fita ko kuma kudi yana shigo masu zaki ga sun dan walwale cikin dan kankanin lokaci.
Tace amma ai kawu yana kokari dasu sosai wallahi ke dai kawai akwai battalanci a cikin harkan su.
Tun farko fa kin san komai basa iya yi da kansu yanzu sai abin ya zama masu sabo a wurin su ga lalurar yara da dawaiyarsu duk ya taru a kansu lokaci daya yai masu yawa.
Na amsa da fadin kinga ke nan dole a taimaka masu ashe tunda Allah ya hore masu yan uwa masu shi da zasu iya tallafa masu din.
Fatima yanzu ke da kanki kike wanan magana har kin mata da irin muzancin da salma da mahaifiyar ta suka dinga maki don kawai kawu ya dauko rikon ki ya kawo gidan har ya aura ki ga dan dakin su.
Murja dane wanan yanzu salma yar uwan maigidane kuma yar uwatace nima ta jini idan ba don lalacewan zumuci ba ai ni jinin su ce dama.
Ki dai bi a sannu kada kiyi zurfi da yawa don su din ba abin yarda bane da sauri.
Nace Allah yasan dalilin sakani a cikin su murja don haka da zuciya daya zan zauna da kowani su.
Kusan wanan hiran muka wuni munayi a ranan sai wani lokaci ka dan fito haraban gidan muna shan iska.
Yara kuma suna wasannin su a inda aka tanada don su suyi wasa karan budan get din gidan da akayi ya mayar da hankalin mu wurin mai shigowa gidan lokacin.
Bamu gane mai shi ba saida motan ya tsaya mukaga mata suna fitowa daga cikin motan data shigo gidan lokacin.
Gaba daya mun mayar da hankalin mu gurin su da farko ban gane su ba sai daga baya na gane ashe.
Hjyn su yayace tare da yan uwanta suka shigo gidan wallahu galibun ala amrihi na fada lokaci daya don nasan da wuya wanan zuwan idan na lafiyane haka.
Tun kan su karaso kusa damu na mike tsaye hakan yasa murja mikewa muna masu sannu da zuwa sai shan kamshi ko wacen su keyi su duka ukun.
Murja data gaida ita karshe tace a,a yar gidan hadiya kema kina nan ne ashe tace hjy nazone dazun tace kwarai naga alama ai don yanzu kowa inda yafi maski ake dafewa a lakaci arziki.
Dayan yar uwar tace yo indai za,a lakata a barka da danka aida sauki amma ina dadin a rabaka da uban dan a kumayi kokarin rabaka da dan ka don samun wuri.
Dan kallon juna mukayi a fakaice nida murja lokacin da dayan ke fadin abindai ma a filin Allah akeyin sa don kawai kwadayi da samun wuri irin na wasu matan .
Yaya zaki aure uba kiba yarki kuma dan kishiya don samun wuri na sake fadin sannu ku mama ina dan dukawa.
Tace yau fatima nice uwarki ko may ko dan mawa ya tilasta maki da ki kirani da mama ban sani ba.
Kamar ban fahinci irin maganan da suke sake min ba a lokacin sai dan murmushi nake a fuska ina nuna masu ban damu ba da abinda sukeyi sai ma na juya wurin maria dake can nesa damu da yara ina fadi cikin harshen turanci kawo su su tari grandma din su maria.
Kowa kallon yadda nake turanci zakace ko wata haihuwar America ceni lokacin.
Maria ta riko hannun yaran tana fadin oya come great her samun wuri ita wanan din wacece hjy Rakiya ta tambaya.
Aidai kin gani da idon ki idan ma ji kikeyi da yanzu ganau kike rainon ma harda maiyin shi akazo tundaga can don samun arzikin banza.
Gaba na fara yi na tura kofan falon daketa kamshi yasha gyara kamar ba mutane ke zama a cikin shi ba duk da yawan mu gidan.
Suma shigowa sukayi suka suna bin gidan da kallon yadda yasha gyara ga haduwa wai ni yaya zancen dayar matar gidan ne anty kanwar ta tambayi hjy.
Yo ina zan san inda yasa gaban sa yanzu an fitar mashi da raiga kowa yanzu ai saidai a tambayi sabbin iyayyen shi kuma.
A daidai lokacin na fito kitchen dauke da katon tire a hannuna dake shake da abin sha dana motsa baki nake jin suna wanan zancen.
Kallon kayan da na aje a gaban su sukayi tanaci gaba da maganan ta tana fadin ya barta can ke nan yazo nan

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login