Showing 123001 words to 126000 words out of 419207 words

Chapter 42 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1447

jummai tace ba tare da furta komai ba a gare su sai umar din ne ya daure yace sannun ku da zuwa ya hanya?
Wani kallo hjy ta jefa mai da yasa ya dan kwantar da kan shi kasa ba tare da ya shirya ba sukan suka juya suka tafi.
A dakin mu ta sauke su basu zauna ba don gabatar da sallah dake a kansu sai da sukai sallah ta gabatar masu da abinci.
Suna zaune suna cin a bincin mukai sallama dawowan mu ke nan daga islamiya lokacin.
Na dan tsaya waje iba magana da Aisha kafin in tunkari part din namu kai tsaye tun a kofan na fahinci akwai baki a part din don takalman roban da na gani aje a kofan shiga part din.
Ban damu ba don na dauka ire iren yan uwan su ne dakan dan leko lokaci lokaci wurin mamu din.
Murya naji kamar na Addah tana fadin kun dawo ya makarantar ina ita A ruwa din tubarkallah masha Allah yara sai dada girma suke yi .
Da sauri na nufi dakin da nake jin muryan nata na daga labulen dakin da sauri wani ihu na yanka da mukai arba dasu ina fadin wayo ni manjo na.
Na nufeta da gudu na fada mata a jiki sai kuma na fashe da kuka a lokaci daya manjo sai fadi take ni daga min kada ki karasani kin wani girma haka kamar ke kadai ake kiwo a gidan nan.
May kuma kikewa kuka yanzu kuma na kasa magana sai kuka nake na makaleta sai manjon itama ta kama kukan .
Muryan mamu daga kofa take fadin yau ka tsiya zaki dagata ki fice nan wanan shegan takar banzan da kikeyi fa ?
Barta suyi Addah ta bata amsa tana fadin kin san tsakanin fatima da babba sai Allah.
To kuma sai akace tazo ta tasa ta a gaba tanawa mutane kukan banza haka ?
Wanan ai sai ki tayar mata da ciwon ta dan Allah daga ki ba mutane guri mara ta ido kawai cikin dan share hawaye manjo tace mata.
Maimuna barta tayi abinta Allah ya nufa ta kara sani a ido ne dana tafi dana barta da dawainiyar dakon kewata a zuciyar ta.
Kai babba ba gaki yanzu tana gani ba zata cikamu da kukan banza haka kawai ?
Da kyat na banbare a jikin manjo naje wajen kiran da mamu ta kwala min a kitchen na samay ta tana dora ruwan abinci tace in kin gama shagwaban naki sai ki zo mu hada masu abinci.
Ina dan goge fuskana nace may zanyi mamu tace ki debo kayan miya ki fara jajagawa a turmi miyar kubewa zanyi.
Haka na daure na kama aiki hankali yana daki wurin manjo na matsu in gama inje in samay su a dakin muyi hira.

Umar yana tsayawa kofan gidan shi wayan shi yana kara ya dauka ganin sunan mama yasa ya furta mama kuma da mamaki karara a fuskan shi don yaga yanzun suka rabu da ita ai.
Ya dauka yana fadin mama lafiya dai ko ?
Tace na kiraka ne in fada maka ba ruwan ka da wa yan nan yan kauyen bakin na maimuna kada inji kada in gani ka barta da mutanen ta don zuciyata ta kasa natsuwa a yadda naga kana wani gaidasu.
Yace mama kada ki manta bakin gidan mu ne fa dole muyi gaisuwa irin ta musulunci ga bakin mu ai.
To ubana fada min yadda akeyi kasan ban sani ba sai ka koya min yanzu yace mama Allah huci zuciyar ki nima ina zasu ganni kuma.
Ta sauke ajiyan zuciya tace yanzu naji magana don nasan wanan makiran tunda ta fara fadin wai kakar yarta ce wai tsigar makirncin ta kulla kuma.
Na gode mama ya fada a gagauce don hango merry da yayi a garden tana murnan dawowan shi.
Ya fito motan da sauri ya nufi girin ta tare da ware hannayen shi alaman tazo gare shi a lokacin cikin so da shaukin ta sosai.
A haka suka shige ciki suna makale da junan su kamar zasu cinye juna a lokacin zaka dauka yayi wata barkatai ne bai garin.

Mamu bata bari nabar kitchen din ba sai da muka kammala aikin mu gaba daya daidai ana kiran sallah na fito don inje inyi sallah .
Bayan na idar na fada dakin na samu manjo ta idar tana jan tasbaha a hannun ta hakan bai hanani zuwa i rabeta ba lokacin.
Ta shafa tana fadin ja,ira har yanzu kina nan da shegen son jikin nan naki haka ?
Adda ta dago tana fadin ke dagata kada ki tumurmushe ta don Allah kin ganki kuwa yanzu yadda kika koma cikkkan mace dake makerin halittan ki ya gama keraki tsab.
Na mike daga jikin manjo ina dan dariya tare da fadin kai Addah ni wani girma na kara a hakan ina kamo hannun manjo .
Nace cikin yanayin damuwa anya manjo kina ko cin abinci a can nasan mugayen ban ba wani kulaki zasuyi ba ai.
Adda ta kalleni tare da dan harara tace a, a da yunwa take kwana tun bayan zuwan ki nan .
Na danyi dariya nace ba haka bane Addah wallahi manjo duk ta zube min a idona wai ina Atika da umman ta na kawar da zancen don gudun maranbarama.
Addah tace ai kuwa har kofan yaya suke da zamu taso Atika kamar ta biyo mi take ji tazo ta ganki sai mahaifin tane dai ba lafiya sosai shima tunda yai wanan hatsarin motar bai kara samun lafiya ba.
Duk sai naji ba dadi a raina don ban manta da irin halarcin da mutanen suka nuna min ba dan zama a azare danayi.
Ina like da su muna ta hira sai ga mamu ta shigo dakin a cikin hijjab din ta tana fadin watau sayadi ba zaki barsu su hutaba kin cika su da surtun tsiya tun dazun.
Ki barsu su huta har zuwa gobe tunda ba yanzu zasu koma ba sai babba ta gama ganin likita.
Manjo da ta koma min shiru shiru yanzu bata son yawan hayaniya tace ki rabu da ita tayi kewan mu ne yar nan.
Ki tashi ki kaiwa gwaggo abincin ta kin barshi a kitchen tun dazun yana sanyi manjo tace watau dai kin kore muna ita da wayau ko ?
Ina shiga part din Amma na samay ta zaune tana jan tasbaha itama na kai abincin inda muke ajewa zan wuce tace dawo yan nema yau kinga kakan ki zumudi ya hana ki tsayawa to ba inda zaki sai na more ki a nan nima.
Kinga dauko min ledan can dake aje dazun maigidana ya shigo min dashi wai ya dawo ikko haka yake tafiyan shi ba salma shi sai dai idan ya dawo mutum yaji.
Ina daukowa nace Amma wani maigidan ki ya kawo maki ko mijin ki ya dawo ne ?
Tace ja,ira kin taba ganin inda aka mutu aka daw????      

                  ! " # $ % & ' ( ) * + , - . / 0 1 2 3 4 5 6 7 8 9 : ; < = > ? @ A B C D E F G H I J K L M N O P Q R S T U V W X Y Z [ \ ] ^ _ ` a b c d e f g h i j k l m n o p q r s t u v w x y z { | } ~  ? o duniya yayan ku dai umaru ne wai ya je ikko ya kawo min tsaraba .
Na bude ledan kaya ne irin na kurmi a ciki kwakwa abarba ayaba da sauran tarkacen kurmi shake da ledan baco mai girma.
Tace ki dabarwa uwar ki don nasan ko yakawo masu nasu ba deban masu jummai zatayi ba sai dai ta aje idan ya rube ta zubar.
Nace kinga ko Amma dama duk manjo ta rame sosai da gani basu bata kulawan daya dace a can .
Amma tace yar nan ke nan azamanin nan ai diya mace kadai tasan zafin uwarta wanan sarakan zamanin babu abinda suka sani banda su mayar da uwar miji banza.
Nace bandani Amma nikan yadda naga su umma saude nawa manjo bani fatan inyi wanan rayuwan da sarakuwata.
Anya A ruwa zaki ko samu hakan gurin sarakuwar ki don babu alaman hakan zai samu sai dai gyaran Allah.
Nace ji Amma kamar kin san wanda zan aura har ki san halin uwarshi kina mun mugun fata haka ?
Tace cikin dariya kai yaro man kaza yo ni ai har na hango sarakuwar taki ko a idona idan baki sani ba san nan ke din nan da nake gani kayya a dai bar zancen don Allah.
Nace Amma Allah dai ya bar muna ke kiga auren namu nan da shekara goma mai zuwa kilama da dan hayi don ni nan kawu yace min sai na zama babban likita a gidan nan.
Kinga kuwa ai ba zancen yanzu akeyi ba ke nan tace hakane fa kinga dauki kayan ki kaiwa uwar ki kafin wa yan nan sarakunan kwadan su fito su saka maki ido.
Nace to sai da safe Amma tunda dau naga yau baki son hiran tamu dake ke tafi can tace min wa zakiwa tako hankalin ki na gun kakar ki sarai.
Na fice ina dariya da kayan a hannu na ina sauri in koma part din mu in fara ba manjo ta sha lemo da ayaba.
Na samu mamu ta gyara masu guri da zasu kwanta inda manjo tace ita a kasa zata kwanta bata hawa gadon da aka gyara masu din.
Haka yasa aka kayar mata da katifa a kasa ta kwanta a nan sai gani na shigo sai dana nunawa mamu tace in kai kitchen in aje har da safe mm ace barin dibawa manjo lemon ta dan sha.
Washe gari nayi sa,a ba zuwa school ranan a na public holiday sai aka hada muna meettime break din mu don haka zamu zauna gida na kwana biyu ke nan.
Ga mamu tayiwa merry alkawarin zamu shigo muga gidan su idan Allah ya yarda ranan ko dana tashi tun safe ban zauna ba ina aiki a part din.
Na gama abinci ne mamu ke fadin nace su Aisha su shirya don nayiwa matar yayan ku alkawarin yau zaku shigo wurin ta don ta matsa da maganan baku je ba.
Take na daure fuskana don ban son zuwa gidan ni dai har ga Allah kyaman su ma nake ji daga matar har mijin saboda arnarcin su sai nakw ganin kamar shima arne ne .
Tunda irin kayan da yake yawan sakawa irin na kafirai nake ganin kamar shi shiyasa ranan da naga yana alwala a wajen gidan mu zaije masallaci saboda gulma har tuntube nake ina waigen shi ko ya iya alwalan.
Ko ba zaki je bane kin tsaya kina wani tunane banza naki kuma kada inji ance ga abinda kikayi na rashin mutuncin a gidan nan.
Mamu ni ina ruwana dasu muje kawai mu gaida su mu fito har zan tsaya wani rashin ji kuma mamu ni yanzu na bar rawan kai fa tunda na girma.
Sai da na dan zauna wurin su manjo muka dan taba hira na shiga wanka yadi da ya kawo wa Amma tsaraba ta dinka ta vani shina saka a jikina.
Don ban taba saka shi a jikina ba sai yau na dauko na saka saboda kawai in kara burge su Addah na saka su san rikon arzikin da ake min a gidan kawu din.
Dinkin da yadin ya kara fito min da surana karara a fili ni kaina dai sai da nasan yau nayi matukar kyau sosai ba kadan ba.
Na kama jelar gashina nayi gawo dashi na nade guri daya na cushe shi san nan na daura dan kwali a kai.
Sai dana gama kallon kaina tsab na dauko sabon hijjab dina na aza saman kayan ya sauko min har kasa sosai ya rufe min kwalliyan dana bata lokaci inayin sa.
Muryan su Aisha ne a falin mu suka shigo na fito kallo na sukayi gaba dayan su Aisha tace kai amma dai fatiman nan.
Wallahi ni ban taba ganin wace ta auri hijjab kamar ki ba a duniya yanzu wanan fitan da zamuyi shine kika dauko wanan jibgegen hijab din kika saka kamar mai zuwa islamiya.
Ke kullun gaki sai kace rainon kauye dake ke kullu banga ranan da zaki waye ba wallahi kamar ba a cikin kano kike ba.
Naja na tsaya ina kallon ta a raine kafin in ce ke ba zaki gane ba Aisha may zanwa kwalliya yanzu tunda ba saurayi nake nema ba a waje.
Ki bari lokacin kwaliyana yana zuwa idan na gama neman illimina lokacin zan faso duniya ta san dani kinga lokacin masunsunina zaizo.
Kinga ko yaga surata a lokacin babu komai domin a yanzu bayyana sura bashi zaisa ka samu kasuwa ba ni dai fatana Allah ya ban na gari .
Yanzu dai ke kadai ne zakka a cikin mu zaki bimu da wanan zunbulelen hijjab din haka kamar matar uztazu.
Baki na tabe lokacin mamu na fitowa tana jin zancen mu dasu tace idan kunbi ta wanan sai ku shekara a nan tana cin ku da wanan baki nata.
Kunga ku kula idan kunje banda sai da hali don Allah kada naji anyi wani abin asha a can.
Daga haka muka fita na rike hannun fauziya don da ita zamu tafi su samir sun fita da kawu tunda safe.
Tare da Amma muka fita don ta samu wanda zai sauke mu a can tunda muka fito yaran hjy maryam suka ganmu suka tsura muna ido.
Murja tace kada ku fada masu inda zamu yanzu zasu fadawa uwar su zancen muna fita sai ga Aliyu zai fita mamu ta tsayar dashi tayi mai magana bamuji mai tace mai ba sai yace muzo mu tafi.
Har zamu zauna a baya sai naji mamu tace ke Aisha ki dawo gaba ki zauna sai su su zauna baya.
Haka mukai zaman motar sai faman kalle kalle muke na kauyanci a motar ga sanyi ga kamahin turare a ciki.
Shiru motar yayi kowan mu na gudun yayi wani dogon motsi da ba daidai ba sai can yace ke wanan hijjab din haka kamar matan malam fa ?
Haka kikaga yan uwan ki ke kullun kamar mai zuwa tafsiri dake nayi dan murmshi don na fahinci dani yake saboda ni kadaice mai hijjab a cikin mu.
Duk rawan kaina ina dan shayin yaran hjy jummai kaf din su musanman tu lokacin da naji sun taimawa mamu nake ganin mutuncin su a idona saidai ba ruwana dasu ne sai gaisuwa.
Ya dab bugi sitiyarin motar yana fadi yarinya duk zaki bar wanan ne nan gaba sai lokacin na bashi amsa da fadin ai ban fatan in bari yaya don shine tsaron mutunci na.
Ganin hakan yasa da ya sauke mu nayi mai godiya kamar yadda kowa yai masa zuciyana fam da mamakin sakar min fuskan da yayi yau ko dai don ba a gida muke bane ?
Ban ankara da inda muke ba sai da na fito daga motar tsarin gidan ya tafi da imanina sai naji kamar a mafalki nake ganin kaina a ciki.
Bani kadai ba har dasu wayayon sai da gidan ya tafi da imanin su tun a waje suka fara santin gidan dan baya naja kadan ina fadin ku ku tsaya ..
Ni dai wallahi naji tsoro ace wanan katafaren gidan wai na dan kawu ne to a ina ya samu kudin dayayi wanan gidan haka ?
Kunga kuzo mu koma mucewa mamu bamu samay su a gida ba zaifi muna alheri don ni wallahi na tsorace da wanan gidan tun bamu shiga ba gabana wallahi faduwa yake yi sosai.
Ke dan Allah mu shiga may ye na wani tsoro kamar sai damu za ayi akace maki yau sai mun ga kwam wallahi.
Aisha ke maganan tana fadi ta jawo hannun fauziya dole nima nabi bayan su inda ya Aliyu ya nuna muna hanyar shiga gidan.
Cirko cirko mukayi a wajen kofan kowa na tunane nace yanzu sallama zamuyi ko may kun dai san ba gidan musulmai mukazo ba.
Ke kika mai dashi kafiri ko jiya daya shigo Amma tayi mai tayin fura cewa yayi yana azumin thursday ne.
Nace kika sani ko nasu na kafirai yakeyi kin san suma fa suna azumin su akace .
Wai ke aka ce maki yaya din shima kafirine kamar matar shi nace in ba kafiri bane yaya ya zauna da wace bata sallah da sunan aure.
Ni kinga kallo daya da matar shi nake masu fa shiyasa ki yazo part din mu yana sallama ban karbawa don ance baida kyau ka karbawa kafiri.
Gashi da girman kai da jiji da kai ko kana gaidashi sai yayi kamar bai sanka ba kullun ba sakin fuska dashi da dan uwan nan nasa guda kusan halin su daya nake gani.
Ke ni ko kannesa su salma bance yana sake masu ba balle mu naja wani tsuki nace ni ban san may yasa mamu ke son hurda dasu ba in anyi magana tace dan uwan tane may ne may ne.
Aisha ta ja tsuki tace ke don Allah muna neman hanya kin dami mutane da surutu nace maganin yan

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login