Showing 321001 words to 324000 words out of 419207 words

Chapter 108 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1514

saude duk mun kai masu ziyara ranan kuma sunji dadin zuwan mu.
Sai gap da magariba muka dawo gida a gajiye part din mu na wuce direct don nagaji sosai a lokacin tun a falo na fara kokarin cire kayan jikina.
Mamu tace kin bar wayan ki a gida ana ta kiran ki na dauka ban gane yaren da matar take min ba yare kuma mamu na tambaya ina kallon ta.
Tace ni kan yare naji tanayi mun ai don ban fahinci may ake fadi ba nace koma waye ai zai sake kira idan wayan ya damay ta.
Har na juya na fara tafiya wani tunane yazo min a raina na juyo ina fadin mamu kodai wanan matar da muka kirane ta kirani yau.
Da sauri tace kuma fa yana yuyuwa gaskiya nace bari na duba na shiga na dauki jakkar da wayan ke ciki ina dubawa daga daki nace wallahi mamu itace kuwa ga sunan tanan da nayi serving.
Ikon Allah mumun kira ranan bata daga ba yau kuma ita ta kira har sau uku ba a daga ba may wanan abin yake nufi ne wai haka ?
Dare yayi yanzu sosai a can zai kai karfe goman dare ko ya dan fi amma dai barin gwada kiranta mu gani ko zata dauka yanzu.
Tace shiyasa mijin ki yace idan zan kira na dinga kiran ki goman safe ko zuwa shaday haka yafi a same ku.
Kiran sunan yaya da tayi yasa na tuna da zancen mu da Ahmed nake tunane sai dai ban mata magana ba duk da an fara kiran sallah hakan bai hanani kiranta ba a lokacin.
Nayi sa,a aka daga wayan da sallama na karba muka gaisa tace kwana biyu nace eh ban dawo ba ina Nigeria har yanzu.
Zancen da mukayi dake ne na kira don nazo ga mahaifiyana na tambaye ta tace min sunan mahaifiyar ta halimatu sadiya amma mahaifan ta suna kiran ta da Siyama a lokacin .
Sai naji tayi wani irin kanbbara da karfi tana fadin nasani nasani kamar yayi yawa wallahi itace itace wace muke nema shekara da shekaru bamu gane ba.
Da gudu na fito falo zuwa wurin mamu sai na sameta zaune tana kuka da alama taji wayan da nakeyi da matar a lokacin.
Ban damu da kukanda takeyi ba na fada mata ina ihu da murna ina rike da waya a hannu na lokacin .
Munyi magana sosai da ita na fahinta ta fada muna mu saurare ta zuwa safe zata kirani ta fada min yadda sukayi da mutanen ta.
Mamu ki bar kuka godiya ya kamata muyiwa Allah da ya karba muna adduan mu a lokacin da mukafi bukatan hakan a tare damu.
Sayadi dole in kuka yau ta fadi tana share fuskanta jin zancen nan nake kamar mafalki nakejin sa yau ubangiji Allah ka tabbatar min da wanan abin ya zama gaskiya a gareni.
Ba zan kara sati ba a gidan nan zan tafi zuwa neman mahaifiyata tunda na gano a inda take yanzu.
Tashi muyi sallah mu godewa Allah lokaci yana shigewa kada muyi wa Allah butulci da halin mu na yan adam a lokacin da ya amsa muna addu,an mu.
Mikewa nayi ina tafiya duk jikina ya mutu da maganan mamu da tace sayadi abubuwa suna damun rayuwana da zancen rashin ganin mahaifiyata zanji koda rashin kwanciyar hankalin gidan nan kullun nike nan a cikin gori da takala da habaici iri iri.
Yanzu idan mahaifiyar mamu tazo yaya hjy zatayi da take yawan mata gori kan hakan irin tunanen da nakeyi kenan ina alwala a ban dakin.
Na fito na tayar da sallah muna idarwa kuma muka dasa maganan ta yadda zamu bullowa maganan do??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????n haka zamu yi shiru tukun na sai mun gama tabbatar da komai da gaskene kafin ta tunkari kawu da Amma da zancen.
Barci nayi sosai ranan don a gajiye nake sosai kamar nayi wani aiki dan fitan da mukayi ya saukar min da kasala a jikina.
Washe gari ne da safe muna karyawa sai ga kira kawu a wayan mamu yace ta turo mashi ni falon shi.
Da mamaki a raina na mike zuwa amsa kiran kawuna a falon na samay shi zaune tare da hjyn su yaya tana cika tana batsewa ganun hakan yasa nasan ba lafiya bane wanan kiran.
Gaida su nayi na samu wuri na zauna daga kofa a kasa ina fadin gani kawu yace Fatima yanzu uwar ku ta kawo karanki wurina.
Kan kin sa drivern mijin ki ya dauko maki mota a gidan mijin ki kin fita dashi jiya alhalin ba a gidan sa kike ba yanzu kin sani.
Dan kallin hjy nayi cikin mamaki nace kawu ban taba motar yaya ba motanace dana bari a can nasa driver ya dauko min da zamu tafi gidan Anty salma jiya.
To kinji jimmai ya fada yana nuna ta da hannu yace jimmai wai may kike nema da wanan yarinyar ne haka a gidan nan ?
Shiyasa ban maki magana sai da tazo don muji dalilin ta na daukan kayan danki bai gari ita kuma a matsayin matar shi.
Motar ta ni bai sheda min cewa tana da mota ba da zai tafi don haka dole inyi magana akan kayan dana don ba kayan banza ya ajeba da kowa zai dinga dauka yadda yaga dama ko wani lokaci.
Kawu bai dago kaiba hankalin shi naga waya sai daya kira aka dauka yasa handfree yana fadin kana lafiya ya yara.
Ya amsa mashi kawu yace yanzun ina zaune mahaifiyar ka ta shigo min da wani magana wai Fatima ta aika gidan ka an kawo mata mota ta fita jiya.
Shine na kira fatiman yanzu gata a gaban mu take fadin motar tace ta dauko ba naka ba ita jimmai bata yarda ba shine na kira muji a bakin ka.
Innalillahi yace munajin shi yanzu daddy don Fatima ta taba kayana shine abin magana wurin mama motar nan nata ne tun a London na saya mata ba fita take nan ba yasa na turo mata dashi gida.
Kai mara kunya inada daman da zanyi magana akan kayan ka idan naga za,a wullakanta maka dukiya tunda ba,asan zafin shi ba.
Mama matatace fa ta taba kayana tana da iko da duk wani abinda yake mallakinane a garin nan yanzu don tare muka same shi a nan.
Lalai babawo ka nuna min an gama da kai har kake fadin haka a kunnuwana yau komai tsiyar ka sai ka rabu da yarinyar nan na fadama.
Mama daga yau nabada baki duk abinda Fatima zatayi da kayan gidana a barta tati natane na mijinta na yaran ta final ya kashe wayan.
Kawu yace tashi kije abinki na dago ido na kallesu tare da fadin nagode kawu na fita daga falon zuciyana ba dadi abinda hjy take min yayi yawa sosai yanzu.
Tayi min tayiwa uwata duk muna daurewa muna shanyewa anya kuwa zan iya nan gaba da halin hjyn su yaya.
Na shigo part din mu mamu ta bini da kallo banyi magana ba son banda niyar fada mata wanan magana.
Lafiya yake neman ki nace lafiya mamu ganin ta kuramin ido tana son jin akan may ake kirana din nace wai hjy ce takai karana na dauki mota jiya daga gidan yaya na fita dashi.
Matarnan tana da hankali kuwa wanan wani maganane haka babu dadin ji ko yaro ai ba zaiyi wanan abinba.
Ta dai daukeni matsiyaci dagani harke tana muna kallon wullakantatu a idon ta.
Mamu hassadane da ne da kyashi ke damun hjy rashin kaunar ki da batayi ya kawo haka garemu .
Niko nasan da hakan don hjy ko kasheni tayi idan ba ta cire min kai taga bana motsi ba hankalin ta baya kwanci.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
17/11/2021, 07:13 - ??5惙5惙5?: Barci nake hankalin kwance don ina jin dadin barci a irin wanan lokacin na ba safiya ba ba rana ba don barci kan min dadi sosai balle yanzu da ga ciki a jikina.
A cikin barcin da nakeyi ne nake dan jin murya sama sama wanda hakan yasa har nakai ga bude idona a hankali.
Bubu kowa a dakin sai sultana dake barci a dakin saman gado a kwance kusa dani ta makale mun a jikina.
A hankali na cire yarinyar a jikina na yunkura na sauka daga gadon na nufi bandaki na kewaya .
Falo na fito mamune ta dauki abu a kitchen zata fita da sauri daga part din mamu meke faruwa na kuma na tambaye ganin yadda take a rude.
Kawun kine baida lafiya ya rikice muna lokaci guda ta bani amsa tana fita daga dakin.
Hankalina naji ya tashi lokaci guda da sauri na bi bayan mamu muka isa falin tare lokacin na sami har Amma tana falin itama.
Yana kwance sharkaf gani daga wurin yin lazimine laluran ya same shi koda mamu ta fita bai karkare fita hayacin shi ba zuwa ta dauko abu ne muka samu ya fita cikin hayacin shi ga baki daya.
Duk yan gidan suna rude sai kuka suke sun rikice a lokaci daya.
Kwatsawa nayi tsakanin su hjy da hjy maryam ina fadin a bani cibi da sauri kada ya datse harshen shi lokacin.
Da sauri aka miko min cibin dake saman table na daga kanshi ina kokarin samun sa,an cibin ya tsaya a bakin shi.
Da dai an kira likita yazo hjy tace ban kula taba sai aikina nakeyi da sauri na dago ina fadin zan samu dan igiya ko yagwai karami haka ?
Wanan ba mafita bane kada aje a jawo mashi matsalan da bashi ba kuma ta kara fadi.
Ba dai wanda ya kula ta a lokacin sai hjy maryam ne tace cikin kidimewa hjy ya zamuyi dashi haka tunda an kira wayan likitan ba,a sameshi ba shikuma Ahmed nasa bai shiga ba.
Tai makon daya samu a lokacin yasa yai wani irin ajiyan zuciya yana fitar da numfashi a wahale.
Zan samu ruwan sanyi da tawul yanzu na fada da sauri hjy maryam ta nufi wurin fridge mamu ta shiga daki ta dauko min tawul ta miko min na dan zuba ruwan ina dan mana mai a goshi da saman zuciya zuwa babban yatsan shi a hankali.
A hankali na dago kai ina fadin don Allah ku dan rage murya kadan idan son samune a dan rage zuwa waje.
Kafin in riki hannuwan shi ina dan murzawa a hankali a lokacin hjy tace kai a daukeshi aje asibiti yafi wanan shiriritan da ake mashi ai.
Hjy wanan halin da yake ciki ina mu mata zamu iya daukan shi haka zuwa waje ai kafin mu fita ya wahala da yawa mamu ke fadi.
Can kawu yai wani irin ajiyan zuciya wanda hankan ya dawo da hankalin kowa a gareshi.
Yace ku dagani don Allah sai dai maganan nasa baya fita sosai daga inda nake gefe rugume da kanshi nace kawu yi shishiru na dan lokaci hakan zai taimaka maka sosai ya rutse idon shi a hankali.
A daidai lokacin na dago kaina wurin mamu ina fadin mamu wayana don Allah.
Ta juya da sauri zuwa part din mu sai gata dauke da wayan a cikin sauri ta miko min na karba har lokacin ina nan rike da hannun kawu ina dan murzawa a hankali.
Karban wayan nayi na dakatar da abinda nakewa kawu na kira wani layi runging aka dauka nace Auwal kana kusa kazo nan gidan kawu da kai da mai aiki guda don Allah yanzu yanzu.
Ya amsa da fadin gamu nan zuwa yanzu hjy na kashe wayan ba a dauki lokaci ba sai ga shiya kirani yana fadin suna kofan gida nace ku shigo gani tafe.
Na fita nayi masu bayani sai gasu da sauri suna bina a baya muka shiga dakin da taimakon su suka kama kawu suka fitar muna dashi zuwa wurun mota yana fadin a barshi yaji sauki ai nace kawu bari aje asibiti dai tunda taimakon gagawa na baka kawai dama.
Auwal da musa mai kula da duk wani kayan gidan suka zo sune suka shiga dashi mota musa ya zauna tare dashi a bayan motar ya dan rungumay shi a jikin shi hjy ta shiga gaba tare da Auwal driver.
Da sauri na shiga dakin mu na saka dogon riga da gyalen shi nacewa mamu ta taso muje tace ai ba sai naje ba tunda ga hjy a can.
Mu tafi nace mamu zuwan mu yana da rana a wurin don Allah jakkata na dauka muka rufo kofa takai yara wurin Amma hjy maryam ke tambaya can zamu tafi na bata amsa da eh muka fita tare har mama hadiye.
Auwal na kira na tambaye shi inda suke ya fada min da kwatancen su mukai asibiti don ni ke jan motan mamu danaji shi duk ya tsufa sai manejin ashe takeyi hakana.
Mun same su a waje ko karban shi ba,ayi ba don akwai mutane damkare a wurin lokacin .
Mun samu hjy tana masifa da masijan kofan likitan kan yayi masu alfarma a duba shi.
Masijan na fadin dole sai sunbi layi zasu ga likita da kike son ganin shi da wuri me ya hana kuyo sammakon zuwa nan.
Ran hjy ya baci ta shiga fada ma masijan bakar magana yana fadin ko dukana zakiyi saidai kiyi amma yau sai kin bi layin nan.
Wani likitane yazo shiga office din yaji hayaniyar yayi yawa ya tsaya yana tambayan ba,asi ana mayar mai na karaso ina mai bayanin halin da kawu ke ciki yana buka gagawan kulawa a lokacin yadda nake mai bayani ya tsaya yana kallona da mamaki har na cikin office din suka fito ya shiga yaga likitan bai dade ba sai gashi ya leko yana fadin muzo mu shiga.
Auwal ya tura keke ina bayan shi hjy tana fada har lokacin muka shiga office din wanda na gani zaune a matsayin likitan mai duba mutanene ya bani mamaki sosai a lokacin.
Shima sunana ya ambata da fadin Fatima Abubakar bauchi yaushe kika dawo kasan nan na kwana biyu na bashi amsa ina fadin kawuna ne baida lafiya yana bukatan kulawan gagawa.
Yace gaki babban likita tare dasu ni wani kulawa zan bashi yanzu a nan ya juya wurin likitan da yai muna hanya yana fadin ka ganeta tare mukai karatu a London sai dai ina gaban ta da shekara uku.
Haba yadda take min bayani yasa na gane tasan wani abu a ciwon mara lafiyan don sai kuma yai shiru .
Bawani bane D Guy ne likitan da muka sama ya mike da kanshi ya taimaka aka dora kawu saman gado lokacin dayan likitan yace mu basu wuri.
Take ya jona mashi ruwa a office din da allurai daya dace ayi mai kafin su fara mashi aune aunen daya dace suyi mai.
Ga na,uran numfashi da zai taimaka mai wajen dawo mai da numfashin shi daidai.
Saida suka gama ya kiramu da hjy muka shiga ya dago kai ya kalleni yace Fatima tun yaushe haka ya same shine ?
Hjy tace haka ya kwana yana jin jikin nasa da safen nan ya karkare rikice muna a gida.
Hjy shine kuka kyaleshi da ciwo haka a gida ke fatima kin san illan hakan kuka barshi har wanan lokacin ?
Idon daya kura min wanda yake min manyattacen kallon da banson nan nasa yana karewa yadda jikina ya kara fresh kowa ya kalleni yassn ina samun hutu lokacin.
Ganin na tsargu da irin kallon da yake min a fakaice ya mike ya koma wurin kawu ya kara masa wani allura har lokacin kawu barci yakeyi bai san inda yake ba.
Muna zaune shiru a gefe daya nida hjy yaci gaba da duban marasa lafiya dake shigowa yanayi yana dan jana da hira ina bashi amsa da kyat game da aikin mu.
Saidai hankalin shi yana gurin kawu yanayi yana dan dago kai lokaci lokaci yana kallon inda kawu yake akwance da ruwa a jikin shi.
Nayi zurfi cikin tunane naga ya mike zuwa wurin kawu likacin na dago kai ina kallin shi ruwan ne ya kare ashi yaje ya zare mai a hankali.
Tare da cire mai na,uran daya jona mai ga hanci na numfashi ya dawo ya zauna yana fadin he be alright insha Allahu.
Amma Fatima kin daddy ki yanzu bukatan hutu da kwanciyan hankali yake so mai yasa kike barin kuna daga mashi hankali hakane ?
Dan satan kallon hjy nayi da take zaune kamar na dole a wurin nace kasan mutum mai iyali ai sai sannu dole a yanzu.
Yace to amma a stage din da yake yanzu bai kamata kuna barin abu yana bata mashi rai ba ko wani lokaci don zaku iya rashi alokacin da baku zataba.
Kawu ne dayayi dan tari ya ja hankalin mu zuwa gareshi ya mike da sauri zuwa bakin gadon yana dan tatabashi a hankali.
Salati kawu yayi lokacin da yake kokarin bude idanuwan shi mikewa nayi na nufi wurin gadon ina mashi sanu da

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login