Showing 300001 words to 303000 words out of 419207 words

Chapter 101 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1444

To barin tashi tunda naga da gaske kake daukana din kazo yi yace ba matsala muje dai .
Haka ta fito ba tare da ta dauki komai ba tabi dukkan matan gidan tana fada masu zata leka gidan mu ta ga saukan mu.
Allah ya tsare a fili kowa yai mata saidai na ciki na ciki a zuciyar kowa da yadda yake fassara zuwan nata gidamu din.
Tsab na shirya komai na shiga nayi wanka nabar yan aiki da yara suna karasa abinda ba,a rasa ba.
Shiya shigo dakin a daidai lokacin da nake kokarin saka riga a jikina ya shigo yace sai ki fito gata nan ta iso yanayi shi kawai na kalla nasan baya cikin dadin rai a lokacin .
Juyawa yayi zai fita lokacin nace yaya wani abin ya faru ne kuma yau dan girgiza kai yayi kamar karamin yaro.
Tausayi ya ban lokaci guda na karasa wurin shi ina fadin yaya nasan nayi kuskure kan biyewa Nafisa danayi jiya sai dai lamarin zuciyane da bata da kashi yasa har na biye mata don furucin data furta min lokacin.
Zarah na dauka zuwa yanzu kinyi hankalin da zaki gane matsalan da nike ciki a kanki da mahaifiyata zaki tayani yakar wanan kudirin nata mu zauna lafiya sai dai ashe nayi kuskuren fahintar hakan gare ki zarah.
Hawaye ne suka zubo min a idona lokaci daya nasan banyi daidai ba tun farko ya rokeni da inshaye duk wani abinda suka bijiro min da shi na dauki alkawarin hakan gare shi.
Nasan kin hakkuri da duk abubuwan da akeyi da kuma wanda ake nuna maki a zahiri kina gani saidai ina son ki sani saida hadin kanki zan samu burina ya cika akan kudirina.
Zarah ya kamata yanzu kisan kina da darajan da za,a iya hasada a kanki har yakai mama tana furta min wai nazo ina bare bare a kanki da mahaifiyar ki.
Nasan dole mama tace haka don ke din matatace kuma uwar yayana da nake alfahari dasu yanzu a duniya.
To idan banyi bare baren da mama ke fadin inayi daku iyalina ba akan wa zanyi hakan bayan duk rabin samuna akan yan uwanane da mahaifana.
Koku iyalina din da suke fadin ina bare bare akanku nasan bakuci ko kwatan kwacin abinda nakeyi yan uwana ba daga cikin abinda na mallaka din yanzu.
Don hakane nake son ki natsu ki ban hankali ki wuri daya mu samu mu shawo kan wanan matsalan a cikin ruwan sanyi kamar yadda na shirya a tsarina.
Ya kamata ki san darajan ki da kimar ki yanzu ya zatar wace zata tsaya ana kananan maganganu irin wanan kin sani zarah ban son yawan magana a rayuwata.
Shiyasa nake komai nawa a dunkule sai bayan nayi wanda duk zaiyi magana daga baya ya furta abindake zuciyar shi gamay dani wanan yafi mun sauki a rayuwata.
So ki shirya hajiya tana zaune a falo tana jiran ki da fatan zaki amfani da magana ta nan gaba yana fadin haka yasa kai ya fita ina jin su daidai zan fito Amma na fada dashi wai ina ita yar gwal din naka munafukan banza da wofi har kun manta da lokacin da kuka dagawa mutane hankali a baya kan auren ku damun bi ta naku da yanzu ina zaku kai wanan alhakin yaran naku ?
Amma gani wanka ya samu na shiga yanzu don kada kizo ki sameni hakana ki dauka haka nake zama a gidana ta dan harareni a daidai lokacin da nake karasowa ina kokari rungumar ta.
Shikani karki karasa ni don Allah yadda kika koma din nan kamar ke kadai mijin naki ke kiyo a gidan .
Su maria ne suka fara fitowa da abinci suna mata sannu da zuwa tana amsawa tare da binsu da kallo tana nazarin su.
Maria daki zaku kai mata komai zatafi sake jikin ta a can na kamo hannun ta ina fadin taso muje daki ki huta kagin lokacin sallah ya karasa sai mu zauna asha labati yaushe rabo.
Nanma yayi min ai har wani daki zan shiga in zauna ina dai wuni kawai zan maku in koma anjima to ai kyaso ki dan kishingida dai ko ?
Don na fahinci bai mata bayanin yana son zata dan zauna damu bane na kwana biyu na samu tashiga dakin da aka gyara mata tana sallama tana fadin a, a a ikon Allah.
Ta kai zaune saman kujeran dakin tana bin dakin da kallon mamakin irin tsara shin da akayi da haduwan shi.
Abincin na fara gabatar mata a gabanta bayan na gama ne na tuna ai murja bata zo ba tare da Amma ina tunane a raina yaya akai hakan kuma bayan ga yadda muka shirya dashi kuma.
Don hakane zai kara kwantarwa Amma da hankali saboda shakuwan da sukayi da murja din wanan lokacin da su kadaine a gida tare da ita a gabanta a matsayin jikan da take gani a gaban ta.
Waya na dauka na fita lokacin danaga Amma ta fara cin abanicin layin murja na kira nake fada mata ta daukowa Amma duk wanin abinda tasan zata bukata a kusa da ita tazo mata dashi muna son su kwana muna biyu nan ita da Amma.
Cikin dan lokaci kadan sai ga murja ta hado mata goron ta tasbaha da wasu kaya kala uku don bukatan ta.
Mamaki ya kamata tana fada da murja don may ta hado mata kayanta kamar wace zata kwana a nan tace yaya yace na hado maki na kawo.
Zai dawo ya samay ni nan abinda zai mun ke nan yaje ya daukoni ina dakina zaune kalau ya kawoni nan inda ko rana bana gani balle lokacin ibada.
Sai dariya nake mata ina fadin muma munada bukatan ki a nan ai yaya bai dawo gidaba har dare har ta kwanta bai shigo ba sai dare sosai ya dawo gidan lokacin har tayi barci ya tayar da ita yace taci nama da abin sanyi daya kwaso mata din.
Sun dade daki zaune suna tatauna matsalolin shi wanda yana daga cikin dalilin dauko ta gidan shi da yayi.
Da wanan tunanen Amma ta kwana a ranta ranan mamaki da tunanen duniya ya cika mata zuciya.
Tana tunanen yadda uwa zata matsama farin cikin danta akan iyalin shi ta matsa sai ta daga mashi hankali.
Gasu su ba irin iya shigen da basuyi mata a gidan a gabanta ko bayan ta tana shanyewa don kawai kawar da kai a zauna lafiya suda mijin su take kawar da kanta.
D???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?onme hjy zata kasa tunanen haka ga yayanta ta lura akwai kishin diyan ta a cikin zuciyar ta .
Hjy saidai addua kawai don ta kula da abinda bahaushe kecewa idan uwa ta faye saka matan diyan ta gaba to walau ta ci fitsarin danta ko ta faye saka son diyan ta a zuciyar ta har yakai tana kishin matan diyan nata.
Ta kula da abindake damun ta ke nan a zuciya don ta tuna da yadda aka kwasa da habbib da ita da matar shi har yakai habbib din yayi fushi tun tafiyan shi har lokacin bai kara leko kano ba tun lokacin.
Wanan abin na hajiya da mai ya kama ko Aisha matar Aliyu haka suka kwasa lokacin haihuwan ta sai da akai jidali da ita da yan uwan mahaifan Aishan kamar Auren zai mutu a lokacin gashi kuma yanzu Umar yazo mata da wani zance na matsin da take mai kan lalai sai ya sakeni na koma dakin uwata da zama .
Washegari ina idar da sallah na fito don in duba Amma da yara sai masu aikin da zasu hada abin karyawa kada suyi wanda bai gamshi Amma ba wurin ci.
Na samesu zaune suna hira da murja a dakin hakan yai min dadi sosai don naga murja tasa ta sake jikin ta.
Saida na zauna na fara gaida ita da kwana na juya nagaida murja don ko banza murja ta girmay ni ita da nafisa gurin haihuwa.
Amma ya dare nace bayan mun gama gaisawa da murja na juya wurinta ina tambayan ta.
Yar mijin ki yazo min da wani magana wanda ya tayar min da hankali jiya gyara zama nayi ina fadin wani magana yazo maki dashi kuma ?
Zancen ku da uwar shi yarnan jiya banyi barci daren jiya ina tunanen wanan hali na uwar ku yaya zaki turo yar ki da batai aure cin mutunci gidan dan uwanta don kawai kiyayya ta batawa yarta kurciyarta.
Dadin da nakeji na salma ke nan yanzu da salma ta kama auren ta ta fita zancen duk wani ingiza mai kantu da uwar zatai mata akan auren ta tun lokacin da sukai wanan takai kan satan data turata taiwa mijin ta kara kama kanta da yake tana son zaman auren nata.
Sata kuma amma na tambaya cikin mamaki tace mu bar zancen nan don baki sanshi ba yanzu dai na fahinci dalilin daukoni gidan nan da mijin ki yayi.
Fahinci wani abu daga cikin magana nan ki mijin ki yana bukatan kulawan a ciki wanan lokacin yana bukatan wanda zai zauna ya dan fahintar daku wasu abinda ku ba zaku iya ganowa ba a cikin zancen nan.
Abinda nake so dake da farko natsuwa mu fahinci inda zamu fara dosowa wanan zancen don ba karamin fitina daga ke har shi kuke ciki ba.
Shiru nayi lokacin da amma ke min bayanin kaina ya kulle sosai ga abunda take fada min wanda da farko ban dauke shi wani matsala ba a wurina.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:32 - ??5惙5惙5?: Ranan sai na wuni sukuku ina tunanen zancen mu da Amma wanda bata fito fili ta baiyana min shi a baiyane ba amma daga baya da muka zauna da murja mukai maganan sai na fahinci hjyn su yaya tana farautan rayuwana da rayuwan aurena ne ashe wanda hakan yake yawan haddasa min mafalkin su ko wani lokaci.
Saidai magana irin wanan bai taba shiga tsakanina da yaya ba ko kadan sai yanzu da nake jin zancen a bakin Amma.
Abinda dai na sani da wuya ayi sati daya banyi wanan mumunan mafalkin ba da ita wanda sai yanzu naba abin ma,ana.
Idan hakane ai garama ta raba auren da takeso ta barni da lafiyana zaifi min sauki don duk ranan da nai mafalkin haka zamu kwana rikice da yaya wani lokaci kuma shine maiyin mafalkin bani ba.
Dabi,ana ne bana fitowa gajal sai na dan gyara jikina kuma ban wuce takwas na safe banyi wanka har yara mun kitsa jikin mu har yan aikina bazaka zo gudan ka samay mu ba dadin gani ba komai sammako mutum kuwa.
Ina shirin fitowa yaya ya shigo dakina da sauri yana fadin zarah fito ga kawun ki yau gidan mu.
Kawu na ambata a fili ina mamaki yace harda su baba balarabe ai kin san dole suzo gidan nan tunda na dauko masu tsohuwar su ai.
Da sauri na biyo bayan shi zuwa falo inda muke jin hayaniyar su suna dararaku a lokacin.
Fitowan mu yasa suka dan tsagaita suka mayar da hankalin su garemu a cikin kunya nakai wurin tare da tsunguna kasa ina gaida su kawu gaba daya su.
Kawu balarabe ne ke fadin gamu mun biyo ku tunda ku bakuje gaida mu ba umar baka san gidan mu ba balle iyalin ka yanzun kuma ka dauko muna uwa zuwa gidan ka.
Yana dan dariya yace baba ba dauke ta nayi ba muma nan muna da bukatantane na dan lokaci a tare da mu.
Ja,iri abinda zai fada maku ke nan ai ya daukoni ya kawoni nan ko tana bana gani sai dadi yake cika min a cikina ba dare ba rana ko nayi barci sai yaron nan ya tayar dani ya bani naci.
Dariya suka kwashe dashi kawu mustapha yace Amma ai hajiya kin canza gaba daya wallahi da gani ba sai kin fada ba.
Daki na mike na shiga na fito da yaran dukan su na kawo su wurin su kawu har yanzu basu son sake jiki da kowa a ckin dabara suka koma jikin mahaifi su suka kara makaleshi.
Allah ya albarkaci zuria kawu balarabe yace yara haka tubarkalla masha Allah yau ina jummai dataga wa yan nan yaran da ina zata kai alhakin hana auren da taso yi nasu.
Kai ke nan da kasan wanan kake fadin haka Amma tace don ita har yanzu ba wai ta saduda bane ta bangaren ta.
Har yanzu tana kan bakan ta ke nan kawu mustapha ya tambaya da mamaki.
Ta nan wallahi yanzu haka halin da ake ciki akan matsen lamba take kan sai yaron nan ya saki yar nan bata barsu hakan ba ta kwashi maganan komai ta fada masu hankalin su ya tashi matuka da jin wanan maganan.
A hankali na mike na bar gurin don ba zan iya jin kalamin su na manya akan sarakuwar tawa ga dan ta a gurin ya dukar da kanshi kasa yana nuna yanayin rashin jin dadi ga kalaman da ake mata din lokacin.
Kawu sani ma baiyi magana ba a lokacin shiru yayi kamar mai nazari a zuciyar shi.
Barina gurin shima ya mike tare da yaran shi zuwa hanyar waje abinsha na umurci mai aikin mu ta kawo masu da dan abin motsa baki duk da safiyane sosai a lokacin.
Kwana biyu da zuwan su kawu gidan mu muka shirya zuwa ziyaran yan uwa damu dashine gaba sai sultana dana rike su Abdul suna baya tare da maria da murja sai Amma.
Ziyaran yayi kyau sosai don yaya yaiwa dagi alheri sosai a wanan dan ziyaran da mukai masu lokacin kayan mu sun iso na rabawa kowa daya dace a cikin dangi tsaraba har wanda ban zataba saida ya samu alokacin.
Ranan da Amma ta cika sati uku muka mayar da ita gida tunda safe kowa sai yaba kyawon da Amma tayi a gidan mu akeyi.
A nan ya wuce ya barmu zan wuni sai dare zai dawo ya dauke mu yace a part din Amma muka yada zango kafin in koma wurin mamu in zauna.
Tare da maria mukazo don laluran yaran na shiga wurin hjyn su yaya na gaida ita muka dan zauna ta barmu nan zaune falo nida yara da maria ta shige daki daga ita har nafisa.
Sai dan autan su yayane ya zauna tare damu yana hira tare da kulawa da yaran karshe dai da zaman ya ishe mu naga hjy bata da niyar bamu lokacin tane na fito na koma wurin Amma daga baya kuma na dawo wurin mamu.
Har akai sallah azahar mukaci abinci ashe hakan danayi kuma wai ya batawa hjy rai matar da anan ta barmu zaune taki kulamu ko yan jikokin nata bata kalla ba balleni da maria.
Sai bayan la,asar yaya ya shigo gidan direct wurin mahaifiyar shi ya nufa inda ya samu ta cika ta hau tayi fam dani.
Yana zama yake tambaya nafisa zarah fa tana inane wai ?
Uwar ta kalleshi tace wa zaka tambaya ita a nan tunda ba wurin mu tazo ba tana gurin uwarta mana yaran da kake kira da jikokina ina zata yarda su rabeni tunda a na daukana mai mugun hali.
Mugun hali kamar ya mama ko ya kike ai bata isa ta rabaki da yan jikokin ba yanzu ni ba gashi amma yau ji nayi kamar kada ta dawo na ba.
Ina ji da kunnuwa yaran nan suna tambayar ta kakasu tace bani bace kakarsu tana can part din ta tana rikesu kada suzo wurina a gaban idona ta nuna min banda hadin komai da yaranta yanzu.
A hasale ya mike bai gama sauraren ta tana fadin ina kuma zaka yanzu iyayyenta su taru suce ban kaunar zaman lafiyan ka da matarka.
To amma mama daidaine ta shigo gidan nan ta hana yaran nan zama a wurin ki bazan taba lamuntar hakaba gaskiya ko ina hakkuri da komai ba zan iya daukan wanan ba gaskiya.
Na daice ka barta harku koma gida kuyi shi can don gaskiya abin bai mun dadi ba nima amma tunda kai kaji ka gani kan zama da ita yaya zanyi da kai.
Ya kalli mahaifiyar rai bace kamar zaiyi magana sai kuma yayi shiru ba tare da ya furta komai ba ya zauna ya dan jima zaune ya mike yana mata sallama.
Kofan part din mamu ya tsaya ya tura dan wurin hjy maryam ya kirani yaron ya shigo ya gayar damu muna zaune ana hira yake fadin ga yayan mu a waje yace ki fito ku tafi.
In fito mu tafi shida yace sai dare zamu tafi kuma na taso na leka har ya fara tafiya nace yaya ya waigo kace mu fito kuma eh kawai yace yaci gaba da tafiyan shi.
Dan jim nayi ina nazarin shi kafin in koma ciki rai bace nacewa maria ku taso mu tafi yana jiran mu a waje don maria taji dadin zuwan mu gidan ta sake sosai a gidan.
A mota muka samay shi

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login