Showing 6001 words to 9000 words out of 419207 words

Chapter 3 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1475

a gidan tare da ya aikin gidan dake masu abinci su biyu .
Da farko ta samu korafin yin hakan daga gun kishiyoyin nata sai dai ta fannin maigidan wanda hakan yai masa dadi yasa maganan tai shiru a gidan.
Bata fadawa kowa zancen ganin maganin da tayi ba a cikin abincin su sai dai daukan matakin da tayi na rashin cin abincin daga ita har yaran nata da bata yarda ta rasa abinda zata basu a part din nata ko suje gun su hadiye ko Amma suci wanda ba surkule a cikin sa.
Yau ma tea ta hada masu da safe suke karyawa dashi ita da yaran nata sallama taji daga kofan shigowa dakin ta karba.
Lami ce mai aikin su ta shigo mata da abin karyawan su ta gaida ita da aiki duk da bata yarda da lami din do ta hannun daman uwargidan nasu ce tu farko a tare suke da ita.
Gashi hjy jummai din ta hana bada daman kowa ya dauki mai mashi aiki duk da suna da halin yin hakan a gidan idan bukatan hakan ya taso masu.
Saidai ido kowa ya saka duk da wani lokaci hjy maryam takan turza akan matsalan Lami mai aiki idan tayi mata ba daidai ba a gidan ko ta batawa yaran ta rai.
Irin dai wanan matsalolin da ba, a rasa ba a gidan yawa irin nasu mai mace fiye da daya haka yake faruwa a kullun sai dai ita hjy maimunan takan shanye nata a ranta.
Wanan yasa ko da yaushe take a takure ita da yaran nata basu da wani walwala sosai a gidan don yawan matsalolin da ake yawan samu a kullun.
Hjy Jummai mace ce mai so mulki a gidan miji ta wanda ta rike damanta na uwargida bata yarda ta bari wata ta kwance mata wanan daman nata ba.
Shine yakesa data ga wani abinda yake son shige mata gaba bata yarda dashi yanzun zata dauki mataki akanshi ta rufe wanan abin ya zamo tarihi.
Yaranta shidda da Alh Sani maza uku mata uku shimkafa da wake inji hausawa inda take kokarin ganin rayuwan yaranta ya inganta tako wani hanya.
Hjy jummai auren saurayi da budurwa sukayi da Alh sani aure na nagani ina so a tsakanin su don haka suna zaman su na jin dadi da kuma gadara da hakan akoda yaushe tana alfahari da uwargidancin ta a gidan.
A wurin hjy jummai gani take tankar duk wata mace da Alh sani ya auro daga baya dole ne su bita subi umurnin ta a gidan.
Hakama yayan da suke haihuwa take ganin gasunan daine a gidan yayan tane masu cikakken yanci a cikin gidan fiye da kowa.
Wanan ra,ayin natane ya sa ba zaman lafiya a tsakaninta da hjy maryam da farko da take ganin ta shigo mata gidan mijin nata don ta hana mata jin dadin ta da mijin ta da yaranta da take ganin su kadaine keda mijin nata da farko.
Sai ga hjy maryam da rana tsaka ta shigo rayuwan su duk da wayen kan hjy maryam din haka hjy jummai ta kasa ta tsare komai sukai ta samun mats??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????ala har hajiya maryam din ta haifi nata diyan kwara hudu a gidan mata biyu maza biyu itama a gidan.
Sin sha faman kishi akan hakan inda hjy maryam din bata yarda da akidar uwargidan tasu ba ko kadan suna cikin wanan rikicin ne kwatsam sai ga zancen auren yar uwarshi yazo masu wanda basu taba zaton hakan zai taba faruwa dasu ba.
Wanan mulkin da ikon nata taso nunawa lokacin da zancen auren yazo kunnen su ga maigidan nasu inda a cikin gadara ta nuna mai hakan ba mai yuyuwa bane a gare shi.
Sun sha rikici sosai da Alh sani kan auren nasa da zai kara kuma wai yar uwarshi ta jini da ta san komai nasu na gidan zai dauko ya saka a cikin su.
Bata tsaya gare shi ba har yan uwanshi sun sha gori a wurin hjy jummai a lokacin inda takance .
Ni da Alh aure ne na saurayi da budurwa mukayi don haka ko gaba dayan ku za,a daura mashi mace dai a bayana take don ba wani abinda ban sani ba wanda ya shafi Alh har ku.
Na aure shi tun bai kai hakan ba arzikina da nasa ne yazo daya har ake kwadayin jefo dangin shi a cikin mu tun yana da mashin har muka kai ga mota yanzun anga samu ake son kowa ya shigo yaci arziki ko ?
Babu wata macen da zata shigo ta girgizani nida gidana don ana hangen samu a wurin shi yanzu.
Sukan maida ita wace zafin kishi ke ci a lokacin don haka basu biyewa babatun ta a lokacin sai ma wasu tsageri kan bata amsa da sai dai maimuna ta shigo gidan Alh kun zauna tare.
Muma aci arzikin nan da kike kurin kun samu tare dashi damu mu samu mai tarbon na arziki idan munzo gidan nan.
Takan basu amsa da fadin ta shigo ai jummaice zata zo ta samay ni kujera nake daidai da duwawun ko wace mace.
Wa yan nan kalaman nata duk suna komawa kunnen yan uwa wanda hakan yake matukar tayar da hankalin maimuna a lokacin .
Sai dai ba yadda ta iya don don auren nan ba gudu ba jada baya a wurin ta don shine farin cikin gwagon nata marikiyar ta a lokacin.
Da hjy jummai taga auren ba fashi sai anyi shi sai ta koma fadin a shigo mana ko wace ke gidan zaune dani may ta gane gun mijin .
Arzikin dai ake kodayi ba za a gane komai ba duk wace tayi gigin shigowa rayuwata don hangen arzikin mijina zata zone zaman hakkuri dani a gidan nan .
Iya gaskiyarta take furta kalaman ta da wasu suke dauka da izgili take yin shi ko shakiyanci don a fasa zancen auren da ake shirin yi din tsakanin shi da yar uwar tashi.
Alh sani dai yakan yi murmushi idan tana haukanta na kishi don inda sabo ya saba da wanan tun akan auren martam da yayi a baya wanda hakan suka kwasa da ita.
Shi Alh sani mutum ne da bai faye magana ba hakan yasa take samun dama sosai a wurin shi take abinda ta fa dama a gidan.
Don kawai a zauna lafiya wanda ita take ganin so ne da fin karfi hakan don a kullun takawo ra,yin ta zai iya sakin nasa ya dauki nata a zauna lafiya.
A bangaren hjy maryam taso tayar da hankalinta akan wanan auren sai da yan uwar ta suka lurar da ita kuskuren da take shirin tabkawa ta dawo cikin hankalin ta.
Amma da makirci da zolaya saida hjy Jummai taja ra, ayinta suka hadewa maimuna kai da ta shigo gidan.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
16/11/2021, 22:35 - ??5惙5惙5?: SARKA MAI, , , , , , , , ,

3??_/Q

ZAINAB IDRIS MAKAWA


GODIYA YA TABBATA GA ALLAH SARKIN KOMAI DA KOWA DA YA NUNA MUNA WANAN RANAN TA JUMMA,A UBANGIJI KA TAIMAKI MUSULUNCIN AKAN KAFIRCI KAYI MUNA DA YAN UWAN MU MUSULMI DAUKI A KO INIA MUSULMI YAKE A DUNIYAN NAN .
JUMMA, AT MUBARAK YAN UWA UBANGIJI YA BAMU ALBARKAN DAKE CIKIN WANAN RANAN MAI ALBARKA AMIN.

WANAN LITTAFIN NA KUDINE DON ALLAH KI BIYA KI KARANTA A NATSE YAR UWA BATARE DA SHIGA HAKKIN KOWA BA NAGODE, , , , ,
DOMIN SAMUN WANAN NOVEL ZAKI IYA KIRAN WANAN LAYIN 08036959257 KO KI TURA KATIN DARI UKU TA WANAN LAYIN 225428015 ZAINAB IDRIS MAKAWA ZINETH BANK KO KATIN DARI UKU KACAL NA GODE, , , ,




Da sauri take tafiya don zuwa kai gulma wurin uwar gijiyan nata da ke dan mata ihisani kan orin wanan halin ko da yake sabone kawai don kowan su na mata abin arziki daga cikin su.
Da sallama ta isa dakin hjy jummai wace ke zaune tana kwasan girkin abin karyawan safen da aka kawo mata wanda sai da aka yaye mata wurin abin miyan kafin a zubawa sauran busashe akai masu.
Ganin yadda ta shigo yasa hjy Jummai sanin da magana a bakin ta ta shigo dakin nata a lokacin haka yasa ta mayar da hankalinta gurin lami din.
Cikin irin yanayin munafukai lami ke magana hjy ashe abinci kike ci barin bari ki gama saina dawo in fada maki abinda ke nan.
Haba yi magana ki mana Lami tunda kin zo ai ba zai hanani cin abincina hjy Jummai dake zaune take fadin hakan.
Hjy dama ba wani abu bane sai zancen wanan amaryan taku ne yanzun naje nakai mata abincin safen ta na samu ta hada nata suna karyawa da yaranta.
Hjy da kanta yake duke ta dago da sauri tana tambayan may kika samu ta dafa a can din, hjy ta tambaye ta da sauri ?
Lami ta gyara zama tana fadin ruwan shayi ne mai kauri sai kwai suke ci a plate .
Da sauri hjy tace Lami kardai ince kwan da aka ajewa Alh na amfanin shi ne ta diba ta dafa da yaranta ?
Lami tace ai shine nazo na fada maki kar aga ya kare a tuhumay mu muda ke aiki ko yaushe a cikin kitchen din .
Kwarai kuwa don kune a kitchen din ko yaushe dama nasan a rina wanan shiga kitchen din din da takeyi ba banza bane a gidan da akwai zanban da take shukawa.
To yau ya kare don asirin ta ya tono a gidan nan gaskiya idan ankai mata abincin suke kin tabawa sai dai ta dawo muna dashi kitchen.
Abincin da hjy Jummai bata karasa ci ba ke nan dama tana da takaicin hjy maimunan a ranta yanzun kuma an kara dada mata wani sai taji duk abincin ya fita ranta ga baki daya.
Da kyat ta yaki zuciyar ta har maigidan ya dawo ansan wace ake don ba zai yuyu maimuna ta dinga nuna masu tsageranci hakaba a ckin gidan.
Ita wacece da bazata ci wanda aka girka wa kowa ba sai tayi nasu ita da yaranta akoda yaushe lami tana ganin ta hada wanan ta mike zuwa aikin ta don tasan yau ko ba komai ta gyarawa uwar dagin nata rai da wanan maganan.
A bangaren hjy jummai kuma bayan sun gama karyawa ne ta tasa yaranta gaba don suje su gaida kakar su Amma tare da daukan kulan data sakawa hadiye dan abinda ta soya din.
Da sallama suka shiga dakin Amma inda ta samu hadiye a dakin suna hira da mahaifiyar ta da murna Amma ta tari yan jikokin nata inda hjy maimuna ke fadin.
Ashema kina nan tana fadin haka ne lokacin da take mika mara kulan data riko masu din.
Hadiye sai cewa tayi mai muka samu kuma a nan tana kaiwa zaune take fadin dan sauran kwanda yaya mustapha ya bamu ne ranan na gidan gonar shi na soya.
Kin san yaran kin ga har yau basu iya cin wanan abincin safen da ake girkawa a gidan nan yau ai kinga basu zo shan kunun gwago ba.
Cikin tabe baki Amma tace na rasa may ake da wanan uban kayan girkin da ake shigowa dashi gidan nan sai ga an shigo da kayan girki mai yawa.
Amma karshe haka za a kawo abincin nan ko almajiri kaba almajiran nan na yanzu ba zasu karba ba.
Hjy ke nan ana ko amfani dashi sosai don da yanzu zaki sashen yar mulkin gidan kiga abincin ta ita da yaranta sai kice ba guri daya aka girka da wanan din da ake kawo muna ba.
Hadiye ce ke fadin wanan magana ta karasa da fadin ni yanzun haka ko budeshi yaran nan basuyi ba don ba zasu iyaci ba ma ko sun bude din.
Nina rasa wanan akidar ace gida kamar wanan wai sai gaba daya za ai girkin da za a ci ranan dana shiga na samay ta tana ci nayi mata magana sai cewa tayi babban goro ai sai budin karfe dole itace za a fara zubawa don hakane na ga nata a hakan.
Tsuki Amma taje tana fadin wanan yarinyar tana daukarwa kanta nauyi da yawa ina zata da wanan alhakin haka a kanta.
Nina rasa hali irin na jummai a ce mutum baida abinyi a rayuwa sai kokarin danne hakkin wasu abin nan ana bayarwa ba ba a kawowa bane amma don kawai ta cutawa yan uwan zama ta kawo wanan akidar banzan haka.
Hjy ni indai zata barmu mu zauna lafiya duk wani akidar ta baya damuna kamar rashin kwanciyar hankalin nan da babu a gidan nan a kullun.
Hjy maimuna ce take wanan maganar cikin nuna damuwan ta da yanayin gidan nasu.
Kasancewar bata da girki yasa takai har sha biyu da wani abu tare da hadiye suna hira kafin ta koma part din ta da yaranta.
Wanda hakan ba karamin bata ran saura natan gidan yakeyi ba don a zaton su zaman zagin su akeyi gurin hadiye din.
Basu san abin ba haka bane kokarin kulla alakan business suke a tsakanin su shine yawan zuwa part din juna da sukeyi.
Bata fito ba tunda ta shige tana cikin sashe nata wanda haka ne komai a ciki duke da yaranta idan ba maigida ya dawo ya nemi yara a gurin shi ba sam bata yarda su fita daga sashen nasu.
Don da farko tana bari har i yaran suki fita ta tillasata masu wai don su saba da yan uwan nasu take yarda su fita da farko.
Sai daga baya ta gane fitan nasu cuta masu akeyi idan sun fita cikin tan uwan nasu don duk sun fisu girma a gidan da yawa kuma.
Shine dalilin da bata yarda su fita ko ina hakan kuma yana ma yaran dadi sosai na rashin fita inda za,a duke su da zagi iri iri.
Karfe biyar duk wani wanda ke gidan yasan lokacin dawowan maigidan gidane hakan ke sa kowa na gidan yake natsuwa.
Matan gidan kuma kowa takan dauki kwalliya don burge mai gida sukan shiga daya bayan daya wani lokaci ida yana da magana zai tsayar dasu yayi masi shi a cikin jam,i.
Idan ko ba wani magana sai a bar wace ke girki ita kadai tare da maigidan ta dauke mai sauran dawainiya kafin ya fita sallah mafariba.
Irin bada abinci miko min yi min wancan sai idan yana da baki suka dan samu su sarara.
Inda shi kuma yakan zauna da yara shi kanana suna hira kafin su fice masallaci dashi da yaran nasa.
Yauma irin hakan ya kasance a wurin hjy maimuna din inda take saye cikin atamfar code, voi,re dinkin zanin da riga half gun sai yaran da ke saye da yar katin su uku ta tasa su a gaba.
Ta makara zuwa gaida maigidan nasu a yadda ta saba zuwa idan ya dawo hakan ya samu dalili ne na tsayar da ita da yan biyun ta sukayi na yin kashi bayan ta shirya su kinsan abu ga mai kananan yara.
Da sallama ta shigo fallon kallon yanauin su kawai tayi tasan da akwai matsala don haka tana gaida shi da ta juya zata bar fallon.
Muryan mijin nasu taji yana fadin dakata maimu samu wuri ki zauna inda ya kalli yaran mm nata yace kuje ku jira maman ku ta dawo ko .
Yaran suka juya don bin umurnin mahaifin nasu yayi da yar mulkin ke zaune a gefen shi tana harare hararen yaran da suka saba da irin kallon da take masu a gidan.
Dan shiru ya biyo a falon sai can Alh ya kira sunan ta inda ta karba da fadin na,am yaya don haushi hjy jummai ta wani kawar da fuska tana mayde bakin ta.
Maimuna wani magana nale jin yanzu wanda banji dadin jin shi daga gare ki in ma har haka kike so ai sai ki gabatar da zancen a gabana in san abinyi ko ?
Hjy jummai bata so haka ba sai haushi ya kamata sosai na yadda yake mata magana a cikin tsigar lalashi itako a cikin sanyin murya tace wani abin akace nayi kuma tunda ba, a raina abin laifi a gidan nan.
Alh baikai ga magana ba yar mulkin ta karbe da fadin kina nufin kake akai maki ko may wa kikafi a gidan nan da bazaki ci abincin da kowa yaci ba sai kin fake ga satan kayan gida kin shige daki kin dafa da yaran ki kuci.
Salati hjy maimu ta saka tare da fadin yau kuma sherin yakai a laka min satan abinci a gidan nan ?
Ji munafuka waisheri cikin tsawa da daga hannu Alh ya dakatar da ita da fadin ke Jummai banson irin haka don Allah ki bari muji dalilin ta na yin hakan saboda Allah.
Falon ya danyi shiru kafin ya nisa yace hajiya babba da hakuri fa aka sanshi kila tana da wani hujjan yin hakan kamar yadda na fada da

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login