Showing 207001 words to 210000 words out of 419207 words

Chapter 70 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1463

a gefena ya dan razanani don ban saba da rike waya ba ko a gida.
Dauka nayi Allah ya taimakeni na iya komai na waya da wayan mamu danakan dan jagula a gida.
Salama nayi naji yace ba tare da tsayawa amsa min ba gobe ki shiga schools din ku kiyi komai don kafin a koma ake komai.
Kudi na nan na aje a wardrobe dakina nasan zasu isheki idan basu isa ba ki bugo min ta wanan layin nawa.
Jin yana sgurin kashe wayan shi yasa nayi saurin fadin yaya nagode Allah ya kara budi na alheri.
Uhumm yace kamar zai kashe wayan sai kuma yace ki dai kula da kanki kin san garin nan sai mutum ya kula sosai ninayi tafiya ban ma kasan a yanzu haka.
Mamaki abin ya bani nace Allah ya dawo dakai lafiya yaya amin yace ya kashe wayan.
Kallon wayan dake hannuna nayi na sauke a jiyan zuciya tare da fadin a shirye nake kawu dana fara auwatarma da aikin daka bani tsakani da Allah.
Shiko ya umar yana kashe wayan ya sauke ajiyan zuciya da kyat ya iya daga kafan shi ya fara tafiya cikin filin jirgin da yake.
Sai faman tunane yake yarinyar dabi,un ta da sauyawan ta suna kashe mata jiki ji dan wanan abinda ya fada yadda yarinyar take zuba mai godiya.
Motan da tazo daukan shi ya bude ya shiga zuwa hotel din da yake sauka idan ya shigo kasan da yar jakkar da yake rataye a bayan shi da komai ya fada saman gadon yana sauke numfashi.
Yana kwance ya zubawa kwaliyan dakin ido cikin kankanin lokaci ya umar ya tsinci kanshi a cikin tashin hankali mara musaltuwa don irin rigiman da suka kwasa da merry kafin ya bar gida.
Take kwakwalwan shi ta dinga hasko mai maganan mahaifin shi yake jin muryan kawu kamar a lokacin ne yake masa maganan.
Tabbas ya yarda komai shekarun ka manya sun fika hangen nesa yayi huci yana dafe kanshi.
Yau ya sani yayi babban kuskuren bin son zuciyar shi na yarda da yaudara irin na mata da har ya yarda da dadin bakin merry ya aure ta.
Bayan irin alkawarin da sukayiwa juna na zama a cikin amana da junan su har karshen rayuwan su .
Sai gashi wai yau merry ce ta fito baro baro take fada mai ba zata yarda yarsu tabi akidan shi ba don haka bata yarda kowa nasa ya mami yarsu a yanzu ba don kada a juye mata zuciyar yarinya.
Ya kare huci yana mirginawa tabbas ba zai daina dora laifin hakan a kanshi ba don tun yana karami yasan manzon rahama ya fada mazaje su zabawa yayayen su uwaye na gari.
Gashi yau sanadin abinda yar kankanuwan yarinyar nan fatima taga merry tana masa har yakai tsoro da shakkun sa sun fara fita idon yarinyar.
Dolene mana ta nuna min hakan yace na biyewa son zuciya don kawai matata taji dadi na take gaskiya da gangan.
Idanuwan shi ya rufe yana fadin gara da daddy ya dawo dani a hanya da nasihohin shi masu kama da wa,azi yana godiya ga Allah da baiyiwa daddy din butulci ba da abinda zai gani sai yafi hakan.
Zai iya jure komai da merry zasuyi mai da yan uwan shi amma ba zai yarda yarshi ta taso da akidan kiristanci ba a rayuwan ta.
Yana tsoron may zai je ya fada a gaban ubangijin shi akan yarinyar..
Bangaren merry kuwa tun bayan yadda suka kwashe dashi a gidan ya fito bai ce mata komai ba ta gane tafiya zaiyi hankalin ta ya tashi.
Don ita tsoron kada ya gudu ya koma kasan shi take ji don saida ta daure taci masa mutunci kamar yadda aka dorata tayi din.
Haka yasa take ta kokarin gwada layukan shi ko zai shiga sai dai amsan daya ne har lokacin wayab shi a kashe take.
Zuciyan ta ya kasa samun natsuwa kan maganganun daya rufe ido ya fada mata lokacin shine ya tsaya mata a rai.
Don cewa da yayi addinin shi ya bashi daman kara mata da yaya ko yaushe ta tuna wanan yana cikin alkawarin su a baya tunkan suyi auren.
Ta gyara zama tana fadin anya kuwa shawaran kawayen ta da iyayyen ta idan tabi har ta hana yarta koyi da addinin mahaifin nata da yake son koya mata zata samu mafita.
Greco ce ta dan zo inda take tana tambayan idan wani abu take so a lokacin ?
Kai merry ta girgiza mata gami da cewa bana bukatan komai hutu nake so yanzu kawai jin hakan yasa ta bar gurin da sauri.
Kamar yadda yaya yace inje school hakan yasa da safe na shirya zuwa clearance din takarduna.
Saida na shiga na fita ban samu matsalan komai ba sai mutum daya nake jira in kammala na samu wuri ina hutawa inda va mutane sosai a wurin.
Hankalina yana gun wayan da a lokacin banda layin kowa a cikin ta sai game da nake yawan yi dama shine aikina idan na dauki waya.
Dan dago kai nayi tare da duban lokaci ina jan tsuki tare da fadi cikin hausa na tsani jira wallahi.
Da sauri matar da ke kusa dani ta juyo tana kallona tace sister ke bahausa ce ?
Kaina kada mata kawai ban iya bata amsa ba lokacin na kara jan tsuki ina kokatlrin mikewa don gajiya da zaman danayi wurin.
Matar data manyace ni sosai ta sake fadin gaki da alama dai kina a cikin damuwa da ganin ki.
Dan murmushi na kakaro a fuskana tare da fadin ba komai nagode nace mata ina kokarin mikewa.
Hannun ta takai saman kafadan ta dafa tana fadin kinga kanwata ban yarda baki cikin damuwa ba don duk wani mahaluki mamanlakin hankali ya dubi fuskanki a haka yasan kina a cikin damuwa yar uwa.
Sai dai idan boye min zakiyi and kinsan abinda yasa nayi saurin fahintar hakan kanwata na sake girgiza mata kai alaman a a.
Tace na dauka idan yan kasa daya suka hade a wani kaaa suna daukan janunan su tankar yan uwane don kamar sunga wani na jikin sune, .
Amma ke sabanin hakan na gani a gareki ya kamata at list ace kinyi farin ciki da ganin yar kasar ku yau koba komai a zamu dinga zumun ci ko ?
Gaki da gani ke yarinyace baki da aure niko kinga macen aurece sai mu zama kamar yada kanwa dake nan ni suna Farida Aliyu daga kano nake tace tana kallona da dan murmushi a fuskanta.
Murmushin dole na kakaro a nawa fuskan nima nace anty farida ke nan ni kuma fatima Abubakar nake nima daga kanon nake a old GRA.
Tace kice dai dukan mu yan gari dayane ashe kinga surutuna da naci bai zama banza ba don kin samu yar uwa a nan ke nan.
Murmushin na sake sakewa a karo na barkatai tace kina tare da iyayyen ki ne ko yayan ki ke nan ko ke dai kika zo karatunan ?
Nace ina tare da yayana ne sai dai gidan shi yana can wani unguwa ni kadai ke zaune a gidana sai lokaci lokaci nake zuwa ganin su.
Hakan yana da kyau sosai don kinga mu bamu da nisa sosai mijinane ya samu aiki a nan ya kwaso mu shine nayi amfani da wanan daman nake karatu kada inyi zaman banza ai kinga gaba idan zama ya mayar damu gida zai amfane mu.
Gama can yadda karatu yake da wahalan nan hakan yasa na kuke saida maigidana ya nema min addimition nan na fara karatu.
Ta nisa tare da fadin well fatima ko kada in cikaki da surutu naga kamar baki da yawan hayani sai dai idan mun kara haduwa ko ?
Nace a ciki murmushi ayya ba matsala wallahi ai na gode ta mike tana gyara gyalen abayan ta ta fara tafiya sai kuma ta tsaya tana fadin ko zaki ban layin ki don muji saukin kara haduwa.
Nace a cikin sakin fuska ayyah kiga kuwa ban hadece layina ba saidai idan zaki saka min naki saina kira ki samu layina din.
Tana fadi ina dauka na danna kiran sai ya shiga a wayan ta tace yashigo sai anjima mukayi da ita ta wuce.
Ranan dai ban samu karasa abinda naje yi ba don haka na koma gida a gajiye saida na dan huta na mike zuwa ciki na watsa ruwa don banda niyar dafa komai ranan kifin gwagwani da bread zanci.
Saman kujera mai zaman mutum uku nake zaune ina kallo ni kadai a gida kamar manya na manta da zancen waya sam don ban saba dashi ba.
Karan wayan ya dan firgitani na zabura daga inda nake zaune na dauko da sauri nayi recieven call.
Sister yaya kike kin dawo gida lafiya ko sai lokacin na tuna da zancen ta mun gaisa har yaran ta biyu taba waya mukai gaisuwa dasu mukai sallama ta kashe.
Ban kai ga aje wayan ba wani kiran yana shigo min a daidai lokacin na dauka.
Ke wata irin dakikiyace wai may ye amfanin wayan dake hannun ki da baza ki kira mutum kiji lafiyan shi ba.
Wai ma da wa kike waya ne tundazu ina kira ana fadin kina busy ?
Wai waye wanan daga kira sai fada min maganan banza kaika ajeni ko may ko a kanka nake na azama nauyi ?
Ina jin yana sake wani irin murmushi mai dauke da takaicin kalaman da na fada mai na nuna ban gane mai magana ba.
Yace yanzu na san ke din ba karamar shedaniya bace ni kike fadawa haka don samun wuri ni zakice wai baki sheda muryana ba komai don shedan ci.
Nace to ni nasan wanda ya kirani ne da kake kirana da shedaniya ka fada min ko waye mana kai tsaye.
Yayi huci tare da dafe kanshi ya kuta ya kashe wayan gaba daya dan tsuki naja ina aje wayan tare da fadin miskilin banza kawai gobe ka kirani ka zageni idan halin kane .
A bangaren shi tun yana mamakina har abin kuma ya bashi dariya yasan da gangan nayi haka don haka bai kara kirana ba nima ban kirashi ba din.
A fili ya furta zan hadu dake yar iskan yarinya mara kunya yaci gaba da aikin shi tun wanan lokacin ya fita batuna.
Haduwa da anty farida yai min dadi don ashe dan kasa kadan suke da layin mu mukan tako da kafa muna hira zuwa gida.
A cikin sati daya sabo sosai ya shiga tsakanin mu da ita sai naji zuciyata ya kara kwantawa sosai na sake banda sauran damuwa ko kadan a tare dani.
Wasa wasa saida yaya ya share sati uku bai leko ba nima ban kira layin shi gashi duk zaman mu da anty Farida ban taba fada mata cewa ni matar aure bace.
Don haka take daukana a matsayin budurwa har take fadin zatayiwa kanin ta kamay idan mun koma nigeria ta hadamu.
Ni dai nakan mata murmushi kawai nakanyi ban bata amsa maganan ta don ban yarda da ta san sirina ba ko kadan dukda ita ta mayar dani tankar wata yar uwanta can ta jini.
Yau ma da zamu dawo mun dade dade tsaye a waje tana ban labarin wani tafiya da sukayi dan duban lokaci nayi nace zan shige gida wai ina gidan naki yake ta tambaya na nuna mata da hannu tace wancan babban gidan wai kike nufi.
Aiko maigidana ya fada min kamar gidan wani dan Nigeria ne na katseta da fadin yayanane ai tace au a cikin mamaki.
Munyi sallama ta tafi na nufo gidan don nagaji saboda na fahinci ita mai yawan dumine sosai bata gajiya.
Na tura gidan na shiga sai naga kofan a bude gabana ne ya wani irin faduwa take laifin da nayi mai yazo min a rai.
Haka na daure na karasa shiga gidan duk da banga motar shi a gidan ba lokacin.
Na shigo falon dake gauraye da sayin AC ga kamshi yana tashi a falon TV kuma yana a kunne lokacin.
Sallama nayi danaga haka na shigo sai dai shiru da babu kowa a folon ko wani motsi bayan na tv da ke aiki a falon lokacin.
Saboda hakan na ratsa ta bayan kujerun falon zan nufi dakin baccina sai dai zuciyata a cikin tsoro take lokacin .
Har na fara taka step din na hangoshi zaune kasa zaune kasa saman rogh carpet din falon ya jingina bayan shi ga kujera daya na falon.
Ya kuma sanya duks hannayen shi guda biyu ya dafe kanshi ta baya ya tsurawa wuri daya idanu kamar mai tunane.
Dan dawowa baya nayi zuwa wurin shi ina fadin a sanyaye sannu da zuwa yaya na hada da gaishe shi.
Da kyat ya iya dago kai ya amsa min cikin dauri ya kawar da kai ta hanyan mayar da kanshi saman kujeran.
Ban tsaya ba na ja kafa da kyat zuwa sama ina tunanen ko may ya samay shi haka ban sani ba.
Sanin yana gida ga kuma yamma yayi na fito a gurguje na dora muna girki don kada kuma inyi laifi a gurin shi.
Cikin dan kankanin lokaci nagama na nufo falon samu nayi baya nan falon lokacin dakina na koma har nayi wanka tare da sallah na fito har lokacin bai fito falo ba.
Har nufo falo sai kuma wata zuciya tace in lekashi dakin batcin shi a kofana tsaya na kwankwasa.
Sai naga kofan dakin ya bude sallama na kara yi yanzun ma a zaune yake a gurin nan da nagani ya tanada don sallah.
Wanan karon godin shine ya dafe da hannun daya shi kadai yasan irin halin da yake ciki .
Gaishe shi na kara yi a sanyaye ya amsa min cikin gyada kai nace yaya na gama abincin yana dining.
Cikin dauriya yace min zan fito amma sai anjima yanzu na gama shan magani mura yana damuna sosai .
Nace Allah ya sauwaka na juya na fita a karon nan naji dan tausayin shi a raina cikin zuciyana ina kuma tunane anya muran ne kawai ke damun shi haka ?

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:17 - ??5惙5惙5?: ASSALAMU ALAIKUM WARAHAMATULLAH, , , , ,


A sanyaye ba bar part din zuwa kasa ina tunanen abinda ya samay shi haka na ganshi a cikin wanan damuwan haka ?
Zama nayi na fara juya abincin cibi biyu sai na kasa ci naji abincin ya fice mun a rai na dade zaune ina tunane har na kaiga yadda kaina saman tablen din na dan kwanta.
Ban san nayi barci a wurin ba gwanin ban tausayi dani idan kin ganni jin ana dan bubuga table din tare da kiran sunana ke fatima.
May nene haka kuma ki rasa inda zaki barci sai a nan kin saka abinci a gaba da alama ma baki ci abincin ba ?
Firgigit na bude idanuna yana tsaye a kaina ya harde hannaye shi guri daya idanuwan shi akaina baya ko kyaftasu.
Ina ganin shi nayi saurin tashi tsaye ina dan matsawa baya tare da fadin sannu yaya jikin yayi sauki ke nan ga abincin nan naka aje.
Ba tare da yace min komai ba ya juya zuwa wurin kujeran dake fuskantan wanda na tashi akai.
Abincin ya bude nau,in abincin mu na gidane nayi don akwai garin semo da miyar ganye don shi ke gareni.
Ganin ya zauna yana kokarin zubawa yasa na juya zan bar gurin ya dago kai ya dubeni tare da fadin ina kuma zaki bakici abincin ba.
A cikin dan murya kamar shagwabe nace na koshi ne yaya daga haka na juya na tafi na barshi a gurin ba tare da ko waigowa ba.
Ajiyan zuciya ya sauke bayan ya gama bina da kallo ina hawa sama tausayi na bashi don ya fahinci yanayin dana ganshi a cikin ne yasa na koma hakan lokaci guda.
Ina shiga daki na rufo ban tsaya yin komai ba nabi lafiyan gadona na kwanta sai barci.
Washegari na tashi kamar kullun ban tsaya komai ba nahau gyaran gida da giriki don nasan dole a nan zaici abinci kafin bakwai da rabi na kammala a gurguje nayi wanka na shirya.
Na fito banji motsin shi a falon ba kamar in fita don ba hurimi na bane shiga mashi daki don a matsayin dayace in dauke shi nake daukan shi.
Wata zuciya tace min ba daidai bane in fita ban lekashi ba bayan nasan ya zo baida lafiya gidan.
Da kwankwasa kofan nayi tare da sallama daga kofan dakin ciki ciki ya amsa min da shigo na dan shigo tare da hangoshi nade a cikin bargo yana kwance.
Ya ina kwana ya karfin jikin naka nace daga inda na dan rage tsawo ina gaida shi a matsayin shi na magabaci a gareni yadda aka koya muna a gida.
Amsawa yayi ciki ciki tare da fadin taimaka ki hada min dan ruwan zafi don Allah a bandaki ya ban tausayi sosai don haka kai tsaye na wuce gabatar mai

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login