Showing 54001 words to 57000 words out of 419207 words

Chapter 19 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1485

maganin yana miko masu ledan magani.
Nasan zamu samu wanan a school don yarda muka barta hankalin ta ya tashi muna komawa muka samay ta can shine muka kawo su gida yanzu.
Ya kare da fadin don Allah ayi hakkuri ga abinda ya faru kuskure aka samu Alh yace babu komai dan albarka mungode hakika hankalin mu ya tashi.
Da yan uwansu suka dawo ba tare da su ba sai dai da suke fadin wai da yan gidan kune suke rikici yasa ban wani daga hankalina ba.
Don nasan gidan ku ba batacen gida bane a garin nan ayi hakkuri dai nagode da fahintana da kukayi mu zamu tafi ke nan.
Godiya Alh dake rike da hannun Samir ya kara yi mai suka wuce sai lokacin Ahmed dake kallon yaron tunda ya fara magana ya yi magana.
Ya akayi yan uwanki suka dawo ba tare dake ba nace da zasu tafi da yaron ban san inda zasu kaishi ba na fito daga motar shine salma tace su wuce su barni.
Nafisa kuma tace wai ina cika su da ihu in ma samir ya bata ai sun rage mugun iri a gidan su ido suka zubo min ina rabbata masu yadda akayi .
Muryan Amma ne bayan mu ta fito cikin tashin hankali tana fadin yaran sun dawo ne ko angansu ne ?
Mamuce tace yanzu aka sauke su ashe asibiti aka kai samir din shine ita kuma ta tsaya tana masu ihu yan uwa suka wuto suka barta a can.
A man tanada gaskiyar ta ina zata dawo tabar dan uwanta a can bata san halin da yake ciki ba su da dauke shi bai abin bai damay su ba ai kinga sun dawo ko ?
Hajiya wa yan nan yara ban san ya akayi haka ya shige su akan yan uwan su ba ga Alh na iya kokarin shi wurin hada kan su guri daya Ahmeda ke fadi cikin bacin rai.
Kaiyya kamar baka san tsatson da suka fito ba ai wa kumbo wa kayan cikin sa mugun akidar da ake cusa masu ne a zukatan su tun suna kanana shine ke aiki.
Hajiya mu shiga daga ciki Alh ya ce da ranshi ke mashi suya kan abinda yaran shi suka aikata amma sun zo gida sun fadi abinda ba shi ba da farko.
Ganin kafan ya farawa yaron tsami yasa na sunkuya na dauke shi na barsu a gurin suna karasa magana don Amma bilhaki take fada yadda wanda duk ke ciki zai iya jinta.
Kasuwan da Alh bai koma ba ke nan ranan ya zauna a gida gashi girkin mamu ne haka ya kara tunzura ran matan shi kunsan mata basu raina abin kishi sai suke ganin hakan da yayi yayi ne don ya gyarawa mamu ranta damu yayan ta.
Bai yi maganan ba sai dai washe gari da muka shirya zamu school naji mamu tace min mu dakance ta itace zata dinga sauke mu school daga ranan.
Hakan yai min dadi a raina sosai don zan huta da shaguben yayan gidan da suke min idan zamu school dasu gara da rana wurin zuwa islamiya don Ahmed ke yawan kai mu kamar yadda yayi alkawarin kaimu din kullun sai dai wani lokaci idan aiki yai masa yawa driver ya kaimu.
Idan kuma yarinya bata fito da sauri ba ko taki zuwa zai dauki matakin haka da kanshi don har kofan uwarta zai tafi ya ci mata mutunci a can sai ta fito ko an fada mai dalilin rashin zuwanta.
Hakan yana bakanta ran iyayyen sosai ba yadda zasuyi don maigidan ya bashi go ahead din haka dole ko subi umurnin shi.
Mun rigasu ficewa gidan don a zaton su bamu fito ba mun makara ne yasa sukaja motar su suka tafi ba tare da sun jiramu ba duk da su Aisha sun ce a dan dakanci fitowan mu mana.
Sai suka yayyako su da masifa dole sukai shiru suka kyale su hakana suna kallo aka tafi badamu ba .
Samir bai samu fita ba ranan saboda kafan shi da yai masa tsami ga zazzabi na barazana akanshi yasa mamu tace ya zauna gida.
Kai rayuwan gidan yawa da gidan da ake da zafin kishi sai a hankali duk wanan abinda ya samu yaron bai sa wani daga cikin matan gidan ta jajantawa mahaifiyar mu ba.
Don banga wanda ya leko part din namu ba da sunan zuwa duban yaron da ake fadin wasu sun tafi dashi a mota ni kuma an barni a school ina ihu.
Hakan yasa na kara fahintar zaman da mahaifiyar mu takeyi a gidan da abokan zaman ta abin duk da nake yarinya a lokacin ya ban haushi da mamaki a raina sai dai babu galin magana a gare ni don mamu ta kwabeni ga hakan.
A school kuma tun bayan gama assemble ina class din mu zaune sai dai ban sani ba ashe maganan ya karde school wai nayiwa headboy rashin mutunci jiya a gaban kowa har yasa security din sa suka zane ni.
Wasu kuma suce ba haka bane kanina ne yayi rashin kunya wa head boy din da kowa ke tsoro ya sa aka hukunta yaron karya dai iri iri gashi nan irin na students ranan yana yawo a school.
Haka yasa yan matan dake rawan kai gare shi sukaji zafi suka shirya daukan mataki a kaina duk ina classa ban san anayi ba ciki kuwa harda salma don itama senior ce a lokacin.
Bayan breakfast sai gashi wata ta zo kirana wai in samay su a bayan shop din school ban faye fita ba during break sai idan zan duba kannena ne nakan dan fita.
Na tattara kayana na nufi inda suke nema din na samay su sun kai su goma sha a wurin ko wace ta murtuke fuska ga wani dogon bulala a hannun wace ta fisu tsaruwa da girma a hannun ta.
Cikin rashin ko in kula na isa gurin tunda nasan ban masu komai ba asalim ko yan ajin mi ni ba abinda ke hadani da kowa.
Ina zuwa nace ance kuna nema na anan ko gaba dayan su suka hayyayako min lokaci guda wai may na taka da bazan rusuna ba zan zo masu a hakan.
Wata tace inda ba ke din yar wata da wani ne wace ke labe a gidan mutane take agolanci zakiwa mutane daukan kai.
Raina ya baci da kalaman ta nace dadin abindai ba shegiya akace maku nake ba mutuwa ce inda ubana yaje uban kowa zai iya zuwa can.
Daga kirana sai ku kama zagina may ya hadani daku ba ruwana da kowa a school din nan abinda iyayyena suka kawo ni yi nakeyi.
Taaaa naji saukan wanan bulalan a jikina sai da na murde a wuri daya kafin in???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? rike bulalan da tayi niyar kara zabga min a jikina again.
Sake yar iska ko na illanta ki yau a school din nan inga uban da kike takama dashi da zai tsaya maki a garin nan.
Ke har kin isa kiwa gentle rashi kunya na rasa may ye dalilin shi na rashin daukan mataki ga wanan yar iskan mara kunya.
Banda kowa sai Allah kamar yadda aka fada maku ina zaman angolanci ne a wurin mijin uwata kuma kawuna.
Allah ne gatana shine gatana a garin nan ke da ubanki zai zauna gadin duniya sai ya zauna na karasa fadi ina mikewa tsaye tare da kokarin tattara bujena don na shirya masu bala,in dana boye a ranan.
Wata tace ji yar iska har mikewa tayi bayan ana fadi tana fadin da takeyi nace ke uwata ce da zanji tsoron ki komay na san dai ban maku komai ba a kan gaskiyana nake don haka wace ta isa ta kara buguna ta gani.
Salma tace ba na fada maku yar iska bace bata da kunya dama yanzu ai zaku gani da idon ku nace salma rufe bakin ki naki bala,in yana zuwa don nasan kece da hadin wanan sherin.
Sai wata tace kunga ku kyale wanan yarinyar ta tafi kunga dai wanan abin ba zai haifa muna da mai ido ba tunda tafimu gaskiya bata san komai ba tace.
Sukai cikin ta da sababi dole tayi shiru a wurin ta koma gefe tana kallon ikon Allah ga bulala na rike a hannu na da shirin bala,i gare su sauran yan makaranta har sun fara zagaye wurin don mutane basu raina abin kallo balle sun samu ana rike tsakanin prefect da jinior din school.
Kokarin kwace bulalan tayi sai ko na hanata nan kokawa ta kaure muna da tasan inda na fito da ita tashin falo tuntube da remote bata gwada hakan gare ni ba ranan.
Na iya kokawa da yan matan gidan baffa shiyasa na samu lafiya ga matan sai mazan kan jibgeni son ransu.
Batai aune ba sai gata a kasa na kashe ta nan sukayo kaina da duka nace in bakayi bani guri suna kai min duka ina ramawa na haukace masu gaba daya sai wuru ya dauki ihu baki daya hankali ya dawo gare mu.
Muryan maza ne suke fadin amma ko kunji kunya wanan yar ficiciyar yarinyar ne kuke haka da ita ta gagare ku wata ta kawo min duka na kustsa cikin taro suna ja da baya sai dana cin mata muka kaure da ita.
Sai da malamai suka zo suka raba da kan su aka kwashe mu zuwa staff room inda da farko aka ban laifi sai na fashe da kuka ina fadi don anga ubana ya mutum zai sa su zageni.
Ina zaune na ban san hawa ba ban san sauka ba suka aika in fito suna nema na ina zuwa suka hauni da zagi da duka wai nayiwa wani gentle rashin mutunci wanda nima ban san hakan ya faru ba don tunda safe nake aji zaune ban fito ba.
Will you keep quiety malamin ya fada da karfi sai wata malama tace amma malam sadiq kabi maganan nan yarinya ka fahinci abinda take fadi.
Nan jikin shi yai sanyi ya fara bin ba,asin maganan dalla dallah har suka fahinci abinda ke faruwa aka gane duk salmace mai hadin a kaina.
Har mansur din da suke kira da gentle aka kira a wurin yayi masu bayanin abinda ya faru tsakanin mu jiya bai rage komai ba nan malamai mata sukai kansu.
Zane su akayi akai muna assemblen kan mu ranan ni hukuncin yin ruduness ga senior na aka kamani dashi inda aka hukunta ni wanan yasa aka san da ni a school din.
Bayan mun dawo gida ban fadawa mamu abinda ya faru dani ba sai yamma ta tsinto maganan a dakin Amma ida su Aisha sukaji a wurin su ikilima yaran hjy maryam suke zancen.
Ran mamu ya baci sosai tace zata canza min makaranta tunda abin yaki ya kare a tsakanin mu sai da Amma tace ta bari Daddy ya dawo zasuyi magana akai.
Ta dawo part din ta ta samay ni ina wa kanne na assigment din su take tambayana may ya hadani dasu salma a school har mukai fada haka ?
Nan dai na kwash komai na fada mata sai naga ta tsura min ido kawai lokacin da nake mata bayanin har na gama sai naji tace ke kan baki biyoni da hakkuri ba hakama mahaifin ki.
Dago kai nayi na kalle ta don jin kalamin ta gare ni tace kwarai da ki barsu ga Allah idan ma sun zageki din ai kansu suka zaga din .
Ita salma tana maki hakane don haddasa wani bala,i a tsakanin mu don su kawo rigiman da Alh zaiji ya tsaneki a gidan nan don su a kullun karshen mu suke son gani a gidan nan.
Daga yau ban son in karaji kinyi fada da wani kan ko may nene ballae wanan dan zagin da hakan yana kan kowa ai kema bada son ranki kike zaune a gidan nasu ba da sunyi hakkuri kwana nawa ne ke mace ce fa kin kara gaba kin bar masu gidan su.
Sannu a hankali mamu ke fahintar dani manufar su salma a kaina wanda ina fahintar ta saida a lokacin kurciya da wauta yasa ba zan gane komai ba don banji zan iya kyalesu suna zagan min iyayye ba a banza su tashi free.

ZAINAB IDRIS MAKAWA

AYI HAKKURI DON ALLAH NA RASHIN JINA KWANA BIYU YAN UWA.
16/11/2021, 22:45 - ??5惙5惙5?: YA SUBBAHANALLAH, KARIMUN, RAHIMUN, YA HAIYYU YA KAIYUMUN, , , ,

A dakin Amma muke zaune dasu Aisha dan na fara dan sakewa dasu yanzu su kadai ne zan dan raba inji dan sanyi a gidan.
Kitso nazo suyi min sai dai har lokacin ban kwance kan ba su suka taimaka min na don haka nafi son zuwa wurin su duk sati suyi min kitson duk da mamu ta iya sosai.
An kusa gama kitson ne mama hadiye ta shigo falon tana fadin hajiya ashe mutumin ki zai zo kasan nan ne dashi da yan uwanshi.
Da mamaki Amma ke fadin wani mutumin nawa a ciki tace umar dai mana dan gaban goshin ki na gidan nan.
Da sauri Amma tace ina kika samo wanan labarin kuma yau ake wanan zancen daurin gindin uwarsu suka samu yo waya sani ko sin kai ga tara iyali ma a can tunda ba wanda yasan wainar da suke toyawa a can yanzu.
Haba hajiya da hankalin su zasu aikata hakan a kan su aiko wani da dangin shi yake kuri haka dai tasu rayuwa yake ba tunanen abinda kaje ya dawo gare su.
Amma ta tabe baki tana fadin idan ma zasu zo Allah dai ta kawo su lafiya idan muna da rayuwa ma gansu .
Lokacin azumi ya gabato saura yan kwanaki a tashi da azumi a fadin duniya don haka ake ta faman shirye shiryen taron watan mai alfarma a ko ina na fadin duniya.
Hiran su bai shafe mu ba har mama hadiya ta gama ta fita zuwa unguwa kasancewa ranan weekend ne bata fita gurin aiki ranan.
Sai da ta fita Aisha ke fadin wai Amma duk hjyan su salma ta haife su su ukun duka.
Amma tace wai kina nufin baku san yannen naku ba da kike tambaya koda yake ba yau yaran nan suka tafi ba har shi wanan da ya tafi daga baya din sai lokacin Aisha tace ya kamal ko shi wanan na sanshi mana yana zuwa gidan mu lokacin da muke gidan Abban mu.
Shi dai zaki iya shedawa su wa yan nan ai sin dade da barin kasan yanzu sun tasan ma shekara goma sha fa da tafi sai nayi karaf nace ashe tsufi ne ba yaraba.
Dariya sosai Amma tayi wa magana ta tace inda ba tsofi ko yar nan karatu suka tafi yi can waje shine shiru basu dawo ba kin san ita jummai tana da son komai nata ace ya fita daban dana mutane.
Yanzu gashi alama ya nuna yaran basu son kasan su ta haihuwa balle yan uwan su na jini kai Allah dai ya kyauta da hali irin na jummai wallahi.
Ban faye sa baki ba idan ina part din Amma ana hiran yan gidan kawu din don horona da hakan da mamu keyi ko yaushe sai wanan halin ya fara bi min jiki.
Koda naga sin buge da hiran sosai yasa na mike ina fadin barin leka mamu in taya ta aiki kafin yamma yayi sai Amma tace zaki gudu ke nan yarinya da radhin son shiga jamma,a haka.
Ina dariya na fita na barsu suna zancen su kodana shiga wurin mu na samu tana sallah bata fara aiki ba nima dakin mu na shiga nayi sallah kafin in fito in fara gyaran ko ina na part din namu don shi nakan fara yi idan zamu yi aiki ko ina gida.

ENGLAND, , , , ,
Suna zaune da merry a falo wayan shi yayi kara itace ta duba ta tabe baki tana fadin is from Nigeria da sauri ya karbi wayan a hannun ta yana duba mai kiran nasa .
Mama ya gani a rubuce saman screen din wayan sai daya dan daga daga yadda suke zaune da Merry din ya gyara muryan shi.
Ya dauki wayan da salma daidai lokacin yana kokarin gaida mahaifiyar tasu ta amsa mai a cikin jin dadi da annashuwa.
Bayan gama gaisuwan su take fadin ranan wanan mondya mai zuwa ne tafiyan ku ko a cikin mamaki yace mama zuwa ina.
Gaban hjy jummai ne ya fadi tace kamar ya zuwa ina kuma ina dan uwanka ya kirani yake sheda min zuwan ku ranan.
Cikin murya mai taushi yace hakane mama saida nada ni bane zuwa ranan sai nan gaba kuma idan Allah ya kaimu zan sa lokacin zuwa don akwai aikin a gabana da zai, , , , ,
Jinan babawo umurni ne ba tambaya ba duk abinda kakeyi kayi haraman zuwa gida a cikin satin nan mai zuwa don nagaji

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login