Showing 12001 words to 15000 words out of 419207 words

Chapter 5 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1476

karatu gwargwado sannu a hankali ya fara harkan kasuwanci da Alhjin shi inda ya fara zama dan hannu ya murje yai kyau dashi ya zama dan gari.
Sai dai suna shan artabu da hjy jummai don ya kasance shi din mai hakkuri ne kamar uban gidan nasa yasa har ya cin ma bukatar shi a duniya.
Lokacin da ta farga da sanin Alh sani ya dora shi ga harkan kasuwancin sa ta nuna rashin yardanta ga hakan sosai sai dai ba yadda zatayine dole ta kawo ido tasa amma duk da hakan takan so bashi umurni wani lokaci yabi wani sa,in ya nuna mata hakan ba mai yuyuwa bane a gare shi.
Wanan ne dalilin da yasa har gobe take tsanan yaron da take ganin baida galihin da za a kaishi ga matayin da aka kaishi a yanzun a gidan yasa suke yar tsama dashi akoda yaushe.

Wana ke nan yana tsaye aka sauke komai da yazo dashi gidan inda ya kasa komai hudu kamar yadda suka tsara da ubangidan nasa tun a kasuwa in yazo za a yi da kayan a gidan.
Bayan ya gama rabawa ne ya shiga ciki ya kira dukka matan gidan harda hadiye dake part din su ta fito kowa da mamaki akan may ake neman su a farfajiyan gidan.
Hjy Jummai bata taso ba sai da dole ya sheda mata abinci aka kawo gashi can a farfajiya ya zube.
Da sauri hjy ta taso jin abinda ya ce mata din sai dai tana tunkaro wurin ta hango yadda aka kasa kayan abincin sai ranta ya baci taja tayi turus ga kuma kowa na fitowa daga part din shi bayan kiran su suma da akayi.
Wanda da can baya idan an kawo kaya ita kadaice mai bayar da ikon yadda za a yi da kayan a gidan tana karasowa ciki fada tace kai Amadu ya naga haka kuma ?
Don har yanzu da Amadun shi, da yazo gidan take kiranshi ita da yaranta ba kamae yadda maigidan ya mayar dashi Ahmed kowa ke kiranshi dashi ba yanzu
Cikin wani murya tace kai Amadu ya nags haka kuma yace hjy may kika gani kuma abinci ne aka kawo Alh yace in mikawa kowa nata a hannu ta idan na kawo ba wani abu bane ai.
Kaba kowa nasa kamar yaya ta bukaci kari bayani daga guri Ahmed din daya mayar da hankalin shi wiri kayan.
Yace eh Alh ne yace indan nazo inyi hakan da kikaga nayi din shine dalilin kiran kowa don ta kwashe nata a idon ta.
Eh lalai wuyar ka ya isa yanka Amadu a gidan nan idan gaskiya ya shuka shi Alhjin yazo da kansa ya bamu din amma da yake yasan bai shuka gaskiya ba shine kai issashe ya turoka kai wana rabon.
To ka koma ka fada mai wana rabin baiyi ba a gurina babu wanda zai raba muna kan gida saboda a gyarawa wata rai taji dadi a cikin mu akai hakan ko ?
Don samu wuri to ba za a raba muna girki ba don kawai wata can a gidan nan sai ka hade shi kamar yadda ka kawo shi ka koma ka fada mai nace ba za, a raba ba.
A, a hajiya Jummai ke wa ga yadda mai gida yace ayi mai da abinsa zaki wani ce ba za ayi hakan ba to mukan namu kwasa zamuyi duk wanda zai tsaya bin dokan ki sai ya tsaya ya biki mukan mun bar bin dokan wata mace gidan nan kuma tunda ba ke kika ajemu ba.
Hadiye ce data iso gurin yanzu take wanan maganan ga hjy jumman ta kara da fadin Ahmed wanine namu daga ciki mu dauka.
Salati hjy jummai ta saka tare da fadin yau ni jummai naga abin al,ajabi abin mamaki ke Hadiya kin kasa zaman gidan mijin ki kinzo nan zaki bata muna namu zaman.
Duk da maganan ya batawa hadiye rai bai sa ta tsaya mayar da martani ba alokacin sai ma umurtan mazan dake tsaye a gurin da tayi akan su dauki buhuhunan su shiga muna dasu sassan mu takare da fadin idan baki da niyar daukan naki kya iya barin shi a gurin.
Tana tsaye tana kallo hadiye ta umurci kattan nan su saka muna kayan abinci a part din mu dole muka bar wurin ba shiri don mu nuna ma mazan wurin da zasu aje muna kayan abincin don akwai store da kitchen a part din kowa dama.
Fin karfi ne yasa dole ake girki gaba daya a gidan na kowa da kowa don ra,ayin uwargidan namu ran gida.
Sai da Ahmed ya tabbatar da an shigar wa kowa da nasa bayan ya mika masu kudin cefane yabar gidan zukatan kowa cike da farin cikin samun yancin kai a gidan ranan.
Ranan ba karamin jidali suka sake yi da Alh sani da hjy jummai ba don ta nuna bata yarda da wanan tsarin raba tukunya a gidan ba.
Inda shi kuma ya dage akan hakan za a yi tunda yana da halin yi kuma mahaifiyar shi ta umurta da ai hakan a gidan dole ne kuma kowa yabi dokanta har shi.
Ranan dai fadan hjy jummai bai tsaya ga mijin ta kadai ba har tsohuwar gidan ta hada ta fada mata abinda ke mata zafi gamay da ita akan zaman ta gisan dasu.
Har tayi ta gama babu wanda ya lekota daga sashen Amma don Amma din ta hana hadiye ta tanka mata tace a barta da zafi abinda ya samay ta ya fi komai ciwo a zuciyar ta.
Sai Alh sani ne da yaga abin nason ya wuce wuri akan mahaifiyar tashi ya fito da kanshi ya tsawata mata.
Ganin ba wasa ga maganan daya furta akan idan ta kara tankawa a gurin zai dauki mumunan mataki a kanta a lokacin.
Tuni ta bar wurin ta koma dakin ta tare da kamay bakinta tayi shiru don tasan zai iya yin abinda yace din wanda tasan akan mahaifiyar shi zai iya yin komai.
Yar ta ta uku ce ta fito daga daki a natse don tunda aka fara maganan tana ji bata fito ba sai da taji shigowar uwar tata ta leko falon nata ta samu guri ta zauna daga gefen uwar tare da kura mata ido.
Jin uwar taja tsuki yasa ta kara dago kai ta kalli uwar tasu kafin ta soma yi mata magana a cikin natsuwa tana fadin.
Mama maiye acikin yin hakan da har kike tayar da hankali ki kan dan wanan abi tunda baba ya zabi a raba ai shike nan ko shi yaga zai iya tunda ba kudi ki bane.
Ni ina ganin ai sai ki kya,, , , , , , , , tsawan da uwar ta daka matane yasa bata karasa abinda tai niyar fadi ba a lokacin inda mahaifiyar taci gaba da fadin wallahi salma ki fita idona a gidan nan.
Idan kema son samay ki kamar yadda suka samu ubanki suna juyawa ni ba su samay ni ba kuma ba zasu taba samuna ba.
Yarinya kamar ba nace ba baki san kishin uwarki ba ko kadan ki sa may yin haka ke nufi kuwa a gare ni a gidan nan hakan na nufin durkushewa na ne ga idon kowa yau ace har an samu macen da akanta za a rushe abinda na dade ina kafawa a cikin gidan don wata can mace yar uwata.
Mama ki kwantar da hankalin ki ba wai haka nake nufi ba nima kaina wanan matar sam batai min ba wallahi don bata kaunar ki nima ba zan taba kaunar ta ba a raina.
Kin san da hakan zakice in kyale saboda ita ai min yadda aka ga dama a gidan nan wallahi bai wanan matar ba a duniyan nan.
Mama ni naga idan kina irin haka sai su dauka abin yaci maki rai ne sosai har kike wanan magana tunda gaba na da yawa mamaki faketa har gaba ai zaku hadune da ita in tana ganin sunyi maki haka yanzu sunji dadi.
Nan gaba zaki kama su a hannun ki amma fa sai idan kin kwatar da hankalin ki har wanan munafukan maman su Rashida ni sam ban yarda da ita ba a???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? gidan nan .
Don da tana bayan ki ai da zata baki hadin kai ku hada kai kar hakan ya faru amma sai kika jita shiru batai magana ba sai komai ya lafa zaki ganta nan tana maki dadin bakin data saba.
Sannu a hankali maganar yar tata ke shiganta wanda yasa a hankali ta fara saukowa daga zafin da zuciyar ta ke mata a lokacin.
Kafin suyi magana wayan uwar yai kara inda ta kasa duba mai kiranta a lokacin sai yar tata ne ta iya yunkurawa ta dauki wayan tare da fadin yaya Abbsa ne ke kiran ki mama.
Ki dauka uwar tace mata don yadda take ji ba zata iya daukan wayan kowa ba a lokacin salman ne ta dauki wayan yayan nata.
Bayan sun gaisa yake tambayan maman nasu tace gata zaune tare damu bata wayan man yace wa kanwar tasa bro ka kira anjima don yanzun bata iya daukan wayan kowa.
What yace cikin wani irin murya tare da fadin may ke faruwa da mahaifiyar tasu ce sai salman tace kawai dan matsala aka samu a gida yau da ita.
Kinga fito fili ki fada min abinda ke faruwa cikin tabe baki tace akan dai wanan matar ta baba ce wai Amma ta tsaya mata akan su raba girki a gidan kowa ya dinga yin nasa a part din shi.
And so what ya furta sai may idan anyi hakan ai an hutar da mamane da wani abu salma tace shi nake fada mata ai yanzun mamane bata ganewa.
Yace common bata wayan muyi magana ta karawa uwar wayan a kunne taji dan na fadin mama akan dan wanan maganan kike tayar da hankalin ki a gidan.
Bayan kin san kina damu gani ga yaya Habbib ga su salma da Abba karami akan may hankalinki zai tashi haka kin san dai zamu iya tsare maki komai a gidan yanzu.
Abbas ba zaku gane abinda ke tayar min da hankali bane ku yarane har yanzu No no no mama kibar fadi hakan don Allah.
Yanzun dai ki kwatar da hankalin ki don Allah wanan maganan kada ya tayar maki da hankali zanyi magana da yaya habbib asan abinda za a yi kan maganan .


ZAINAB IDRIS MAKAWA
SEENABU
16/11/2021, 22:37 - ??5惙5惙5?: ALLAH SARKI YAU YAZO YA TAFI KE NAN UBANGIJI YASA MUN AIKATA ALHERI A CIKIN WANAN RANAN ALLAH YA SADA MU DA RAHAMOMIN SA YA GAFARTA MUNA KURA KUREN MU GA BAKI DAYA AMIN.


Mai karatu zaki dauka zancen yaran hjy Jummai zai kwantar mata da hankali ne don da farko har ta dauki maganan yaran da muhinmanci a ranta.
Ta sakar da maganan duk da ranta yana matukar sosowa da zancen don ya tsaya mata a rai tana ganin hakan komawa baya ne a gurin ta.
Shigowan hjy maryam part din yasa maganan yarta Salma yazo mata a rai dama tayi tsamanin hakan da farko kallon ta tayi ta watsar sai da hjy maryam din da yake makirace ta in ma bakinta tace.
Giwan gida kada ki dauki wanan maganan da zafi haka don ni tun ranan da aka kitsa hakan na sanda zancen sai dai banyi magana bane sai na gano abinda ake kitsawa din.
Don ina ranan da kika fito gaida tsohuwar nan kina fada kan suna labewa da Alh suna hira a can ba ranan girkin ta ba.
Tun wanan ranan aka kulla hakan a gidan sun riga da sun kulla abinsu dama aiwatar wa ne da tsohuwar taga baiyi ba yasa ta fadi a fili.
Dama ni a tayadda na samay su ranan nasan akwai wani babban al,amarin da zai faru a gidan nan don samun su nayi suna raha suna zaune kamar wasu kawayen junna.
Zancen tafiyana kuma da nayi wa Alh sai cewa yayi sai dai idan da maimuna zanyi tafiyan don itama tana da abinyi a bauchin.
Nuna masa rashin yardana da hakan da banyi ba shine mfarin rashin zuwana har yau da banyi ba tunds naki yarda inyi tafiya da yar gwal din gidan shi.
Jin hakan ya sasauta zuciyar hjy jummai tace ke kuwa gaki wace bata san abinda takeyi ba mana ba dole ki tafiya da ita ba tunda kowa na tsoronta kamar yadda ya take juya shi.
Ita wanan da taki zaman aure ta kaso tazo ta zaunawa mutand gida har da yara biyu dama abinda suke so ke nan su samu dukiya suyi yadda suke so dashi ta samu yanzu ji abinda ta fada a wurin.
Ni wallahi na dai bari an kai min nawa ne don kada ace mutum ya karya dokan maigida a sashi ga baki.
Ji munafuka bayan ta gama dariyan mugunta a daki yazo tazo nan tana dadin baki don kishiyar tata ta kara tunzura.
Nan ko mai zafin kishi ta hau ta fara fada tare da fadin dama nasan da manufa akai mi hakan don kawai aga bayana a gidan nan .
Anzo a taru a wawashe dukiyar banza a watse daga baya a koma ana fadin bai da komai yanzun don haka suke so wallahi zanyi maganin kowa a gidan nan har hadiyen dake zaman kama mata su ga yan uwa ko ?
Ni da naga tasbaha a gurin zumunta banji tsoro ba shida kafin ka gama da dan uwa daya ya biyo hannun ka.
Sun dauki lokaci suna zancr daya a dakin tana kara iza ta akan itama zata dauki mataki kan abinda ake masu a gidan cewar hjy maryam din.

Ya kasance yau ranan girkin hjy jummai ce a ranan ta kudirci yin magana da maigidan ba wani abin kirki tayi ba don kamar kullun yan aikin gidan tasa suka shirya mai abinci kamar na kullun.
Sai da ta gama abinda take ta tun kari part din maigidan da harta samu yana shirin kwanciya a lokacin ta shigo da sallaman ta dakin.
Ya dago tare da amsa mata sallaman a takaice don yasan har yanzun fushi take da shi kan abinda ya faru dan kwana biyu a gidan don babu walwala a tare da ita tun lokacin.
Don hakane shima bai yarda ya bata kafan da zafa kawo mai zancen ba don Ahmed ya fada mai duk yadda ya faru a gidan ranan.
Muryan tane bayan ta samu wuri ta zauna tace Alh magana nazo muyi ni dakai ba tare da ya daina abinda yakeyi din ba yace umhumm ina sauraren ki ai.
Gaskiya Alh bangane abinda kake nufi damu a gidan nan ba kokarin zama shima yake tare da fadin kamar ya dake da wa kuma ?
Tace dani da kowa na gidan nan da wanan maganar ta shafa kana tsamanin ban san abinda kukeyi ba a gidan ko ake shiryawa don dai kawai aga an kuntata ma rayuwan mu.
Wai kina fadin ana kuntata maki dake dawa kifito fili ki yi maganan da zakiyi kin tsaya kwana kwana.
Hakan ma zakace tunda ka na kokarin fifita wata akan mu yau ka fada min da abinda maimuna tafi mu dashi a gidan nan da tun shigowan ta kake kokarin muzanta muna haka akanta
Kai Alh ya girgiza lokacin da tayi wanan maganan tare da fadin nikan Jummai da zaki bi shawarata da sai ince kifita harkan yarinyar maimuna tun tana ganin ki da daraja a gidan nan.
Wallahi Alh yau dai ayita ta kare don sai ka fada muna abinda ta fimu dashi don ban gane may kake nufi ba da bin ra,ayinta
Mtss yaja tsakin takaici yace ke a tunanen ki haka ake daukan girma idan Allah yaba mutum don zaki zubawa da kanki da kima a idon kowa ne.
Kefa babbace ba sai na tsaya maki bayanin daukan girna a cikin lumana akeyin sa .
Indan fa kin matsa a kanta komai na iya faruwa na iya faruwa tazo bata girmamaki a cikin gidan nan wanda ni kaina ba zanso hakan ya faru ba a gidan nan kodon yarana dake kallon ku.
Don kina dai gani tun bata iya baki amsa har gashi yanzu ta fara budan baki tana magana a gaban kowa ba komai bane fa halin yau da gobe ne ya fara isarta.
Ita may yasa kuun bata kawo zancen kunyi mata abu koda kuwa din kunyi sai dai kune a kullun tayi maku wani abin mussanman ma ke jummai why ba zaki tayani gyara gidan nan ba kamar yadda naso sai kokarin bata min gida.
Da kike maganan ina kuntata maku ai ita maryam nan tazo tayi min godiya kan abinda hjy ta bada umurni ayi nakumayi sai ke ne da baki gudun halakana zaki zo ki sakani a gaba kina wanan babatu haka ina ilimin ki da hankalin ki yaje ne wai.
Abin nan fa sauke nauyi ne a gare mu duka akayi idan kin gane ko da basu magana amma kema kin san ana

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login