Showing 129001 words to 132000 words out of 419207 words

Chapter 44 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1479

fada min wai kun dawo kina nan kinawa gwaggo rikici.
Ke ba wani rikici da tayi tsaraban fitan su ne wai take tayar da hankali a kai kada kice tayi rashin hankali.
Kallon kayan da mama hadiye ke budewa a gaban ta tayi da ido tana fadin kayan may ye hakan ?
Nayi tsuru tsuru da ido sai mama tace Umar ne da zasu dawo gida ya biya dasu shago yace kowa ya zabi abinda yake so su wa yan nan sakarkarun wai sai biscuit suka dauko.
Ita ko diyana sarkin wayau kinga sai ta zabo wanan kayan haka shine fa take nan wai tsoro fadan ki takeyi.
Inda nake ta kalla take fuskan ta ya sauya tana fadin sayadi wanan rashin hankalin fa haka ?
Kin fi yan uwan ki ne da suka tsaya iya matsayin su sai kece zarara kika kwaso wanan kaya haka kamar hauka.
Muryan mama hadiye ke fadin ke tayani ganin abin mamaki wai fa super ne atamfar nan ?
Sai mamu tace wanan hauka daga ina hakan nan Aisha tace wallahi mama A ruwa bata san zai saya ba kai tsaye kin santa do tsokana don yace kowa ya dauki abinda yake so shine ta dauko su haka .
Idan yayi magana ta rama haushin fadan da yai muna a mota tayi wani rashin hankalin ne kuma ko ?
Bayan wanan shima umar zai biyewa karamar yarinya haka ai wanan abin magana ne gidan nan idan hjy ta sani sai ta gaskanta abinda take fada a kan mu.
Ikon Allah yanzu don umar yaiwa wanan yarinyar hidima haka shine abin tsayawa bata baki don zamani ya canza ko aimu da garemu wanan abin alfahari ne gare mu.
Don an baka toshi gwaggo wanan fa ba toshi bane rashin hankaline irin nata kawai sai amma tace yanzun dai na fahince ki sosai watau dai kin raba daya biyu a tsakanin yaran nan dai.
Jikin mamu ne yayi sanyi tace ba haka bane gwaggo wallahi abin ne naga kamar yayi yawa duk irin nasihan da naiwa yarinyar nan sai da ta zubar da kimanta a idon su.
Abu haka kamar wata zararariya har ina yar nan tasan ta zabo kaya haka masu kyau da tsadada sauri nace bafa ni na zabo ba yan wurin nace su tayani zaba.
Tace ina kinji rashin hankalin gwaggo tana kallon Amma data kawar da kanta daga kallon mamu din tana jawo ledan goron ta.
Ta juyo tana fadin ki fita daga idona maimuna tunda ke baki san abin arziki ba dai kayane kuma nace yar nan sai ta saka su a gidan nan kowa ya gani.
Mai mutuwa yaje ya mutu da bakin ciki ganin ran Amma ya baci sai mamu tace ban hanata sakawa ba ai amma ta bar wanan halin don watarana.
Kuma ta raba da yan uwan ta suma su samu da sauri Amma tace la,la,la haramiya wallahi ba wanda zata ba su a yanzu gaba daya ita zatai amfani da abinta tunda tana so waya hanasu su zaba cuncan ai dama ya basu Allah ya cisheta daga gare shi.
Dole mamu taja bakin ta tayi shiru tunda ta fahinci Amma ta daure min gindin abin dole ta kyale badon taso ba.
Mamu ta juya zata bar shiyan tana fadin ki kwaso kulolin abinci idan zaki dawo Amma tace yaki nan maimuna.
Sai mamu ta dawo dan shiru Amma tayi tana kallon ta kamar yadda kowa na fali yai shiru yana sauraren ta tace kada inji kada in gani kin yiwa yarinyar nan magana a bayana don zan saba maki sosai.
Ki godewa Allah kin samu yarinya mai tunane da har samun ta bai wuce muba tun yanzu don turamay nan da kike gani ra dauko da gaiya da sunana dana kakarta da yar uban ta saike ta dauko su tun can.
Wanan abun datayi ashe ba zai zama abin alfahari gare ki ba su wa yan nan sakarkarun ai kinga kayab shirmay da suka kwaso a can .
Sai magana na biyu wanan magana a barshi a nan inda akayi shi a tsakanin mu duk wanda ya fitar da zancen nan waje ban yafe mai ba bandai ki shi mijin naki ba zaki iya fada mai don ko baki fada ba ninan zan fada mai komai.
Don haka shine maganata dana kiraki sai mamu ta sauke ajiyan zuciya jin an hanata ta yi min fada da tasha alwashin yau sai naji a jikina sosai a gurin ta .
Mamu tace gwaggo ni ba nice uwarta ba ga anty hadiye nan ita ya kamata ta dauki na uwar bani ba.
Aiko da sauri Amma tace haram ai na fada maki ko kyale ba za a tabawa yarinyar nan ba yadda ta tsaro abinta haka za a yi.
Su gobe du kara idan haka uwar su tayi masu tarbiya da abin kwadai maza kwashe kayan nan ki tafi dasu kibi uwarki idan kuma kika bata shi ban sani ba ban yafe maku ba.
Kai hajiya ai abin bai kaican ba may ye na abin Allah ya isa a cikin maganan mama hadiye ta fada adan hasale tana barin falon.
Ni dai na kwashi kayan nabi mamu dasu a baya tare da dauko kulolin abincin Amma din na mara mata baya da kaya nikiniki a hannu na.
Sai dai muna fita mukai arba da hjy maryam da yaran ta a barandan part din ta zaune wai suna shan iska duk da wutan nepar da akedashi.
Dagani har mamu babu wanda ya kalli inda suke yayin da gaba dayan su suka tsuro muna idanuwan su a kan mu.
Ikilima ce tace A ruwa ina kuka je yau baki shiga islamiya ba nace inda kika aike ni sai uwar daga inda take tace magani ki ke nan da tambaya ina ruwan ki da ita aikin samu amsan bakar magana yanzu.
Mu dai muka shige muka kyale su a nan ina ta dari dari da mamu kada tayi min fada don naga ranta ya baci..
Sai dai muna shiga ganin manjo zaune a falon yasani matawa da fadan mamu na zube kayan ledan a gaban ta na kai kayan dana kwaso na abinci kitchen na dawo ina cire hijjab dina.
Yar nan ina kika shige haka duk yinin yau baku yini damu ba kafin in bada amsa Addah tace an fada maki sunje gaida matar yayan su na nan gidan ne ita da yan uwanta tace to to ai na manta wallahi.
Muna nan zaune da manjo muna hira da yake ina fashin sallah yasa na ban rama sallolina ba da akayi muna waje.
Kiran sallah ne ya tayar damu a gurin sai da muka fito bayan kawu ya shigo ya gaidasu manjo ya fitane na dauko ledan ina fito da turamay zannuwan daga cikin leda.
Wanda duk na dauko da sunan kowa na mika mai don na barwa Amma nata tunda zan dauko kayan a part din ta.
Turmin suke bi da kallon mamaki har na gama mika masu wanan fa na maynene Addah take tambaya ?
Nace wanda mukaje gidan sa ne ya saya muna su ni dama da sunan ku na zabo do yace kowa ya zabi abinda yake so.
Nan dai na sake na basu labarin komai da ya faru lokacin fitan namu manjo ta kalle ni tace A ruwa duk wanan kayan haka mai yawa ya saya maki a lokaci guda haka ?
Ko dai da wata a kasa ne yana toshi ba sani ba nace kai kaji manjo kuma sufa masu kudine ana fadin kudin kayan ya mika kati aka zare kudin.
Manjo yau naga gida wallahi wai fa duk nasa ne bana kawu ba wanan ma ai ina yafi kawuna kudi nake gani.
Ikon Allah kuma kawun ki ne ya haife shi nace shine babba dan sa ina gani ni dai ban sani ba son yawa ke gare su kuma fa uwar su daya dukan su.
Shigowan mamu yasa naja baki na ba tsuke don kada tace min na cika zuba kallon kaya tayi tana zama sai Addah tace gamunan muna sauraron ikon Allah wai fatima ce tayi muna tsarabab kaya haka.
Anty Addah wanan yarinyar ni ban san irin ta ba yau ai gwaggoce ta kwace ta a hannuna don tace kada in fara in mata fada zata saba mun in banda hauka irin na yar nan daga ance ku zabi abinda kowa ke so sai kiyi diban hauka haka.
Kurciyace wataran zataji kunyar yin hakan shine wanda kuka gani jiya da kuka iso suna magana da uwarsu a waje babban dan maugidan nan ne a kasan waje yake zaune da italin shi ta fada a takaice.
Amma tana fada muna yanzu wai gidansa abin tsoro ne kamar gidan dan yankan kai.
Da sauri mamu ta kallo inda nake zaune tana hararana tace wanan yar da sheri take wallahi umar din ne dan yankar kai ?
Bakinki kanin kafan ki duk na sake jin wanan magana zan saba maki sosai wallahi nan dau ta shiga fada masu irin aikin da yakeyi a can nima na bade kunne na ina sauraren sirin da ban sani ba.

Ya shigo gidan ya nufi gurin hjyn su sun gaisa ba wani damuwa ya dan taba hira da ita take mai maganan bukin yar uwanta da take son su halarta ranan asabar yace mama ai tunda muna gari zamuje daurin auren insha Allahu.
Ya mike yana fadin zan leka wurin Amma kwana biyu bamu hadu ba sai hjy ta tabe baki tana fadin ai kunfi kusa da ita kadaiyi takan tsantsan don kasan kansu a hade yake da wanan.
Yi yayi kamar bai fahinci may take nufi ba yace babu komai mama insha Allahu ina kiyayewa ai taji dadin samun kansa yadda take so a ranta.
Ya shigo da sallaman shi tana zaune saman kujera three seater inda ta mayar kamar shine wurin zamanta.
Shidai da zai samu sai yace Amma ta koma gidan sa da zama har matar shi ta haihu sai dai yasan hakan ba zai samu ba.
A yadda yasan Amma tana taushe zuciyar tane kan shi da matar shi don kawai, kawai a gare shi don haka ne ya kasa fadar manufan shi ga hakan tunda yana ganin wata kila merry ta haihu a kasan nan kafin su koma.
Tunda aikin daya dauka wasa abin ya wuce nan saboda wasu abubuwan sai a waje ake sayosu can.
Wanan matsalan ya kawo mai cikas ga komawan nasa inda da kyat ya samu ya shawo kan merry ta yarda ta zauna na dan lokaci ga kuma can iyayyenta ba faman kiran waya ta dawo kada haihuwa ya rutsa da ita a nan din.
Zama yayi a gefen Amma saman kujeran da taks zaune a kai tace nikan ban gane wanan auren ba yanzu tun zuwan matar ka sai ka share fiye da sati baka shigo gidan nan ba.
Ya dan kalleta yana fadin dama nasan da haka ina zuwa sai dai a kuraren lokaci nakan shigo gaida mama wani lokaci ma ban samun dady a gida idan nazo.
Eh lalai kuwa yanzu na fahince ka watau har ka shigo gidan nan ka fice sadauki baka damu da ka leko nan inda nake ba ?
Yana dan dariya yace tuba nake tsohuwa mai ran karfe kaina a kasa kin san ni ban iya karya ba a rayuwana ko nayima kamani akeyi.
Turmin zanin da ke shan kallo a gurin Amma tu lokacin dana bata ya gani aje a gefe yace wai ke Amma har yanzy kina dinki da kanki ne haka ya mika hannu ya dauki turmin yana juyawa tare da fadin zanin nan ko yana da kyau sosai.
Amma ta dan kalle shi tana murmushi tare da fadib kaima dai ka fada din daga masu kaunana zani yafito yasa yake da kyau sosai haka kowa na fadin kyawon zanin ai.
Su waye masu kokarin kife min gwaunati a furin ki har kike murna haka Amma a sanina dai nine dan gaban goshi naki tace har gobe kuwa.
Don wanan zanin daka gani daga gurin ka ya fito ya fada hannuna saboda so da kauna.
Da sauri ya kalleta yace ni kuma Amma yaushe akai hakan tace gashi nan dai ka tuna idan zaka iya.
Ya dan girgiza kanshi yace ban tuna ba gaskiya tace to ba wani ya bani ba sai amaryan ka cikin wanda ka saya mata dama wamu ta????? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? ? 
zaboshi ko dakin uwar ta batakai ba ta kawo min nan.
Da sauri ya aje zanin saman kujera yana tsuke fuska Amma tace ni wanan hadin naku yafi min dadi dana sauran .
Ta dago kai tana kallon shi ganin yadda ya bata rai tace ya kuma naga kamar bakai murna ba da hakan ko ita kaso ta daura zanin kagani a jikinta ?
Kai Amma da wani zance kike ni ban ma san abinda ta dauka ba a shagon don hankalina baya gare su.
Dan murmushi Amma ta sauke a fuskan ta tare da fadin sadauki ina fatan ba uwarka taci galaba bane a kan ka yadda na dauko maganan yarinyar nan ka bata ranka haka.
Yace No ai idan nace zanyi abu zanyi ne tunda kikaji na amsa zanyi din ne da ba zanyi ba tun farko zan bijire maku kan zance sai dai ina son farin cikin daddy mu nima tunda hakane burin shi.
Shiru Amma tayi tana dan nazarin maganan shi a ranta kafin tace sadauki shin tsakani da Allah ko zaka auri yarinyar nan don kada azo ai abinda za a dawo daga baya ana da an sani a cikin sa.
Yace watau Amma har yanzun dai baki gama fahinta ta ba ke nan tace ina zan fahince ka dan nan da wanan maganan taka.
Yace ba wani abu bane Amma sai rawan kan yarinyar dayai yawa dole daddy ya bamu time har zuwa lokacin da zatayi wayau.
Ikon Allah A ruwa din ce yarinya dan nan yarinyar data dade da zama mace mu lokacin da akai muna aure aiko faduwa bamuyi don a dakin mijina na fara al,adata ganni nan ko har yanzu ba abinda ya samay ni.
Amma maganan da kikeyi ba na yanzu ba zanso ace anbar zancen nan har nan da shekaru masu zuwa nan gaba daidai lokacin ta kara karatu sosai tasan komay.
Kaima sadauki da wani zance kake ai indai ina raye yaran nan ba zasu kara shekara ba a gidan nan nan gaba.
Yace amma Amma tace hakan ne buri na gare ku sadauki kaji na fada maka.
Shiru yayi yana tunane a ranshi kafin ya mike ba tare daya kara furta komai ba yana fadin ni zan tafi Amma sai wani lokacin.
Tace ka gaida iyalin naka idan ka isa gida maganata dai babu fashi a cikin sa baice komai ba ya nufi hanyar fita tace wai ko kasan kakan yarinyar nan tazo tana garin nan kaje ku gaisa.
Ya kulu matuka ji yake a lokacin kamar ya hadiye ranshi don haushin maganan tsohuwar shi da yazo da niyar su danyi hira ta dauko mashi magansn wanan fitsarararan yarinyar kuma.
In ko banda biyayyan mahaifa kamar shi za ace wai za aiwa irin auren nan na hadi haka kai tsaye.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:07 - ??5惙5惙5?: YA ALLAHU YA RAHAMAN YA ZUL,JILLALI, WAL,IKIRAM ALLAH,


Kawu ya dawo a gajiye yau girkin hjy jummai ce yasan ba wani kulawan da ya dace zai samu a wuri ta ba.
Ga mamaki shi hajiya ce ta shigo dakin dauke da kayan abinci yau bata turo yar aiki ta kawo mai ba kafin ya dawo a jera mai sai dai ya dawo gidan ya samu an aje .
Zama tayi bayan ta aje abincin tana mashi sannu da zuwa ya amsa mata a cikin sakin fuska don yaga yau tazo gare shi da shiri.
Sai dai yasan ba zuwan Allah da Annabi bane dole akwai wani shiri da tayi a kasa da take son gabatar don ya gama sanin halinta kamar yunwar cikin shi.
Remote ta dauka tana rage karan tv don karan yai mata yawa shidai bai tanka ta ba yana kallon ta sai da ta rage take fadin .
Yau ka jima a waje mana tana kallon shi yace eh abubuwa ne suka tsayar dani don kayan da Ahmed yaje daukowa suna gap da shigowa kasan nan.
Sai ta dan nisa tare da yin shiru kafin tace amma ina ganin lokaci yayi da Ahmed zai daina wanan tafiyan a samu wani daga cikin naka su fara wanan hidiman da kan su.
Dan murmushi ya sauke irin na manyan a fuskan shi yace jummai ke nan a cikin yaran nan yanzu wa kike ganin zan dorawa wanan nauyin mai wahala a kansa ya iya dauka .
Ko kin dauka aikin wasa yake fita yi can din kawai tace koma may nene shi ya

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login