Showing 96001 words to 99000 words out of 419207 words

Chapter 33 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1412

merry how dear you come here ?
What bout you here ?
Suna ganin shi dayan ta miko mai hannu tana fadin O Omar so you are around nice to meet you ta miko mai hannu ya rike suka dan rugumay juna ya dan bubuga mata baya kadan ya sake ta ya juya wurin merry din ya rike mata hannu sukai kamar yadda sukayi dana farkon sai dai ita bata sakeshi ba sai ta makale a jikin shi.
Kawu dake tsaye ya daskare a wuri daya ga wani irin malolon bakin ciki yana taso mashi.
Sai can umar din ya tuna da daddy su na gurin ya saketa bayan sun gama tabaran su ya gama shafan cikin jiki ta a gaban daddy ya juyo yana fadin.
Kawu wanan ce matana da na aura a can merry ya juya wurin ta yana fadin merry meet my Dad dan my brothers.
Tace wanderfull daddy nice to meet you tana dan rusunawa kadan da sauri kawu ya kawar da kanshi gare su ba tare da ya amsa ba
Hjy ta fito ya nuna ma merry mahaifiyar shi a cikin yanayin rashin jin dadin abinda dady yayiwa merry din na nuna mata kyama a gaban ta.
Hjy kan ta dan washe karan kada ham tana karewa merry din kallon mamakin abinda yaja danta a ga wanan bakar arniyar dake gaban su yanzu.
Ganin su a tsaye waje yasa hjy cewa ku shigo daga ciki da sauri kawu ya juyo yana fadin kada ki soma ki shiga min gida.
Ya fadi a tsawace gaba dayan su dake wurin sai da suka razana don irin tsawan daya daka a lokacin.
Ran hjy jummai ya baci itama tace don may zaka hana ta shiga gidan bayan kasan bamuwar danka ce gata dauke da jinin ka a jiki.
Wanan hayaniyae da suke yi ya jawo hankalin sauran mutanen gidan gare su suka fito waje da gudu.
Jini na fa kikace jummai a ina badai a jikin wanan kafirar data shigo min gida haka tsiraci waje ba tir da wanan rayuwan da danki ya zabawa kanshi.
Yaya gaskiya hjy ta fada idan baka raga mata don komai ba zaka raga mata ko don cikin jinin mu dake kike jikin ta ai balle ba a kore bako don da dalili tazo nan din da bata da dalili saita wuce ko kallon gidan nan ba zatayi ba ai.
Ke ke maimuna ni kike son koyawa ilimi ko may a gidan nan har ke kin isa in kafa doka kice zaki min nasiha.

Tun lokacin dana fito daga aji na dauko yan kanne na zuwa wurin da zamu shiga mota na hango taron students da alama wani rikici suka samu akeyi.
Ban damu ba sai dana tsaya nasaiwa fauziya ruwan leda da tace kishin ruwa take ji suka sha na riko su zuwa inda zamu shiga mota.
Tun daga nesa nake jin muryan yan ss3 suna fadin gobema ki kara yiwa wani iskanci ki gani a school din nan.
Fuskokin yan gidan mu na kalla naga yanayin su ba dadi a lokacin na kara ina dan lekawa inga abinda ke faruwa a wurin salmace wanan ya zaga wanan ta dangwara.
Kallin su ikilima nayi ina fadi ido rufe ku mai kuke jira baku shiga???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?r mata ba a hankali tace ke sinours ne fa ke fada kuma ai mu bari a nuna mata darasi.
Wani kallo nayi mata na kama ture mutane ina kutsawa cikin taron wallahi kada wace ta kara dangwaran ta .
Nace daga bayan su dayan tace idan aka dagware ta may zakiyi nace may tayi maku da zakuyi mata wana abin.
Wanan yar iskan agolan gida ce mai rashin kunyar tsiya ko idan ta isa ta tanka ki gani a nan.
Nace anty salma tanka masu don Allah muga tsiya salma na tsaye kimkam taki ko motsawa wata tace idan bata tanka ba bari mu, mu tanka mata ki gani.
Tana kai hannun ta saman jikin salma ina kai mata doka ta baya daga inda nake sai fada ya kaure tsakanina dasu Nafisa na ganin haka itama ta fara kai masu duka salma ma ta fara sosai na nuna masu tashin kauye daban yake dana birni.
Fada mukayi sosai sai da sauran malam dabasu wuce ba suka raba tare da daukan sunaye mu suka tsaya saida kowa ya watse a wurin.
Sai ga motar mu tazo daukan mu muka shiga ranan ba zancen da mukeyi sai na fadan har muka dauki su Aisha mukaje gida.
Muna zuwa muka samu tashin hankali a gidan wanda yafi namu na shirmay da muka baro a school.
Don daga Amma zuwa kowa na gidan suna waje cirko cirko dasu a cikin tashin hankali muka samay su.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:02 - ??5惙5惙5?: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM ALHAMDU,LLAHI RABBIL ALAMIN, , , , , , ,


Tun muna daga get muke jin hayaniya muryan Amma dana kawu sai na hajiya jummai dayafi na kowa tashi a gidan.
Abinda sukewa fitinan basu sani mamu ta kaita shiyan ta don kada su bar abin fadi wa dan su a baya.
Har ta fara gabatar mata da abin sha sai dai merry da taki kwantar da hankalin ta ga abinda taga sarakain nata sunayi wanda tasan saboda dalilin zuwanta ne gidan da tayi
Sai dai a lokacin mamu na iya kokarin ta wurin ganin ta kwantar da hankalin merry din a lokacin a part din mamu din.
Lokaci daya suka juyo suna mamakin rashin ganin su merry a gurin da suka barsu a tsaye lokacin da rikici ya kaure tsakanin Alh da hjy jummai akan kada merry ta shiga mai gida hjy kuma tace sai merry din ta shiga .
Ba inda zata da lalura a jikinta tunda don dan su tazo gidan sai dai in gaba daya zai hada ya kori merry da dan nasu.
Shine ya haukace yace sai Umar ya bar maigidan shi yau din nan ya kwashe takarcen matan shi yasan inda zai kaita shi dai kan ba dai gidan shi ba.
Mamu ta sulala ta kira Amma da mama hadiye suka fito shine har ta samu ta shige da merry part din ta.
Anyi daidai da zuwan mu umar ya jawo yar troler din kayan sa kannin shi na binshi a baya ya tsaya a sasanta zancen yana fadin kada su damu zai san yadda yayi indai wanan zai kara kawo rikici a tsakanin iyayyen nasa.
Ido rufe Alh ya juyo yana fadin ina kafiran ta shiga min a cikin gidana hjy maryam da bata san idon su Aliyu yana kanta ba ta nuna part din mamu da hannu.
Rai bace ya nufi gurin kofan ga su salma da basu san dalilin kukan uwar su ba suma suna kuka don ganin mahaifiyar su na magana a cikin kuka.
Haka yasani saurin zubewa a gaban kawu ina wani irin kuka mai ban tausayi ganin ya tunkari kofan mahaifiya na da tuzajara a fuskan shi kawu kayiwa Allah da manzon sa kayi hakkuri kada kaje kofan mamuna don Allah ka barta kawu.
Cak yaja ya tsaya wuri daya don jin kalamina na sake fadin kawu kayi hakkuri don darajan Allah da annabi kawu.
Suma su salma yadda nayi suka zube a gaban shi don dun dan fahinci abinda akewa rikici a gidan yanzu.
Nikan ban san komai ba na dai dauka fadan harda mamu ne yasa zai shiga yai mata rashin mutunci a part din ta lokaci.
Hannaye a hade ina rokon shi suma su salma suna a yadda nake har kannen mu muna kuka a cikin tashin hankali.
Amma tace ka duba yanzu ko abinda yaran nan sukayi bai isheka ishara ba kan dan abinda za a sulhunta ka tsaya kuna tashin hankali da mata.
Yace hajiya akan may zanyi magana su nuna min ban isa ba dasu karan bude part din Amma din yasa duk muka waiga wurin ta fito tana fadin.
Gwago tana part dina na sauke su a can don abinda ake a gaban su bai dace ba kodon cikin nan da halin da boyar Allah nan take ciki bai kamata ai mata yadda yaya yake nufi ba.
Kada ka manta jinin kafa ta biyo nan bata san kowa a garin nan bayan shi da Allah yau in abinda ta haifa ya girma ta bashi labarin abinda akai mata ranshi ba zaiyi dadi ba.
Kamar fa koran kare ake shirin mata a gidan nan fa alhalin da aure danka a kanta shiru kowa yayi a wurin lokacin da mamu take maganan
Maimuna may ke kanki kike son jifa kanki da abinda bai shafe ki ba a gidan nan ya shafe ni yaya tunda ya shafi jinin ka kamar nima ya shafe ni ne yau .
Duk abinda mutum baison aiwa nasa watarana ba zaiso shi ga dan uwan shi ba Ahmed dake gefe yana kallon rikicin gidan mai kama da sarka mai rikicin gangan yace.
Alh gaskiya hjy take fadi namu fa matar nan ta biyu yau ashe itama tana cikin ahalin ka ke nan don idan wani abu zai samay ta a garin nan kamar ya samu kowa na tare dakai ne ai.
Sani wai kanka daya kuwa idan hankali ya bace ko rai ya baci hankali fa ke nemo shi maimuna ki rike ta a wurin ki wanan umurni nane tana fadin haka ta juya rai bace ta bar gurin.
Kallon inda muke muna kuka yayi kamar zaiyi magana sai kuma ya juya ya wuce part din shi ya bar mu wurin tsugune muna kuka.
Kallin mu mamu tayi tana fadin ku tashi kuje ku cire wanan kayan don Allah ta wuce zuwa wurin bakin ta.
Daga hjy jummai har yaranta a wurin muka barsu a sandare suna mamakin abubuwan dake faruwa matar da yanzu suke maganan a kanta ta zamay masu bango yau.
Har mamu takai kofa ta juyo ta kara komawa wurin su tace don Allah hjy ki ja yaran nan ku bar wurin nan kada mutanen su kai ga fahintar halin da ake ciki a gidan nan.
Kuyi hakkuri da halin Alh har da girma a cikin al,amarin shi yanzu sai hakkuri da tsoho don Allah ku shiga daga ciki wanan tsayin baida amfani anan.
Kamar umurnin ta suke jira habbib ya karbi troler hannun yayan nasu ya nufi part din su da kayan hjy jummai ta daga kafanta da kyar ta juya zuwa part din ta.
Yana shiga yace mama zan wuce tace ina kuma zaka yanzu a wanan halin yace zan dan fita in dawo akwai abinda zanyi yanzu.
Tace samu wuri ka zauna ba inda zaka yanzu sai ka huce idan ka fita ai yarinyar ba zataji dadi ba.
Aliyu yace ki barshi ya fita tunda daddy ya rufe idon shi yace bai son ta zauna mai a gida may zata zauna yi kuma.
Ku baku san komai ba maganan maimuna data fada koda a munafunci tayi shi gaskiya ta fada barin yarinyar nan gidan nan yanzu ba zai haifa muna da mai ido ba a gurin ka nan gaba sai taga kamar an kyamace tane hakan.
Habbib dake shigo ya kalli yayan nasu dake tsaye ya dafa kushin yace yau nasan ko waye hjy maryam a gidan nan matar nan ita fa ta nuna ma daddy inda merry ta shiga dayake tambaya.
Na gani nima Aliyu ya fada a sanyaye yace ni na dade da karanta matar nan don yaranta ma idan kun lura ai basu ba daddy hakkuri ba kamar yadda yar wurin maimuna tayi.
Don itace ta sare mai jiki da kalamab data hadashi dashi yasa jikin daddy yayi sanyi hjy da ke jinsu tace wanan ai neman kindin zamane kawai har uwar duk abinda take badon Allah takeyin shi ba.
Nafisa dake rakube da salma tayi caraf tace a, a mama ba wanan ba dubi fuskan anty salma wallahi yau ba don A ruwa ba da sai kinje kin kwaso anty salma a school don taro yan ajinsu sukai mata ita daya su iklima na kallo basu shiga ba nima saida naga ana danbe da A ruwa na shiga akayi dani.
Abin da ya basu dariya ke nan dukan su a falon banda umar da uwar da shi murmushi yayi kawai don jin abinda kanwar shi ta fada ita kuma hjy haushi taji har cikin ranta.
Ta kalli salma tace amma anyi yar kawai yanzu may wanan yar kwalar zata shigar maki fada a wurin nan kafin uwar ta rufe baki Nafisa tace kwala mama bakiga yadda take daga katai bane tana kai kasa wallahi karfi gare ta sosai kamar mai aljannu.
Rufa min baki da maganan takaici kun bani kunya wallahi kun badani salma salma dai batace komai ba sai turo bakin da tayi gaba kawai tana dan magana ciki ciki .
Aliyu yace salma yaya akayi haka ya faru kuma tace wallahi yaya ban iyasu ne sun tarar min ni daya zuwan A ruwa ne na samu karfin fada nima kada naji kunya.
Daidai lokacin na shigo falon da sallama na gaida su ina fadin mamu tace wai yaya umar yazo bakuwar shi tana kiranshi.
Ina fadi na juya don zanine da katon hijab a jikina kawai a lokacin na tube uniform ke nan zanyi wanka mamu ta kirani ta aike ni.
Har na juya naji muryan Aliyu na fadin ke A ruwa a she ke shagoce a wurin danbe ance yau kin kada mata a fage ko ?
Dan dariyan gefen fuska nayi kawai na fita a daidai lokacin uwar ke fadin kada ka soma cewa zakayi wasa da wanan yar na fada maku.
Mama yanzu ai ya zama dole tunda tana shirin zama matar dan uwan mu yaya zamuyi da ikon Allah tace kadai ji na fada ma kada ka kawo min maganan banza a nan.
Ina shiga suna zaune sun wani isheshire kafa a falon namu mamu tana gefe dinining din mu tana zubawa yara abinci na shigo ina fadin mamu na fada mai.
Har na wuce naji dayan mai ciki tana fadin beauty sister what is your name na dan juyo nace mata fatima a takaice zan wuce.
Tace a cikin turanci yaya akayi nafi mijin ta kyau tana miko min hannu wai mu gaisa kallon inda mamu take na danyi naga ta kada min kai don yana daga cikin huduban da take min kan kada in yarda in hada jiki ko da mace yar uwata ce bata yarda da hakan ba gare ni.
Hannun na mika mata ta dan kama yaba hallitana ni dai duk a tsarge nake da matan don basu kwanta min a rai ba a yadda naga shigan su sai naji kyaman su a raina.
Duk sai na matsu da ta dauke hannun ta a nawa nace nima a cikin turanci ina son inyi wankane sai da ta danyi murmushi kafin ta sakeni tana fadin haka na da kyau.
Na shiga naji mamu na fadin idan na fito in samay su a part din Amma in bar bakin su huta a nan na dan dauki lokaci na fito da shirin zuwa islamiya daga can na nufo falo ina sauri.
Sai dai abinda na samu a falon ya ban mamaki don a makale na samay tsaye yana shafan cikin dake jikin ta wanda ni sai a lokacin ma na kula da mai ciki ce matar.
Yi nayi kamar ban gansu ba zan shige sai matar tayi magana tana fadin wanan sister din naja tafi ka kyau sosai how comes na dauka a gidan ku ba wanda ya kaika kyau ai.
Yayi dan murmushin da baikai ciki ba yace merry ke nan tace kada ka damu ina son ka hakan kayi mun fiye da ita ta fada tana dariya tana rogumoshi a jikin ta.
Ni dai na fice da sauri har kafana yana hardewa wurin sauri ina fada da mamu a raina data barsu suka shigo mata shiya suna iskanci haka do ban taba ganin mace dana miji a haka ba sai a film din tura idan muna kallo.
A part din Amma na samay su suna magana ina shigowa take fadin kin dauko abincin na zauna ina bata rai nace mamu wa yan nan mutanen suna nan fa harda wanan yayan su salma din da kika ce in kira masu yana ciki suna maki iskanci a falo.
Iskanci yar nan mutun da matar shi ki kira masu iskanci kallon mamaki nake wa Amma dake magana nace.
Amma wanan arniyar ce matar sa gashin doki da wani dan buje ta sa a jikin ta fa na fada a cikin mamaki.
Amma tace sai ki koyi zama da su don hakan dabi,an su yake ke dai kada ki koyi halin nasaran nan danagani yau a gidan nan.
Nace da sauri Amma a nan zasu zaune tare damu a aurin mamu na tambaya ina kallon ta tace yanzu wa sanar masu ni abin duk ya daure min kai ai.

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login