Showing 75001 words to 78000 words out of 419207 words

Chapter 26 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1435

ashe akwai aiki Amma ke nan da yake gani da saukin samu tayi mashi haka ina ga iyayyen shi kuma ?
Tafiya yake kamar wanda kwai ya fashewa a ciki jiki ba kuzari can ya hango Ahmed da mamu sun shigo da kayan da suka dawo dashi daga asibiti kallo daya yai masu ya kawar da kanshi gare su.
Idan da sabo ta saba da halin yaran mijin nata wurin nuna ita ba kowa bane gare su don haka ne abin bai damuwan ta gashi dai tana son mai godiya sai dai ba fuskan hakan a wurin shi tun a dakin Amma dataji shiyasa a dauko manjo tana son mashi godiya ya daga mata hannu alaman bai son hakan gare ta ta kyaleshi.
Hakama Ahmed da shima yake nuna bai damu dasu ba don akwai tsana karara a idanuwan su indan sun hade dashi saidai da yake maza ne basa fitarwa fili.
Mamu ta shigo da sallama tana aje flask din data dauko a gefen kujera ina daga kitchen naji muryan ta, na fito ina mata sannu da dawowa.
Bayan ta amsa take tambayana ya aiki nace na kammala gyara wurin nakeyi naji muryan ki tace sannu da aiki sai dai da zan samu a dan sa min ruwan zafi kadan tuwo nake son tukawa yanzu .
Nace tuwo kuma mamu may zakiyi da tuwo na tsare ta da ido ina tambaya tace asibiti zan tafi dashi nace asibiti kuma wa naki ke asibiti ?
Sai da ta mike tsaye take fadin wasu ne baki san su ba amma dai da sauki jikin maishi yanzu.
Mamu da gaskiyane Manjo ke asibiti garin nan kika boye min na karasa fadi kamar zanyi kuka.
Ta kalleni da mamaki tace a ina kikaji haka itace a asibiti ?
Ammace tayi subul da baka ta fada dazun tunda naji ko ta fada tunda tana boyewa nasan da gaske ne don zuciyana taki natsuwa da maganan.
Ta mike tsaye tana fadin eh itace don baki da natsuwa komai kuka yasa na boye maki don kada ki tayar muna da hankali.
Sai na dora hannu a kai na fashe da kuka ta daka min wani tsawa da sauri na shaye kukan dana fara tace wawiyar banza ai kinga irin haukan naki ba.
Ke yanzu dadin kine a yadda akazo da babba garin nan wani ya sani a samu abin goranta maki nan gaba kul naji zancen nan ya fita sai na saba maki a gidan nan wallahi.
Da sauri na ja bakina na rufi na bita da kallo har ta shige dakin ta na sudada na koma kicin ina aiki ina kuka a raina ina fadin kila ma mutuwa manjo xatayi yasa basu fada min ba tunane kala kala nayi shi a gurin ni kadai.

ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 22:50 - ??5惙5惙5?: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM, LA, ILLAH HA,ILAH, LA HAULA WALLA QUWATI ILLA BILLAHI ALLIYAL AZEEM

Don kada inga fuska mamu ta kara daure fuska gare ni ina kallo bayan ansha ruwa ta fice zuwa asibiti ita daya a cikin motar ta.
Sai dai sa,a na daya ta manta da wayan ta a falo yana caji ina zaune ina faman sake saken a raina can idona ya killo min wayan ta a caji.
Take wata dabara ta fado min a rai na dauki wayan na kira layin ya Ahmed nace yazo mamu tace in kirashi yazo ya kaini asibiti in kai mata waya.
Da mamaki yace anya Fatima maman yan biyu zata ce hakan tasan zan shiga massalici yasa tace in huta abina.
Nace itace tace haka da zata fita yace to shike nan gani nan zuwa ya bani amsa yana kashe wayan .
Zubur na mike tsaye nacewa yan kanne na suzo i kai su part di Amma su jirani a can yanzu zan dawo.
Ko dana shiga har lokaci ran Amma yana bace karewa ma abinda ban taba gani ba na sama tana kwance wai bata da lafiya tun kan asha ruwa.
Nayi mata sannu na fito bayan nayi wa su Aisha bayani ina fitowa Ahmed yana zuwa yace muje nace to yana gaba ina binshi baya har wurin motar shi muka dauki hanyar asibiti.
Har mun kusa ya rage gudu yace ke Fatima da gaskiya maman ku tace kizo asibitin nan kodai shirin ki ne ?
Nayi kasa da kai ba magana ya ja wani dogon tsaki yace dama nasan karya kike don karyan ki baya kai ko ina tunda baki iya ba zan sauke ki kiga abinda kike son gani a can.
Amma ki sani idan kika kuskura kika ce nina kawo ki kika mayar dani mutumin banza ga mutanen da nake jin nauyin su da kunya wallahi kema ranki zai baci fiye da nawa.
Baki san halina ba yasa kika sakani cikin shirmay ki fita min daga mota mara hankali kamar wani ubana har jikina yana cire na balle motar na fita da sauri.
Sai bayan ba fita na fara kalle kallen wurin da nake tsaye ga duhu ga hasken kwan lantarki a lokaci daya sai lokacin tsoro ya kamani.
Na juya naga yana kokarin ribas da motar shi nayi saurin kaucewa wurin na rasa inda zan nufa a cikin gurin .
Har na fara surfawa Ahmes zagi a raina sai naji muryan shi a bayana yana fadin wuce in kaiki dakin da suke.
Sai dai karki manta kika kuskura kika fada masu nina kawo ki asibitin nan sai ranki ya baci dani.
Har kofan dakin da suke ya nuna min ya juya da sauri ya bar asibitin saida na tsaya yin shawara kafin in tura kofan da sallama na shiga.
Idona akan manjo wace ke kwance kamar gawa sai na,urorin ??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????dake zagaye da ita a ko ina bata san wanda ke akanta ba a lokacin.
Dea sauri na karasa wurin gadon ban farga da wace ke sallah ba a dakin lokacin sai muryan Addah na naji tana fadin wacece wanan ?
Na juyo da sauri zuwa gareta na fada jikin ta sai kuka mai karfi ya zo min da sauri mamu data kagu ta sallamay sallah ta sallama.
Tace ke ke waya kawo ki nan may kika zo nema ko kinzo ki tayar mata da hankali ne kuma ?
Maza ki fice daga dakin nan tun ban saba maki rai ba yanzun nan maza ki fice ki bamu wuri tace a cikin wata murya mai karfi ba shiri na bar dakin dafe da bakina daya cika da sautin kuka.
Sai bayan na fita Addah ke fafin maimuna may yasa kika koreta haba dai kin san fa irin kaunar dake tsakanin su da babba.
Yanzu da kika koreta ina zata tafi mamu tace damay tazo dama ta nan ban san wanda ya kawo min ita nan ba wallahi shegen naci ne da ita.
Ina fitowa a tsorace hankalina tashe ban san inda zan dosa ba a lokacin na dade tsaye bakin get din ina sake sake a raina kafin in yanke shawaran bin kafa in koma inda na fito.
Do zan iya gane hanya don yanzu na dan san garin sai dai akwai tazara da gidan kadan da asibitin.
Ga garin sai walkiya ake alamun hadari zai taso a garin banyi nisa da tafiya ba aka fara iska a hankali na kara sauri don kada ruwa ya fado.
Tafiya nake don da kyat nake ganin gabana don iskan dake mayar dani baya duk kura ya cika min ido sai dai hakan bai hanani rike wayan mamu a hannu na ba gam.
Tasowan hadarin yasa abin hawa suka rage gudu a titin sai jefi jefi suke gilmawa .
Haka nake dan hadawa da gudu don in isa gida da wuri ina cikin tafiya mai kama da sarsarfa har ban san na hau titi ba a lokacin.
Karan taka burki danaji da karfi gaf dani yasa na rufe idanuna sai na jini a kasa tim na cikin motar ya leko daga tagan motar daidai lokacin da nake kokarin tashi tsaye yace ke wata irun mahaukaciya ce kamar dabba baki kallon hanya zaki wani hayewa mutane tsakiyan titi kamar na gidan ku.
Muryan yayi min kama da na yan gidan mu ina dan dangesawa na mike don jayewa a saman hanyan.
Ya sake fadin kauce dan Allah kina bata min lokaci har ruwa ya sauko ko na latse ki a wurin in take banza ke har da watan azumin kike fita yawon banza ki ?
Da sauri na matsa daga wurin da sauri ina kaucewa saman titi ina kallo ya ja motar shi ya barni a gurin sai lokacin naji kafana yayi min tsami na fara tunane naji ciwo a kafan.
Sai kuma na fara tunanen waye a cikin su da sauri na tuna shine habbib a cikin su nace lalai wanan yakai mara imani da rashin tausayi .
Ka buge ni kuma bai tsaya bani hakkuri ba ya hauni da fada da zagi lalai ba karya yaran hjy jummai basu da imani a zukatan su ko kadan.
Nasan duk ya gane ni amma ya nuna kamar bai san daga inda na fito ba har yake zargina da yawon banza haka dan iska kaci arzikin manjo yau don ba fada ne a gabana ba yanzu lafiyan kakata na damu dashi yanzu.
Da tunane kala kala har na karaso gida lokacin an fara dan ruwa da karfi ina zuwa na tura get naji a rufe na shiga duka.
Abin mamaki mamu na gani a tsaye ta kauce a hanya na shiga ba tare da tai min magana ba har muka shiga part din mu ina dan dangyasawa.
Mamu bata nuna min tausayawa ba ga abinda ya samay ni sai dai ko ba a fada na hango damuwa a fuskanta karara.
Ruwan sama mai karfi akayi ranan tun shigewa na daki nake jin dan zazzabi na son kamani ajikina wasa wasa kafin asuba sai ya rufe ni lif.
Gani ban fito ba yasa mamu duba dakina a cikin fada sai ta ganni dunkule a cikin bargo tundaga kaina har kafa.
Abinda yasa ta karaso inda nake ke nan tana fadin ai kinga na wanda baijin maganan iyayyen shi yanzu hankalin ki ya kwanta kin gano ma idon ki tashin hankali.
Dama kwancin kike son yi ke ma saj kije asibitin ku kwanta da kakar taki tunda haka yafi maki yarinya bajin magana .
Ta fita daga dakin can abin da da mahaifi sai gata ta dawo dauke da cup da magani a hannun ta tace oya tashi ki sha magani mara jin magana.
Banda wani katabus a jikina kamar ma na zautu a ranan komai sai ido nake bi dashi kawai ban iya yin maganan komai da kowa.
Ina kubawa naji tea ne mai zafi ashe na dan hade maganin ina miko mata kofin tace cikin tsawa kurbe shi maza ki shanye.
Haka na daure na sha fiye da rabi nayi kokarin aje kofi zan sauko daga kan gado tace ina zaki kuma nace zan shiga ban daki ne mamu.
Ta kauce tana bina da kallo sai lokacin ta kula ban tafiya daidai tace da sauri ke may ya samu kafan ki kuma ?
Nace mota ta buge ni a hanya ta tsura min ido kamar mai nazari kafin tace kin tabbatar nace wallahi mamu ina tafiya ban san na hau titi ba ashe mota na tafe ban sani ba.
Tace a ina ta buge ki na dan daga rigan dake jikina ina nuna mata wurin abinka ga farar mace wurin yayi wani irin ja da sauri mamu tace amma yar nan kikaki fadan wanan rauni irin haka ?
Nan dai na barta a tsaye na ja kafana a hankali zuwa bayin da kyat na iya dukawa da kafan na gabatar da uzurina lokacin.
Har na fito na samu mamu a dakin sai na nufi hanyar falo tace ina kuma zaki nace ruwa zan sha mamu.
Dawo ki zauna in dauko maki tana fadin haka ta juya ta fita sai gata da goran ruwa mai dan sanyi kadan ta miko min na karba ba kurba kadan na mika mata ta fita.
Sai gata ta dawo da man tiger tace in bude wurin ta shafa min tana tsaye na koma na kwanta ta sake fita.
Ban falkaba sai takwasa ranan na iya mikewa zuwa sallah fada ma Amma abinda ya faru dani mamu tayi sai gata ta shigo gaida ni tana ta faman tsinewa wanda ya kade ni da mota.
Nan dai na daure cikin karfin hali nace mamu dan gidan nan ne fa ya kadeni da mota kuma ya zageni da yar iska mahaukaciya wai na fito yawon banza.
Nan ta saka salati tana fadin yaran nan ko suna da imani wani irin bakin ciki suke son sauke muna a gidan nan ne wai.
Dama wanda yabar akidar shi ba wani imani ne da shiba ance yaren ka addinin ka kowa yabar gida gada ta barshi babu alherin da yarab nan suka koyo ga wanan tafiyan nasu sai bakin ciki da takaici idan kwai ya tashi fashewa a gidan nan tsiyan abin ba kan uwarsu zai tsaya kadai ba bakin cikin har mu zai shafa duka.
Mamu bata gane may Amma ke nufi da zancen ta ba sai tace ai basu dawo da wani matsala ba sai dai daukan kai da rashin ganin darajan mutane.
Uhhummm kawai Amma tace tare da fadin Allah dai ya kyauta yar nan ta juyo gareni tana fadin wanne daga cikin su yai maki wanan karen aikin haka ?
Gwago da ki barsu ai itama bata jin magana saj da na cewa yarinyar nan kada ta fita ban san yadda akayi yarinyar nan tasan vurin nan ba don bakin bin kwakwafin ta na tsiya ai sune maganin ta.
Amma gwago don Allah a bar zancen sai gaba idan sun kara don irin kawaicin da dan uwansu yayi muna kan kakarta kinga ina ganin har yanzu mahaifiyar tasu bata da wanan labarin.
Amma tace toh shike nan daba don haka ba wallahi da yau mai shi ya jini a gidan nan wanan an kashe ta yaso yin don haushin ta da suke ji.
Ta dade tana fada a kaina har zuwa lokacin da suka fita daga part din lokacin zazzabin ya kara taso min na kwata barci mm ai nauyi a dunkule.
Ban garen Umar yana jiran yaji kiran mahaifin su kan maganan su da Amma kamar yadda yai tsammani kira daga gare su tun bayan maganan su da Amma.
Sai dai har gashi ana ta faman shirin sallah har lokacin baiji wani abu ya taso akan zancen ba ko canjin fuska a gurin iyayyen shi.
Sai Amma din daya rasa gane ma inda ta dosa tun ranan da sukai maganan ta canza mashi kwata kwata bata bashi fuska yanzu ko kadan.
Yanzu ma yana son zuwa ya gaida ita sai dai yanayi daure fuskan da take mashine baya so ko kadan haka dai zai daure yaje su gaisa din.
Don Amma din wani babban makami ne a gare shi nan gaba a abubuwan dake shirin tasowa tsakanin shi da iyayyen shi nan gaba.
Da sallama a bakin shi ya shigo falon tana zaune tayi tagumi ta zuba ma wuri daya ido jin sallaman shi yasa ta dago tana kallon shi.
A sanyaye ta amsa mai sallaman ya shigo yana fadin dazun zan shigo naga ficewan ki nan sai na fasa shigowan .
Tace cikin dan bata rai wallahi naje duba wanan yar ne kuma yace wata ya ke kullu sai kin tafi duban ta ne kuna shagabata tana kara narkewa.
Kai ma ba haka nai maka duk cikin jikokina kaf ku fi tsaya min a rai ku biyun ban don naku yafi zuwa daya da nawa ko yanzun ma wani mara imani ya kade da mota a cikin gidan nan jiya da dare.
Amma mota fa kika ce tace zan ma wasa ne kafa yana nan ya hau sosai kuma uwarta da kawaici ta hana a fadawa mahaifin ku don gudun fita da halarcin da kai masu.
Amma Amma wanan aiba abin kyalewa bane don ba karamin magana bane idan tsotsayi ya kaishi ga kashe ta fa ?
Ganan min hanya kadai dan nan nima abinda na hango ke nan zan bincika in san ko waye don gaba tace shine daidai don bai kamata a kyale zancen ba don wani dalili can rayuwa ne fa .
Can dan shiru ya biyu baya saj Amma take fadin dama ina neman ka akan zancen kayan nan gasu aje har yau baka ce komai ba kuma har gobe jajibur.
Kaya Amma ya kallo ta yana tambaya yana rike da haban shi da hannu daya yayin da kafan shi daya ke tankwafe saman kujeran da yake zaune a kai.
Tace kayan da kasa aka shigo dasu nan mana tayi mai bayani yadda zai gane may take nufi da maganan ta.
Yace kai Amma suna aje ashe naki tsaraban ke nan ai da zaki rabawa mutane su dan jikan ki ya dawo kibawa yan uwa gaba daya mama ma na bata na bangare su ai ita da yan

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login