Showing 78001 words to 81000 words out of 419207 words

Chapter 27 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1424

uwanta.
Kai dan nan Allah yayi maka albarka ai ban san manufarka ba ke nan ya mike yana fadin zai fita nan Amma ta shiga kasafa kayan ita da mama hadiye mukan yan gaban goshi ne na samu tsaraba masu yawa sosai wanan lokacin don ammace mai rabon.
Wanan labarin yaje kunnen hjy jummai ta kulu da danta sosai sai dai saukin abin akwai da shakku da shayi tsakanin ta da dan don shi kaifi daya ne idan ya furta abu.
Tayi ta dakon shigowan shi bai shigo ba sai kuma ga su Aliyu sun shigo lokacin shan ruwa suna fushi yayi masu fada kan buge ni da mota da habbib ya tashi yi.
Suna shigowa uwar ta tare su tana fadin yaya na ganku haka Aliyu yana zama yace dan matsala suka samu da big bros a waje.
A gigice take fadin matsala kuma akan may kuka samu matsala kai da dan uwanka har haka sai Aliyu ne dai ke iya bata amsa da fadin.
Don kawai ya buge wanan yarinyar shine yake masa fada akan ya kula kin san hahbib shine yaso taso mashi ya dakatar dashi a cikin fada.
Kallon habbib tayi ranta na mata kuna tace wace yar ka tashi duka yace ba duka fa ba da mota ya kade ta lokacin da iskan nan ya taso jiya.
Habbib yace wallahi mama abinda bros keyi wani lokaci haka ya tursasa ni akan sai nayiwa wata tsohuwa can da Amma tayi magana aiki ashe kakan shegiyar yatinyar nan ne ma wa kuke kiranta yar agolan gidan nan taku.
Dam dam zuciyar hjy jummai ya harba take ranta ya fara baci idon ta ya rufe ta mike tsaye ta fara fada.
Lalai munafincin gidan nan yakai dama nasan yaron nan ba a banza aka barshi ba har abin yakai a hada min diyana fada a gidan nan.
Aliyu yace bafa fada sukayi ba mama ki kwantar da hankalin ki don Allah shi bros din ne yayi ma habbib fada a kan ya daina kada tsautsayi da kadara yasa ya kashe ta kinga ko gaskiya ne ai ya fada mai.
Suna tare uwaf amma ina tayi gaba ta fara da wurin mu na samu na dan tashi ina buda baki don mamu saboda ciwo na yau sau daya ta leka asibiti wurin manjo.
Daga sama mukaji sababin ta tana fada da tonon asiri kala kala wanda hakan ne ya jawo hhankalin sauran mutanen gidan suka fara fitowa daga part din su don gane ma idon su abinda ke faruwa dasu.
Alh sani shima ya fito hankali tashe yana tambayan mai ya faru a hasale ta juya inda yake tana fadin munafuncin gidan ga mana.
Diyana basu taba fada a tsakanin su ba sai a kan wanan bakar annoban yarinyar A ruwa ta kai muna ko ina a cikin gidan nan saboda samun wuri.
A ruwa fatima ke nan kike nufi munafuncin may akai maki keda diyan naki ?
Hjy jummai tace a munafunci mana tunda har aka iya boyen min abinda aka tursasa shi yayi wa dan uwanshi abinda rashin bai so ba.
Ke nifa ban fahince ki ba ki fito fili kiyi magana kin tsaya muna kwana kwana.
Sai ta boye zancen kade ni da mota ta fito da zancan asibitin kawai muryan Aliyu ne da tun dazu ne ya shigo ya tsaya yana sauraren ba tare da sunsan yana nan ba.
Yace mama yanzu fadan da nayi mai kan ya kula da kada tsautsayi ya gitta ya kashe ta iyakan fadan da nayj mai ke nan .
Mahaifin su yace wai shin wa aka kade Amma dake fitowa tace A ruwa ya kade ta fito asibiti duba kakarra jiya da dare.
Ranan sun ji nacin ran mahaifin su ya nuna ma uwar har diyan bacin ranshi akan abinda suke nuna min gidan yace shi amana ya dauko ni yana riko ba agola ba kamar yadda suke fadi.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 22:52 - ??5惙5惙5?: BISSIMILLAHI RAHAMAIN RAHIM , ALHAMDULLILAHI RABBIL ALLAMIN, , , ,

Ranan haka mukai buda baki babu dadi a gidan kawuna mijin uwata wanda hjy jummai fadan ta duk akan taimakon da danta yayiwa kakanane take fadan.
Rayuka sun baci a ranan don kowa yana wurin har mamu ta kasa hakkuri take fadin ban taba zaton don Umar ya taimake ni a gidan zai zama laifi ba don ko yaya dai su din diyan dan uwana ne ko ba aure a tsakanin mu.
Tace alfaharin ki ke nan dake da ma su zuga ki to ban haifarwa duniya da ba idan kina so ki jira naki su aimaka maki daidai lokacin Umar ya juya yabar gurin don zai iya cewa bai taba zaton haka daga mahaifiyar su ba.
Ganin ya fita suma sauran suka juya suka nufi hanyar fita waje suna mai mara mai baya sai dai kafin su fito ya riga da ya shiga mota yabar unguwan gaba daya.
Zuciyar shi cike da kunan rai ga halin da mahaifiyar tasu ta nuna a gaban su ranan ya fahinci wani abu sosai a zama gidan da take yawan korafi akai.
Tsaye sukayi cirko cirko a kofan gidan mai karatu abinda kika sani ne a wanan zamanin mai hali koda shine karami shike juya kowa.
Balle shi da yake babban su a gidan kuma suna sane da abinda iyayyensu ba su sani ba a gamay dashi jiran dan wani lokaci yake kafin ya baiyana kanshi gare su.
Har goman dare bai shigo gidan ba wanda hakan mahaifiyar tashi bata ji dadin yin hakan ba don tasan a ranan ran kowa a bace yake a gidan.
Sai dai bata damu ba abinda ya damayta shine rashin walwalan diyan nata da tagani a tare dasu gaba dayan su sun kasa sake jiki har lokacin da suka dawo gidan.
Shiko yana barin gida wani katafaren hotel yaje ya kama a nan ya kwana tare da kashe wayoyin shi.
Haka yasa uwar ta kara shiga damuwa don kashe wayoyin da yayi a lokacin dan haka tun da safe ta samu mijin su da zancen .
Nan kuma sabon rikici ya kara barkewa a tsakanin su tun sunayi a daki har abin ya kaisu ga zancen ta bar mashi gida hakan ya jawo hankalin kowa a gidan.
Haka akayi jajibirin ranan rayuka a bace a gun kowa babba da yaro don hajiya ta hanawa mutane zaman lafiya dadin takaicin ts shine rabon tsaraban da Amma tayi na danta .
Halin da ake ciki bai hana tayi fadan haka ba sai da maigidan yace duk ta kara tankawa ranan sai ya sake ta ganin da gaske yake yi yasa ta ja bakinta tayi shiru akan maganan.
Ita ko Amma kamar da gaiya dan duk wa yanda batai tsamani ba sai da Amma ta tsakura mata tsaraban ana sa albarka sai bugo waya mutand keyi suna godiya gurin hjy jummai din.

Nikan ina fama da kafana daya hanani shakat a rayuwana don ko wajen ban iya lekawa ba tun dawowana dana shige sai dai ina samun kyakyawan kulawa don Alh yasa an duba min kafan an ban magani.
Sai na ke samun sauki sosai ga kafan washe garin sallah haka na tashi sumul kafan ya huce sai dai alaman a aurin don jan da yayi bai bace ba har wanan lokacin.
Rigan da Amma ta bani cikin tsaraba mai kwaliya sosai na duwatsu na saka tare da rolling din dan kwalin shi a kaina zuwa kafada na.
Ranan har kwalliya nayi sosai a fuskana tsurana ya fito tsab na mace yar matashiyar balaga.
Sai dai duk abin da nake a cikin dauriya nake yin sa don hankalina yana gurin manjo dake kwance sharkaf a asibiti.
Ina dakewa ne don in nunawa mamu yadda take so dani don hankalina ya daga akan korar da tayi min a saibiti ranan har na hadu da kaddara macuci ya buge ni da mota a hanya.
Badon komai nake dakewan da dauriya ba sai don mamu taga nayi hankali ta barni in je in duba kakata dake cikin wani haki lokacin.
Mun gama duk wani abinda zamuyi har abinci na danci tare da fauziya don dai mamu taga na sake kamar yadda take so din.
Ganin muna zaune sai kallo nace ma fauziya ta tashi mu leka Amma muyi mata barka da sallah a part din ta.
Muka fito zuwa wurin ta a daidai lokacin duk yan matan gidan suna waje suna daukan photo tare da yannen su.
Gaba dayan su kallon su ya dawo gare mu kowa da abinda ke a cikin zuciyar shi ba kamar Umar da yagano rigan da ya sayawa mahaifiyar shi a jikina abinda yasa shi kura min ido ke nan lokacin da muka tun karo wurin da suke don shiga wurin Amma din.
Bazai mata da rigan ba don kudi ya bayar mai yawa yace a zaba mai riga ta kece raini a cikin mata.
Mai shagon ya zabo mai to yaya akayi wana rigan yazo hannun wanan yarinyar sai ya tuna da marrry yabawa ta saka mai a cikin kayan hjy jummai ke nan surin Amma na samay shi ke nan.
A lokacin Aisha kece min dana karaso gurin da suke A ruwa zo kema mu dauki photo da su bros yau take sallah a tuna baya wata rana.
Ke Aisha wace A ruwa kuma can don kema kin samu an laba ki ciki shine zski muna kalar dangi a nan sai Ikilima yar wurin hjy maryam tace wanan namu yan gidane bada yan ci rani ba gaskiya iya mu jikokin Amma zamu dauka.
Ke mayar da yukan ki kube, don ni ina da tarbiya don ba zanyi photo da mazan da ba Ahalina ba nasan mutuncin kaina ku da kuke ganin hakan wayewa sai ku mayar da hinma ai na wuce abina zuwa cikin part din.
Na fadi haka ne a daidai lokacin da hankalin mazan yake gurin da suke kallon wani a waya suna dariya hankalin su baya gare mu.
Ashe duk sun jini wani kallo suka jefeni dashi a lokaci daya na mamakin abinda na fada Aliyu ne yace ke wanan yarinyar may take daukan kanta.
Kada kaga laifin ta don su suka fara takalan ta da basu fada mata irin maganan nan ba da bata basu amsa daidai da su ba Aisha ke fadi.
Ni har mamakin yariyar nan nake ji wai tana ganin kamar tafi kowane ko may Habbib ya tare shi da fadin haka.
Nan dai aka shiga aibantani inda umar yana jin su yayi shiru kamar baijin abinda ke faruwa a wurin tsakanin yaran ya mayar da hankalin shi ga wayan shi.
Sai lokacin ya dago kai yana fadin na lura kuna cikin bada gudun mawan tashin hankali a gidan nan yanzu da yarinyar nan ta biyo nan wa tayiwa magana a cikin ku ?
Sai kowan su yayi shiru ganin yadda ya ke magana don da kyat duka fsayar dashi ayi photo bukin sallah yaci gaba da fadin.
Yarinyar nan kun sata a gaba ku kwantata ku gani idan kune a matsayin ta yaya zakuji idan ana maku hakan dan magana kadan kunsan zai iya zama babba a gidan nan.
Yana fadin haka ya juya yabar wurin sauran ma basu dade ba suka shigevwurin mahaifiyar su photon da aka fasa dauka ke nan dasu.
Ina shiga dakin Amma tana zaune an kewayeta da kwanonin abinci a gaban ta tana fisgan nama a bakin ta mukai sallama muka shigo.
Tana hadewa take kokarin magana ashe kafa yayi sauki har kin samu fitowa yau nace ina zama dana sani da ban fito a yanzu ba ai.
A jaka fada idan kayi magana ace baka da gaskiya da ke da waye yanzu kuma ta tambaya tana maida dubanta gare ni.
Ban bata amsa ba sai kokarin hayewa kujeran da nakeyi don in mike kafana dana dan tako yake min zugi a lokacin tunda ba wani fita nakeyi ba sosai.
Kafin muci gaba da magana sai ga Aisha ta shigo tana fadin kai mutumiyar wanan shiga haka kamar wata balaraba dake wallahi bakiga yadda kika tafi da imanin mu ba a gurin lalai hajiyan ki tana ji da budurwan nan nata.
Ido naga Amma ta kyat min sai kawai nayi dan murmushi na gane may take nufi na basar da maganan da Aisha take min ta zauna a kusa dani tana fadin .
Amma dai ba a kasan nan aka sai maki wanan rigan ba wallahi duk kin fimu mu haduwa baki ga yadda sallama ta tsuke fuska ba da tana muna sallo a cikin nata sai gashi sun ga naki ya cunawa nasu din.
Ranan hira mukayi da Amma da Aisha sosai do ban fito ba saboda nauyin da kafan ke mun yasa na dade a zaune a gurin.
Da yamma lis na fito don komawa part din mu a daidai lokacin Ahmed ke fitowa daga wurin Alh da yazo gaida shi da sallah.
A yadda na hango kofan falon da takalman maza da yawa ya nuna cewa Alh yana da baki a lokacin.
Tun daga nisa Ahmed dake kokarin saka takalma yake min murmushi abinda bai taba yi mun ba sakin fuska.
Haka yasa nima na mayar mai da martanin murmushi a fuskana na tunkari inda yake ina fadin Ya Ahmed barka da sallah.
Yana kallona a wani yana da ban iya fassarashi yace yau kanwatace haka a cikin kwaliya kamar wata yar sarkin larabawa ?
Wai ya Ahmed kayan sunyi min kyau ne kowa sai yabon kwalliyata yakeyi yau dama ai kaida mamu kuke hanani kwalliyan ai dama na iya abina tun a gida.
Yanzu dai barin nuna maki kyaun da kikayi gyara in dauke ku photo dake da fauziya ku gani nan yayi ta daukan mu photo muna dariya.
Sai ganin mutane na fitowa fallon wanda yaran gidan ne su uku sai wasu biyu da van sani ba a bayan su naji daga cikin bakin na fadin .
A a Ahmed ashe baka tafi ba ya dan yi dariya so guilty yana fadin wallahi wanan kanwar tawa ne ta tsayar dani da shiririn tan ta.
Nan ya tafi ya barmu da wayan shi muna kallo a cikin sa sai da muka gama naba fauziya ta kaimai inda nake hangen su.
Kwana biyun ranakun sallah mun sha gasan kwalliya a gidan wanda akeyi kamar ko wani gida da ke da yan mata duk da ban kai su shekaru ba ina tsone masu ido.
Har na bar fita ranan na uku ga sallah da safe sai ga mamu a dakina ta tsaya daga kofa tana fadin ki shirya idan mun gama girki muje wurin babba asibiti yau.
Wani irin tsale nayi ina murna da sauri nabi bayan ta ina tambayan ta may za a girka don in dora da wuri mu gama.
Tace tuwo don kin san shi tafi so don yanzu tana cin abinci har da yunwa yaso yai mata illa saboda rashin kulan da bata samu sosai a can.
Haka na zage nayi aiki mamu tana duba min har na gama muka shirya gaba dayan mu zuwa asibitin .
Mun fito ne daidai lokacin da baki ke zuwa gidan na sheda su kannen kawu ne su kawu bala da kawu suleiman muka tsaya muna gaisawa dasu a wurin .
An dan taba yar magana tsakanin su da mamu wanda ni ina bakin motar ta banji abinda suke magana akai ba tazo ta shiga muka tafi.
Ashe mun bar baya da kura a gidan don Amma ce ta aika suzo gaba dayan su tana son ganin su wanda dama suna da niyar zuwa sai dai ba a lokaci daya sukan zo ba don haka ta nemay su a wanan lokacin.
Duk da kiran bai daga masu hankali ba don takan nemay a haka idan wani magana mai muhinmanci ya taso gare ta daya shafi kowan su .
Sai da suka shiga wurin dan uwan su suka taba hira dashi suka fito zuwa jin kiran da tsohuwar ke masu a lokacin.
Su shiga sun samay ta zaune da diyan ta mata su biyu a lokacin suna dan maganan su ba mata shigowan su aka fara gaisuwa a tsakanin su.
Bayan gaisuwa da yar hiran lokaci kawu bala ya fara magana akan neman da mahaifiyar tasu take mashi a lokacin.
Sai kowan su ya natsu yana sauraren dalilin kiran a cikin ladabi gaba dayan su suna kasa zaune har matan sun sauka ka kujeran sun zube a kasa kamar yadda yayyu su sukayi.
Dan kallon gefen Alh sani tayi tana fadin zanso kafin in fara magana a kira min matan ka gaba dayan su do suma maganar ta shafe su.
Alh sani yaji wani iri don yana zaton irin iya shegen da iyalin ke yawan yi ne a lokacin wani abu ya shafi tsohuwar har zatai magana.
Don Amma bata da yawan magana kan sarakanta ga

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login