Showing 324001 words to 327000 words out of 419207 words

Chapter 109 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1472

jiki ya bude idon gaba daya ya sauke su gareni yana fadin fatima kece ?
Kawu nice yace Allah yai maki albarka Fatima kinji nace amin kawu a sanyaye.
Muryan hjy ce a bayan mu tana fadin sannu Alh a daidai lokacin da likita take tayar da kawu zaune daga kwancen da yake.
Ya zaunar dashi tare da jinginar dashi a jikin bangon da gadon yake na dan fita zuwa wurin su mamu dake waje nace su shigo kawu ya falka.
Tare muka shigo dasu office din sai faman sannu suke mashi da godiya ga Allah da likita.
Nunani likita yayi yana fadin ga wace ya dace kuyiwa godiya don ita ta bashi kulanwan gagawan daya dace kasancewar ta babban likita data san aikin ta.
Da badon ta bashi abinda ya dace ai mashi da faduwan shi ba da abin ya zama babban matsala yanzu.
Hjy maryam.tace ko za dan bashi ko tea ya shane don bai karyaba koda abin ya faru dashi.
Yace komai zai iyaci a yanzu ba wani matsala ai ta juya tana fadin bari aje gida a dauko kayan tea ke nan.
Likita yace No zaku iya zuwa dashi ai gida ba abinda zai faru insha Allahu ai ita aikin tane ta sani yana nunani da hannu.
Muryan hjy ne take tamnaya nawa zamu bayar likita sai mu koma gida yace haba dai mama.
Kuna iyayyen Fatima kuma zan karbi wani abu a hannun ku kawai dai a daina bata mashi rai dan gujewa irin haka yanzu.
Ga wanan maganin su zaku saya ya dinga amfani dashi ya kalleni yace kin dai san doze din da zaki bashi ai.
Da dai ka fada muna likita zaifi ya danyi dariya yana fadin hjy sai naga kamar kin raina karatun wanan yar taki dai ?
Wanan fa ko a can London babban likitace don bata taba faduwa karatun ta ba har ta gama nayi mamakin da ta dawo kasan nan ta labe a guri daya haka gashi ana neman manyan likitoci irin ku a kasan nan yanzu don matsalin mata da yai yawa.
Kyaleshi tayi don da ba don taimakon da yai muna ba da yasha bakar magana a wurin ta lokacin yadda ya bata haushi yana wani yabona gaban kowa haka a samu abin bara,dawa kuma.
Kawu da kanshi ya taka yana kara yiwa likitan godiya suka fita na juyo a hankali na kalli likita nace a sanyaye doctor mun gode zamu tafi sai wani lokaci kuma ?
No ba godiya tsakani mu ai kin sani nace nagode na juya na zan fita ya bini da kallo har nakai kofa na kama zan bude yace wai ina mijin ki ne Fatima ?
Yana nan na bashi amsa yaran ki nawa yanzu naga ga wani ciki a jikin ki kuma uku na bashi amsa a takaice yace mijin nan naki ya faye wayon tsiya ya tare ko wani kafa.
Ni dai na juya na fita daga office din da sauri zuwa wurin dasu mamu suke na samu suna jirana don key yana hannu na lokacin .
Kafin mu zo har hjy tasa an tayar da mota sun dauki hanya sai motar mamu ya dan bamu matsala wurin tashi da kyat na samu ya tashi ina fadin mamu wanan motar take ai ta tashi aiki sai wata sabuwa kuma ke nan .
Kowa sai mamakin yadda kawu ya murmure kamar bashi aka kwasa ruwa ruwa zuwa asibitu ba a lokacin.
Falon na kawu suka nufa nikan na shige part din mu don in watsa ruwa a jikina kafin inyi sallah.
Sai da nayi sallah na fito na samu abinda naci don ban ko karya ba muka fita daga gidan.
Bayan sallah la,asar na shiga wurin kawu in kara gaida shi da jiki a nan na samu matan nasa duka yana zaune kasa ya mike kafa kamar ba kawu bane da safe ya daga muna hankali sosai.
Da sallama na shigo falon na samu karshen kujera dake kofa na tsuguna ina gaida shi da jiki yace Fatima jiki da sauki.
Aiku keda sannu keda likita hjy maryam tace ai yaron nan yasan aiki shi sosai wallahi jifa Alh kamar bashi ba ni abin ya bani mamaki sosai irin hakane fa kwanaki har ya kwantar da Alh kwana da kwanaki asibiti.
Mamu tace bakiji a waje yayi karatun shi ba ga kuma kayan aikin da suka saka asibitin yanzu ai shi yasa mutane yanzu suke tururuwan zuwa asibitin nasu.
Wasu dai ke karatu waje su karanto abin kwarai wasu kan insunyi sai dai su rike kwali sunan su likitane ba a san komai ba.
Amma a gaban kowa yace fatima tafishi kokari don ita tayi abinda ya dace kafin aje can hjy maryam tace .
Kai maryam da wani magana kike wallahi zai fito fili ya fadi gaskiyane a gaba kowa kai hjy komu fa nan munsa yarinyar nan tayi kokari kafin aje can.
Tayima kanta ai ba wani ba murmushi kawu yayi yana fadin Fatima yaron wani garine wai nace kawu dan garin nan ne ko dan gidan Alh canji naji akace yake .
Au kice dan manyane ya samu karatu yadda ya dace ko can ai inga kudi kudin suna aiki sosai.
Kawu yace yanzu ai na samu likita sai dai matsalan kada na takura mashi don farawa da iya yaki karban kudi.
Kawu muna mutunci dashi tun a nan dan aji su anty salma ne shi yana gaban mu sosai a makaranta.
Ai kaji abin hjy ta sake fada yanzu ina wani mutunci ga macen aure da wani namiji don Allah ai irin abinda akewa gudun ke nan.
Na mike ina fadin kawu Allah ya kara sauki ya amsa da amin fatima na gode kinji nace kai haba kawu.
Ina fita mamu tace umhumm kai duniya yau aka fara karatu ina dai karatun nan dan kowa yayi shi a gidan nan kowa kuma yasan yadda yanayin karatu yake ai.
Maimuna kawu yace ki bar zancen nan don Allah kinji abinda likita ya fada kafin mu dawo gidan nan.
Duk wanda yai jifa a kasuwa yasan wanda ya jefa akace don haka tankawa yabawa tunda ita bata girma a rayuwan ta.
Tau yau kuma taron dangi za ai mun ne a gidan nan don na tabo ya gwal din ku ai komai zanji kenan a gurin ku ashe ?
Ke bari na fada maki jimmai ba tsorin ki nake ji ba gidan nan baki haifeni ba baki kuma girmay ni ba asalima a karkashina kike zaune.
To wanan fitinan ya isheni haka ki sakewa yar mutane mara tayi fitsari a rayuwan ta kin hana yarinyar nan zama da danki.
Yanzu kuma kina kokarin neman sheri ki lakamata naji karatun banza fatima tayi ashe tayi kokari tunda tayi har ta karbi kwalin ta.
Ke aiko secondry naga kin kasa tsayawa ki karbi kwali shi a hannun ki saboda takwallancin tsiya.
Kai haba wanan abin naki da me yai kamane haka a duniya kullun mutum bai maka kirki sai kokarin ganin sherin mutum kike nema ki fada.
Keko ba mai fadan maki hakan baisa kin gano ida matsalanki yake ba balle ki gyara kowa gidan nan yasan bakin cikin ki da yarki ya kaini kwance bawai ba a sani bane .
Ido na saka maki ingani ko zakiyi nadama da abin kunyar da kuka jawo min a garin nan dakuma wurun yan uwana.
Yanzu Alh ni kake fadawa wanan maganan haka yace an fada ke wacece da ba za, a fada maki ba jiran yaran ki suzo garin nan nakeyi muyi zaman karshe dasu akan matsalan ki da yarki.
Yanzu Alh akan maganan nan danayi kake fada min wanan magana haka dan waye baida matsala a duniyan saukin abin dai a tare muka haifeta tare kuma muka bata tarbiya dakai.
Tana kaiwa nan ta mike tabar falon fuuu ta fice acikin fushi taji zafi da nauyin wanan maganan da yayi mata a gaban kishiyoyin duk da tasan sun sani.
Saidai bata bada kafan da wata zata samu fada mata shiba a gidan shiyasa ma yanzun din bata yarda taji kunya ita kadai ba .
Zama nayi ina tunanen kalaman hjy gareni na dan murmusa don zuwa yanzu na gama fidda rai ka kaunar hjy a gareni kuma.
Wayana na kalla dake gefena namika hannu dauka naga ya kamata in kira inji na daukane naga miscall din yaya har biyu.
Kiranshi nayi ya dauka bai bari nayi mai sallama ba koshi yayi yace ina kikaje kibar waya na ringing baki daga ba.
Mun tafi asibiti ne wallahi subbahanallahi baki da lafiyane komai nace a,a kawune yau jikin nasa yadan rikice masa amma yanzu da sauki mun dawo gida dashi.
Innalallahi ya fada kafin yace mai ke damun shi ne har asibiti nace damuwane kawai nake gani don faduwa yayi sume dazu din Allah dai ya kawo sauki wallahi amma abin ba dadi gaskiya.
Yana ina yanzu nace yana gida yanzun ma nafito gaidashi ya danyi shiru can yace Allah ya sauwaka.
Ina Sultana tana barci na bashi amsa zan kashe in kira daddy yanzu inji yaya yakeji da jikin nasa nace a gaida min da yara zasuji yace yanzu sunyi barci tun dazun.
Muna kashewa ya kira daddy sun gaisa yake tambayan shi yaya jikin nasa yace da sauki suka dan taba hira dashi akan jikin kafin ya kashe wayan shi.
Anyi haka da kwana biyu sai ga yaya da yan uwan shi sun shigo gari da dare sun dade a falon mahaifin su kafin su fito zuwa part din mahaifiyar su.
Basu tsayaba don dare yayi a lokacin don haka ban ganshi ba a ranan sai washe gari da suka shigo ya fara shiga wurin mu suka gaisa da mamu daya samu a falo.
Jin muryan shi yasa na yunkura na fito falon ina mashi sannu da zuwa lokacin mamu ta fita daga part din ta barmu.
Ya dago kai ya kalleni yana fadin may yasa wanan kunnuwan naki basa jin magana zahra ya fada yana kallona.
Cikin mamakin abinda nayi na dago kai ina kallon shi fuska dauke da mamaki shi nace may kuma nayi yanzu yaya ?
Kin san nazo gidan nan jiya baki fito kin ga saukan mu balle har in samu darajan samun tarbo daga wurin ki zahra.
Ciki shagwaba nace yaya shine nafito fa yanzu in maka danaji muryan ka ka shigo ya miko min hannu na make kafada na alaman ban zuwa.
Yace me kike nufi da hakan nace kaima kasan ba daidai bane ai tunda an muna iyaka a tsakani mu.
Kema kinbi zancen kenan yanzu nace tun ranan da kawu ya furta hakan na dauki zancen don har yanzu wace kawu ke jiran saukowan ta bata da niyar sauka daga maganan.
Illa ma kiyayya a tsakanin ni da hjy a kullun kara karuwa yakeyi a zuciyar ta don haka dai nake ganin ya kamata mu hakkura da junan mu zaifi mu alheri musanman ma kai yaya da maganan a wurun mahaifiyar ka yake.
Zahra you are very stupid ni kike fadawa wanan maganan haka a tsakiyan idona .
Ki fada min laifina a cikin zancen da kikeso yanke mi hukunci haka banga laifi ki ba don kinga kamar na daga maki kafa da maganan yasa haka yana fadin haka ya tashi ya mike yabar falon .
Ya barni zaune ina binshi da kallo nikuma ban damu da fushin shi ba don yin haka shine mafita a wurui mu.



ZAINAB IDRIS MAKAWA
17/11/2021, 07:13 - ??5惙5惙5?: Na dauka ya fita daga gidan ne ashe suna part din mahaifin su sundan dade dashi suna ganawa kafin su fito su shiga wurin Amma.
Ana nan sun dade wurinta shi da yan uwanshi tana magana kan fushin da habbib keyi na rashin zuwa gida daya dauke kafan fashi don dan matsala da suka samu da mahaifiyar su.
Amma tace ashe da kaine dan uwan ka yaya ke nan zakayi kiri kiri sun rabashi da matarsa don kawai wani dalili na su can .
Jin haka ya umar ya mike tsaye yana fadin ina sauri ne fa suma yan uwan suka mike daga inda suke.
Tare suka fita daga gidan ya Umar da yan uwan shi duk da basu inda zasu tafi bi a lokacin ido kawai suka sawa yayan nasu.
Lokacin ina gyaran falon mamu da ya sha gyara sai kamshi yake bayan na gama don kannena sun tafi school lokacin.
Part din Amma na koma muna hira don ranan murja tana gida bata fita ba zuwa school bata zama yanzu suna final year din su ke nan.
Amma ne da tai shiru tana tunane can ta juyo tana fadin hankalina baya kwanci idan ba naji kiran yaron nan akan maganan komawan ki gidan shi ba.
Allah yasa dai wanan karon a shirya don kamar karfin maganan wurin hjy yake ai kawu ya zuba mata idone ko zata sauko daga kudirin ta nayi mai auren da tace ai.
Sallaman mamu dake rike da hannun Abdulsalm tana fadin ga baki kunyi fa.
Mamakine kwarai ya kamani ganin yaran don yaya bai fada muna cewa tare suke tafe da yaran ba dazun daya shigo ya fita yana fushi dani lokacin.
Na mance a gaban mamu da Amma nake na rugume yarana a cikin murnan ganin su suma kankameni sukayi suna murna tare da tambayana cikin harshen turanci may yasa na tsaya nan na barsu su kadai ?.
Kowa yayi shiru a falon yana kallin mu ashe kuna da aiki idan jiran komawar uwarku kukeyi gidan ku mamu ta fada da hausa tana juya zata fita.
Mekike nufi da wanan maganan da kike yawan yi ne maimuna tace gwaggo gani nayi dai mahaifiyar umar bata da niyar saukowa ga kudirin ta har yanzu ai.
Kudirin tana banza da wofi ita ba zaune take a gidan mijin ta ba lafiya iya shegen da takeyi a gidan nan idan ba yaron nan bane wazai daukan matashi haka .
Juyawa nayi aurin maria muna gaisawa na fita zancen su ina tambayan ta bayan robon mu.
Maria ta hade hannayen ta guri daya tana rokona inyi hakkuri mu koma tare wanan karon.
Murmushi nayi mata kawai ina dan kwantar da yaran a jikina ina jin wani yanayi mara dadi yana sauka min a zuciyana lokacin.
Ido na lumshe ina ci gaba da tunanen halin da rayuwan aurena ya fada cikin matsala saboda uwar mijin da ban mata komai ba a rayuwana.
Ranan dai tare da yarana na wuni a gidan sai dare ya aiko aka dauke su hakan kuma shi ya jawo magana wurin hjy.
Cewa tayi yara sunzo na hana suje gurin ta na hana su santa a matsayin kakan su na hana mata shakuwa da jikokin ta su saba da ita tun yanzu.
Zance yakai har wurin Amma don kawu yanzu ba a son yawan bata mashi rai sosai haka yasa Amma tayi masu iyaka da tayar mai da hankali.
Bayan ta gama magana Amma ta juya wurin mamu tana fadin maimuna da yaran sukazo basuje gurin ta bane jiya ?
Gwaggo bansan ko an kaisu ba ko ba akaisu don ni jiyan ina hidima da Alh ban zauna ba.
Yanzu kunyi min adalci ke na maimuna kina kokarin rabani da yaran nan
Ida ba baki kaddaran daya hada dana da yarki ba da babu ta jnda zasu hadu ko ki taba gani inda aka hada tsiya da arziki a wuri daya. .
Kada kiga nai wanan maganan kice ko yaran yarki sun dameni ne a raina a, a idan ma kun rike abinku duk dayane don dama wanda bai gajiya arziki ba ko sashi a baitalmali duniya tsula zai fito daga cikin shi.
Baki san zafin uwa ba maimuna haka ma yar ki yasa a kullun kuke kokarin kuga kun rabani da dana mafi soyuwa a gareni.
Hjy inda kece ke bayar da arziki ba Allah sai ince na debe rai ga wanan arzkin da kike kira kullun har yau ke kuma banga arzikin da kika tarawa kanki ba a gidan nan.
Kai da kun bar wanan magana haka hjy maryam tace yara ko anki ko anso yanzu sun zama na mutum biyu ai a gidan nan irin wanan fada kan yaro ko fili sai Allah ya dau ran guda daga cikin ku a zauna lafiya.
Maryam ni kike kokarin fadawa magana a fakaice hjy tace don taki jin azo magana hjy maryam ta dan kauce mata yanzu zata nuna mata bacin ranta a gurin.
A, a hjy akan me zan fada maki magana kamar ina jirake dake gani dai nayi abin bai kaiga kallo ba.
Hjy amma dai da kike fadin wanan magana kin san na shiga dasu su gaida ke kika barmu a falo zaune.
Irun wanan ba jiya kika fara yi mun haka ba idan na shiga part din ki sanan ina son ki sani mamu dai ba shegiya bace da uban ta a duniya kuma

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login