Showing 99001 words to 102000 words out of 419207 words

Chapter 34 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1416

Sallaman Umar ne a kofan falon suna bayan shi wani haushi naji don na dauki abinci ke nan zanci suka shigo dakin yana gaba suna bayan shi.
Ya samu wuri ya zauna yana nuna masu wuri a gefeb da mamu take zaune da sauri na kalli mamu sai naga ta dan mike tana fadin ku zauna ga wuri nan ta koma gefen Amma ta zauna.
Yace Amma ga merry nan nakawo ta ta gaida ke da kaina Amma tace uhmm naga mari sai dai ba haka akaso ba wai kanin miji yafi miji kyau.
Amma zaki fara ko yanzu kuma may tai maki ya fada yana dariya yace m hjy maimuna wanan itace merry matata ita ma yar nan kasan ce sai dai ba a nan aka haife ta ba haka yasa bata jin hausa ya kalli merry a cikkn kulawa da so da kauna yana gabatar mata dasu mamu da amma da matsayin su gare shi.
Ya mike yana fadin zan kaita ta gaida mama sai mu wuce inda zan sauke su don wanan ne zuwan ta na farko kano.
To,to to wani wurin zaka kaisu su sauka ko ai hakan yana da kyau don tafi sakewa a can gata da juna biyu ga tafiya da suka sha a hanya.
Ta fada tana dariyan yake a fuskanta wanda baikai ciki ba da gani kakaroshi take kawai a zauna lafiya.
Mamu tace abincin dana basu nasan basu ci ba yace No kada ki damu na gode yana mikewa yace nagode da kulawan ki gare mu sosai .
Mamu tace ai hakan yiwa kaine bakin ka ai nawane Umar sai dai idan baka dauka haka ba shidai baiyi magana ba ya kalli arnan nasa yace su tashi suje gun mummy shi su gaisa.
Suna fita Amma tace wai da ranka kasha kallo a duniya wanan may ya gani a wurin wanan mai kama da iccen .
Dariya muka kwashe dashi a falon mamu tace gwago kin san goban wani zuman wani shi abinda yai mashi ne ya zabawa kansa.
Amma ta tabe baki tana fadin a hakan kamar anyiwa icce kwalliya mace ba gaba ko wani fasali in banda abin maza may ya gani anan har yake fuskantar wanan tasgin hankalin.
Sai dai hakkuri tunda ya riga da yayi yanzu Allah dai yasa ta gane yayi jihadi Amma ta wani kallo mamu tace ki bari don Allah yar nan.
A hakan kinga ruwan musulunta a gurin nan mace zata zo gidan sarakanta da wanan matsiyacin shigar na banza.
Sun samu hjy jummai ba yabo ba fallasa ta karbe su sun gaisa tare da mata ya gida duk a cikin harshen turanci suke maganan da ita.
Taji dadin samun yan gidan suna jin harshen ta haka ya nuna mata su din wayayyu ne ba jahilai ba a yadda tayi tsammanin samun su.
Don haka take ganin komai zai zo mata da sauki sai dai daddy sune bata fahinci fadan dataga yana yi ba dazun din.
Hotel ya kai su inda yake ya kara kama daki daya ya don aminiyar ta linda data rako ta tasauka a ciki shi kuma suka zauna dayan dakin da yake din.
Sai dai ranan da za a tona aga abinda ke ranshi da mutum zaiyi mamakin wayayyan da yakeyi a lokacin don baiyi farin cikin zuwan merry din Nigeria ba don duk plan din shi merry ta rusa mashi su yaso ko zata biyo shi nan sai ya kammala abubuwan daya sa a gaba shi da bai fadawa kowa ba har lokacin.
Don mamaki yake son ba kowa nasa sai gata tazo saura kiris ya rage mai ga abinda yake hadawan sai gata ta fado masu kasan.
Don shi mutum ne mai zurifin ciki mutum bai iya gane cikin sa ko inda ya dosa gashi rashin maganan shi yayi yawa hakan ya kara mai zurfin cikin nasa.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:02 - ??5惙5惙5?: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM .


Yau asabar bamu shiga school tunda na dawo islamiya goma na safe nayi wanka na dawo falon mu na kwanta saman dogon kujera inda kanne na suke kallon katon don sin saba da kallo shi sosai tun ban sha,awa har yanzu ina dan binsu nima.
Ban san sun fita ba sun bi mamu part din Amma inda take kwashe ma Amma kai takan mata soro hudu a kai duk sati biyu biyu.
Shi ke gaba tana bayan shi Umar da tun daga nesa ya hangoni kwance kyakayawa sura kafana suna waje a baiyane sun fito daga kasan bujen dake jikina na atamfa.
Subbahanallahi ya ambata a zuciyar shi yana saurin kawar da idon shi inda nake kwance na shaga da kallon katun din yaki ana guje guje.
Saboda gaba daya sharaba na duk a waje yake sunyi lub lub dasu tankar bana taba kasa dasu.
A hankali ya karasa shigowa cikin falon yana mai kara salma ta yadda zan iya jin su da sauri na dago kai sai lokacin na lura da yaran duka sun fita a falon.
Shigo sukayi yana nuna mata wurin zama tare da tambayana ina maimuna take ?
Haushin tambayan naji sai nake ganin yayi rashin kunya wa uwata ko dan saya sunan babu zaice wani maimuna haka gatsau dashi.
Ina kokarin tashi ba tare da na bashi amsa ba illa daure fuska danayi a lokacin ban kalle su don shigar ta tayau ma dai buje ne da riga iya cinya sai bakin coth din mata data dora saman farar rigan ciki.
Ya kara maimaita nace ina maimuna na turo baki gaba nace tafita naji ya furzo da iska daga bakin shi ya sake kallona yace ke baki iya gaisuwa bane halan ?
Ba yanzu kuka shigo ba kana tambayata mamata yaushe zan gaishe ka hakana kuma ya kalle ni kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya juya wurin matar nasa yana fadin.
Ta zauna zai shiga ciki ya dan fito sai su je gun maman shi haka ya juya ya fita ya barni da arniyar zaune tana wani faman tatara bujen ta don zama dakyau.
Tace a cikin raha common baby i forgot your name nace Fatima tace oh sorry fatima who are you today nace mata lafiya ina juyawa gurin tv abina.
Sai naji tace how old are you now Fatema ?
Ina mikewa nace fifteen years daga haka na wuce zuwa kitchen in hado mata abin sha don in mamu ta samu ban aje mata komai na motsa baki a gabanta ba fada zansha gurin ta.
Ruwa da cup na fara kawo mata na koma na hado mata fruit din da nagani a cikin fridgen din na kawo mata ina kokarin zama ya shigo tare da kallon abinda ke gaban ta din yace ok nasan kina son lemo barin bare maki ko ?
Ya zauna gap da ita yana bare mata lemon yayin da idanuwan ta ke a kaina tana kalle min halittana tsab.
Zan fita daga part din naji tace i like dis dress can you saw it for me yace why not if you like it.
Ya bini da idanuwa yana kallon kayan dake jikin nawa da take magana a kansu bujene da riga na atamfar hausa sai dan kwalin shi dana daura a kaina.
Murmushi naga ya sakar mata mai laushi yana fadin zai so ya ganta cikin su ai ko wani lokaci ni dai naja guntun tsuki ta yadda ba zasu jini ba ina kokarin fita falon .
Wani kallo ya jefa min tare da fadin ke wakikewa tsuki nace ni daku nake halan daga haka na fice abina na barsu nan falon mamu zaune.
Can na samay ta suna soron karshe ganin na shigo ta dago tana kallona na san fada zatayi min na bar mata part babu kowa ba tare da na rufo mata ba.
Nace wanan yayan ne yazo da arniyar nan suna falon zaune shine na fito na basu wuri da sauri tace Umar sun shigo ne shine kike kokarin zama baki fada min ba.
Ina dai ai yanzu ta shigo ko kada ki koya mata jin tsoron yaron nan nan gaba tasha wuyan su don banga laifin ta fito ta basu guri ba da wanan tabaran nasu ai.
Amma gwago yayanta ne fa koma ince kawunta tunda dai ai umar zai haifi sa,anta ko ?
Daga baya ke nan ko zai haifa bai haifa din ba ai kuma ba A ruwa ya haifa ba don haka kada ki matsa mata a kansu don Allah.
Shiru mamu tayi don ba wurin magana bane don mamu bata san komai ba akan alkawarin da kawu yayi damu ga iyalinshi.
Da sauri ta kai tsoron ta lakabe jiki ta fita ta barni nan a wurin Amma ina ganin ta fita nace Amma ni bansan abinda yasa mamu ke jan arniyar nan a jiki ba haka wani karni fa matar naji tanayi.
Aisha dake zaune kusa dani ta kwashe da dariya tana fadin matar big bros din ke karni Fatima bari yajiki yayi maganin ki a gidan nan.
Amma tace yo karya ta fada ranan daya shigo min da ita nan na dade ina kyamar falon nan nawa musanman wurin nan data zauna.
Da sauri na kalli wurin anan nake zaune nai azaman tashi Aisha ta rike ni tana dariyan keta tana fadin dallah ja can da suke koya maki a school fa ?
Nace ai ban zuwa kusa dasu ko a can nisa da nisa mukeyi nida su gata da son tambayan tsiya wallahi.
Haka dai muka zage ta tas amma tana tayamu zagi sai gasu tare sun shigo shiyan sai kuma Amma ta ban mamaki kamar ba itace ke zagin arniyar yanzu ba.
Sai gata tana haba haba da ita kuma ita dai merry idon ta yana kaina duk abinda ake a falon Aisha ta mike ta dauko mata ruwa sai tace wai ita dai dress dina take so yafi daukana sosai bisa ga na Aisha data daura zani.
Amma ke tambayan may take fadi yana mayar wa Amma din tare da tambayana yana kallon inda nake yace a ina ake maku wanan dinkin ne ?
Ban sani ba mamu ke kawai na bashi amsa kamar ban son maganan ina kawar da kaina gefe daga kallon su.
Bai kara kula ni ba sai cewa da yayi Amma ina son taje su gaisa da daddy ta matsa min tana son zuwa wurin daddy su gaisa.
Amma tace eh hakan yana da kyau sosai sai dai mahaifin naku ne dake nuna mata kyama karara a fuskan shi bai iya kokarin boyewa kamar yadda kowa ke boye nasa.
Yace Amma har kema kyaman merry kike ke nan ko mai sai Amma ta dan tabe baki yayin da ni da Aisha muka tsura mata ido muji abinda zata ce muna dariya kasa kasa.
Tace yoni waye da ba zanyi kishin addinina ba sadauki ai ba komai saya kaga muna haka ba sai horo da addinin mu daya haramta tsakanin mu dasu.
Shiru yayi ya dafe kanshi ba tare da ya iya magana ba itako dabata san abinda ake fadi ba tace Fatema can teach my ausa i want lean it.
Dan dariyan yake nayi don jin yadda ta kira hausan da wani gurbatacen kira nace nima koyo nake ban iya ba sosai.
Ido ta waro waje tana fadin bata yarda ba don gashi ina yi da grandma taji Omar ma yai min na basa amsa.
Hankalin shi kamar ba a wurin mu yake ba alhalin yana saurareb mu sarai sai dakalan wayar shi yakeyi kamar baijin mu da ganin sa abin duniya yayi masa yawa a rai lokacin.
Itama Amma fita batun shi tayi don ta fahinci amsan data bashi ne yai masa zafi ya ja yana fushi gefe daya.
Daga inda nake na mike don barin falon tace ina zanje nace zan koma wurin mom dinane part din mu.
Sai naga ta mike tana fadin zata koma can ne ita ma ta kwanta kamar in sa hannu a kaina nace na fasa sai dai babu halin hakan sai Aisha dake min dariyan keta na dan buge ta ya dago kai a cikin takaici yana kallon mu don ya gane abinda mukeyi sarai yace a cikin tsawa kai may kukeyi haka yana fito da ido waje.
Mu dai muka fice har Aishan da zata bini gulma part din mu muka barshi zaune da Amma.
Baya fitan mu yace Amma abinda yaran nan sukaga ana nuna min suke kokarin nuna wa ga matana da sauri Amma ta katse shi da fadin.
Kaga kada ka tsargi yaran nan suna nasu zaka dora masu zancen daba shi ba may suka gani gare ta da zasu tsarge ta .
Ya mike yana fadin zan leka mama daga can zan wuce zan barta a wurin maimuna.
Yana fadin haka ya fita ba tare da ya tsaya jin abinda Amma zata fadi ba sai daya shiga wurin mama ya hjy jummai dake zaune a falon ta tana waya taga ya shigo.
Sallama tayi da mai wayan tana kallin dan nata da ya dan fada kadan yana zaune ya dafe kai ya rufe idon shi ruf yana tunanen halin da ake nuna ma matan shi a gidansu.
Sabanin gidan su merry din da kan nuna mashi kauna da nuna shi na gidane gare su idan yaje ziyaran su.
Hjy jummai ta dan kura mai ido na wani lokaci sam shi bai san tanayi ba saida ta kira sunan shi da babawo may ke damun ka kuma ?
Ya bude idon shi da sauri yana sauke hannun shi daya dafe kai yana gaishe ta kwana ta amsa har lokacin fuskanta yana garshi.
Tace mai ya faru nagan ka kamar da wani damuwa a tare dakai kuma ko baka da lafiyane kuma ta tambaya tana tsure shi da idanuwanta kanana.
Ya dan dago kanshi yana fadin mama lafiyata lau wallahi may kika gani mama ?
Tace naga ka fada ka shiga tunane da zaman ka yanzun haka kila ko abinci bakaci ba kana tunanen banza .
Umar ya danyi murmushi tace kana son wani ciwo ya kamakane a hakan kan wani tunanen banza indai akan wanan auren ne da ake son lakaka maku ba zai yuyu ba na fada maku.
Yace mama ni wanan baya damuna matsalata a yanzu kan zuwan merry kasan nan ne kawai.
Tace wani abin kuma aka karayi bayan wancan yace ba ai komai ba mama sai dai yadda ake karbanta ne a gidan nan bai mun dadi.
Hakkuri zaka kara dama kasan halin mutanen mu ai ga kuma yadda suke ganin tazo din a cikin kananan kaya shi dai ne abinda zasuyiwa tsegumi ko?
Zata gyara ai mama nima nasan da hakan don yanzu itama ganin shigar yaran nan tace tana so zan ba maimuna tayo mata wanda zatai amfani dashi kafin ta koma.
Hjy jummai ta wurgawa dan nata harara tare da fadin wace maimuna kuma ?
Kai baka rabuwa da zancen yatinyar nan naga kamar kana zurfafa kanka gareta fa don kawai kaga tana irin kissan nata gun matar ka.
Wana wani makircine namu na mata ni kar nake kallonta don daidai nake da kowa a gidan nan don na riga da nafi karfin su ko na shiga gaban kowa a gidan nan.
Umar da kanshi yake kasa yana jin kalamin mahaifiyar nasa ba dadi har cikin ranshi don shi maimuna ta gama masa komai tunda baiga wani kyamatar merry a gurin ta ba ko kadan.
Shi dai bai ga abinda wanan baiwar Allah takeyi ba da mama take kiranta da wa yan nan kalaman nata haka.
Haka dai ya gama jin ta da zai tafi tace ya kawo kudin kayan ta sa a dinka ya sa hannu a aljihu ya miko mata ta karba tana duban kudin kamar basuyi mata ba
Ya dawo part din mu yana fadin zai shaga gari sai yamma zai dawo su tafi.
Mamu ta dan kauce ta basu wuri don du gana yadan dade gurin da ita kafin ya kira mamu yana fadin ina son don Allah a dinka mata sutura irin na nan koda kala biyar ne ta matsa min kan kayan da taga yaran nan sun saka.
Ya fito da kudi masu yawa yana mikawa mamun sai mamu tace indon wanan ne ka barshi zan saka ai mata yau zuwa gobe insha Allah.
Zanso nima idan ta saka sai in kaita wurin Alh su gaisa don nasan yana daga cikin abinda yake kyamatar ta a yanzu don shigan nan nata haka daya gani.
Dan murmushi ya sakar mata a karon farko yana fadin na sani maimuna nasan abinda daddy ke gudu da sannu komai zai zo karshe.
Ya sa hannu a aljihun shi ya ciro dubu dari yana mika mata kallon kudin mamu tayi tana fadin nace ka bar kudin ka za a dinka mata insha Allahu.
Ba kalman godiya ya kada kai ya fita ta juya wurin merry dake kwance saman dogon kujera take fadin ta tashi ta shiga ciki

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login