Showing 237001 words to 240000 words out of 419207 words

Chapter 80 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1414

sa .
Mikewa nayi zuwa dakin ban ko juyo ba har na shige daidai na samu yanzu an canza komai na dakin ga baki daya haka ma komai na gidan an canza zuwa sabbi wani kallan kuma wanka na shiga na gyara jikina na fito ina zaune na gama saka kayan jikins naji an turo mi kofan dakin an shigo.
Dago kai nayi ina kallom mai shigowa lokacin da merry mukayi arba tana tsaye a kofan dakin har lokacin wanan shegen rigar daine a jikinta saye.
Kawar da kaina nayi daga kallon ta ina rufe man dana gama shafawa lokacin tace tana iya shigowa dakin ?
Nace zaki iya kofa a bude yake har lokacin kallon mamakin sauyawana take min lokaci guda,
Ta karasa shigowa ta samu wuri ta zauna a bakin gado na juyo ina fuskantan ta kafin tace dani.


ZAINAB IDRIS MAKAWA
16/11/2021, 23:21 - ??5惙5惙5?: ASSALAMU ALAIKUM YAN UWA MUSULMAI , , , ,

Saida ta dan kura min ido na wani lokaci nima kallin ta nayi ido cikin ido kamar yadda take kallon nawa ba tare da yau naji wani shayinta ba ko kadan atare dani.
Karfin adduan mudulunci ke nan da hausawa ke fadin addua makami mumuni na gwada a gare ta.
Fatema nazo wurin kine da magana don nasan zaki fahinceni fiye da maigidana ta fadi tana kalona ido cikin ido.
Nan nace Allah yasa abinda zai yuyune kikazo dashi ta kara kallona karo na barkatai tace ko zaki tuna wancan karon kin tafi ba tare da sanun mu a gidan nan.
Kan wani dalili da nake zaton ko kin sanshi ko baki sanda zancen ba wanda ba wani abu bane sai zance yata guda daya tilo da nake da ita.
Kallon ta nake a cikin mamaki don ban san may take son fada min ba lokacin sai zuba take.
Nasan da biyu kika zo kasan nan kada ki dauka ban san may ya kawo ki kasan nan ba Fatema ?
Da sauri ba dago ina kallon ta cikin mamakin jin tasan zancen auren mu da yaya ashe dama nunawa ne batayi ba.
Nayi kasa da kaina cikin kunya jin tasan mijin ta na aure na bata nuna min komai ba.
Saida naji tace don kawai ku dauke wa yata hankali ga addinin mu aka turoki kasan nan ki zauna damu.
Saidai baku san cewa mu din dagani har yata ba a London muke zaune ba don haka nazo da murya mai kaushi don baki warning kan yata.
Wanan can karon kin fada mata abinda bata taba sani ba zancen ku yan uwantane kuma tana da grany da aunts da sauran su a Nigeeia.
Wanda da kyat na samu ta bar zancen nan a ranta don haka nake son inyi warning din ki wanan zuwan kada ki fara ki shiga harkan yata har ki fada mata wani zance gamay daku can .
A jiyan zuciya na sauke da gama adduan bakina na kalleta jin inda ta dosa na dakatar da zancen ta da fadin .
Nace wait merry zancen fadin wai ya takice ko wani abu duk bai taso ba don zaki iya fadin haka a yanzu saidai nasan nan gaba fadan hakan zai maki ciwo.
Don ko wani dan Adam yana daraja danginshi ne a duniya yana basu girma da sanin kimar su kada ki zalunci yarki don wani manufa naki merry bance ko anty ba wanan karon.
Kallona take da mamaki nace yes idan Amina bata nemay muba a yanzu nan gaba zata iya neman mu dole ne wanan sai ya faru.
A yanzu zanyi kamar yadda kike so merry don ni ba wanan ne ya kawoni gidan nan ba nazo nan bisa tursasawan dan uwanane kawai.
Yar kice Amina saidai ki sani nan gaba ba da yarki kawai yaya zaiyi alfahari ba don zai iya haihuwan wasu da wata mace yan uwa da dangi kaf su sosu a bar taki a gefe yadda kike so.
Shin idan anyiwa yarki hakan zakiji dadi a rayuwan ki kuwa naji daga yau na daina kulaki har yarki.
Saidai ki sani gida daine gidan dan uwanane ina da right din shigowa kamar yadda kema yan uwan ki suke zuwa duk lokacin da suka ga dama.
Maimakon inga bacin rai ga merry dake min wani irin kallon mamakin yadda na tsaya ina fada mata magana haka sai naga murmushi a fuskanta.
Tace kinyi kokari wurin fada min wanan magana saidai zan so ku san cewa dani da yata yanzu keda iko da komai a gidan nan na Omar.
Don nice matar gidan queen kuma diyar mu ce kowa a kasan nan ya san da hakan so banga wani dalili da Omar daku yan uwanshi kuke kokarin sakamu gaba hakan nan ba ?
Dan murmushin karfin hali na sake don maganan ta ya razana nani sosai jin abinda tace dani yanzu saidai ban nuna mata razana na ba kadan lokaci.
Komai zaki iya fada a nan merry saidai kada ki manta kin aure hausa man wanda keda addini daban da al,addu daban da naki ki rubuta ki aje komai zai yi faruwa daga baya wanan haka yake.
Wani kallo tayi min tare da tafa hannayen ta tace yarinya kinyi kokari kin nuna min aikin ki yana tafiya daidai a yadda wanda ya turo ki ya koya maki karfin halin jajircewa don yanzu idanun ki sun nuna a bude suke sosai.
Dama nasan da zaman ki a cikin dangin Omar kina daya daga cikin masu kyamata na tun farko saidai darajan mahaifiyar ki da kimar ta ba zai bari in dauki wani mugun mataki a kanki ba don ni mutum ne da bana mance halarci a rayuwata.
Nace realy ta gyada kai alaman kwarai kuwa don steps mother tayi min abinda ba zan taba mantawa ba a rayuwata danaje gidan ku.
Kin san da hakan kike kirarin cewa wani aiki aka turoni yi a kanki da yarki in ma wanan kike tunane ki cire a ranki don ba wanda zai tsaya yana wahal da kanshi kan mijin ki ko yar ku don ba shi kadai iyayyen mu suka haifa ba.
Kin san mu musulmai wanan ne fa,idan yin aure gare mu fiye da mata daya da kuma yara da yawa don idan wata ko wani ya kika ba zaka rasa wanda zai soka ba.
Don haka cewa Umar nakine keda yar ki ina son ki gane cewa kin makaro ga hakan don dai shi din musulmi ne mai alfahari da addinin shi.
Kofan a bankado da karfi ya Umar din ne a tsaye yana muna kallon tuhuma dukkan mu gaba daya wurin.
Merry may hakan ke nufi ne ya tambaya lokacin da yake karasowa tsakiyan dakin da tarin tambaya da fargaban abinda muke tsutaunawa a tsakanin mu.
Don yanayin kowan mu ya nuna ba maganan arziki mukeyi tsakanin muba a lokacin yadda yanayin fuskan kowan mu yake hade.
Sake tambayan ta yayi may ya kawo ki wurin ta yanzu bayan ki san ba lafiya ke gare ta ba kece kika matsa tazo nan ko zata samu karfin jikin ta.
Wani kallo ta watso min don amsan da bata samu bani ba ya shigo yana cin zuciyar ta.
Banga alaman mara lafiya da kake fadi ba a nan don wanan yariyar alama ya nuna min garau take ba abindake damun ta.
Yayi mata wani kallo shekeke yace zaki iya fadan hakan don ciwo ba a jikin ki yake ke da yarki ba ko ?
Tayi mai wani kallon wullakacin ba tare da yin magana ba ta fice daga dakin tana fita ya juyo yana min kallon tuhuma ?
Na kawar da kaina daga kallon shi da sauri yace may kika fada mata yanzu na juyo ina kallon shi nace amsan abinda ta fada min kawai.
Kamar zai sake magana sai kuma naga yaja ya fita dakin da sauri ya banko min kofana kafada na daga irin mai nuna ko a jikina.
Dakin barcin su ya nufa a nan ya samu merry tana zariyo a tsakar dakin tana ganin shi ya shigo ta tare shi da fadin sister din ka ta fada min magana masu zafi Omar.
Yace kamar yadda kema kika je kika fada mata ko wanan ne dalilin da yasa kika yaydareni akan a kawo ta nan zaki kula da ita ?
Kashedi nayi mata a kan diyata dani sai na fahinci yanzu yarinyar ta wuce yadda nake tsamanin ta.
Don ta fada min abubuwan da tun farko hankalina ya kawo a kanka rashin wayau ya hanani gane hakan da wuri.
May ta fada maki ya tsure ta da ido yana tambayan ta kasa bashi amsa tayi sai hannayen ta data dunkule tana dukan juna dasu da gani dai tana cikin wani irin yanayi lokacin na bacin rai.
Ya gaji da tsayi don jin bai samu amsan tambaya shi ba gun ko wacen mu ya nufi gadon kwanan su zai zauna tace.
Omar muna nan akan alkawarin mu dakai ko ka canza ra,ayin ka garemu yanzu yayi murmushi may kama da yake yana kallon ta yakai zaune yana fadin wani alkawari nayi maki ada da kike tunanen zan canza yanzu.
Dole in tambaye ka don abubuwan da nake gani dama wanda yar uwanka ta fadamin yanzu sun sa na shiga halin tunane ?
May ta fada maki gamay dani wanda har yasa kike ganina mai karya alkawari gareki ?
Kallon shi tayi tai murmushi ta karaso bakin gadon ta zauna ita ma shiru sukayi na dan lokaci yayin da shi yaya yake jiran amsa a gareta na abindana fada mata din.
Don a tunanen shi na fada mata abindake tsakanin mu dashi na aure hankalin shi inyai dubu ya tashi maimakon ta bashi amsa sai ma yaji ta buge ga waya da abokanta na nan da zasu zo su fita.
Ganin ta kyale shi ga dare yayi lokacin ya kasa zaune ya kasa tsaye a dakin kamar ya sani ya fito a daidai lokacin da nima na fito rataye da jakkan dana zo dashi da zuman barin gidan.
Ke yace a cikin wani irin tsawa daya daka min yana fadin ina zaki yanzu ciki wannan daren haka ?
Kina da hankali kuwa waima ko ke kinsan darajan kanki kuwa zarah da bin dare a kasan nan bai zama maki komai ba?
Hawaye suka soma zuba min a idanuwana shifa ya daukoni ina gidana zaune cikin rufin asirina zuwa gidan matan shi.
Tazo tana fada min maganan banza akan abinda baishafe niba yanzu kuma har yana kirana da ban san darajan kaina ba.
Ganin irin hawayen da nake daga inda naja na tsaya yanayin fuskan shi ya dan sauya kadan ya tako zuwa gareni yana fadin .
Kiyi hakkuri ke kika daukan min alkawarin zaki taimaka min kan yata sanin haka da merry tayi zuwan ki na iya jan ra,ayin yarta zuwa gare ki yasa tayi wanan zaman dake.
Kada kice zaki fushi ki kara barin gidan nan don shine burinta taga kowa nawa bai mamay mu ba da zakibi daren nan yanzu baki tsoron wani abu yaje can ya samay ki a hanya kasan nan fa ba kamar tamu bane Nigeria.
Yaya haka ya isheni na fadi a cikin kuka tun yanzu matar ka bata san alakan dake tsakanin mu ba tana nuna min hakan ina ga ranan da tasan cewa ni matar kace ta sunna ?
Idan ta sani saimay zara iyaka dai rabuwa zamuyi idan bata iya zama dani dake don ke ba saki a tsakanin mu har abada.
Ka daina fadin haka yaya kada ma kasa zama da kaida nakeyi na har abadane tsakanin mu ko ka manta da abinda ke jiran mu a gidane bayan wanan ?
May ke jiran mu a gida zarah nace cikin kallon shi da mamaki yaya har ka manta da hjyn ku tana kalubulantar auren mu ne.
Dan murmushi yayi yana fadin wanan ba matsalan ki bane tsakanina da mahaifiyatace zarah don haka bai shafeki ba yana matsowa inda nake yake magana.
Yace ki duba yadda kike shirin fita a gidan nan wai mako kinsan darajan auren dake a kanki kuwa zarah ?
Kina da darajan da babu wani mahalukin da zai ganki a haka bai kara kallon ki ba kallon kaina nayi don sai a lokacin naga yadda nake shirin fita daga gidan dagani sai dan riga irin tasu dake saye a jikina lokacin.
Kunya da nauyin hakan ya kamani koshi da yake kare mun kallo haka a lokacin jin motsin merry data fito ta tsaya tana kallon mu bai hana shi riko hannuna ba ya rungumay ni a jikin shi yana dan bubuga min baya alaman rarashi.
Jin nayi shiru yasa ya ja hannuna zuwa dakina sai da ya kara ban magana ya fita daga dakin sai bayan fitan shi daga dakin na sauke ajiyan mikewa nayi zuwa kofa na rufe da key na dawo saman gado har lokacub ba komai a cikina da naci tun karyawan safe daya tursasani nayi a gaban shi.
Wani tunane yazo min nayi zubur na mike zauna daga kwanciyan ruf da ciki danayi da farko.
Na fahinci akwai rikici a tsakanin yaya da matar shi a wanan yan watannin da suka shude duk dai a kan rikicin yarsu ce hakan ke faruwa tsakanin su.
Daman kine wanan sayadi damaki ne hakan a ruwa muryan mamu da Amma ne ya ziyarci zuciyana lokaci guda.
Ba sai mun koya maki yadda zaki samu kan mijin ki ba kije ilimin ki da kika samu ya fitar dake a matsayin ki na diya mace.
Abinda zan kara maki shine juriya da hakkuri da al,amarin rayuwa sayadi sai ladabi da biyayya da zaki kara dashi mamu ke fadin haka lokacinda Addah ta kaini gurinta muyi ban kwana.
A ruwa ke mace ce don haka ba sai na koyar dake komai saidai zan kara da hakkuri da kwantar da kai ta haka ake cin ma manufa a saukake A ruwa.
Nasan zaki iya kawun ki baima saudauki zaben banza ba don kece kika dace da daidai da rayuwan shi ki kula da addinin ki a duk inda kika riski kanki addua ko takobin mumune Aruwa a kula da yawaita yin addua ko yaushe.
Amma ce take fada min hakan wani dare saura kwanaki bukin mu na dawo daga misau ina korafi gareta na banyin aure mai mata kafira.
Yo itama kafira ina tasan kissa irin namu na nan a ruwa ko zama gidan nan kadai ya isheki koyon duniya abinida iyayyenku keyi a gidan nan.
To ta ina zan fara wai idan ma har na saki jiku dashi na dan lokacine wanan kulawan dayake bani don kawai sun samu matsala da matar shine har nake samun sakin fuska gurin shi kwana biyun nan.
Ranan da suka daidaita fa tsakanin su suka koma shiri da ita idan na sake jiki har sabo ya shiga tsakanin kwana biyu kaina abin zai koma tunda ba sona yake ba yadda yake fadi kuma ya nuna.
Ke nan nice da mahaifiya ta za a cuta a karshe tunda nice zan yi hasaran kimata da martabata na mace .
Ni da wanan zaman ai garama ina gidan mu gaban iyayyena yafi min zama mai kamar ukuba dashi.
Kaina gyada ina fadi a fili anya nayiwa kawu adalci idan naki dan shi da yake sa ran gyarauwan komai a dalilina.
Ya zama dole dai in bi shawaran mutane in fara wani abu nima a bangarena kodon wanan bakar arniyar mai zagin iyayyen mu a gaba don na kula taki jinin kawuna don dashi take adawan ta.
Ranan dai barci rabi da rabi nayi shi gidan wasu na fatan suje kasan waje suji dadin rayuwan su ni kuma da na samu zuwa ga irin ukuban zuciyar da nake ciki tun zuwana.
Washe gari kodana tashi na gama yanke shawara a raina wanka nayi tsab na shirya cikin green din kaya duk da ba kala na bane kayan dai sun karbi jikina sosai nayi rolling din kaina na tsaya gaban mirrow ina karewa kaina kallo.
Ban fito ba saida na kara shafe jikina da oud dina masu kamshi sosai tun tun karowana falon kamshi turaren jikina ya daki hancin su.
Dago kai sukayi suna kallona direct wurin table din abincin na nufa kai tsaye fuskana a washe kamar ba wani abindaya faru daren jiya din.
Shina fara gaidawa kafin in juyo ina kokarin zuwa wurin yar su nace anty merry good morning ina zaton ba zata amsa min ba sai naji ta amsa min gyatsire da morning dear taci gaba da cin abincin ta.
Dan rugumar yarinyar nayi nakai mata kiss a goshin ta tare da fadan morning my dear ta tabure fuska can ta dago tana fadin .
Ina kikaje bana ganin ki ina tambayan Mumm tace kin koma garin ku da zama dan kallon uwar yayi ya kawar da kai nace da yarinyar ina zama yanzu ai gani na dawo gare ku

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login