Showing 51001 words to 54000 words out of 419207 words

Chapter 18 - Sarka Complete Hausa Novels By Zainab Idris Makawa.doc

29 Oct 2025

1500

akan sauran matan shi yanzu
Washe gari ko da muka tafi school har muka dawo gida ba wanda yai mi magana a ciki su nasan sun hade min kaine don su matseni a gidan.
Sai dai mun dawo mun samu farin ciki a gidan don a ranan Alh ya gabatarwa matan shi da kyautan motocin da dan shi ya turo masu.
Haka yasa mamu zuwa part din hjy jummai tayi godiya akan alherin da danta ya aiko masu don yaba kyauta ai tukwaici ne.
Sai dai tayi da ta sanin zuwa duk da dai ta debe mata hakki zama a tsakanin su dan ta yayi masu alheri kuma ta gode.
Don hjy cewa tayi bani ya kamata kiwa godiya ba ai tunda bada miyau bakina aka sai maku motar ba aima baku iya ba da kuke son gasa dani ai da sai diyan da kuka haifa su sai maku ba dana a tillasata mashi ya saya maku ba don kawai ana son yin gasa dani a gidan.
Mamu dai godiyan ta dada yi mata ta fito ta barta tana mita akan zancen danta ya saya masu mota wai a munafuce ta .
An tillata mashi dole don ya sai mota mota suma sai ya saya masu mamu na fita daga part din ta takasa hakkuri ta nufi part din Amma a fusace.
Muna falon lokacin muna dan hira da Amma sai su Aisha da bilki dake kitso a gefe daya ganin ta haka Amma tasan ba lafiya ba wanan shigowan da tai mata a part.
Wanda yanayi ta ya kara tabbatarwa Amman da hakan don bata shigo idan ta zo da safe sun gaisa sai kuma wani washegarin idan ta shigo gaida ita.
Gaida ita mukayi nice ta karshe bata karba muna gaisuwan namu ba sai makarin hawa fushi da tayi.
Tun daga tsaye take fadin hajiya gurin ki nazo Amma tana fadin ai gani nayi but na mike ina fadin yan kanne suzo muje.
A daidai lokacin ta juyo inda muke tana fadin ku bamu guri zamuyi nagana sai tayi rashin sa,a don ni har na daga zan bar wurin ko.
Amma tace ai ita wana tasan ta ido do harta mike kafin ki kora su ko idanuwan ta sun kada sunyi ja saboda fitina.
Sai da taga ficewan mu a falon ta kara kallon Amma tace hajiya gurin ki nazo Amma ta dago kai ta kura ma yanayin da take ciki na tashin hankali ido kafin tace.
Samu wuri ki zauna ki natsu jimmai naga ranki kamar abace yake a yanayin da kika shigo wuri ta samu ta zauna kafinta fara fadin.
Hajiya Alh bai son zaman lafiya a kidan nan asalima shike kawo rikicin komai a cikin gidan nan yanzu hajiya ya dace ace Alh ya turasawa yaran don sun min abu yacd sai sunyiwa sauran matan shi .
Babu haufi babu ko jin nauyi da dogon turanci Amma tace kwarai don ko shi ya haife su kamar yadda kika haife su matuka suna son albarkan mahaifi ya bibiye su.
Sai dai ban tari numfashin ki ba na kai ga baki amsan maganan ki bansani ba ko yayi haka ta hanyar da sharia ta hanane kinga anan kuma maganan ki gaskiya ce.
Kallon Amma takeyi kamar ta kurma ihu a lokacin saidai jin maganan ta na karshe ya bata kwarin gwiwan cigaba da maganan ta.
Tace hajiya kin san komai a gidan nan yanzu ya dace don kawai yaran nan sun saya min mota Alh ya tursasa su akan sai sin sai ma sauran matan shi dole.
Shi sanin ya akaita hakan idan ko hakane bai kyauta ba Amma ta fadi tana gyara daurin dan kwalin ta.
Hakan ne ma hajiya don ban sani ba sai da motocin suka zo dana yi magana yace min ban isa ba Amma ta katse ta da fadin.
Shi umarun ya fada maki da bakin shi an tursasa shi ya sai masu mota ko wani ya fada maki haka ?
Hajiya kin san halin yaron nan ba zai fito fili ya fada min kai tsaye ba da binkice nane na gano hakan ya faru.
Amma ta girgiza kai tana fadin hasashen ki da binciken ki ya fada maki karya jimmai idan ma gaskiya ne haka ne ina abin farin cikine ya samay ki a gidan nan.
Yau har Allah ya nuna maki ranan da dan da kika haifa zaiyi alheri irin haka kinga ke nan ko a nan kin nuna kina sama dasu ke nan tunda har danki yana iya aiko masu da alheri irin haka.
Kinga Allah ya nuna masu ke har kullun kina gaba dasu ke nan don har dan ki bake ba zai iya kyautata masu da abinda basu dashi.
A lokacin hjy jummai ta sauke wani ajiyan zuciya Amma taci gaba da fadin kin ga kuma maganan nan Allah yasa a gabana akayi shi.
Zaki tuna da ranan da kika daki tagwayen nan har zazzabi ya kama su aka kaisu asibiti bayan sun dawo uban ya shigo dasu nan ya zauna ke nan sai ga umar din ya bugo wa mahaifin nasa waya.
Suna gausawa yaji kukan yaron da murya na ina fadin yaron yayi shiru uban yayi waya shine umar din ke tambayan ina kusa ne yaji murya na a gurina uban yake yace eh.
Shine yakd fadin a bani wayan mu gaisa bayan na karbi wayan yakd fadin ke dawa ke fada nake cewa nida kanin ka mai irin zubin ka ke muna kukan banza don raki.
Nan dai nake fada mai abinda ya faru a lokacin ne yace damu suyi hakkuri zai saya masu mota maman su taita shiga dasu.
Jimmai kinji yadda zancen sayan motan nan yazo don haka ba wanda kike tunane bane ya tilasata wa danki sayen motan nan.
Ta lumshe ido a hankali tana mai jin zafin tsohuwar kan maganan dafa fadi mata lokacin
16/11/2021, 22:43 - ??5惙5惙5?: BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM TAWAKKALTU ILLA, LAH, LAUHAULA WULLA KUWATI, INNA BILLAHI ALIYAL AZEEM, , , , , , , ,

Ina zaune a class fuskana yana ga littafin lissafi da aka gama koya muna don kawai in gane nake da naci ga karatu idan an koya muna malami ya fita ban tsayawa surutu kamar yadda da yawan mu ke samun sakewa idan ba kowa a cikin ajin mu.
Jin shiru da ajin yayi sai kuma kanshin da yadaki hancina yasa ni dago kaina da sauri a zatona wani malamin ne ya shigo muna.
Sai dai ina dago kai na gansu a gabana seniors din makarantan ne wanan da ranan su salma suka gudu don shi yana tsakiyan su mutum biyu biyu a gefen shi su biyar sun shi a tsakiya.
Gabana ne ya fadi na juya da sauri naga duk yan ajin a mike suke sai ni kadai da kaina yake duke lokacin da suka shigo ajin ban sani ba haka yasa nayi yunkurin mikewa a lokacin.
Kamar yadda naga kowa yayi masu a ajin sai ya nuna min hannu ba tare da yai magana ba alaman in koma in zauna.
Dam kara juyawa nayi in ga ko da wani yake magana sai naga akasin hakan gare shi ba da kowa yake magana ba kuma yaki budan baki yayi magana.
A hankali na koma kamar yadda nake da farko ina gyara littafina da ke saman table a bude ya juya ba ba tare da ya tafi ba sai wani yace min.
Ke may ye sunan ki na dago a hankali nace wa ni ina nuna kaina gare shi yace dake nake may ye sunan ki akace.
Fatima Abubukar azare na basu amsa a takaice ina fadin haka ya fara tafiya sauran suka bi bayan shi suma.
Har lokacin ajin na tsit ba wanda ke magana a cikin students sai da suka fice ajin da kamar minti biyar dan kus,kus ya fara a ajin sai ga su sadiya sani sun zo table dina sukace ke may kikai wa su gentle yau ?
Waye kuma gentle na tambaye su a cikin tsiwa don ban son abinda zai hada ni hurda dasu don na lura yin kawa babu abinda ke cikin sa sai munafunci da saka wasa yasa nake jaye kaina ga kowa.
Don ina ganin yadda kullun ake turke a cikin ajin ba mazan ba ba matan ajin ba sai kuma wasan banza a tsakanin yan mazan da mata da zaran babu malami a jin.
Ganin haka ke sa da zara babu malami zan dauko littafina in dinga bita da sannu har in gane abinda aka koyar damu may yake nu.
Da mamaki suke kallo na har suna hada baki wurin fadin ke baki san Gentle ba duk zaman ki school din nan ga yan mata na rushing a kasa duk yawancin seniors din son shi sukeyi.
Yana masu yanga da han aji kuma mahaifin shi a garin nan last done ne na kudi shi din ma ai ba a nan ya tashi ba daga baya ne suka dawo nan kasan.
Bansan shi ba kuma bani son sani don ba abinda nazo yi ke nan ba don Allah ku ban wuri abu nake anan yanzu.
Ina fadin haka na dukar da kaina naci gaba da karatun da nake ba tare da nasa abinda nake karantawa ba a lokacin.
Don haushi da takaici daya lulube lokaci daya karshe ma rufe littafin na kifa kaina a table ina tunanen da ban samu amsan shi ba don ban san dalilin tambayan sunana da seniors din sukayi ba.
Bayan mun tashi daga school har lokacin ban sake ba can na hangi kanne tafe yana dangyashi alaman yaji ciwo a kafa shi da sauri sauri na karasa gurin yaron.
Ina tambayan shi samir ke cewa wai wani moniter din su ne ta duke shi har ta fadi a hasale na dago daga duken da nake ina tambayan shi waye monitor din ajin nasu ya nuna mi wata bakar jeep dake gefen mu.
Ba tsaya wani abu ba na nufi motar a hssale rike da hannu kanina lokacin driver yana kokarin rufe kofan motar yara sun gama shiga ciki.
A tsiwace nace malam kada ka rufe kofa zanga yaro dake cikin motar nan dan Allah ya juyo da mamaki yana kallona duk da kakin dana gani a jikin shi bai sa naji tsoron shi ba.
A ckiin harshen turanci ya kara tambayana na fada mai sai yayi kokatin rufe kofan ashe ma bashi bane driver driver yana gaban mota yana jiranshi.
Rike kofan motar yayi kokari yi sai nasa karfina na tare kofan daga ciki motar naji ana bashi umurni da ya bude.
Ya sara kafin ya bude motar wanan ne da suke kira da gentle zaune a bayan motar tare da wani karamin yaro da yarinya dukkan su saye da uniform din school din.
Juyawa nayi wurin salim dake yamotse fuska nace kai waya tabe ka a cikin su yaron a hankali ya dago hannun shi yana nuna min cikin motar cikin tsawa nace bazakai magana ba ka tsaya kana nuni da hannu.
Yace a hankali wanan ne ya nuna min yaron gaba dayan su sun tsare da ido har security din nasu nace.
Kai may yai maka kajin masa wanan rauni haka a kafa halan a gidan ku ba,a koyama tausayin na kasa dakai bane?
Haiy haiy make faruwa ne wai wanan gentle din ya dakatar dani daga magana ta yaci gaba da fadin may ya faru ne da kafan tashi yana magana da karamin yaron a cikin yanayin kallon shi.
Banji may yaron yake fada mai ba sai dai karshe da yace nikuma na dake shi, nace don ka fishi girma ko may ?
Ke dakata su fada muna yace kamar baison magana shiru nayi ina murguda vaki har ya gama tambayan yaran ba,asin maganan su.
Ok ka bashi hakkuri yace bayan ya gama sauraren yaran akan abinda ya hada su tare da fadin John ina son mu kai yaron nan asibiti a duba kafan shi.
Nace ku barshi tunda ya bashi hakkuri ai maje gida a duba mai lokaci ya kure a yanzu ina fadin haka na juya zuwa wurin motar mu.
Wanda sai lokacin ns kula ashe hankalin mutane duk akan mu yake ban kula da hakan ba illa jan kanne zuwa wurin motar mu daya riga ya faka ko.
Muna zuwa na dinga tura yaran a mota sai da naga sun shiga sun zauna na yun kura nima na shiga wurin zamana dake can baya inda salma ta bani tun ranan farkon zuwana school din.
Sai dai ina zama naga wanan Gentle din yazo har bakin motar mu ya zura hannu ya dauki yaron ya juya zuwa wurin motar su.
Kkarin fita nake daga inda nake zaune sai dai kafin na iso har motar tasu ta daga daga wurin ko tana kokarin barin makarantar.
Na shiga uku ba furta ina kokarin bin motar da gudu sai dai ina motar har ta halba saman titin ko tana kokarin bace min da gani.
Ba sanin garin nayi ba don haka ban san inda suka dosa da yaron ba a lokacin iba kokari tsala ihu baji salma na fadin.
Kai wana masifan da daddy ya kwaso muna da may yai kama don Allah yarinya kamar yar mahakaciya gata nan kina shiga mota ko mu wuce mu barki a gurin nan yanzu.
Sai Adawiya tace don Allah kyale ta da haukanta anty salma akace mata bata zaiyi ne a wurin su waye bai san yan gidan general ba a garin nan ?
Koma sace shi sukayi ai sun rage muna fitina a gidan mu ne tunda ba su kadai bane yara Nafisa ke fadin wanan maganan .
Na kalleta shekeke tare da fadin dama kowa yasan fatan ku ke nan a garin nan kuna bakin cikin buda ido ku ganmu a gidan ku.
Sai dai kun makara don jini ya riga da ya gauraye da ruwa mun zamay maku ciwon ido ko sai kallo ko tsiyayyan hawaye.
Zama salma tayi a mota tare da ba driver umurnin da su tafi ina kallo sukaja mota suka barni gurin tsaye.
Sannu a hankali ake watsewa a haraban makarantar har aka dauki yaran karshe.
Ya rage saini sai security makaranta kowa har malamai sun watse a school din na hada kai da gwiwa ina kuka a hankali mara sauti ba abinda zuciyata keyi sai tunanen halin da dan uwana yake ciki.
Ko su din su waye da har zasuyi min gaba gadi haka da dan uwana jin karan motan da nayi baisa na dago kaina daga yanayin da nake ciki ba.
Muryan nan mai kama dana izza nasa ya karade min kunne yana fadin ke tashi kuje gida time na shigewa kada a ga kun dade.
Da sauri na dago kaina ina kallon su na sauke ga kanina dake rike a hannun shi an daure kafan da bandage.
Cikin wani kuzari na mike tsaye ina fadin samir ina suka kai min kai may sukai maka samir.
Maikon yai magana sai kawai ya jingina kansa a jikina yana lumshe ido kamshi na shafa a hankali ina ma yaron sannu samir.
Ina kokarin rike hannun yaron muka fara tafiya ba tare da nasan inda zamu dosa ba don a mota muke zuwa kullun sai gashi yau zamu a kafa tunanen da nakeyi ke nan a raina .
Horn din mota mukaji a bayan mu na juyo sune na kawar da kaina da sauri daga kallon su muryan shi naji yana fadin ku shigo mu sauke ku gida.
Kamar in ce a,a sai na tuna ban san hanya ba don haka banyi gardaman shiga ba wani irin kamshi da sanyi naji ya doki hancina da gangan jikina a lokaci daya.
Duk sai na raina kaina a karo na farko a gaban wani na zauna a takure wuri daya can nisa dashi kadan kannen shi da samir suna tsakiya mu haka yasa nagane basu je gida ba suma har lokacin.
Hanya kawai nake iya nuna masu ban san sunan unguwa ba lokacin da muka kai kwanan unguwan na nuna a cikin sauri da fadin wanan ne unguwar mu.
Da kwatance na nuna gidan muna tsayawa mamu da Alh tare daAhmed suna kokarin shiga mota muka karaso a gaban su muka sauka daga motar fuskokin su da alaman damuwa karara.
Ina kallon ajiyan zuciyar da mamu tayi da mukai arba da ita na fito da sauri ina fadin mamu wallahi ba da gangan na tsaya ba samir ne yayi targade a kafan shi shine, , , , ,
Muryan Gentle ne ya katse ni da yake gaidasu Alh a cikin ladabi tare dayi masu bayanin abinda ya faru tsakanin yaran a class.
Ya kara da fadin shine muka dauki yaron zuwa asibitin mu don a duba kafan idan baiji ciwo sosai Alhamdullahi mun samu dan targade yayi a kafan shine aka daure tare da bashi wanan

Chapters

Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login