Showing 288001 words to 288773 words out of 288773 words
Chapter 97 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt
idan ta dira kuka tsakiyar dare, haka raihana za tayi ta jijjigata ko ita ko mama haleema, shima wasu lokutan har karb'ar ta yake ya taya su. A rayuwar khaleefa ya tsani kuka sai gashi Allah ya jarrabesu da yarinya mai kuka...... Har Saida suka k'ara watanni sannan ta fara daina kukan dare.
A lokacin tuni khaleefa ya tubure halin raihana tayi da gani haka ta azabtar da ummie da kuka, ita da mama haleema dai sukan yi dariya idan suka ji ya fad'a haka....
A haka raihana take managing tana zuwa makaranta tana kula da yaranta da mijinta, sosai ta zama busy ta ko'ina ba sauk'i saida ta zage dantse ta zama jaruma.
*Nigeria*
B'angaren Imran da shaheeda kuwa, haka shaheeda ta dinga k'untatawa hajiya tafeeda ba tare da Imran ko sauran mutanen gidan su sun sani ba, zatayi abu amma inka kalli fuskarta saika rantse da Allah bata aikata ba. Tun hajiya tafeeda na juye abun kan d'anta har ta gaji ta fara dawo da laifi kan mai aikata shi, zuwa lokacin mamy har bata son had'uwa da k'awartata cox kullum sai tayi complain akan saleema, harta fara gajiya daji ma, tun tana yiwa yarinyar fad'a harta gaji ta daina tana ganin kawai hajiya tafeeda bata da hak'uri ne.
Lokacin da Shaheeda ta fara laulayin ciki mai wahala sai abun ya sake k'ara yin gaba, gashi wata irin soyayyah ta shiga tsakanin Imran da shaheeda, saboda shak'uwa da kusancin da suke k'ara samu a kullum safiyar Allah.
Lokacin da cikin shaheeda ya isa haihuwa sai rigima mai k'arfi ta b'arke tsakanin su har ta kai hajiya tafeeda ta kore ta a gidan Imran zuwa gidan su gurin mamanta, ita kuma sameera hakan daya faru yasa ta lashi takobin y'arta tabar auren Imran har abada don tunda akayi auren basu zauna lafiya ba, daga wannan sai wancan sanadiyyar rigimar ko magana yanzu basa yi da tafeedan.
Haka Imran ya dawo daga Lagos ya tarar da wannan rikici hadda cewa saiya saki shaheeda.
Sosai rigima ta dinga kai kawo har a k'arshe mahaifin Imran ya shiga ita ya yanke nata igiyar auren, yace kuma muddin ta sake magana akan saki to ranta sai yayi mummunar b'aci. Haka ta koma gida jiki a sanyaye a shekarun da ta huce zaman gida.
Har shaheeda ta haihu ana d'auki ba dad'i duk da zuwa lokacin hajiya tafeeda tayi kwatakyes, itama shaheeda jin har an saketa sai jikinta yayi sanyi, ta fad'awa Mamie asalin laifinta da musabbabin shi, ranta ya b'aci kuwa ta balbaleta da masifa, ta tusa ta a gaba kuma har gidan su tafeeda ta bata hak'uri, ta bawa dad ma hak'uri ya maida hajiya tafeedan d'akinta.
Daga nan sai aka zauna lafiya bayan an raba musu gida da ita don wani kusancin shi yake kawo matsala, sannan halin sune baizo d'aya ba shi yasa indai zasu ci gaba da zama kusa da juna sai an samu matsala.......
_Wannan kenan_
*Bayan wasu shekaru*
Abubuwa da yawa sun faru cikin shekarun nan na dad'i da akasin su, khaleefa ya gama aiki da asibitin da suka zauna tuni har ya dawo gida Nigeria inda mahaifin shi ya gina mishi babban private hospital nashi na kanshi suna kula dashi shida Ahmad.
Yasmine ta k'ara haihuwar yara biyu don haihuwa bata d'aga mata k'afa ba, raihana kuma ta k'ara haihuwar y'arta mace, itama ta gama karatun ta har ta karb'i result, sai dai bata fara aiki ba, batasan ma ko gogan zai barta aikin ba ko a'a.
Komai yana tafi musu cikin nasara, watarana zuma watarana mad'aci, dama hakà rayuwar duniya ta gada......
Abba ya basu wani babban gida suna zaune shida Ayman komai iri d'aya. Suhaana ma ta haifi d'anta namiji sai kuma ta tsaya planning don tana tsoron haihuwa tunda tayi sau d'aya taji.
Tammat bihamdullah! Da wannan na kawo k'arshen littafin JARUMAR UWA, abinda mukayi na dai dai Allah ya bamu lada, abinda mukayi na kuskure kuma Allah ya gafarta mana albarkacin wata mai alfarma da muke tunkara. Wanda muka b'atawa cikin ajizanci irin na d'an Adam Allah ya huci zuciyarshi.
A madadina da twin sieterna doctor ferhyeezerh ina taya d'aukacin y'an uwa musulmi na duniya murnar zuwan wata mai alfarma da albarka watan ramadhan, Ina fatan Allah ya bamu ikon yin ibada lafiya ya karb'i inadun mu, ya samu cikin y'antattun bayi.
*RAMADHAN KAREEM*
Mie wattsapp no👇
08134288477
Merhreeyaertou✍🏻