Showing 234001 words to 237000 words out of 288773 words
Chapter 79 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt
yaci a gidan iya. Wata zazzafar iska ya furzar daga bakin shi sannan ya k'arasa k'ofar gidan ya kwankwasa, minti kad'an al'ameen yazo ya bud'e, yaron yana ganin shi ya russuna yana gaishe shi, Ayman ya amsa yana d'orawa da tambayar dalilin da yasa yau baije school ba cikin kulawa, (kamar abinda aka tura shi kenan🤔).
"Bani da lafiya". Yaron ya bashi amsa.
"Ayyah Allah ya sauwak'e". Ya mik'a mishi jakar hannun shi, "gashi inji auntie ka kaiwa maman ku". Al'ameen ya karb'a bayan ya durk'usa.
"Ka gaishe dasu jidderh". Ya k'ara fad'a kafun ya tsallaka ya koma inda ya parking motar shi.
*****Al'ameen yana shiga ya mik'awa ummie da take zaune a parlor jakar, "ummie wai gashi inji auntien su yaya khaleefa?".
Cikin rashin fahimta ummie tace, "wane khaleefan kuma?".
"Mijin auntie raihana fa".
"Ohh! Shiya kawo".
"Kae! Ummie Yaya khaleefa ya dawo kuma ba muga auntie raihana ba....Yaya Ayman ne ya kawo yace ma a gaishe dasu jidderh".
Ummie da mamaki ta fara duba jakar, tsarabar saudiyyah cikin k'atuwar leda daban, sai ragowar kayan da k'aramar takarda anyi rubutu jikinta. Warware takardar tayi ta fara karantawa, "socks da sweeter naki ne hibbatullah, (Kamar yadda kika fad'a a waya, hak'ik'a gangar jikin auntyn ku raihana yayi nesa daku, amma zuciyoyin ku suna kusa da juna) ragowar chocolate naku ne keda su al'ameen gaba d'aya, nasan kunyi kewar auntien ku sosai kamar yadda kuke yawan fad'a a waya, shiyasa na had'a da sako muku kayan snacks data girka da hannunta ba tare da saninta ba, Allah yasa lokacin da auntie zata k'araso basu lalace ba, koda yake in sun lalace ma zaku ji k'amshinta da girkinta da kukayi missing, a k'arshe ku gaishe da ummie sosai... Ku fad'a mata raihana tayi kewarta da yawa....".
Murmushi tayi bayan gama karanta takardar ta mik'awa al'ameen da yake ta tambayarta menene a jiki. Ita Kuma taci gaba da duba kayan, koda ta warware kayan snacks d'in meat pie ne da doughnut sai cake, duk da ba suyi komai ba tasan sun sauya d'and'ano, cake d'in ta gutsira ta kai bakinta idonta na cikowa da ruwan hawaye..... Maganar zuci na futowa fili ba tare da saninta ba, "hak'ik'a nayi kewarki raihana, Ina fatan kina cikin k'oshin lafiya kamar yadda kike yawan fad'a a waya".
Tasa tafin hannunta tana share hawayen cikin fakar numfashin al'ameen da hankalin shi yake can kan kayan da khaleefa ya aiko musu dashi da takardar.
Karb'e jakar tayi a hannun shi ta maida komai ciki tace, "Bari a fara nunawa abban ku tukun sai kuyi duk yadda kuke so dashi ko...". Al'ameen cikin farin ciki yace, "toh, ummie kinga irin wannan chocolate d'in da Abba ya tab'a kawo mana? Hadda shi a ciki fa Yaya khaleefa ya aiko mana".
"Na gani Allah ya saka mishi da alkhairy". Ta fad'a tana mik'ewa ta bar gurin.
****Da dare tana zaune kusa da Abban suna hira take bashi labarin sak'on da auntie ta kawo musu, ta k'arasa fad'a tana jawo jakar da take gefe d'aya cikin d'akin.
"Allah sarki kunyi mata godiya?". Abba ya k'are da tambaya a lokacin da yake ganin kayan da ummie take d'agawa,
"A'a bari nayi ka dawo in na nuna maka kayan sai naje koda dare ne na mata godiya da sannu da zuwa.....".
"Ai ya kamata kam wannan uban kayan sweet kamar za'a bud'e shop".
Ummie tana dariya tace, "wannan kuma aikin d'anka mijin y'ar".
"Wa kenan kinsan yaran ba d'aya na aurar ba".
Wata dariyar ta sake yi tace, "toh first Born nake nufi".
"A'a raihana, dama doctor Germany taje ba saudiyyah ba?". Ya tambaya.
"Ina ganin duka k'asashen biyu taje". Ta k'arasa da d'auko mishi cake d'in da taci da rana cikin tsarabar.
"Wannan ku tayiwa tafiyar ma kawai... Hadda cake?". Abba ya sake fad'a yana kallon cake d'in hannunta da take mik'o mishi.
Ummie tace, "Kai dai karb'a kaci mana".
"Kin manta ni bana cin kayan zak'i".
"Wannan ko da zallar sugar aka had'a ba zaka kasa ciba, kuma in kaci ba zai saka tashin zuciya ba cox yazo ne daga hannun wadda ita kad'ai take yi maka shi kaci a duniya.....".
Tun kafun ta gama fad'a ya karb'e ledar cake d'in ya fara warwarewa yasa a bakin shi ya tauna.....
Ummie tana dariya tace, "ka gane daga hannun wadda yazo ne ka hau ci".
"Raihana! Ita kad'ai ce ta dangaci abinda kika lissafa".
Tayi murmushi "haka ne kam bata San ma mijinta ya aiko dashi cikin kaya ba".
"Allah sarki raihana Allah ya albarkaci rayuwarsu ita da mijinta". Ummie da take gefe tace ameen".
Sunyi shiru kafun ummie ta tambayeshi, "yanzu in ka gama sai mu tafi ko?".
"Alright ba damuwa zuwa anjima saina kai ki?".
Barka da zagayowar sabuwar shekara, fatan Allah ya had'a mu da alkhairan dake cikinta ameen.... Happie new year once again to follower's of in-identical twins.... Wish you guy's all de best😍
*Ga masu tamtama akan saki da ciki👉🏻 a shari'ar musulunci idan aka saki mace da ciki saki d'aya, biyu, uku toh saki yayi, koda zata haihu a take a gurin babu abinda zai k'ara maida wannan auren tunda har ya sake ta sakin daba kome, idan kuma saki d'aya ko biyu ne kad'ai, zai iya maida ita kafun ta haihu, idan kuma akayi sakin koda da minti d'aya ne ta haihu, toh sai an sake d'aura wani auren sakin ya warware wancan kenan. a JARUMAR UWA Suraj ya saki surayyaa sakin daba kome da ciki, auren su ya haramta har abada...... A k'aramin sanina fa amma*
Masu comment Ina godiya da jinjina👍👍👍😊 fatan Allah ya bar k'auna💓, Ina yinku fiye da yadda kuke yina.
*Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo muku dai dai da zama, Maryam sulaiman maman almustapha tazo muku da duk abinda kuke buk'ata cikin kwarewa, iyawa da gwanancewa, ga duk mai buk'ata sai ta tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka 08028175615*
_Comment and share✍️_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)
_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_
_Story and written by_
*Merhreeyaert lerwerl*
Page sixty six6️⃣6️⃣
Da dare Abba ya tafi kai ummie yiwa auntie barka da zuwa da godiya har gida, amma fa bayan an jawa su al'ameen kunne banda rigima tunda su aka bari a gidan.
Ko futowa a cikin motar baiyi ba sai ummie ce ta shiga gidan, karo na farko data tab'a zuwa gurin surayyahn.
Wani matashi da yake musu aikace aikacen gida da aike shi ya yiwa ummie jagora har parlon auntien.
A lokacin tana operating computer ta ita kad'ai mama haleema yau ba a nan zata kwana ba, Ayman kuma ya futa gyaran kai da aski zai dawo.
Da farin ciki ta taryi ummien, ta shiga suka gaisa ta mata sannu da zuwa, tana son tambayar yata baro su khaleefan sai dai tana kunyar kada aga tayi hakan ne saboda y'arta.
Kamar surayyah tasan abinda yake ranta, haka ta dinga bata labarin raihanan da kirkinta, ita dai ummie ta kanyi murmushi, data tashi tafiya ta ajiye mata cooler lafiyayyen dambun shinkafa data shirya da wadatattun kayan lambu.
Aikuwa auntien taji dad'i tayi ta mata godiya, har bakin k'ofa ta rakata suka gaisa da Abban sannan sukayi sallama ta tafi.
***Kwana uku da dawowarta Ayman yana bin takunta kamar wadda ta satar mishi wani abu, gaba d'aya ya daina futa office sai a late, ya kasa ya tsare so yake kawai yaji tace zata futa aiki coz yayi alk'awarin ta daina futa office d'in nan, tayi aiki tuk'uru tun suna yara, yanzun kuma lokaci yazo daya kamata ta hak'urar wa ranta aikin ta zauna gida ta huta kamar kowacce mace.
Ganin har an shiga weekend bata ce zata futa aiki ba saiya saki ranshi da tunanin ta yadda da maganar da suka yi lokacin data kwanta ciwo asibiti.
*Germany*
Zaune yake a office d'inshi ya kwantar da kanshi cikin kujerar da yake zaune, k'afafun shi biyu zube kan table dake gaban shi, tun d'azu yake son tashi yaci wani abu kafun shigarshi theatre sai dai yana tunanin me ma zaici yaji d'and'anon shi irin yadda yake so a bakin shi.
A haka Muhammad ya turo k'ofar offishin ya shigo bakin shi d'auke da sallama, Ahmad biye dashi ksmar makaho da d'an jagora, khaleefa sam baiji shigowar ko d'aya daga cikin suba bare sallamar da sukayi har saida Muhammad yayi shaking k'afafun shi.
Ya bud'e ido yana kallon shi bayan ya janye k'afar ya maida ita k'asa.
"Kana son wasa da basudaniyar likitan nan kamar yadda kake son wasa da cikin ka...".
Ahmad ya d'auki zancen bayan Muhammad ya aje, "ai shiyasa bata sassauta mishi ko magana zatayi dashi saita fara d'aure fuskarta tam tukun, yanzu dai kasan da ita ta ganka yadda muka shigo muka same ka ba abinda zai hana kasha fad'a ko?....".
Squeezing fuskarshi yayi yaja tsaki a fili yace, "Mtss! Am not feeling okay gaba d'aya kunzo ku kuma zaku k'ara mun da maganar ku....".
Muhammad yace, "Then why not ka tafi gida tunda komai d'an lafiya ne".
"Ashe kuwa zai dawwama a gidan don kullum a haka yake....". Ahmad ya fad'a yana kallon shi.
Muhammad ya sake cewa, "kuma fa hakane, lallai Ahmad kasan khaleefa farin sani ni kaina na fara noticing hargitsewar shi cikin watan nan gaba d'aya".
"Cikin watan nan kad'ai kaga hakan? Ai man ya hargitse tun wata d'aya saura mu kammala karatun mu.... Koda yake ya d'an samu nutsuwa kad'an farkon dawowar mu..... Duk da yanzun wata sabuwar matsalar ce daban take neman damula mishi lissafin shi.....".
"Ayyah Soo sorry man! Komai yayi farko yana da k'arshe haka komai yayi zafi maganin shi Allah, nasan ka sani but ina sake maka tuni da sake mik'a lamuran ka gare shi". Muhammad ya fad'a cikin kulawa.
Murmushi Ahmad yayi ya tattara nutsuwarshi rankatakaf ga khaleefan yace, "wannan matsalar tasha banban da irin abinda kake tunani Muhammad, saboda a yanzun khaleefa yana ta yak'i ne da zuciyarshi da gangar jikin shi kan abinda suke sooo, am i right?". Ya k'are maganar da sigar tambaya yana d'auke idon shi daga kallon tsakiyar idanun khaleefa da yake aiko mishi da sak'on gargad'i ta ciki, tea ya tsiyaya a k'aramin plask da yazo dashi cikin funjali ya kai bakin shi ya fara sipping.
Muhammad kam cikin jinjina girman k'arfin halin khaleefan yace, "kace kai match ka taro... Akan wane dalilin ma zaka hukunta kanka da mafi zafi da rad'ad'in hukunci?".
Khaleefa da yake kallon Ahmad warce plask d'in shayin shi yayi ganin zai shanye mishi tea d'in don sai cika k'aramin cup yake yana shanyewa sauri sauri don salon mugunta....
"A'a rowa kuma zaka fara?". Ahmad ya fad'a yana kallon shi.
"Ehh". Ya bashi amsa fuska sam ba annuri.
"Toh ai bani zaka yiwa rowar ba tunda Muhammad ne bai shaba".
Kallon Muhammad d'in yayi, "Kai malam baka sha tea a gidan kaba yau kafun ka futo?".
Da son kunna shi Muhammad yace, "na sha amma wannan d'in ma zansha tunda har naga kana rowar shi nasan zai zama na daban ne....".
"Matsa shi ya maka aman wanda yasha don ya shanye hadda rabon ka".
Basu iya daurewa ba su duka biyun saida suka mishi dariya, abinda ya sake tunzira shi kenan, ya mik'e yana nuna musu k'ofa, "na fahimci kun cika cikin ku shiyasa kuka zo nan ku k'arar da kuzarin ku gurin dariya kamar shi aka d'auke ku ku aiwatar.... Toh office d'ina baiyi kama da physiatric ba you can silently move out....".
Ahmad kam wata dariyar khaleefa ya sake bashi, shi in yaga ya zage yana irin wannan maganar da iya gaskiyarshi abun dariya had'e da mamaki yake bashi, sam d'abi'un shi na yanzu ba suyi kama dana asalin Abdallah Suraj daya sani shekarun baya ba, da gaske yana cikin damuwa ta gasken gaske saboda ya rarraba kwakwalwar shi da tunanin shi rukuni rukuni yasa yake misbehaving haka, kuma a hakan so yake lallai sai ya nuna babu wani abu tare dashi.
ata b'angaren Muhammad kuwa shiru yayi yana nazarin khaleefa yana sake tabbatar da gaskiyar abinda Ahmad ya fad'a a kanshi, shiyasa baici gaba da dariyar ba.
Kafun suyi wani kwakkwaran motsi akayi knocking k'ofar,
"Come in". Khaleefa ya fad'a cikin bada umarni.
Ta tura k'ofar offishin ta shigo da sallama, duk suka zuba mata ido lokaci d'aya kuma suka tashi tsaye bayan sun shiga taitayin su.
"Dama office yayi kama da gurin had'a majalisar hira....".
Dukan su shiru sukayi kafun Ahmad yace, "sorry doctor".
"Oya kowa ya koma bakin aikin shi". Babu musu duk suka d'auka hanyar futa, har Muhammad ya murd'a handle ta dakatar dashi ta hanyar kiran sunan Ahmad, "zaku tafi X-Ray tare da mutumin da zaka yiwa theatre jibi, yana jiran ka a offishin ka".
Gyad'a mata kai yayi cikin karb'ar umarninta ya fuce, shi kuma Muhammad ya d'auki excuse ya koma gurin khaleefa yana mishi magana k'asa k'asa yadda ba zata jiyo ba, "Babu abinda ya kai yak'i da abinda kake so a zuciya wahala, kai gara ka yak'i maza d'ari a filin daga daka ce zakayi yak'i da zuciyarka akan abinda take soooo... So please man just give up and stop deceiving yourself okay...".
Gyad'awa Muhammad kai yayi don ya nuna mishi ya gamsu.
Bayan futar Muhammad komawa yayi ya zauna itama taja seat ta zauna tana sake karantar yanayin shi,
"Ga yunwa, ga gajiya, ga rashin bacci da damuwa, rashin kwanciyar hankali duk a tare da kai! Taya zaka iya fuskantar aikin gaban ka har kayi abinda ya kamata, farkon fara koyon aikin ka da lokacin daka fara aiki mutum ne kai mai aiki tuk'uru ba wasa, amma yanzu a hankali ka sukurkuce ka koma kana buk'atar kulawar likita kaima,,,,, bare a d'ora maka alhakin kulawa da wani, shin menene ainahin gundarin matsalar ka a rayuwa Abdallah?....."
Tunda ta fara magana kanshi yake k'asa bai yarda ya d'ago ba har ta dire, jikin shine ya sake yin sanyi, kwantaccen sautin data yi amfani dashi gurin mishi magana yasa shi jinta kamar mahwifiyar shi.
"Ina tambayarkane yanzun ba'a matsayin likita abokiyar aiki ba, sai a matsayin uwa da take da y'ay'a take jinka kamar d'aya daga cikin su". Ta sake fad'a tana sake nazarin shi, Shirun dai ya sake biyo baya daga ta b'angaren shi.
Fahimtar da gaske ba zaice komai ba yasa tace, "shikenan! Da yamma in ka tashi tafiya gida ka same ni a office kafun ka huce...". Gyad'a mata kai yayi ta mik'e zata futa, har ta kai k'ofa ta tsaya ta sake tuna mishi, "kada ka manta".
Yanzun ma baiyi magana ba sai kai daya gyad'a.
*Bayan wasu mintuna*
Ahmad ne yake tafiya cikin ward d'in sauri sauri kamar yayi fiffike ya tashi sama, ba don kada ya runtuma a guje mutanen gurin su d'auka bashi da hankali ba da aguje zai isa gurin khaleefa ya sanar dashi abinda ya gani ra'ayal ayn yanzu yanzun nan.
Yana tafe tana bin bayan shi itama ba gajiyawa, yawan adadin saurin shi, yawan adadin nata saurin itama, yana kama handle na k'ofar offishin khaleefa zai murd'a ta dakatar dashi ta hanyar riga shi d'ora nata hannun, da mamaki ya tsaya yana kallonta kafun ya tambayeta, "akwai matsala ne doctor?".
"Babbah ma kuwa! Wannan amanar ban baka ita don ka bud'e ta ga kowa ba yanzun, biyoni office d'ina".
Jikin shine yaji yayi sanyi, bashi da zab'i sai bin bayanta don masu iya magana suka ce ta inda aka hau, ta nan ake sauka,,,,,
A office d'inta kuwa Ahmad tattare gaba d'aya hankalin shi yayi gareta yana sauraron jawabinta, "da farko zan fara da tabbatar maka abinda kayi zato har kake sauri ka tabbatarwa abokin ka khaleefa, patient d'in dana d'anka amanar kula dashi a hannun ka, Suraj Abdallah tofa ba kowa bane face mahaifin abokin ka khaleefa". Duk da Ahmad yayi tunanin hakan saida yaji shock da doctor andal ta sake tabbatar mishi, "khaleefa dai doctor?". cikin sake tabbatar mishi tace, "kwarai kuwa khaleefa dai da muka sani ni da kai, da farko ai shina dank'awa ragamar kula da mahaifin shi, toh amma daga baya due to wasu dalilai dani kad'ai na barwa raina sani saina mai dashi hannun ka, Ina so kamar yadda na daure raina kaima ka daure naka, ka gargad'i bakin ka kar kace komai gare shi daga yanzun har