Showing 96001 words to 99000 words out of 288773 words
Chapter 33 - JARUMAR UWA Complete Hausa Novels by merhreeyaertou.txt
suka tsinci kansu cikin farin ciki kamar basu ne suke zaune a bai bai tun ranar da khaleefa ya dawo har zuwa jiya ba. A nan haleema ta kawo musu abinci suka ci su uku, Ayman yana ta zolayar khaleefa da son yaga ya tunzura shi, shi kuwa gogan ya fuske abinshi yana cin abincin shi ko kallon shi beyi ba.
Da yammacin ranar kamar yadda sameera tayi alk'awari sai gata bayan ta dawo daga gidan sunan data halarta, a bedroom d'in Auntie na sama suka k'ule suna tattaunawar sirri, inda surayyah take mata magana cikin tsantsar farin ciki, "k'awata maganar muce ta taso fa?". Sameera itama cikin farin cikin tace, "Toh doctor surayyah wacce magana kenan? naga tunda nazo yau bakin ki yak'i rufuwa".
"Ba dole ba! Ai yau bakina bazai rufu ba mammie, maganar auren Nur da Ayman nake miki kinsan d'azu na fad'a miki yadda mukayi da khaleefa too zan ajiye maganar shi a gefe har zuwa lokacin da zai sake d'auko mun maganar zai koma inda ya futo, a lokacin ne ni kuma zan murza kambu na, shi kuma Ayman bazan tauye shiba, a fad'awa mahaifin Nur gobe insha Allah su malam zasu zo da dukiyar auren su, nan da 4weeks ayi biki tunda already an gama shirya komai, har na yiwa malam d'in ma waya"
Saida gaban sameera ya fad'i da taji abinda ya futo bakin k'awarta a yau, sai ta tsaya kawai tana kallonta da sakakken baki, wato saboda y'ay'anta y'ay'an mace ne shine take tunanin itama nata yaran hakan take, toh duk lalacewar mahaifin su matsayin mahaifin su yake bata tauye masa hak'k'in shi akan yaran shiba, d'awainiyar suce da yaji bazai iya d'auka ta yau da kullum ba ita ta d'auka har shima zai shiga ciki ya samu mafaka albarkacin yaranta. "yaa k'awata tunanin me kike kuma?,,,,,". Saita sauke ajiyar zuciya a b'oye ta sake kalmashe k'afarta a gaban k'awar tata, "Ina jinki likita yadda kike so haka za'ayi, sai dai wani hanzari ba gudu ba yau mun share a k'alla shekaru talatin ba kad'an tare cikin aminci, kinsan ni! Kinsan asalina! Kinsan mijina! Kinsan iyayena! Babu wani abu b'oyayye ko bak'o da baki sani a tare dani ba, sai dai ta b'angarena ni ke kad'ai na sani sai su iya, har yau ko a sub'utar baki, baki tab'a fad'a mun labari d'aya daya danganci mijin da kika tab'a aure ba, duk da yadda mutanen gari suke munafuncin ki da yaranki hadda su iya ma amma baki tab'a bani labarin wani abu da zai warware gaskiya ba, shin surayyah baki ji kin aminta dani a iya tsawon wad'an nan shekarun bane?".
Tunda sameera ta fara magana surayyah ta tsaya tana kallonta da wani irin yanayi mai wuyar fassaruwa farat d'aya, sai take ganin kamar ba sameera data sani ce yau keyi mata wannan maganar ba, koda yake fiye da haka ma zata tambaya tunda itama d'an Adam ce me numfashi kamar kowa.
Sai ta d'auke idon ta gefe ta mik'e tsaye ta goya hannayenta duka biyu a bayanta, taku biyu zuwa uku tayi ta tsaya a tsakiyar parlon ta soma maganarta cikin murya mai nuna tsantsar b'acin rai, "kin fad'i gaskiya sameera, tabbas bai kamata ki d'auki y'ar ki Nur kiba d'ana aure rana tsaka mu gudu miki da ita inda ba zaki sake ganin ta ba, k'arshen butulci, nasan wannan shine tunanin ki ba? In ba haka ba kuma kada kije ki had'a zuri'a da yaran da basu da asali cikakke bari na ari kalmar taku *shegu*. Nasan dai abu biyun nan ne suka sa kike son kisan wani abu daya danganceni nida yarana,,,,, Toh sai dai Ina so ki san cewa tarihina wani shud'ad'd'en al'amari ne dana dad'e da binne shi cikin k'ark'ashin k'asa ya nitsa can k'asan k'asa, ban tab'a bawa baki amanata ba komai amincin da muke yi da mutum kuwa, saboda duk maganar da ruhi yaji bakin shi baya iya hak'uri watarana sai ya furta ta, Soo try to understand bake kad'ai ba a tsawon wad'an nan shekarun dama sama dasu ban tab'a bawa wani tarihin rayuwata ba ko na yarana,,,, tun yana raye a cikin zuciyata har zuwa yanzu daya mutu ma..... Idan kin yarda dani ki tsarkake ranki ki futar da maganar mutane a cikin zuciyarki mu k'arasa ladan mu...." saita k'ara takowa ta durk'usawa gaban sameera ta dafa kafad'arta, "mu manta da waccen maganar k'awata shin kin amince zaki bawa Ayman auren Nur?". Shiru sameera tayi tana kallonta da tsantsar mamaki da zargi kala kala, lallai akwai k'amshin gaskiya a maganar tafeeda k'awarta, duk tushen da aka cika b'oye shi bashi da kyau, toh amma yadda surayyah take da mutumci da taka tsantsan da maza ko ita bata dashi haka,, sau da yawa in suna tafe tare maza da yawa sunsha kawo mata hari, tun kafun tayi shekarun haka ma a lokacin da take ganiyar k'uruciyar ta, manyan mutane masu fad'a aji kuma, amma bata tab'a kulawa ba bare har ta shaide ta akan bariki, idan kuwa har a yanzu tana kyamatar had'a alak'a da duk wani namiji shaida ce da take nuna lallai da k'uruciyar tama batayi barikin ba, toh y'ay'anta in hakane ba zata kira su kai tsaye da shegu kamar yadda mutanen gari kan kira suba, toh amma kuskure d'aya fa! A lokuta da yawa idan suna hira sai taji tana bada misali da kuskure d'aya da mutum in yayi har ya k'arashe rayuwar shi gaba d'aya yana karb'ar sakamako...... Sake kallonta sameera tayi, idonta ya ciko da hawaye yana sauka d'aya bayan d'aya kan kuncinta, amma kwayar idonta wani irin bak'in ciki da b'acin rai ne ke kai komo a cikinta.
Sanin maganarta a yanzu ba k'aramar kwab'a zata jik'a ba, sai ta d'auki Jakarta da mukullin motarta ta mik'e tsaye tana kallon surayyahn, "Ina ganin mu ajiye maganar auren yaran nan a gefe, idan har babu Amana to banga amfanin k'awance ba, ki zauna kiyi dogon tunani akan maganata, banyi haka da nufin yi miki butulci ba, har abada bazan manta tarin alkhairan ki a gare niba doctor surayyah, saboda kin taimake ni a lokacin da kowa yake guduna saboda ana ganin na zama wahala, a lokacin da nake tsakanin rayuwa da mutuwa, a lokacin da takaicin d'a namiji yake neman shafe tarihina a wannan duniyar, kece dai doctor surayyah mace d'aya tilo da ban tab'a ganin me kyawun zuciya da yin abu domin Allah kamar ta ba, amma haka ba yana nufin bakya kuskure ba, tabbas kinyi kuskure, duniya taci gaba haka mutanen cikinta, ki ajiye b'acin ran da yake zuciyar ki, ki nemo dangin mahaifin yaran ki su sauke nauyin da Allah ya d'ora musu na aurar dasu, domin sune a hak'k'u dasu aikata haka......" Sameera tana gama maganarta tayi gaba, sai dai har ta kusa futa daga parlon surayyah ta biyo bayanta ta rik'e rigarta ta baya, da muryar kuka take magana yanzu, "har abada!!! Indai sai na koma ga Suraj da ahalin shi zaki bawa Ayman auren nuriyyah toh Allah ya had'a kowa da rabon shi.....".
Tana gama maganarta ta saki mata rigar, itama sameeran bata juyo ba saboda zuciyarta zata iya karyewa in ta ganta tana kukan nan, haka ta huceta a gurin, ta shiga motar ta da take parkee a k'ofar gida ta bata wuta a guje tabar arean anguwar.
Haleema da take sak'a a cikin parlon auntien a gabanta surayyah ta biyo bayan sameera ta furta mata wad'annan maganganu dai dai k'ofar bedroom d'inta, ta tabbatar wani abu marar kyau yana faruwa, sai ta ajiye k'ulun hannunta ta mik'e ta nufe ta, sai dai tun kafun ta k'araso ta d'aga mata hannu, ta shige d'akinta da gudu ta murza keeyyy. Kan gadonta ta fad'a ta fashe da wani irin kukan mai ban takaici da cin rai.
@@@@@@
A yammacin ranar iya da malam suna zaune kan tabarma tare da bak'in su don su kawo dai daito tsakanin su, neman yafiyar malam suke akan biriskullen da sukayi dashi a shekarun baya, hakan ya samo asaline daga rashin fahimtar shi da sukayi, malam da yake jinsu yace, "ya huce har abada mun yafe muku tuni, dama kuma bamu tab'a rik'e ku da komai ba". Malam yana ajiyewa iya da take jira ta d'auka, "A'a malam kai dai ka yafe musu bani ba..... Don nikam bazan tab'a yafe musu b'ata mana suna da sukayi a k'auyen nan ba, kuma wallahi ba wata nadama da sukayi, saboda sunga ka samu abun duniya suka lallab'o suka dawo zasuce wani a yafe musu, ba wani nadama ni ba abinda zan sake saurara a gurin su, neman hanyar da zasu k'ara cutar damu kawai suke". Tana gama maganar ta kakkab'e jiki ta tashi tabar musu gurin, harira zata bi bayan ta malam yayi saurin d'aga mata hannu, "rabu da ita yanzu ta d'au zafi ba zata fahimce kuba, in ta huce anjima zata fahimta a hankali". Sai Suka koma suka zauna tare da gyad'awa malam kai cikin nadama mai tarin yawa.
Da daddare tana zaune a cikin d'akinta malam yazo ya sameta, zama yayi a gefenta aikuwa ta sake d'aure fuska ga zaton ta ko maganar su harira yazo yayi mata, sai taji sab'anin hakan daga maganar daya fara, "wani abu mai girma yana tunkaro surayyah". Sai ta sassauta fuskarta ta kalle shi, "tun kafun khaleefa ya dawo kake fad'ar haka ni na kasa fahimtar me kake nufi". Malam jinjina kai yayi yace, "Ni kaina bansan meye ba abinda na fad'a miki shi kad'ai nake ji a jikina, shiyasa cikin satin nan nake tsananta addu'a ta akanta da yaranta, sannan Ina ganin lokaci yayi da abinda take b'oyewa zai futo sarari, lallai lokaci yazo da zata futar da abinda yake ranta take b'oyewa tsawon shekaru". Shiru iya tayi tana jinjina al'amarin, duk abinda malam ya jinjina shi ya sake jinjina shi lallai ba k'aramin abu bane, toh ita dai tana fatan Allah yasa alkhairy ne zaisa ta fallasa abinda yake b'oyen.
Itama sai tabi da addu'a kawai, "yanzu yaushe zaku kai kud'in auren Ayman d'in?". "gobe insha Allah amma zan jira naji daga gareta kafun nan". Allah sarki Ayman Allah ya tabbatar da alkhairy yasa abokiyar arzik'in shice, ni khaleefa naso ya fara yin auren ma wallahi". Malam yace, "toh shima dai yana hanya mu taya shi da addu'a kawai".
Daga nan suka rufe wannan matter, suka shiga wata.
************
Sameera kuwa tana Isa gida wayar shaheeda ta fara kira, cikin sa'a ta d'aga, "kina Ina?" Ta jefa mata tambayar kai tsaye, "mammie yanzu na futo daga makaranta" "toh maza ki taho gida yanzun nan". Daga nan d'akin nuriyya tayi, ta sameta zaune tana chat a waya, "mik'o mun wayarki" ba musu ta bata, tana karb'a ta futa daga d'akin, shaheeda ma tana zuwa wayarta ta karb'e ta had'a data Nur tayi switch up d'insu ta adana su a d'akinta. Duk saita jefa yaran cikin tunanin abinda yake faruwa. Suna nan zaune a parlonta tsuru sun kasa yin komai saboda tsorata da sukayi da yanayinta har baban su ya dawo, heedaya ce ta fara taryar shi tana fad'a mishi mammie tana ciki tace bata son kowa ya dameta, tambayar shaheeda yayi, "Wai hakane?". Shaheeda tace, "eeh Abba tun d'azu take rufe tak'i cewa kowa komai". "toh Ina haeydar kuma?". "bai dawo ba". Suka bashi amsa kusan a tare, Lokaci ya duba yace, "har yanzu? Toh meya tsaida shi?".
Babu wanda ya bashi amsa cikin su, sai ya nufi d'akin da take ya murd'a handle ya shiga, tana kwance a k'arshen gado ta zubawa kasan d'akin ido, kan drower kusa da ita ya zauna y zuba mata ido yana kallonta, daga yanayinta ya tabbatar yau ranta a mugun b'ace yake. Sai ya kira sunanta bada hargagi ba cikin kwantaccen sauti, da kyar ta iya amsawa, yaso da farko ya rabu da ita amma kasancewarta mai kula dasu da walwalarsu a gidan sai yaji bazai iya share ta yana kallonta cikin damuwa ba, koba komai masu iya magana sunce gaida me gaishe ka, ko bazai amsa ba. "me yake damun ki sameera?". Sai ta tashi zaune ta kalle shi tace, "damuwa ta ba wadda ta shafe ka bace, kuma kona fad'a ba zaka iya yimun maganinta ba, toh abinda zaifi don Allah ka barni inji da abinda yake damuna kawai".
Kamar ya tashi still dai kuma sai ya kasa yace, "kina ganin wannan itace amsar daya kamata matar kwarai ta ba mijinta?". Bata ce mishi komai ba sai ya sake kiran sunanta, "sameera!" Ta amsa mishi tana kallon shi, "ki fad'a mun meye damuwarki". Sai data nisa sosai kafun ta labarta mishi duk yadda sukayi da surayyah d'azu, shi kanshi abun ya d'aure kanshi, gaba d'aya da ita da k'awartata basuyi tunani ba, sai ya gyara zama don ya kawo musu gyara da maslaha, "duka kunyi kuskere sameera, amma naki kuskuren yafi nata". "dama nasan haka zakace wallahi, kai komai nayi sai kace banyi dai dai ba, kana nufin Ina ji Ina gani saina d'auki y'ata na ba d'anta auren shi bayan ta b'oye mun asalinta mun shafe tsawon shekaru tana nuna min halin rashin yarda.....". Saida ya bari takai Aya sannan ya fara magana,
"Toh ai baki bari kinji abinda zan k'arasa fad'a ba kawai kin hau fad'a, ni ba Ina nufin ki bata auren Nur ba, wannan tunanin tun farko ya kamata kiyi shi, tabbas itama bai kamata ta b'oye miki komai a yadda kika d'auke ta ba, sirrin ki komai kin d'anka a hannunta amma ita bata tab'a yarda kinji komai nata ba, tun a lokacin da kuka shirya auren Nur ya kamata ki mata tambayar da kika yi mata yau, abu na gaba kuma iya zaman ki da surayyah kin tab'a kamata da wani abu na laifi kamar ballagazanci ko wani abu makamancin haka.....?" Shiru tayi batace komai ba, sai yaci gaba da maganar shi, "toh kinga ashe ba zaki d'auki wancen zargin zuwa kanta farat d'aya ba, watak'ila akwai abinda take b'oyewa yaran da bata son yaje kunnen su shiyasa bata tab'a yarda da wani dan Adam me baki ta fad'a mishi sirrin taba, a family ai ba'a rasa rigingimu tsakanin matar da aka auro da dangin mijinta, maybe itama hakan ne, shiyasa tak'i yarda su san dangin uban su tunda uban ya mutu take ta fad'i tashi dasu ita kad'ai..... Toh yanzu da kika hana auren ma ya zakiyi da yaran da Suka zurma cikin son junan su...".
Abun duk saiya taru ya yiwa sameera yawa, ta rasa da wanne zataji, tabbas ta yiwa ranta alk'awarin ba zata tab'a bada y'arta ga mace ba, Dole ta nemo dangin uban su suma ta basu hak'k'in su da Allah ya d'ora musu akan yaran.
Sai taja dogon ajiyar zuciya, "Allah ba zan bawa Ayman auren Nur a hannun surayyah da malam ba, saboda shi kanshi malam d'in an dad'e ana rad'e rad'in basu had'a komai ba, tabbas surayyah macece mai mutumci nutsuwa da kamala had'e da kamun kai, amma ina ji a jikina wannan yaran sunzo ta silar kuskure guda d'aya tak da bazai gyaru ba har abada... Wannan kuskuren da take yawan fad'a, yanzu kuma lokaci yayi daya kamata ta ajiye komai a gefe, in ma family issue ko wancen abu daya faru ta bawa dangin ubansu hak'k'in su da yake kan yaran a kawo maslaha ta daina tafiya dasu a duk'unk'une........".
_shiyasa akace rayuwar duniya a komai kada ka zurfafa........_
_Comment and share_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)
_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_
_Story and written by_
*Mareeyeart lawal*
Page twenty eight2️⃣8️⃣
Abun mamaki yaba shi, sai ya saki baki yana kallonta da d'unbin al'ajabi, shi ko a mafarki bazai yarda sameera zata iya yiwa doctor surayyah irin wannan danyen rashin mutumcin ba, kamar wadda aka shiga tsakanin su,, sai ya mik'e tsaye saboda abinda zai fad'a bame dad'in ji bane, "idan har ke idonki ya rufe bakya iya fahimtar komai bakya gane komai sai kanki, toh ni bazan goyi bayan wannan butulcin da zaki yiwa matar da ta taimake ki a lokacin da kika fi buk'atar taimako ba, ta maida ke mutum mudubin kallo ga kowa, har yaran ki ta maida su kamar y'ay'an cikinta, ba don kwad'ayin wani abu da Suka mallaka ko neman shiga ba ni zan je da kaina naba Ayman auren Nur ko kin amince ko baki amince ba,,,, in yaso ki janye tallafin da kike yi mana ni dasu gaba d'aya........". Yana gama maganar shi ya fuce ko jiran jin abinda zatace beyi ba
A parlour ya samu yaran cirko cirko, saiya shiga cikin su ya zauna, "k'unci abinci kuwa?". Girgiza mishi kai sukayi, shaheeda ta tambaya, "me yake damun mammie". Kallon yarinyar yayi da tausayawa yace, "bata jin dad'i amma tasha magani yanzu zata samu bacci kuje maza kuci abinci ku kwanta gobe kowacce a cikin ku tana da makaranta, shi haedar har yanzu bai dawo ba?".
Suka bashi amsa da, "ehh" "maza kuje kuci abincin ku Allah yayi muku albarka kunji". Ba musu suka ja hannun heedaya suka tafi suna tunanin da gaske mammie bata da lafiya ko kuwa dai abban su ya b'oye musu ne.
★★★★★★
Gidan surayyah kuwa